Showing 75001 words to 78000 words out of 218311 words
Chapter 26 - AJIYA A DUHU BOOK 2 By Billyn Abdull.txt
kake masa ba bazaka taɓa sanin yayin ba. Dan kawai ta juyo cike da neman magana murya a dashe ya ce, “Wash....”
Ai wash ɗin nasa ma bata gama fita ba ta juyo garesa, akan hannunsa da aka saka ruwan ta fara sauke idannunta, ganin komai lafiya lau ta maida kan fuskarsa, gira ɗaya ya ɗaga mata yana ɗan marairaice fuska. Fahimtar neman magana ce ta sakashi yin abinda yay ɗin sai ta dalla masa harara. Idanunsa ya ɗan lumshe ya sake buɗewa a kanta alamar lallashi. Baki ta tura masa cike da shagwaɓa. Sai shima yay kamar zai taɓe baki a yanayin murmushi amma ba murmushin bane. Barcine ke rinjayar idanunsa, tun yana kallonta ƙasa-ƙasa har barcin ya ɗaukesa.. Idanu kawai Maanal ta zuba masa cike da zurfafa a tunani. Dai-dai nan akace, “Hello Madam” a bayanta. Juyowa tai duk da batai tunanin da ita ake ba, a mamakinta sai taga ɗaya daga cikin mutanen jiya ne da suka tarbosu a airport. Kanta ta jinjina masa, ya ƙaraso wajen yana gaisheta da turancinsa mai wahalar fahimta saboda nauyi harshensa da yarensa ya cinye. Amsa masa tayi, kafin ta tambayesa yaya yasan suna anan ya fara mata bayani yaje hotel ne ake sanar masa. Cike da gamsuwa ta jinjina masa kanta. Ya jajanta mata rashin lafiyar sannan ya mika mata ƙyaƙyƙyawan farin mayafi na saƙa yana faɗin ta lulluɓama AA ɗin saboda akwai sanyi. Amsa tayi tai masa godiya, kafin a hankali ta yunƙura zata janye hannun AA dake cikin nata, idanunsa ya ɗan buɗe, cikin yanayin barci ya kalleta, itama dai kallon nasa take, Mr Li dake kallonsu sai ya shiga yimasa sannu. Luuuu ya ɗan kallesa, sai ya lumshe idon ya buɗe alamar amsawa. Da wannan damar Maanal ta miƙe ta lulluɓa masa mayafin tun daga ƙafafunsa har wajen wuyansa, hakan sai ya bama fuskokinsu kusanci sosai, ta ɗago da niyyar gyara masa mayafin daya ɗan haura zuwa lips ɗinsa suka haɗa ido. Yanda yake binta da kallon idanunsa a shanye da nauyin barci sai tsigar jikinta ta shiga tashi, jitai ta kasa janye wa, kallon juna suke da wani irin yanayi mai wahalar fassara, kafin a hankali ta janye jikinta baya, wajen zamanta ta koma tana fidda numfashi ɗai-ɗai daga ƙirjinta zuwa maƙoshi. Yayinda shi kuma ya maida nashi ya rufe ruf saboda barci da yaci ƙarfinsu. Shi dai Mr Li na kallonsu ta gefen ido cike da pretending ɗin ba kallon nasu yake ba. Ƴar bag ɗin hannunsa ta takarda kalar ruwan ƙasa ya miƙa mata, ganin taƙi amsa tana kallon jakan kawai sai yay mata bayanin coffee da milk tea ne a ciki.
Amsa tayi tai masa godiya. Ya sake miƙa mata iPad nan ma ya sanar mata ta AA ce, ta ajiye masa. Shi zai koma hotel ɗin domin kai sauran abokan tafiyarsu wani waje. Nan da awa ɗaya zai dawo, tunda yaga sai nan da awa ɗaya da rabi zasu sallame su zuwa biyu. Yay maganar yana nuna mata ƴar computer ɗin dake jikin ƙarfen ƙarin ruwan. Mamaki ya kama Maanal, a ranta tace tab da'a Nigeria ne maybe mara lafiyar ne ma zai sace na'urar koda bai san amfani ta ba. A fili kam sai ta jinjina masa kai kawai...
Zaman shirun ne ya ishi Maanal, dan haka ta ɗauka iPad ɗin ta duba, babu wani security a jiki, apps ɗin ta shiga dubawa tana neman games, babu ko ɗaya, dan haka sai kawai tai downloading a app store. Game ɗin ta fara bugawa tare da ɗaukar cup ɗin milk tea ɗin ta fara sha dan cikinta ya fara mata zafi. Ji tai batun azumi ya faɗo mata a rai, ko yanzu Nigeria sun ɗauka oho, dan bata san yanzu acan dare bane ko rana, anan dai tasan suma zuwa gobe zasu tashi da shi ne....
Kamar yanda Mr Li ya faɗa kuwa bayan awa ɗaya sai gashi ya dawo, bai wuce minti talatin ba kuma Nurse ɗin nan tazo ta cirema AA ruwa. Tare da sanarma Maanal Doctor nasan ganinta a office ɗinsa. Buɗe idanu AA yayi yana kallon Nurse ɗin, sai kuma ya maida kan Maanal, yanzu kam Alhmdllh sun rage mugun jan da sukayi, sai dai ɗan kumburowa irin na wanda yay barci. Kamar zatai kuka itama take kallonsa, sai batare da yayi magana ba ya jinjina mata kansa alamar taje. Miƙewa tai idanunta a kansa, shima dai kallonta yake har suka shige da Nurse ɗin. Basu sameshi a office ba, dan haka Nurse ɗin ta nunama Maanal wajen zama ta fita. Babu jimawa sai gashi ya shigo yana cire safar hannu alamar daga wani aikin yake, a abin shara ya jefa sannan ya zauna yana kallonta fuska da murmushi. Ita dai basarwa tayi, tare da jinjina masa kanta ciki-ciki ta ce, “Good morning”.
Amsawa yay shima da nashi turancin mai fita da harshensa, “Ajwaad Aliyu wife right?”.
Kanta ta jinjina masa. Shima ya jinjina nasan yana ɗaukar wani folder yana dubawa, fin mintuna biyu ya sake gyara zamansa, yanda ya maido gaba ɗaya hankalinsa a kanta sai ya sata nutsuwa itama.
“Mrs Ajwaad baƙya son mijinki ne?”.
Da mamaki ta kallesa yanzu kam sosai jin banzar maganarsa, sai kuma ta ɓata fuska taƙi magana. Shima sai yay murmushi yace, “Sorry! Nima ina da dalilin faɗar hakan. A yanayin da yake ciki nayi mamaki da akace min yana da aure harma yana tare da matar anan. Kin san mi yasa?”.
Kai ta girgiza masa.
Mijinki yana cikin wani hali sosai na buƙatar mace, a binciken da mukai masa ya jima a wannan takurar har takai yana sakashi suma ma idan abin yay tsanani, wannan babban haɗari ne ga namiji, dan yau da ace baku yi saurin zuwa asibiti ba zai iya shiga babbar matsala, kuma ko a yanzu matsalar bata kau ba a tare da shi gaba ɗaya, kawai dai mu mun bashi taimako ne ya ɗan dai-daitu”.
Da sauri ta sake kallosa idannunta na tara hawaye. Sai kuma ta maida kanta ta risinar.
“Karki damu zai samu lafiya, amma sai da taimakon ki. Dan babu abinda yake buƙata kuma zai taimakesa samun lafiya gaba ɗaya sai ke. Bama ta jikinsa kawai ba harda brain, dan a hanlin da yake yanzu yana fuskantar tsintar kansa a tashin hankali da damuwa (anxiety) saboda buƙatar ta yi masa yawa kuma bai samu wani taimako mai ƙyau na saukewa ba, hakan ya haifar masa da tashin hankali da rashin nutsuwa a brain ɗinsa dan ma na fahimci shi ɗin gentle men ne na haƙiƙa. Dan irinsu nada matuƙar ƙoƙari wajen kamewa akan abubuwa har sai kiga ma sun cutu wani bai sani ba. Dan matakin da yake ciki da mutum mai ƙarancin nutsuwa ne da tuni ya samu matsala babba. Amma kinga shi normal a zahiri ya iya riƙe damuwarsa shi kaɗai duk da yana fuskantar matsanancin ciwon mara da jin zafin fitsari (blue balls. epididymal hypertension), saurin fishi, koyaya akai masa abu ransa na ɓaci zuciyarsa na masa nauyi sosai sai ya ji damuwa da yawan bugun zuciya. Shiyyasa ma yake suma da gajiya saboda yawan tunani da damuwar. Yanzu abinda nake son ki fahimta ke kaɗai ce hope ɗinmu, kece zaki taimaka masa ta hanyar warware masa waɗan nan matsalolin idan ba haka ba zasu cigaba da girmama ta yanda matsalar da tafi hakan zata iya biyo baya. Dole ne ki dinga kwantar da hankalinki a duk sanda ya taɓaki, ki bashi haɗin kai batare da nuna firgita ko ruɗewa ba dan shigarki wannan yanayin zaisa ya ƙyaleki kuma shi matsala ne a garesa. Kasancewa da namiji ba mutuwa bace ko wata azaba mai girma. Wahalar kaɗance kuma ta lokaci ne kafin komai ya zama normal. Please ki taimaka masa zaki gode min wataran okay?”.
A hankali Maanal da kanta ke a ƙasa ta jinjina kai, dan wlhy wani irin ji take kamar ta nutse a cikin ƙasa. Shi dai mai jan kunne babu ruwansa a kwai buɗe aiki kai tsaye. Wai a haka ma dan da turanci yake gaya mata komai, da ace a hausance ne ai sai ta gudu saboda girmansu.........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖3️⃣7️⃣
______________
.........Tare da shi suka fito inda AA ke zaune har yanzu idanunsa a lumshe. Zama Maanal tayi kanta a ƙasa, shima doctor ya zauna a kujerar gefen AA daya ɗan buɗe ido yana kallon Maanal ɗin. Ya buƙaci Mr Li ya basu waje, dan zai yi ma AA magana ne da yaren da yasan Mr Li ɗin zai ji. Tsakanin likita da mara lafiya kuwa akwai babban sirri musamman irin wannan. Cike da kulawa Doctor ya kira sunan AA, a hankali ya janye idanunsa akan Maanal ya maida ga doctor. Murmushi ya masa, kafin cikin tausasawa ya fara magana da harshen Chaines da Maanal bata fahimtar komai, “Na tattauna da matarka, na kuma bata shawarwari, sai dai na fahimci a tare da ita akwai tsoro da kunya sosai. Ana samun irin wannan yanayin ga mata, musamman idan wani abu ya taɓa tsoratasu a baya mai kamanceceniya da hakan, da kuma haɗi da halittarsu ce kunya. Irinsu suna buƙatar a kasance da su cikin rashin da kulawa ba gaggawa ba, dan in har aka matsa zasu iya sumewa ma, ko jin tsanar namiji a kusa da su. Dan haka su a nasu tsarin ba'a zuwa musu kai tsaye da buƙata, ana binsu mataki-mataki ne, sannan ana basu lokacin sabawa da fahimtar dasu bawai tarayyar kawai akafi buƙata da su ba kai tsaye. Kai inda hali ma, a basu lokaci na hana zuwa garesu da tarayya sai romancing kawai. Idan aka bi wannan matakin zai cire mata damuwa da tsoron zuwa wancan matakin da take fargaba. Dan haka a yanzu matakin romancing, Hugging, nuna mata ma baka damu da abinda take gudun ba zai taima sosai. Yawan tausasa mata, kulawa, da tattalinta. Duk da nasan kai hakan zai sa ka cutu saboda a matakin da kake tarayyar kawai kafi buƙata, sai dai kaima hakan zai taimaka maka dan zuwa kai tsayen zai iya cutar da kai kuma ta wata fuskar. Zan baka waɗan nan maganin da in kaji rashin juriya sakamakon kusancin naku kasha zaka samu natsuwa har lokacin da zaka kai matakin daya kamata. Sannan ka ƙara ƙarfin motsa jiki da kake yi, ka rage cin abinci mai sugar da kitse, bada ƙarfi a ayyukanka fiye da shagaltuwa da kasancewar ku a waje guda ku kaɗai duk da dai na fahimci tuni kana bin waɗan nan matakan shiyyasa ka jima a cikin yanayin batare da ka cutu ba gaskiya. Dan da ace baka yin waɗan can abubuwan dolene ka samu matsala fiye da hakan, kai bama zaka iya riƙe ƙanka zuwa yanzu ba gaskiya. Ga card ɗina idan kana buƙatar wasu shawarwari zaka iya nema na. Nagode sosai”.
Kai AA ya jinjina masa tare da faɗin, “Thanks you doctor” ƙasa-ƙasa dan duk abinda ya faɗa masan shi ya jima da sanin a binsa. Dan tun lokacin da al'amarin ya fara neman fin ƙarfinsa ya fara karance-karance a addinance da kuma likitance akan hakan, saboda yama kansa alƙawarin komai tsahon shekaru zai jirata, idan ma bai sameta ba zai ƙarasa rayuwarsa a haka. A dalilin wannan yanayin ne ya fara workout na tashin hankali, ya kiyaye abincin da zaici, ya sake kusanta kansa da malamai domin neman ilimin addini, ya ƙara ƙarfafa ibadarsa, ya koma azumi irin na Annabin ALLAH. Ya kauda idanunsa ga duk wani abu daya shafi mata, kai yama haramtawa kansa kallonsu da suffar matan gaba ɗaya, ya maida kansa busy a neman nakansa, ya yawaita alkairi ga mutane. Hatta ita Maanal ɗin yana ƙin shige mata ne a yanzu saboda hakan, ko a wannan gaɓar kawai tana tsorata ne amma shi baya zuwa gareta dan yin abinda take ma tsoron, to amma ya fahimci tunda a yanzu doctor ya buɗe masa aiki a wajenta kawai zai zauna da ita ne ya mata bayani ta kalar yaren da zata sake fahimtar.....
Tunaninsa ne ya katse sakamako miƙewar doctor da zuwan Nurse ɗin nan wajen da ledan magungunansa. Amsa Maanal ɗin tayi, sannan sukai sallama da su dan Mr Li ma ya dawo. AA ya ɗan sake kallonta ya janye idanunsa, sannan ya fara ƙoƙarin janye mayafin data rufa masa, yana gama janyewa ya miƙama Mr Li, shi kuma ya waiwayo ya sake kallonta. Fiskarta a ɗan tsuke take, amma cike da kulawa murya can ƙasa ta ce, “Yaya jikin?”.
Idanunsa ya ɗan lumshe tare da buɗewa a kanta, sai kuma ya miƙa mata hannu alamar ta kama shi. Ajiyar zuciya ta ɗan sauke itama, duk da tasan ba lallai ta iya kama shin ba haka ta saka hannunta cikin nasa daya miƙo mata. Ita ta fara miƙewa, sannan shima ya yunƙura tana riƙe da shi ɗin ya miƙe. Cikinsa ya saki gaba ɗaya, sai dai kasala da nauyin jiki irin na mai ciwo da zama a waje ɗaya. Sallama suka sake ma Nurse ɗin nan dan tana a wajen har yanzu, kafin su fara takawa a hankali, Mr Li na gabansu suna biye har suka fito. Motar da akaje ɗaukarsu jiya a airport ta gani. Mr Li ya buɗe musu ƙofa, AA ta taimakawa ya fara shiga, kafin itama ta shiga. Ya rufe su ya zagaya mazaunin driver ya tada motar suka fice a asibitin.
AA dai tuni ya jingina da kujera ya lumshe idanunsa, sai dai hannunsa na riƙe dana Maanal yaƙi saki. Ita dai tana ɗan kallon waje ne da mutane dake ta kai kawai duk da rana ta ɗan ɗaga. Basu wani jima ba suka iso hotel ɗinsu, nan ma suna rike da hannun juna suka fito, Mr Li ya taimaka musu da kwasar ƴan tarkacensu zuwa ciki.
An gyara ɗakin nasu tsaf an canja bedsheet. Mr Li dama daga ƙofar ɗaki bai shigo ba ya juya, sai itace ta amshi kayan ta shigo da su ciki. A bakin gado AA ya zauna, ita kuma ta ajiye kayan data amso inda ya dace. Kafin ta kallesa murya a ƙasa ta ce, “Ko zaka fara yin wanka ne?”.
Idanunsa ya ɗan zuba mata, ganin tai saurin janye idanunta a kansa sai yay ajiyar zuciya. “Uhmm” kawai yace mata ya ɗauke nasa shima. Itama bayin ta nufa batare data sake kallonsa ba. Bata wani jima ba ta fito, kallo ɗaya ta masa ta ɗauke idanun ta dan ya cire jallabiyarsa daga shi sai boxer, muryarta har ɗan sarƙewa take wajen sanar masa ta haɗa. Shima sai baice komai ba ya miƙe ya nufi bayin. Itama kayan da zai saka ta fiddo masa, ta kuma fidda nata ta ajiye gefe. Fin mintuna ashirin sai gashi ya fito sanye da fara tas ɗin bathrobe. Baima gama zama ba ta ɗauki nata kayan ta wuce bayin, bata fito ba sai da ta shirya tsaf. Tako yi ƙyau cikin doguwar rigan, sai dai tana ɗan jin takura saboda yanda rigar ta wani lafe mata a jiki ta kuma fitar da shef ɗinta yanda ya kamata, duk da bata matse mata jiki bane, kawai taushin rigar da yanda aka fitar da ita da ainahin shef na mutum ya kawo hakan. Haka dai babu yanda zatai ta fito, sai dai ta saki mayafinta ya rufe mata ƙirji har ma zuwa cikinta. Bayan ne dai babu yanda ta iya. Fitowarta dai-dai ana knocking ƙofa, canta nufa, hakan ya bama AA damar ganin bayanta. Ai da saurinsa ya janye idanunsa a wajen maƙogwarinsa na wani irin kaiwa sama ya dawo ƙasa a cikin wuyansa. Maanal dai data buɗe ƙofa bataga kowa ba, sai ɗan abun nan na kawo abinci kawai a ƙofar. Ɗan juyowa tai ta kalla AA daya duƙar da kai yana danna iPad...
“Abinci ne?”.
Ta faɗa a taƙaice. Batare daya ɗago ya kalleta ba muryarsa a ƙasa kamar tatan ya ce, “Ni nai order”. Kanta kawai ta jinjina ta jawo ɗan keken ciki ta maida ƙofar ta rufe. A gaban gadon ta tsaida shi dai-dai inda yake. Ganin zata kai ƙasa ya kalleta, da ido yay mata nuni da gadon, tai ɗan jimm sai kuma ta miƙe ta koma ta wajen ƙafafunsa ta zauna.
“Ko dai zaka koma can kaci abincin ne?”. Tai maganar tana nuna inda kujerun suke. Wajen ya kalla shima, sai kuma ya maido idanunsa a kanta. Batare daya janye ba ya ce, “Naki ne ai”. Itama kallonsa tai da ƙyau, “Kai da zaka sha magani ya dace kaci, ni bama najin yunwa nasha tea a asibiti ma”.
Komai bai ce ba, sai ma ajiye iPad ɗin yay ya sauka a gadon, jan keken yay zuwa inda ta nuna, ya shiga fidda abincin yana jerawa a table ɗin wajen, sai da ya gama tsaf sannan, batare daya kalleta ba yace “oyaaa taso”. Ganin yanda yay da fuska batai musu ba