Showing 126001 words to 129000 words out of 218311 words

Chapter 43 - AJIYA A DUHU BOOK 2 By Billyn Abdull.txt

Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_My TikTok account 👇_*


https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1


*_Instagram👇🏻_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_Arewabooks_*


Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


*_WhatsApp channel_*


https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R




_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_


*_BOOK 2_*
🅿️➖6️⃣2️⃣




______________




........Babu wanda yay musu akan hakan, tunda dai agaban idon kowa komai ya dinga faruwa. AA sai wani munafukin murmushi yake a kaikaice. Mamy na lura da shi sai ko ta ƙara ƙulawa. Amma dai ta dake yanda kowa yay addu'a itama tayi. A zuciya kuwa kaf family ɗin Darma sai da ta tsine musu yau, a ganinta munafunci ne kawai. Da ƙyar ta iya riƙe kanta aka tashi a wannan zama. Ko ganin hanya batayi sosai ta nufi sashenta, tana shiga sai ga Maman Saheeba ta kirata. Kamar bazata ɗauka ba tadai daure ta ɗauka ɗin, ko sallamarta Maman Saheeba bata amsa ba a haukace ta fara magana wai yanzu Baban su Nuratu yazo ya sameta da batun Baba Sardauna ya sameshi ɗazun da yamma ita bata nan yace masa ayi haƙuri a ɗan basu lokaci akan bikin nan suna neman alfarma. Ita kanta Mamy gigicewa tayi dan taso ace ita zata zauna ta tsara ma su Maman Saheeba ɗin ashe mugun tsohon sai da ya fara zuwa can, da alama ma daga gidan nasu sukayo airport. Cikin son kwantar mata da hankali ta ce “Nana!”.
Ƙin amsawa tayi, ta cigaba da masifa, sai kan Mamy ya dinga wani irin sarawa na ciwo, ga masifar Maman Saheeba na haura mata har saman kan. Sai kawai jiri ya kwasheta ta zube a ƙasa. Sai Haule ce ta taimaka mata ta tashi da ƙyar, ta kamata domin takaita bedroom tace ta ƙyaleta. Haka ta taka zuwa bedroom ɗin nata da ƙyar ta kwanta. Wani irin ciwon kai kamar ana buga mata guduma na cikinta. Sai hawaye sharrr-sharrr. Waya ta jawo da ƙyar tai kiran baban su Nuratu. Bugu ɗaya kuwa ya amsa. Cike da girmamawar da yake bata ya shiga gaisheta. Ta amsa cikin sanyin murya tana tambayarsa miya faru? Yaya sukai da Baba Sardauna.
Sai da ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce, “Aunty, Alhaji Sardauna magana yay min ta fahimta kuma ta gamsuwa. Kawai ƴar uwarki taso tada hankalinta ne da naki. Ya tabbatar min tunda Nuratu tazo gidan nan naku take jan rikici tsakaninta da ita matar Ajwaad, shiyasa suka ga za'a iya samun matsala ace an haɗasu a muhalli guda. Tun rikicin na iyakar su biyu zai koma ya taɓa zuminci ne tunda yau da gobe sai ALLAH. Shiyyasa shi Ajwaad ya nema alfarmar a bashi lokaci zai mata gini sai ya sakata a ciki, idan kuma tafi son nan gidan sai ita matarsa ta koma can ita Nuratu ta zauna nan kusa da ke. Dan ALLAH ina wuyarta ga daɗinta a wannan shawarar? In ce sauƙi ma aka samawa kowa. Amma ta yada hankalinta gata can harda yanke jiki ta faɗi sai da aka saka mata ƙarin ruwa. Ko saurarena na gama mata bayani ma batai ba fa ta hau bori tai kiranki”.
Ajiyar zuciya Mamy ta sauke. Sai kuma a hankali tace, “Shikenan ka bari zan shigo Kanon gobe da safe.”
Cikin jin daɗi yace, “ALLAH ya kaimu aunty sai kinzo”.
Mamy na yanke kiran tai lamo, sosai take fassara maganganun baban su Saheeba ɗin dalla-dalla. Wani sashen na zuciyarta najin gamsuwa da zancen, wani ɓangare kuma na nuna mata yaudara ce kawai, ba kowa ya shiryata ba kuma sai Oum. Ko kuma ta kitsama Ajwaad ya faɗama Baba Sardauna, in ba haka ba ta ina Baban yasan wani anyi rikici da azumi? Koda yake akwai munafukan yaran nan ƴan hutu, suma zasu iya fa. Dan ita bata san AA yaje Kano kwana biyar da suka wuce ba. Kawai dai tasan yayi tafiya, amma bata san ina yaje ba. Sosai zuciya ke tunzurata akan taje ta samu Oum, amma wata na kwaɓarta akan ta fara bari Ajwaad ya dawo ta fara tuhumarsa sannan. Wani gefe na nuna mata ba lokacin fito-na-gito bane yanzu. Ta bari sai ƴaƴanta sun gama dawowa tafin hannunta ta hanyar auren zaɓinta gaba ɗaya tukunna. Dan haka ta cigaba da lallaɓawa ai auren nan na Nuratu da Ajwaad, shima Fawzan ya auri Amani dan yarinyar kullum sake shige mata zuciya take, kullum sai ta kirata a waya sun gaisa. Ganin haka bata taɓa tuhumarta batun Fawzan na kiranta ba, ita kuma Amani batai mata maganar ba itama. Shi ko Fawzan dan karma Mamy tai masa maganar Amani a tsaitsaye yake shigowa gaisheta da safe, idan ya dawo aiki kuwa sai gab da magriba shaf-shaf yazo ya fice. Ganin kuma bai sake cewa komai ba sai ta ɗauka yana kan lallaɓa Amani ɗin ne su daidaita. Taso yaje da sallar nan amma sai Maman Saheeba tace ta bishi a hankali, wataran ma bata sani ba zai je wajen Amani ɗin tunda har ya yarda suke waya..


_________★


Sosai akema Maanal gyara na fitar hayyaci, ciki da wajenta ga wani uban ƙamshi na bala'i a dukkan motsinta. Fatan ta kuwa wani irin santsi da take da walƙiya abin ba'a magana. Ita kanta ji take a jikinta komai ya canja. Hatta gashinta, ƙafafunta da tafukan hannunta gyara Hajiya Shuwa ke musu na balan bala'i. Kai Hajiya Shuwa tasan sirrin gyaran mace na bala'i ƙwarai da gaske. Dan hatta baki da lips ba'a bari ba. Ga wasu manyan lectures na zaman aure da take buɗema Maanal ɓaro-ɓaro. Idan ta nuna jin kunya ta mata daƙuwa da faɗin.
“Kaniyarki, ba batun kunya muke ba anan, ki nutsu ki fahimci komai nake so. Kina dai ganin gogaggiyar yarinyar da ake so a aura masa mai ido a tsakiyar goshi. Mijinki ba ƙaramin mutum bane ba, sannan yana masifar sonki. Haƙurin da yay na shekaru karma kiyi zaton zai raga miki. Sannan yana zaga duniya yana gamo da mata kala-kala baki sani mugun halin wata ba, wasu matan da shirinsu suke kasancewa akan ƙwace miji wlhy. Mu kammu munsha wannan gwagwarmayar a lokacin ma duniya na barci balle yanzu da idonta ke a buɗe ƙyar”.
Ire-iren irin wannan nasihar ke sanyaya jikin Maanal ƙwarai da gaske. Sai ta ƙara nutsuwa tana ɗaukar komai yanda ya kamata. Wani gefe na zuciyarta kuma najin kewar su Oum da su Ammie. Dan kowa ma Hajiya Shuwa ta hanata waya, acewarta so take ta bata hankalinta gaba ɗaya. Aiko ta bata ɗin, dan Maanal ɗin a kallo ɗaya zaka fahimci makarantar Hajiya Shuwa ba tasiri a gareta yanda ya kamata....


Ata ɓangaren Oum kuwa shirin biki suke mai ban mamaki, dan sai ka ɗauka ma sai yanzu ne za'a ɗaura auren. Ta ƙarƙashin ƙasa kuwa Abah da AA da RK da Babban Yaya na shirya na Yaya Fawzan, dan an gama komai amma su kaɗai maza suka san da auren ko su Oum basu sani ba. Ita kanta Hajiya Majdiya Baban su Najma kawai ya sameta cewar zaima Najma aure. Da farko rikicewa tayi, amma da ya zauna ta mata nasiha da tabbatar mata zatai farin ciki daga baya sai ta kwantar da hankalinta, dan tasan bazai cutar da ƴarsa ba, kuma yana da dalilin ɓoye matan. Za'a ɗaura aure ne kawai biki sai Najma ta gama jarabawarta da take shirin farawa nan da sati ɗaya. Dan haka su idan za'a kaita su zasuyi nasu bikin. Kuma hatta shi Fawzan ɗin bai san da wannan batu ba, dan AA da RK sun gama shirya komai da komai har gayyatar abokansa....


Mamy ma taje Kano, sai dai aranar ta dawo. Da alama kuma ta ciwo nasarar sasantawa da Maman Saheeba. Sai dai Nuratu babu lafiya wai tana ma asibiti an kwantar da ita. Dan tunda batun ɗaga bikin nata ya shiga kunnenta ta yanke jiki ta faɗi, tun kwana biyu da salla ta koma gida dan yin shiri biki dama. Baiwar ALLAH Oum, tana ji ta tasa ƴan hutunta gaba da bazasu koma ba sai anyi biki sukaje suka duba Nuratun. A can suka sami Mamy da Saheeba dan tunda rana suka tafi su. A mazan dai su Babban Yaya babu wanda yaje, shi AA ma baya nan yana Lagos, ya kuma ce bazai dawo ba sai ana saura kwana ɗaya....


________★


Hakan kuwa ce ta kasance, ranar Alhamis ya dawo, a kuma ranar baƙin abokansa da bai san da zuwansu ba suka fara isowa. RK da Yaya Fawzan sun riga sun tanadar musu masauki. Anan ma gida tuni ƴan Kano sun fara isowa, zuwa yamma sai ga tawagar su Nene da sauran tarkacan Maanal, harda motocinta na lefe, sai kayan kawai aka sauke anan su a gidan Shahidah suka sauka. Dan itama Maanal can gidan Hajiya Shuwa ke shirin maidata.
Ya subahannallah, kunga Maanal kuwa, tayi ƙyau harta gaji, ga ƙunshi ja da baƙi an zuba mata. Gashi yasha wanki duk da itama tasha kuka a wajen gyaransa. Ƙamshi ba'a magana ko kana nesa da ita ta gitta sai ka jishi. Bayan sallar zuhur Hajiya Shuwa da Ameerah suka kaita gidan Shahidah. Tuni ta faɗa jikin Nene tana murna, yaran kuwa suka zagayeta kowa na farin cikin ganin Mie-mie kamar yanda suke kiranta. Nene sai latsa jikin Maanal take tana santi. Su kansu su Amaal bakinsu ya kasa yin shiru. Dan gaskiya Maanal ta gyaru sai Masha ALLAH. Jin Ammie bazata zo ba Maanal ta samusu shagwaɓa, ta kira Ammien tana kuka. Lallashinta tayi da tabbatar mata nan da sati biyu zatazo in sha ALLAHU. Da ƙyar-da-ƙyar Maanal ta haƙura. Ranar kam ansha hirar yaushe gamo, dan su Maanal suna son junansu sosai.


Washe gari juma'a Mothers event, na rana ne ƙarfe uku za'a fara. Kusan sha biyu sai ga su Aneesa sun iso daga Kaduna. Sosai Maanal tayi farin ciki, dan ba wasu ƙawaye tare da ita sai jikokin Nene da suma sai yau suka iso daga Kaduna ɗin. Isowarsu babu jimawa Najma da Maimoon, Batool, Lailah suka zo, suma sunce gara su dawo nan kusa da amarya cikin ƙawaye. Tare suke da akwatin kayan da zatai amfani da su. Kuma Uncle RK da AA ne suka saukesu. Sai da Maanal taji ranta ya sosu ganin AA koma ya nemeta, ba komai zata rama. Kamar wasa sai ga su Amraah suma sun iso, ashe Daddy ne ya tarkatosu kaf yace dole suzo ayi bikin da su.
Ba ƙaramin girgiza sukatan su Nasiba yayi da ganin gidan Shahidah ba, dan ba taɓa zuwa sukayi ba har Amaal ma dake a cikin Kaduna basu taɓa zuwa gidanta ba. Su Shahidah kam tarba sukai musu ta mutuntawa, dan ko'a fuska basu nuna musu komai ba. Lokacin da suka iso ma har an fara shirya amarya, kowa kuma nata ƙoƙarin shiryawa sai kawai suma suka shiga ayari........✍️




To lokacin shoshalewa yayi, kowa sai ya tsuke ƙugu dan dole ne muyi rawar a ƙame ƙam🥱🤣🤣🤣🏃








*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*


*09032345899*






*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
















*_💞AJIYA A DUHU....💞_*








*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*




*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_My TikTok account 👇_*


https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1


*_Instagram👇🏻_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_Arewabooks_*


Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


*_WhatsApp channel_*


https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R




_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_


*_BOOK 2_*
🅿️➖6️⃣3️⃣




______________




.......Gaba ɗaya AA mamakin ganin sabon bikin da suka shirya yake yi, dan Oum kanta da su Hajiya Majdiya ko lokacin kansu basu da. Shima sai abun ya fara sakashi nishaɗi da jin karsashin ango fa yake sabo fil-fil a leda, dama a wancan karon bai gayyaci kowa ba saboda bai kawo Bestyn tasa ce zata zama matarsa tasa ba, shiyyasa ya sallama komai babu wani shiri da yayi.. Al'amarin Oum ɗin tashi da ƴan uwansa bai gama girmar kansa ba sai da Fawzan ya kaisa masaukin da suka tanadarma abokan nashi, yaje ya sameshi harma da wanda baiyi zaton gani ba. Aifa nan suka tasashi gaba da mitar rashin sanar musu auren nasa, dan sai da suka iso suke jin ai an rigada an ɗaura sure tun kafin salla. Bashi da bakin bayani sai kawai ya bar Yaya Fawzan da musu sharhi...


________★


A can gidan Didi Shahidah kuwa wani shegen kwalliya mai natsuwa akema Maanal, komai dai-dai misali ba'a cika shi da shirme ba. Dan mai kwalliyar ƙwararriya ce tun daga Lagos Hajiya Shuwa ta ɗakkota dan komai daya shafi amarya itace keyi. Hatta kayan da Manaal zata saka duk shirin Hajiya Shuwa ne. Matar ta gogu da sanin takan duniya ne ƙwarai da gaske. Ƙarfe biyu da arba'in an gama shirya amarya Manaal cikin doguwar riga na lass daya tsaru da ɗinki matuƙa. Fitet rigace a ciki har ƙasa ta wani irin fidda ainahin surarta tamkar zane a takarda, sai akai wata a sama tamkar after dress sai dai itama da lass ɗin akayita ta sauka har tana jan ƙasa. Matuƙar zaunuwa ɗaurin kan Maanal ya zauna. Sarƙa ƴan kunne zuwa bangles kam ba'a magana. Dan dan ƙareriyar sarƙa ce da akama ma wani irin adon fararen stones ya rabba. Dole ka kalla wannan amaryar ka sake kallo dan takai zama abin kallon. To dama Maanal gidan gayu ce, balle yau ɗin ta dabance a gareta. Ita kanta sai take jin kamar ba ita ba. Lokacin da mai kwalliya da Hajiya Shuwa data iso suke fito da ita falo sumar zaune su Basira sukayi, su Zeezah kuwa suka shiga faɗin, “Woowww!!“ Suna miƙewa. Kafin kace mi hasken camara ya fara hasketa tako ina.
Dai-dai nan motar ɗaukar Maanal ke isowa, dan yau ba ango ne zaizo ɗaukarta ba. Babban Yaya da kansa ne yazo ɗaukar ƙanwarsa, a tare dashi akwai Uncle Najeeb (ƙanen Abah da suke uwa ɗaya uba ɗaya kun dai gane wanda akai bikinsu da su AA).
Sai da kowa ya gama fita suka shiga motocin dake can waje suna jiransu dan Babban Yaya ne kawai ya shigo ciki sannan Amaal da Hajiya Shuwa suka fita da Maanal. Babban Yaya dake murmushi ya ce, “ALLAH na gode maka, yau ga Lilly ta fito a amryar ta, amaryar ma ta Auta”.
Dariya Amaal da Hajiya Shuwa sukayi, Uncle Najeeb ma ya murmusa dan shima dai gwanin tsare gida ne. Kan Maanal da idonta ya cika da hawaye a ƙasa ta rissina ta gaishesu. Kafin Amaal ta sanyata a motar. Amaal ce kawai ta zauna tare da ita, Hajiya Shuwa motarta ta shiga sai ta ɗauka su Nene.
Masha ALLAH waje kam ya haɗu, dan ko makaho ya laluma yasan an gyara wajen. Ga ƙaton symbol da ke rubuce da sunan AA dana Maanal ɗin, yayi ko masifar ƙyau duk da babu hoto a jiki dan Alaj AA ya hana. Abinka da manya komai yana tafiya cikin natsuwa da tsari, dan sai da mutane duk suka shiga sannan Oum ta fito ita da Hajiya Majdiya cikin kwalliya domin shiga da amarya. Ango dai ba yanzu ba kamar yanda aka tsara.
Wani irin rungume Maanal Oum tayi, jitake kamar yau ne aka ɗakkota daga KD aka kawo musu. Ga madarar ƙyau da Maanal ɗin tai mata. Hajiya Majdiya dake murmushi ta shiga haska musu camara. Kafin itama ta rungume Maanal ɗin.
Ashe daga wajen hall ɗin wasan yara ne. Sai ka shiga daga ciki zaka tabbatar da eh an shirya bikin ƴar gata. Mata ne zalla a cikin hall ɗin, ƴammata da manyan iyaye da sukafi kowa yawa. Yara ma ɗai-ɗai ne a wajen. Tunda mc ya fara zubama amarya kirari hall ɗin yay tsitt, kowa ya zubama ƙofa ido musamman ta ɓangaren Darma Family da dangin Mamy, dan daga ƙarshe dai sun ajiye komai a gefe acewarsu sai an gama biki suma sun shigo tawagar dan suna son komai ayi akan idonsu ta yanda idan na Nuratun ya tashi ba'ayiba su sami nayi ƙorafi. Hajiya Majdiya ce ta fara shigowa, bayan kusan minti ɗaya ƙofar ta sake zuge kanta Oum da Maanal suka bayyana. Oum na riƙe da hannun Maanal ɗin. Tuni hall ɗin ya ɗauka ƙananun ƙunƙuni na ambaton Masha ALLAH dan harga ALLAH ko maƙiyi yasan Manaal tayi ƙyau sosai. Mamy kam da ƴan uwanta babu wanda bai ji abu ya sokar masa ƙahon zuciya ba.
Oum ta zaunar da Maanal a kujerar da aka tanada domin ita, ta ɗan gyagygyara mata rigarta kafin tai shirin barin wajen. Hannunta Maanal ta riƙo cike da shagwaɓa, Oum ta juyo tana kallonta. Sai kuma ta dawo ta riƙe hannunta cike da kulawa tace, “Miya faru?”.
Idon Maanal cike da hawaye ta ce, “Oum dan ALLAH ki zauna tare da ni anan, ko Didi ta dawo, bana son kowa na kallona”.
Murmushi Oum tayi sosai, tare da kai hannu ta ɗaukema Manaal ɗin ƴan hawayen da suka taru mata a gefen ido. “Yau ranar farin ciki ce Baby na ba ranar kuka ba, ki yi haƙuri yanzu Auta zai iso shima bake kaɗai zaki zauna ba ai. Kin taɓa ganin amarya ta zauna da mamanta ai sai a mana dariya ace ango yaƙi zuwa”.
Yanda Oum ɗin ta faɗa sai ya bama Maanal dariya. Murmushi ta saki mai sanyi daya wani mata ƙyau. Oum ma sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login