Showing 27001 words to 30000 words out of 218311 words
Chapter 10 - AJIYA A DUHU BOOK 2 By Billyn Abdull.txt
fito daga elevator tana danna waya fuskarta da murmushi dan kuwa charting take da su Aneesa. Dai-dai ta danna zata ma Zeezah vn aka zare wayar a hannunta, da sauri ta ɗago idanunta, sai ko cikin na AA dake kallon wayar alamar karanta charting ɗin yake. Hannu takai zata amshe wayar, ya janye jikinsa batare daya daina karanta hirar tasu ba.
Kamar zata saki kuka ta ce, “Amma dai haka babu ƙyau ALLAH”.
Bai tanka mata ba bai kuma daina karantawar ba, sai ma fara tafiya da yayi, binsa tayi tana jinta duk a ruɗe, dan tsokanarta su Aneesan keyi a kansa. Acewarsu har an gama cin amarcin ne ta dawo aiki. Amasar data tura musu cewar (Ai ba sai an gama a gida ba zasu cigaba da ci a office) yasa suka tasata gaba da shaƙiyanci irin na ƙawaye. Itako tana bama kowa amsa dai-dai shi. Dan tafi sakewa tai musu surutu a charting fiye da zahiri. Son amsar wayar yasa Maanal bata ankara ba har sun shigo office ɗinsa. Sai da yakai zaune a rukunin kujerun ta ƙara kai hannu zata fige wayar batare daya daina abinda yake ba ya saka mata ƙafa ta faɗo jikinsa sannan. Da sauri ta kalla inda take, aiko dai a cinyarsa take ɗare-ɗare babu ƙarya. Miƙewa tai yunƙurin yi, yasa hannunsa ya sake rungumota da ƙyau, tare da saka idanunsa cikin tsakkiyar nata da wani salon ɗage gira sama.
“Bake kika ce za'aci amarcin a office ba! Miye na pretending kuma amarsu ta ango?”. Yanda yay maganar kamar mai raɗa ya saka tsigar jikinta tashi, ga kunya na neman halakata tamkar ba tana tare da Bestyn ta dake goyata a bayansa ba ko bayan kekensa, wanda suke cin abinci a kwano ɗaya. Wanda yasha yimata wanka da mata tsarki, wanda yasha wanke mata underwears harda masu jini a jiki batare da ƙyanƙyami ba. Wanda y.....”
Knocking ƙofar da akai ne ya katse mata tunani, bama tasan ta daka tsalle ta miƙe daga jikin nasa ba gaba ɗaya. Bai hanata ba, amma ya kamo hannunta ya zaunar a gefensa gab, kafin ya danna remote ƙofar ta buɗe a hankali ta hanyar rabewa biyu. Kallo ɗaya AS yay musu ya duƙar da kansa. A haka ya ƙaraso gabansu ya ajiye basket ɗin hannunsa yana faɗin, “Sir gashi in ji driver”. Bai jira amsarsa ba ya juya ya fice, ƙofar ta koma a hankali ta rufe kanta. Ajiyar zuciya Maanal da kanta ke ƙasa ta saki. Kallonta yayi, ganin ta kauda kai gefe ya ɗan laɓe baki, sai kuma ya gyara zama ya fara fiddo kulolin da ke cikin basket ɗin wanda babu tantama yasan na gidansu ne, kuma tabbas daga Oum suke. Sai da ya gama buɗe komai ƙamshin abincin ya bulale office ɗin sannan ya juya yana kallon Maanal dake satar kallon sa shi da abincin ta gefen ido.
“Mrs Darma aikin kine wannan! Tashi ki bani abinci”.
Kallonsa ta juyo tayi, ya ɗage mata gira ɗaya. Cike da neman magana ya furta, “Kin san dai anan babu Aban naki ai balle kice bazaki yi ba”.
Sosai ta tura baki gaba. Batare da tace komai ba ta matsa kaɗan bakin kujerar ta ɗauka plate ta fara haɗa masa abincin. Idanu kawai ya zuba mata, ransa fes da kasancewarsu a hakan. Sai yanayin ke tuna masa wani lokaci acan baya daya shuɗe. Murmushi ne ya shiga ƙawata fuskarsa dan tamkar a yanzu ne komai ke faruwa. Harta kammala bai farga ba, sai da ta ɗan bubbuga spoon a plate ɗin sannan. Cike da basarwa ya haɗiye murmushinsa, batare daya ce komai ba ya gyara zama abinsa ya hau cin abincin bayan ya ɗauka wani spoon ɗin ya ƙara alamar nata.
“Nifa na ƙoshi”.
“Ɗura kike so kenan? Garama kici da arziƙi”.
Tasan zai aikata kuwa. Dan haka ta ɗauka spoon ɗin kawai itama. Jujjuya abincin kawai take amma ta gagara kai lauma ko ɗaya, baice mata komai ba, face ɗibowa ya nufi bakinta da shi. Yanda yay wani kicin-kicin da fuska babu alamar wasa yasa ta amsa ɗin.
“Gulmammiya dama abinda kike so kenan”. Ya faɗa yana dungure mata kai tamkar ba shine yay maganar ba.
Ita sai abin ma ya bata dariya, amma bata dara ɗin ba ta dai yi murmushi dan ya tuna mata baya. Idan ya lallaɓata taƙi cin abinci musamman in tana fushi da shi sai ya ɗiba ya bata a baki tare da dungure mata kai sannan yace mata gulmammiya. Murmushin nata ba ƙaramin ɗaukar hankalinsa yay ba, amma yasan yana yin magana zata birkice masa, dan haka yay shiru ya cigaba da cin abinsa yana ɗiba yana bata kuma. A mamakinsu sai gashi su ci sosai abinsu. Sun kammala kenan tana gyara wajen kiran waya ya shigo masa, AS ne ya sanar masa ma'aikata fa sun taru domin masa murnar aure. Amsa ya basa da cewar suna zuwa. Daga haka ya yanke kiran.
“Oya let's go mutane na jiranmu”.
Da mamaki Maanal ta bishi da kallo dan ya nufi inda rigar suit ɗinsa take, “Wai mi?”. Ta faɗa cikin sigar tambaya.
Batare daya kalleta ba yace, “Zasu tayamu murnar aure ne”.
Kasa sake cemasa komai tayi, ta ƙarasa tattare komai kawai ta maida a basket ɗin sannan ta miƙe, veil ɗinta ta gyagygyara tare da ɗaukar wayarta a inda ya ajiye sannan ta nufi ƙofa inda yake tsaye yana jiranta.........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. 🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣4️⃣
______________
.........HUZNAH
Sosai gaɓɓan jikinta ke mata ciwo, duk yanda take tunanin iya daurewa hakan ya gagara. Kuka kam taci harta godema UBANGIJI. Zagi babu kalar wanda Sageer bai sha ba a wajenta. Gashi bata sake jin motsinsa ba a gidan sai bayan magrib. Tana zaune wujiga-wujiga har yanzu bata gyara jikinta balle sauke nauyin sallolon dake a kanta ya shigo ɗakin. Kallo ɗaya yay mata ya ɗauke kansa, batare da damuwa da hararar da take binsa da shi ba ya wuce bathroom ɗin ɗakin. Ruwa mai ɗumi ya tanada sannan ya fito, batare da Huznah data cusa kanta a ƙafafunta tana sabon kuka na takaicin ganinsa ta ankara ba taji kawai an cicciɓeta. Mutsu-mutsu ta farayi na son sauka, amma da yake ƙarfi ba ɗaya ba ko gezau ya shige bayin da ita. Tana kai masa duka da komai da fisge-fisge ya taimaka mata. Sai da ya tabbatar ruwan ya ratsa mata jiki ta samu ƴar nutsuwar da yake buƙatar ganinta a ciki sannan ya fito a binsa muryarsa babu alamar wasa ya bata umarnin yin wanka tare da gargaɗinta mintuna biyar ya bata tazo tai sallolin data tarama kanta. Idan kuma ba hakaba zata sha mamaki.
Haka kawai taji wata masifaffiyar shakkarsa, babu ɓata lokaci ta gabatar da duk abinda ya sanyata ta fito tana ɗingisa ƙafa ɗaure da towel. Duk da ta bashi dariya da tausayi duk sai ya danne, fuskarsa babu fara'a ya miƙa mata riga da hijjab, komai batace ba ta ɗauka ta sanya ta fara gabatar da salla. Sai da yaga har tayi raka'a biyun farko sannan ya fita domin zuwa massallaci shima......
______★
Ƙarfe biyar Abah ya kirata yace ta fito su wuce. Lokacin tashi yayi, amma akwai aikin da take yi, sai dai bazata iya cema Aban haka ba, sai kawai ta tattara aikin da abinda duk zata buƙata ta tafi da su bayan ta kashe wutar office ɗin ta fice. Kai tsaye inda AS ya nuna mata zata dinga ajiye key dan masu shara da safe su gani ta ajiye. Batare da tabi takan AA ba ta fice abinta ta samu su Abah. Cike da girmamawa ta gaisheshi sannan ta shiga driver ya maida ƙofar da dama shine ya buɗe mata ya rufe. Fuskar Abah da murmushi ya danƙa mata tsarabar da yayo mata, dan shi fa har yanzu kallonta yake tamkar su Naufal a gabansa. Cike da jin daɗi tai godiya ranta fal farin ciki...
Sam AA bai san da tafiyar Maanal ba. Aiki ya masa yawa harya shiga over time ɗin nasa na tsiya. Kiran magrib ya sashi kallon ƙawataccen agogon dake a office ɗin. Ɗan tsai yay cikin tunanin Maanal data faɗo masa a rai. Sai kuma ya ɗauka waya yay kiran AS dan yasan tunda bai shigo masa sallama ba shima yana nan bai wuce ba. Ilai kuwa hakanne. Yana ɗauka daga can AA ɗin ya furta, “Zo mana”. Ya yanke kiran. Babu jimawa sosai AS ya shigo, sai da ya masa sannu da aiki kafin yace, “Gani sir”.
Batare da AA ya ɗago daga abinda yake ba ya ce, “Besty fa?”.
Sam AS bai gane kan zancen ba, dan haka ya ce, “Sir Besty kuma?”.
Karan farko AA ya ɗago ido ya kallesa, sai kuma ya dafe goshi ya ɗan murza. Cike da basar da suɓutar bakin nasa ya furta, “Maanal”.
“Oh I'm sorry Sir, ai inaga tun five ta tashi”.
Jimmm AA ɗin yayi, sai kuma ya jinjina kansa batare da ya sake cewa komai ba yay masa nuni yaje. AS na gama fita AA yaja numfashi ya fesar, sai dai a zahiri baice komai ba. Saima miƙewa da yay ya nufi bedroom yay alwala. Koda ya fito tattara dukkan abinda zai buƙata yay a cikin briefcase ɗinsa, dan dolensa yay aiki a gida kam daren yau. Yana fitowa AS ya amshi kayan hannun nasa ya haɗa da nashi shima, a tare suka sauka ƙasa. Sai da suka fara salla a massallaci su ƴan tsiraru dan akwai irinsa ƴan over time sannan suka nufi gida shi da drivern sa, AS ma tashi motar ya shiga ya nufi nasu gidan.....
Lokacin da AA ya isa gida tuni Maanal ta jima da hutawa. Dan har taya Oum girki tayi kasancewar rigimar Abah ta tilasta mata komawa kan duty. Bayan sun kammala ne suka nufi ɗaki yin salla. Ana idarwa tai zaman yin karatun Alkur'ani Oum kuma na lazimi har akai isha'i sannan suka fito. Sashen Abah Oum ta tafi, hakan yasa Maanal zama ta shiga duniyar tunanin nata na fama.
Gaba ɗaya kwanakin nan hankalinta ba'a jikinta yake ba. Dan al'amarin su Mamy yayi matuƙar jijjiga mata zuciya. Dauriya kawai take tana danne komai dan kar kowa ya fahimta musamman AA da Oum. Hatta a office yau dauriya kawai take da ƙarfin hali. Dan tasan idan kowa bai fahimci halin da take ciki ba shi zai fahimta. Shiyyasa ma ta toshe duk wata hanyar kasantuwarsu a waje guda a gidan kafin yau, yayinda shi kuma ta fahimci yana fushi da ita akan hakan duk da dai yanda suka kasance yau a office kamar ya huce...
Bayan wucewar Oum zaman shurun ya isheta, gashi tana son yin waya da Didi Shahidah. Tasan kuma dole ta nemi inda zata kawaice idanun mutane kodan abinda zasu tattauna. Fitar Oum zuwa sashen Abahn ya bata damar ɗaukar novel ɗinta da glasses ta yafa ƙaramin veil a kanta batare data ɗaura ɗan kwalin atafar doguwar rigarta ba ta ɗauka ruwa da popcorn dake ajiye a dining. Compound ta fito, sai da ta gama bin ko'ina dake ƙwanyar da hasken security light da kallo sannan ta nufi hanyar inda AA ya taɓa kaita kwanaki dake da swimming pool, dan tasan can ɗin ma sharr ne da hasken tamkar rana. Shigarta wajen ya sakata lumshe idanu saboda busowar wata ni'imtacciyar iska mai ƙanshin furanni a cikin hancinta, murmushi tayi, zuciyarta na sake zumuɗin ƙarasawa gaban ruwan. Sai dai me tana ɗaga ƙafa dole ta koma ta tsaya cak, sakamakon saukar muryar Mamy cikin kunneta. Magana take a kausashe, cike kuma da bada umarni. Kai kawai Maanal ta girgiza cike da takaici zata juya dan bama ta buƙatar jin baƙaƙen maganganun da Mamyn ke faɗa akan Oum, amma mi sai taji Muryar AA a bazata yana faɗin, “Amma Mamy yanzu baƙya ganin hakan zai zama wani abu daban idan nace yarinyar nan ta dakata da zuwa Company na. A yanzu fa Maanal matata ce, a ganina ta wuce dukkan wata alfarma kuma sai iko ma da take da shi akan komai na. Kema fa gashi faɗa kike kullum akan Abah, dan na tabbata da ace baku haɗa miji da Oum ba amintarku har abada bazata taɓa rawa balle har kukai ga wannan matakin. Duk da dai daga ɓangarenki ne aka samu rashin fahimtar, dan har zuciya wlhy Mamy kina a zuciyar Oum da girma da daraja. Ni dai Mamy bazan gaji da baki haƙuri da faɗa miki gaskiya akan wannan al'amarin ba. Dan ALLAH ki ajiye makamanki akan Oum, bana son lokaci yakai ƙurewar da wani a gidan nan zai ji wani abu akan hakan, musamman sauran ƴan uwana da Abah. Sannan batun aurena da Maanal kiyi haƙuri, hakan wani hukuncine na UBANGIJI dake rubutacce a ƙaddararmu, kodan yanda abubuwa suka faru a baya, da yanda suke a yanzu yakamata mu fahimci al'amarin nan fa mai girma ne.....”
“Hakane ubana”.
Mamy ta faɗa cike da hasala da gatse kuma. Murmushi AA yayi na tsantsar damuwa. Sai kuma ya ɗan kalleta da idanunsa da suka kaɗe sosai. “Kiyi haƙuri idan kalamaina sunyi nauyi da yawa Mamy, har abada ni mai biyayya ne a gareku ku duka ukun nan. Sannan zan bama kowanneku kariya daga cutarwar ɗan uwansa.....”
“Kai ka sani kuma wannan. Na baka kafin nan kafin fara azumi kazo min da cikakken bayani akan ma'anar Maawad kamar yanda na faɗa maka, tare da dukkanin takardun kadarorin ka...”
“Mamy ki gafarceni, wlhy ban san yanda zan iya tunkarar Oum na amshi abubuwan nan a hannunta ba”.
“Okay haka kace? Toni zan tunkareta na amsa tunda ba uwata bace ba ai”.
“Mamy Please....”
Ko kallonsa batai ba ta wuce fuuu. Ja baya Maanal tai ta laɓe a ɗan lungun da akai adon wajen. Dan bata buƙatar Mamyn ta ganta. Zuciyarta kuwa wani irin zafi take mata, matuƙar tausayin AA na ratsa mata ɓargon jiki. Kenan shi Mamy ta bayyana masa ainhinta, tana kuma amfani da damar tana tursasa masa yin abubuwa dan tasan yanda Oum keda muhimmanci a garesa. Murmushi ta saki mai matuƙar ciwo, sai kuma da sauri ta share hawayenta ta bar jikin bangon tamkar yanzu ne take shigowa saboda jin ƙarar taku alamar shine zai fito. Bayyanarta ya sashi tsayawa cak, itama sai ta tsaya ɗin tana kallonsa, dan duk yanda taso basarwa ta kasa hakan. Tausayinsa ne ke neman fin ƙarfin zuciyarta.
AA da ganin Maanal ɗin ya sashi jin shock wani irin tsinkewa zuciyarsa tayi, addu'a yake ALLAH yasa yarinyar nan bataji tattaunawarsa da Mamy ba. Dan bazai taɓa son hakan ta kasance ba sam. Cikin son basarwa ya shiga haɗiye nannauyan abinda ke tsaye a maƙoshinsa ya daidaita fuskarsa. Sai kuma ya cigaba da takowa a hankali har zuwa gabanta. Kayan hannunta ya ɗan zubama ido, kafin ya janye ya maida kan fuskarta. Cikin tausasa murya da ƙanƙanceta ya furta, “Daga ina?”.
“Sama”.
Ta bashi amsa.
Murmushi yayi a karo na farko, tare da lumshe idanunsa ya sake buɗewa a kanta. “Bakin nan dai bazai daina ma mutane baƙar magana ba ashe?”.
Samun kanta tai da ɗan sakar masa murmushin itama sai kuma ta kauda kanta gefe tana mai laɓe bakin kaɗan. Shima murmushin ya sake saki dan nata murmushin wani sanyi ya saukar masa a zuciya. A hankali kuwa ya saki ajiyar zuciyar tare da matsowa gab da ita. Matsawa tayi baya tana mai waro masa idanun kaɗan, irin na (lafiya dai?) shima sai ya bita. Danganewa tayi da bango, hakan sai ya bashi damar dafe bangon da hannu ɗaya ya mata rumfa da jikinsa. Gaba ɗaya ta jita kamar a keji, ga wani irin watsal-watsal da zuciyarta ke mata, sassanyan ƙamshin turarensa kuwa na saukar mata da kasalar jiki da gaɓɓai. Shima ɗin wani irin haurawa yaji jininsa nayi a saman kai, a hankali muryarsa cike da taushi da nauyi ya furta, “Bestie, please give me a hug mana”.
Sosai zuciyarta ta harba, duk yanda taso daurewa ta kasa, idannunta ta ɗago slowly ta sauke akansa, shima kallon nata yake, sai taga kamar idanunsa na ƙyallin hawaye, duk da tasan wannan normal ne a garesa, dan in har ma yana cikin farin ciki sosai idanun na fari tas-tas zakaga tamkar kuma an bisu da mai ne. Amma na wannan yanayin babu abinda take hangowa a cikinsu sai tsagwaron damuwa da ɓacin rai........✍️
_To bazawarin Huznah dai kazo da bidia, runguma kuma? Gaskiya wannan