Showing 111001 words to 114000 words out of 218311 words

Chapter 38 - AJIYA A DUHU BOOK 2 By Billyn Abdull.txt

laifinsa ba dan aiki ne na asiri.....”
Caraf Saheeba ta amshe da faɗin, “Wlhy nafa asiri Mamy, kuma lokaci ne zai warware dan uban mutum sai ya wulaƙanta. Cikin ma waya sani ko a waje aka yayo aka manna masa”.
“Ke wulaƙanta ma kaɗai kike tunani Aunty. Wawuya jaka kawai ya kika gani yanzu. Yamin ɗaya an miki biyu, nan gaba ma ni ce zan miki ba Mamy ba karuwa kawai mai cikin shege”.
A mamakin su wani kalar murmushi Maanal tayi, sai kuma ta sauke hannunta daga saman fuskarta ta kalla Mamy. Murmushi ta sake sakar mata batare da tace komai ba ta miƙe abinta. Cike da wani irin takun ƙasaita da isa taje gaban su Saheeba ta tsaya. Manyan idannunta ta sauke akan Saheeba data saki baki da hanci da ido tana kallonta. Cike da wani irin salo Maanal ta ɗan ranƙwafa kanta tare da kallonta cikin ido. “Madam kar kiyi gaggawa, kin san ita zuru bata cin zuru sai dai a haɗu a zuru-zuru. Shi kuma cikin shege da kike faɗi, ai tare muka roroshi a waje da ubansa dan kin san shine kwarton nawa, ɗan soyayya kenan ba haɗin gambiza ba auren haɗin iyaye da tsiya-tsiya”. Sai ta wani kashe mata ido ɗaya, tare da sake sakar mata murmushi. Ta kuma miƙe a nutse ta juya ga Nuratu. “Ita ai uwa ce, dan ta mari wannan fuskar tamkar ta isa ne kodan darajar wanda ta haifa min. Babu kuma babbar wawuya jaka kamar ke da saurayin da kike kwaɗayi da burin aure ya ɗaga hannunsa a lokacin da yake rungume da matarsa a ƙirjinsa, a gaban ƙannensa, mamansa, abansa da yayunsa, Uncle ɗinsa, yayarki, ƴan aiki, ya sharara miki marin da har ki koma ga ALLAH sayinsa ya zauna raɗam a cikin zuciyarki ne ba akan fuskarki ba. Kinga ko KARUWAI kawai akema irin wannan wulaƙantawar.” itama ta kashe mata ido ɗaya tai gaba. Har ta wuce sai kuma ta dawo, duƙawa tai dai-dai saitin kunnen Nurry cike da raɗa ta furta, “Idan kikace zaki zuba wasa da ni tofa fuskarki ce zatai ta shan maruka wajen Mijina har sai kin fara ɓoyewa daga kallon mutane ke har ni ma uban ubanki zanci. Dan Ajwaad baya iya ɗagama wanda ya ko harareni ƙafa, ga assignment zan baki, ki ajiye a ranki Mijina nawa ne ni kaɗai dan bako wane nama yake iya ci ba, dan wani naman wurinsa yafi mushen jaki cika waje. Na barki lafiya mayyar mijina, ki kuma kiyayi haɗuwarmu dan waɗan nan marukan biyu sai na dawo dasu taki fuskar....”
Wani irin rawa jikin Nuratu keyi, a fusace ta wani irin yunƙurawa ta riƙo rigar Maanal, baya ta fisgota tana faɗin, “Kafin ki maido min su ɗin ni bari na ƙara miki da nawa dan ubanki”. Aiko a bazata Maanal na juyowa ta antaya ma fuskar Nuratu mari, ta sake ɗauketa da wani na biyu, zata ƙara na uku Saheeba ta zaburo, itama ɗaga hannu Maanal ɗin tai zata wanka mata marin, sai kuma mita tuna oho ta fasa tai murmushi kawai. Gira a sama ta ce, “Kinci darajar Babban Yaya”. Daga haka tai gaba abinta. Wani irin sake ƙoƙarin fisgota Nuratu da jikinta ke rawa tayi, kawai skirt ɗinta ya harɗeta sai gata a ƙasa wanwar. Wata banzar dariya Maanal dake ƙarasa ficewa ta saki. Mamy da Saheeba da sukai sumar zaune suna kallon Maanal suka zabura kan Nuratu a tare.......


Sosai wani irin zuciya ke cin Maanal, ta kuma hana kanta yin kukan dake taho mata. Ba marin bane kuma ya sakata kukan, ba kuma maganganun su Nuratu bane dan ko kaɗan basu mata zafi ba. Mamakin Mamy ne ke cizon zuciyarta da tausayin su AA da tausayin Oum. Kai dama family ɗin Darma gaba ɗaya. Yanda ALLAH ya bama mutanen nan haɗin kai da ƙaunar juna al'amarin Mamy ba ƙaramin girgizasu zai yi ba duk randa suka fahimta, ita kanta Mamyn tausayi take bata, dan tabbas in har aka kai ga wannan gaɓar ta tabbatar zatayi loosing, komai zata rasa, miji, ƴaƴan da take yaƙi a kansu, dama rayuwar farin cikin gaba ɗaya.....
“Ya rabb! Aunty Manaal miya samu fuskarki haka ne?”.
Firgigit Maanal ta dawo hanyyacinta, kallon Najma tai mai maganar, sai ta saki murmushi cike da basarwa ta ce, “Ba komai inaga barci da na ɗanyi ne a massalaci”.
Cike da rashin yarda Najma ta ce, “Barci ko mari, wannan mari ne Aunty. Waye ya mareki? Nuratu!”.
Murmushi Maanal tayi, zatai magana a bazata sukaji maganar RK dake faɗin, “Lafiya!?”. Duk juyowa sukayi, cike da damuwa Najma tace, “Aunty ce aka kira sashen Mamy, kaga ta fito fuskarta duk sayin mari”.
Kallon Maanal ɗin RK yayi, suna haɗa ido sai tai yunƙurin barin wajen. Cikin wata irin dakewar murya da Maanal bata taɓa sanin RK ɗin ya mallaka ba ya ce, “Maanal!”. Cak ta tsaya sai dai bata juyo ba. Takawa yay a hankali ya koma gabata, fuskar tata ya kalla da ƙyau, tabbas kuwa sayin mari ne. Sai kawai ya kauda kansa. Shiru na kusan sakan biyar kafin ya dawo da kallonsa kansu. Babu alamar wasa a tattare da shi ya juya ya bar wajen yana faɗin, “Ku biyo ni”. Ji Maanal tai kamar tace bazata je ba, amma sai ta kasa hakan, dan koba komai RK fa matsayin kawun su AA yake, ƙanen Oum ne uwa ɗaya uba ɗaya. Ƙanen Abah... Bama ta gama tunanin ba Najma taja hannunta suka bishi. Tacan bayan sashen baƙi sukaje. Ita Maanal ma bata taɓa sanin akwai wajen zama a wajen ba sai yau. Ya zauna suma ya nuna musu wajen zama. Zaman sukayi, batare da ya kallesu ba a yanzu ya furta, “Nuratu ce ta mareki?”.
Murmushin takaici kaɗan Maanal tayi, kafin itama cike da girmamawa ta ce, “Uncle wacece Nuratu da zan zauna ta dake ni”.
Kansa ya jinjina ya ce, “Saheeba ce?”.
Kai itama ta girgiza masa alamar a'a.......✍️








*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*


*09032345899*






*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
















*_💞AJIYA A DUHU....💞_*








*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*




*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_My TikTok account 👇_*


https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1


*_Instagram👇🏻_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_Arewabooks_*


Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


*_WhatsApp channel_*


https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R




_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_


*_BOOK 2_*
🅿️➖5️⃣5️⃣




______________




.........Maimakon sake tambayarta wani sai kawai ya kaɗa kai dan ya fahimci wadda yake hasashen ce. Kansa tsaye ya furta, “Kin san wani ɓoyayyen abu daya shafeta ne dama kafin yau?”.
Shiru Maanal tai ta kasa magana. Tsohon minti biyu bata da niyyar cewa komai. RK da yay mata kallo ɗaya ya ɗauke kansa ya ce, “Tsahon wane lokaci kika san ainahin ta?”.
Idanu ta ɗago ta kallesa, ganin babu alamar wani wasa a tare da shi a Uncle ɗinsa yake yasata maida kanta ta duƙar, hannunta na wasa da ɗayan hannun ta ce, “Uncle miye amfanin tone-tonen? Taci darajar wanda ya ajiyeta da waɗan da take tada jijiyar wuyan a kansu. Ni harga ALLAH bana buƙatar wani ka-ce-na-ce a kanta. Matsalata da damuwata ɗaya ce ta yanda zan bama Oum garkuwa da ga sharri da tuggunta ita da ahalinta. Amma dama kai kasan ita wacece tuni?”.
“Tabbas tun kusan shekara biyu da suka wuce wasu abubuwanta suka fara sakani a shakka. Sai dai akan auren ku na samu tabbacin da nake buƙata a baya gaba ɗaya hasashe ne kawai da zargi”.
“Saboda haka ka aikata abinda ya faru?”.
“Hakan da nai shine ya kamata. Maanal ki bar wani pretending, kina sonshi kamar yanda yake sonki. Soyayyar da AA ke miki bata wasan yara bace, dan na jima ban taɓa ganin soyayya irin wannan ba. Kuma har abada bazaki taɓa samun wanda zai soki kamar Ajwaad ba....”
Ɗagowa tai ta kallesa. Ɗauke kansa yay daga saitin su, ya haɗiye wani abu mai nauyi a cikin maƙoshinsa, yana kuma addu'ar UBANGIJI ya nisantashi da sheɗanin dake kissima masa shi a zuciya. Dan yayima ALLAH alƙawarin har abada bazai sake kallon Maanal da wata siffa ba bayan ta matar ɗan ɗan uwansa. Jinjina mata kai yayi da cigaba da faɗin, “Yes da gaske nake Maanal bazaki samu ba indai a ɓangaren soyayya ce irin ta namiji da mace dake a buri da bigiren zama ma'aurata. Kema kuma kin san haka, idan ma baki sani ba duk randa aka bashi ke zai tabbatar miki nayi imanin hakan. Dan tun farko ƙuruciya dama kece kike kallon tarayyarku matsayin abokai kawai wanda suka shaƙu, amma ga Ajwaad sam ba haka bane, tun asali tun fari sonki yake. Domin tabbatarwa kije da wannan ki karanta, karki bari ya gani dan bai san na ɗauka ba nima shiyyasa na naɗe bayan book ɗin da wannan takardan, zuwa anjima kibama Najma ta kawo min”.
Hannunta na ɗan rawa ta amsa, ƙaramin jotter ce an nannaɗe ta da farar takarda ta yanda ba'a ganin ainahin bangon.
RK daya ɗauke kansa daga kallonta ya cigaba da faɗin, “Kince kina son bama aunty garkuwa, tofa ta hanya ɗaya ce jal zamu iya yin hakan, amma duk sauran da zaki hanga ko hasashe ba masu yiwuwa bane ba, dan koba komai zamu kalla darajar masu daraja a kanta.”
Najma zatai magana dan ita duk sun rikitata RK yay mata alamar zipping, shirun kuwa tayi, tare da saka hannunta ta ma riƙe bakin. Maanal data fara jin nutsuwa da tattaunawar ta ce, “Wace hanya ce kenan?”.
“Yafewa Ajwaad, yimasa afuwa daga laifinsa. Duk da nasan abune mai wahala kuma mai ciwon gaske, amma idan aka tuna alkairin baya sai a yafe wannan a kallesa a matsayin kuskure da ajizanci na ɗan adam da kuma jarabawa. Ke da kanki a diary din da kika bani babu inda Ajwaad ya taɓa ko gwada aikata abinda ya aikata a gareki koda da wasa, mizaisa baza muyi tunanin wannan daya faru akwai wani abu a ƙas ba musamman idan muka kalla shan zoɓo kamar daga shi komai ya fara....”
Da wani irin mamaki Maanal ke kallon RK. Tace, “Zoɓo Uncle?”.
Cigaba yay da faɗin, “Yes dole akwai wani abu a cikin wannan zoɓon da kuka sha, kuma koma minene Ajwaad ya sanshi daga baya ɓoyewa kawai yake yi. Akwai dalilin kuma da yasa ya zaɓi yin AJIYA A DUHU. A yanzu bayan haɗuwarku, zuwa yanzu da kuke ma'aurata ya taɓa tada miki waccan maganar?”.
Kanta ta girgiza alamar a'a.
“Ya taɓa baki haƙuri koda a wata siga ne balle nuna shi mai laifi ne babba a gareki?”.
Nan ma ta girgiza kai.
“To wannan ya isa ya zame miki hujja babba. Amma kuma na miki uziri, dan wancan abun ya faru kina da ƙarancin shekaru, shiyasa baki taɓa zama kinyi nazarin komai a kansa ba, kawai dai kinyi jiyyar shock da kika shiga, sannan rabuwarku ta haddasa miki ciwon zuciyar da kika sha fama, sai kuma jin zafin abinda ya farun dan dole ne hakan ga kowacce mace da irin haka zai faru da ita....”
Da sauri nan ma ta kallesa. Ya ɗan ɗage kafaɗa ya ce, “Kar kiyi wani musu, shiyasa nace miki kina son AA kema har yanzu. Kin san kuwa ƙarfin da ciwon zuciyarki yayi Maanal? Kinfa je wani mataki ne da komai zai iya faruwa dake. Amma tunda Ajwaad ya dawo rayuwarki bayan farko-farko daya motsa ciwon ya ƙara motsa miki?”.
Gaba ɗaya ji Maanal tai kunya ta lulluɓeta. RK daya fahimta ya cigaba da faɗin, “Duk da nasan an ɗoraki a magani mai ƙyau da inganci da ace baki sake haɗuwa da Ajwaad ba a tsakanin tasirinsa kaɗan ne kuma zai zama na ɗan lokaci ne. Amma da yake zuciyar ta samu abinda take so yanzu gashi komai normal ba. Bawai ke kaɗai ba shi kansa AA ɗin ya shiga makamancin halin da kike cikin ne, koma fiye da naki dan sai da ya shiga wani mugun depression fa a shekarun baya da kowa ya fara ɗauka brain ɗinsa ya taɓu ne ma, amma tunda yau akace kin zama mallakinsa kinga ya sake yin wani any cuta data shafi hakan? Bazaiyi ba saboda zukatan sun kasance a tare sun kuma samu abinda suke so. Dan haka ina roƙonki, ina kuma baki shawarar ɗaura ɗamarar bama mijinki haɗin kan zama lafiya, ki kuma ajiye komai gefe ki bashi irin soyayyar da yake so. Wannan shine kawai dafin da zaita cizon matar can ya kuma faranta ran Aunty Dan a duniya aurenku ke da Ajwaad da haihuwar Fawzan ce kawai damuwar dana san tana damunta. Na biyu auren Najma da Fawzan waɗan nan biyun zasusa ta samu cikar burinta na tabbatar”.
A wani irin firgice Najma ta kalla RK. Ya harareta, sai tai ƙasa da kanta. Maanal da wani kalar farin ciki ya lulluɓe ta ce, “Uncle da gaske wai?”.
Ƴar dariya RK yayi da faɗin, “Da gaske kuwa. Munafukai suna ɓoyewa ne kawai. Amma ni ina son komai ya fito fili zuwa bayan salla a haɗa da bikinku ayi nasu. To in dai mukai ma matar can wannan dukan zai gigitata ne bana wasa ba. Hakan ne zai bama Aunty garkuwa daga tarkon da take son ɗana mata, dan burinta ai yanzu ta yanda zata ƙwace su Ajwaad ne a hannun Auntyn, bayan kuma ita da hannunta ta bata, tasan kuma aikata hakan zai iya kai rayuwar Aunty ƙarshe ta mutu ta bar mata mijin da ƴaƴan shiyyasa, babu kuma ta hanyar da zata iya hakan sai ta aura musu matan da take so, su kasance kuma daga ɓangarenta yanda ko Aunty ta rasa ranta taci nasara akan yaran suma kansu ta yanda basu isa bijire mata ba ta kowace fuska, ƙaryarta kuma tasha ƙarya, tunda tai wannan ƙyautar har gaban abada bazata koma a hannunta ba wlhy, kuma in sha ALLAHU Aunty da Yaya da yaran nan uku suna tare da juna sai dai ita ta fita a cikinsu”.
Cike da farin ciki Maanal ta ce, “In sha ALLAHU Uncle, ai zata sha mamaki dan wannan faɗan mu da ita ne Oum na barci abintama za'ayi sa”.
Dariya yayi, tare da faɗin, “Wato tana barci?”.
“Sosai ma kuwa. Ai yanda matar nan take ta yaƙar Oum ita kuma bama tasan tana yi ba ai AJIYA A DUHU kenan, babu faɗan daya kai wannan baƙin ciki, kaita zama cikin baƙin ciki da takaici mutum da shirya masa tuggu da mugunta shi kuma baima san kanayi ba kuma yana zagaye da farin cikin da baka ƙaunar ganinsa a ciki, ka kuma kasa cin nasara tako wace fuska wlhy AJIYA A DUHU kenan”.
Dariya sukayi yanzu kam har Najma, sai kuma Maanal ta rungume Najma dake ɓoye fuska. Ta shiga jero addu'ar ALLAH ya tabbatar da alkairi ita da Yaya F. RK na amsa mata da Amin. Ɗari bisa ɗari Maanal ta gamsu da bayaninsa. Kuma ita harga ALLAH dama zuwa yanzu ta huce koba duka ba akan jin zafin AA. Kuma tama ranta alƙawarin zata bashi dukkan haɗin kai na kulawa da soyayya bayan tarewarta kodan farin cikin Oum ta kuma baƙantawa Mamy, dan wlhy wannan marin datai mata tayima ALLAH alƙawarin sai ta ramashi a zuciyar Mamy da salon ban mamaki akan AA....
RK ya katseta da faɗin. “Kasancewarku ku biyu Aunty zata samu garkuwa masu tare mata faɗan, dan na fahimci so take itama tai amfani da waɗan nan ƴan iskan yaran da take ta aurama su Ajwaad ɗin wajen tare mata faɗa. Kunga kuma sai ki zuba da su idan tai tsami a tsakanin ku da su sai mu tafi plan c. Abu na ƙarshe kuma Maanal dole ne ki dawo Maanal ɗinki ta asali ta baya, wato ƴar rikici, sarkin takalar faɗa, mai kuma tsiwa. Ki ajiye wannan sanyin da miskilancin, ki kuma ajiye wannan shiru-shirun da noƙe-noƙe, kinyi karatu, kin shiga cikin mutane masu mabanbanta halayya, na tabbata kina sane da komai miskilanci ne kawai ya sa kike nuna kamar baki san komai ba. To dan ALLAH ayi haƙuri a dawo kamar da dan wannan abun da muke gani ƙarami wlhy ba ƙarami bane ba. Babban yaƙi ne, kuma ba'akan komai zai kasance ba sai na kwatar Yaya (Abah) da su Ajwaad. To idan su suna shirin yaƙin hakan, mu zamu shirya na bama Aunty Garkuwa ne kamar yanda kika faɗa, hakan kuma bazai muku daɗi ba sai kun yi fito na fito da waɗan shegun su Nuratun”.
Sosai sun gamsu da wannan bayani nashi, sai Maanal taji zuciyarta tai mata wani sakayau, duk wani ƙunci da nauyi ya tafi sai sauke ajiyar zuciya take. Sun sake tattaunawa sosai kafin shi ya fara tashi ya wuce, su kuma sai da suka tabbatar an tafi sallar azhar sannan suka fito a wajen dan yace baya buƙatar kowa ya fahimci komai.....

__________★


Sosai Nuratu ta fasa lips, goshinta kuwa yayi irin ƙullutun nan abin dariya. Yanda take kuka da rantsuwar sai ta kashe Maanal yau

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login