Showing 123001 words to 126000 words out of 218311 words

Chapter 42 - AJIYA A DUHU BOOK 2 By Billyn Abdull.txt

bama ta fahimci na Fawzan da Najma ɗin ba sam.
Fara shigowar motocin baƙi yasa hotunan sake ɗaukar armashi. Dama gidan Darma a ranar salla matattarar baƙi ce sosai. Isowar su Didi Shahidah ya saka Maanal kwasa a guje ta rungumeta. Dan bata sanar mata zasu zo ba. Tuni Barru da Haneef sun rungumeta suma Haneef harda kukansa dan yana bala'in son Maanal. Uncle Sadeeq kam sai suka bashi dariya. Dan da ƙyar suka bari Maanal tazo ta gaidashi da masa sannu da zuwa.
Cikin ƙanƙanin lokaci gidan ya tara mutane. Tuni an gama shirya abinci a garden kamar yanda akeyi duk shekara. Can aka ɗunguma cin abinci. Manaal dake manne da Didi duk sanda ta ɗago sai sun haɗa ido da AA. Dan cin abincin sashin maza daban na mata daban. Anci ansha an godema UBANGIJI. Baƙi suka cigaba da zuwa, Maanal ta gaisa da Ammie ta video call, ta kuma kira Daddy shima tai masa barka da salla. Da Nene da duka kawunan su ƴaƴan Nene. Sai Didi Maanal itama da suka jima suna hira dan ɗakin Oum suka shige ita da Didi sukai hirarsu ta yaushe gamo. Sai ga kiran su Aneesa suma. Nan ma sun sha hira sosai. Bata sake ganin AA ba tunda suka shigo. Sai bayan sallar la'asar da su Didi suka tafi tai kira Mah-mah ta kano (Nasan kun gane Maman su Oum kuma tasu RK😀) harda Abbah suka gaisa da su Yaya da aunty Rufaidah da amaryar RK Nuwaira. Shima RK ɗin ya amsa suka gaisa cikin girmama juna. Hakan yayama Mah-mah daɗi ta dinga sakama Maanal albarka ita da Abbah. Maanal ta dinga amsawa a kunyace. Daga nan Baba Sardauna ta kira, shima suka gaida harda Ummah, su Uncle Mahmud, Hassan, Hussain duk suna nan tare da matansu suma duk suka amsa suka gaisa. Sosai abinda tai ɗin yay musu daɗi, dan su Saheeba basu taɓa ɗaga waya sun kira wani a cikinsu ba, sai dai in Kanon sukaje ko su sunzo Abujan. Itako Maanal a wajen Najma duk ta amshi numbers ɗinsu. Daga nan Baba ta kira. Wato mahaifin Abah shima ta gaisheshi shi da Mamma matarsa, nan ma ta gaisa da su Uncle Najeeb da matansu. Kowa sai saka mata albarka yake. Tana yankewa ta kira Gwaggo Khadijah, mahaifiyar su Nuwaira kenan, baiwar ALLAHr nan kamar ta zuƙo Maanal ta wayar ta goyata dan farin cikin wannan girmamawa datai mata. Itama ƴayanta na gidan suka gaisa. Hajiya Majdiya ce ƙarshe. Ita kam ai tamkar uwa take, nan fa ta fara mata hira tana sanar mata ta shirya salla da kwana uku zatazo Abuja da kayan gyara dan sai ta gyarata tsaf kafin tarewa. Kunya duk ta ishi Maanal. Suna yin sallama ta fara neman layin AA, ganin har biyar ta wuce a tunaninta ma baya gidan. A mamakinta sai taji karar wayar a cikin ɗakin, da sauri ta juya bayanta sai ganinsa tai tsaye a bakin ƙofa ya wani harɗe hannaye a ƙirji ya jingina da bango ya zuba mata idanu. Sosai ta waro nata idanun waje dan sai kamar taji tsoro, harga ALLAH bata san ya shigo ɗakin ba balle sanin tun yaushe yake a wajen.
Ganin yanda ta daburce sai yay murmushi, cike da basarwa ya iso yana faɗin, “sarkin tsiro”.
Cikin tura baki ta ce, “ALLAH ka bani tsoro fa. Babu ƙyau irin haka kaɗan ya rage na fasa ihu ALLAH”.
Kusa da ita ya zauna ya jawota jikinsa ya rungume. Cikin magana ƙasa-ƙasa ya ce, “Sorry bazan sake ba.” kanta ta jinjina masa. Ya ɗagota yana kallonta cikin ido gira a ɗage. “Kina missing ɗina ne?”.
“Bance ba”.
Ta faɗa tana kauda kai gefe.
“Uhyimm! To miyasa ake kirana? Bayan ba'a taɓa ba!”.
“Ni bakai zan kira ba, kuskure aka samu”.
Kwanciya yay ya ɗaura kansa a cinyarta, hannayensa harɗe a ƙirjinsa yana kallon fuskarta cike da shauƙi ya ce, “Ba ƙyau ƙarya fa, gashi nan idanunki sun nuna kina kewar ɗan saurayinki”.
Murmushi tayi tana kauda kanta gefe. Yasa hannu ya dawo da fuskar ya hanata hakan. Dole ta haƙura ta tsaya. Bai saki fuskarta ba sai ma murza babban yatsarsa daya cigaba da yi a hankali kamar mai share mata hawaye, yana kallonta da wani irin sanyin yanayi ya cigaba da magana a hankali. “Ina can ina barci sai mafarkinki nake yi, da ƙyar na daure na fara zuwa sallar la'asar amma nazo ban ganki ba. Da ƙyar Oum da taga na damu taji tausayina tace min kina nan”.
Samun kanta tai da ɗaura nata hannun itama akan lallausar sumarsa data sha gyara, yanda ta tura yatsunta cikin sumar yasa AA lunshe idanunsa a hankali yana sauke ajiyar zuciya. Sai kuma ya buɗe idanunsa slowly ya ce, “Thanks You”.
“For what?”.
Ta faɗa a hankali.
“Everything Babie”.
Ya bata amsa cike da raɗa yana lumshe idanun da buɗewa a lokaci guda. “Kin kira dukkan ahalina kin gaishesu, ke ta dabance a rayuwata Manaal”.
“Oh ahalinka ne kai kaɗai?”.
“No sorry ahalinmu”.
Murmushi tayi, sai kuma tace “Nima ai Ammie da Daddy da Nene sunce ka kirasu ka gaishesu tun ɗazun”.
Murmushi kawai yayi, cikin son kauda zancen ya ce, “Ina son mu ɗan fita yawon salla fa”.
Ɗan jimmm tai sai kuma ta ce, “Yaushe?”.
“Yanzu idan anyi magrib. Sonai tun la'asar ma, amma ba damuwa zuwa bayan magrib ɗin ma yayi”.
“Amma kai zaka gayama Oum?”.
“Babu damuwa. Sarkin kunya.”
Yay magana yana ɗan jan lips ɗinta masu taushi da santsi..........✍️








*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*


*09032345899*






*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
















*_💞AJIYA A DUHU....💞_*








*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*




*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_My TikTok account 👇_*


https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1


*_Instagram👇🏻_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_Arewabooks_*


Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


*_WhatsApp channel_*


https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R




_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_


*_BOOK 2_*
🅿️➖6️⃣1️⃣




______________




........A falo kam a kusan dai-dai lokacin ne Ameeran Hajiya Shuwa ke shigowa gidan. Riƙe take da hannun ƴar gidan yayanta Ameer sai ƙaramin basket mai ƙyau ɗauke da ƙyawawan bowl a cikinsa. Mutanene sosai a gidan, dan haka kanta a ƙasa take gaida duk wanda ta gamu da shi harta isa sashen Oum. Anan ɗin ma dai da mutanen, haka ta daure ta shiga ciki bakinta da addu'a. Dai-dai tana saka kai ciki shi kuma babban yaya ke fitowa hannunsa riƙe da waya yana magana. Sai kawai sukaci karo dan su duka hankalinsu baya a gabansu. Cikin sauri tai ƙasa zata tallabe basket ɗin shima ya duƙo zai tallabosa batare dama yaga wacece ba. Wani kalar bugar hancinsa mayataccen ƙamshin turarenta yayi, ya wani irin zuƙa ya lumshe idanunsa irin na AA. Ita ɗin ma dai nasan ƙamshin ne ya wani kalar ratsata. Sai da taja numfashi kamar mai asthma ta haɗiye. A tare suka ɗago, yana ƙoƙarin ce mata sorry itama tana ƙoƙarin cemasa sai kowa yay shiru. Sai kuma ita ta saki murmushi da faɗin, “Lah Babban Yaya ashe kaine. Good evening fatan anyi salla lafiya”.
Sosai wani abu mai girma ya tsargama babban Yaya, kasancewar sa ba gwanin murmushi ba shi sai ya tsareta da idanu kawai. Muryarsa a ƙasa ya furta, “Ameerah kece haka?”.
Murmushi tayi tana mai duƙar da kanta cike da kunya. Shima sai ya wani lumshe idanu ya buɗe kamar mai shirin suma. Sai kuma ya bata hanya yana faɗin, “Kin dawo lafiya ya karatu?”.
“Alhamdullahi Yaya an kammala.”
“Masha ALLAH, ALLAH ya sanya albarka sai aure ko?”.
Kalmar ta suɓuto masa batare daya shirya hakan ba. Ɓoye fuska Ameera tayi cike da kunya ta ce, “Yaya ba yanzu ba”.
Murmushi yayi da ɗan taɓe baki ya ce, “Idan mun yarda mu yayye kenan. Oya shiga Oum ɗin na ciki”.
Ai da sauri Ameerah ta shige. Dan harga ALLAH kallon da baban yaya ke mata ba ƙaramin rikita mata lissafi yay ba yau ɗin nan. Oum na ganinta ta fara murna da mata oyoyo, ALLAH sarki Oum uwa maba da mama kenan ita kowa nata ne, shiyyasa da wahala kaji mutum yace baya sonta. Rungumeta Ameerah tayi cike da farin cikin ganinta, dan itama tayi missing ɗin Oum sosai. Dai-dai nan Maanal da AA suka fito daga bedroom ɗin Oum. Ameerah ta ɗan kafe Maanal da kallo, sai kuma ta juya tana kallon Oum idanu a zare ta ce, “Oum Maanal ko?”.
Oum na dariya ta ɗaga mata kai. Cikin wani kalar farin ciki Ameerah ta juyo tana sake kallon Maanal, dan tasan labarinta sosai a wajen Oum. Ta ce, “Woow Oum ƙyaƙyƙyawa da ita”. Sai kawai taje ta rungume Maanal ɗin tana faɗin, “My twin sister nayi farin cikin ganinki”.
Murmushi Maanal tayi kaɗan duk da bata santa ba, suna haɗa ido da AA ya ɗauke kansa. Ameerah data ɗago itama sai ta kalla AA ɗin. “Oh Yaya AA shine koka faɗa min Bestynka ta dawo, bayan ranar har gaisheka nai ta WhatsApp”.
Hararrata ya ɗanyi ya raɓasu zai wuce. Ameerah bata damu ba dan tasan halin kayanta. Har cikin rai ɗaukar su AA take kamar Yaya Ameer, suma kuma suna mata gata irin ta yayu da ƙanwa. AA ɗin ne ma dai bai cika sakewa ba. Kuma tunda ta fahimci halinsa kenan bata wani damuwa da wani ɗaure-ɗauren fuskarsa ko rashin yawan magana. Oum ce taima Maanal bayanin Ameerah, dan ranar data fara ganin Hajiya Shuwa a gidan ta bata labarinsu kaf. Oum nace mata su Najma ma nan cike da farin ciki taja hannun Maanal suka nufi garden dan su Najma nacan. Aiko suma su Najma na hango Ameerah suka taso a guje suna ihun murna dan abokiyar wasansu ce idan sunzo hutu. Nanfa hira ta ɓalle dan Ameerah babu ruwanta.....


_________


Washe garin salla AA ya damu Abah da maganar Yaya Fawzan da Najma. Mamaki ne ya kama Abah sosai, amma sai murmushi yake na farin ciki.
“Naji daɗin wannan al'amari ƙwarai da gaske Ajwaad. Kuma ina sha ALLAHU bazayi ƙasa a gwiwa ba a yau ɗin nan zan kira Baba na sanar masa. Idan so samu ne a satin nan akai kuɗi a haɗa bikin da naka ma. Dan na jima da fahimtar Fawzan na buƙatar ƙara aure”.
Murmushi AA yayi shima, ya ce, “ALLAH ya tabbatar Abah, kaga shike nan ma an huta ta ƙarasa karatun a ɗakinta”.
“Sosai kuwa haka za'ai in sha ALLAHU, in ma zai yi hakuri sai a ɗaura kawai idan ta kammala jarabawar tunda wata ɗaya ne sai ta tare. Kaima kuma dama ina nemanka akan naka auren da yarinyar nan Nuratu”.
A take fuskar AA ta canja. Abah na lura da shi yay ɗan murmushin manya. Kafin ma yace wani abu AA ya fara magana murya a cinkushe.
“Abah wai maganar yarinyar nan baza'a barshi bane. Nifa ko ƙaunar ganinta banayi a gidan nan balle kallonta a wani matsayi mai kusanci dani. Yarinyar nan bata da tarbiyya sam, sannan rawar kanta yayi yawa. Haba mace babu nutsuwa ai ba mace bace. Dan ALLAH Abah ni dai ka rufa min asiri ka rushe maganar nan matata ta isheni wlhy”.
Sosai abin ya ba Abah dariya, dan kamar fa AA zai masa kuka. Amma dai ya danne cike da kulawa ya ce, “Karkace haka Ajwaad koba komai ƴar uwarka ce ita. Sannan bamu san inda rana zata faɗi ba nan gaba ALLAH ya jarabceka da sonta. Kuma kaga an riga an tsaida magana da iyayenta bai kamata mu zama ƙananun mutane ba ai ko”.
Sosai zuciya ta tokare maƙoshin AA. Da kyar ya iya furta, “Shike nan Abah, amma dan ALLAH ba yanzu ba, a ɗan bani lokaci idan na shirya da kaina zan maka magana”.
Ɗan jimmm Abah yayi na tunani, sai kuma ya jinjina kansa, “Okay ba damuwa, amma ina son ka kira Baba kai masa bayani da kanka, dan gaskiya bansan yanda zan tunkaresa ba. Tunda na hannun damarsa ne kai nasan zai saurareka”.
“In sha ALLAHU zamma je Kanon gobe”.
Nanma dariya sai da ta kusa kufcema Abah, ya ta dai danne da ƙyar. “Okay ALLAH ya kaimu, sai batun Maanal, zata koma gidan Shahidah...”
“Saboda mi?”.
“Saboda Oum ɗinku ta nema alfarmar hakan, wai zasu mata ko gyaran jiki na amare kasan dai mata.”
Sam AA baiso hakan ba, amma har gaban abada bazai iya musu da Oum ba. Dan haka yace, “Shike nan Abah. Dama akwai kaya da suka iso na lefenta, suna hannun Babban Yaya. Amma da zai yiwu ba sai an kaisu ko'ina ba, kawai a ajiye mata Abah”.
“Masha ALLAH, ALLAH yay maka albarka Ajwaad. Hakan yayi sosai, tunda ankai wancan na wajen Rafeeq kada mutane suga kamar wata fariyya ce. Amma in aka ajiye mata ƴan uwanta kawai suzo su gani ya wadatar.”
“Nima abinda nayi tunani kenan”.
Albarka sosai Abah ya dinga saka masa, daga haka suka cigaba da hirarsu....


WASHE GARI


Da safe AA ya wuce Kano, lokacin Maanal ma na barci ko sallama basuyi ba. Kai rabon daya samu zama da ita tun daren salla da suka fita yawo sai 12 suka dawo. Jiya ita da su Oum da yaran duka a gidan Shahidah suka yini sai dare suka dawo. Yau kuma gashi zai wuce kano tana barci. Ashe Oum ta shirya masa, dan sun gama tsara komai ita da Hajiya Shuwa, dama Maanal ba gidan Didi Shahidah zata zauna ba, nan gidan Hajiya Shuwa ne. Oum ta ɓoye hakan ne dan kar ma AA yace zai dinga zuwa gidan wajenta ya ɓata musu aiki. Aiko a ranar da yamma Oum ta amshe wayar Maanal aka kaita gidan Hajiya Shuwa babu wanda ya sani hatta da Abah. An kuma gargaɗi Ameera. Gaba ɗaya sai Maanal taji ta damu batai sallama da AA ba. Amma dai ta dake ko'a fuska bata nunama Oum komai ba.


A ranar AA bai dawo ba sai washe gari, yanata baza idon ganin Maanal shiru. Da ga ƙarshe dai ya daure ya tambayi Oum tace ba Abah ya gaya masa zataje gidan Shahidah gyaran jiki ba. Kasa cewa komai AA yayi, dan Oum ta wuce gaban ka-ce-na-ce a wajensa. Duk kuma yanda tayi dai-dai ne. Aiko bai ƙara magana ba bawan ALLAH, sai ma ya tattara ya koma aiki. Maanal kuma ya saka aka ƙara rubuta mata sabon hutu bayan wanda suka sha tun daga dawowa Chaina.
Mamy ma dai bata ganin Maanal a gidan, bata tambaya ba amma abun naci mata zuciya. Gefe shirye-shiryen bikin da suke ya ɗauke mata hankali. A haka aka ci kwanaki sati ɗaya. Saura sati ɗaya biki kenan. Da yamma babu zato suka samu baƙuncin Baba Sardauna tare da Uncle Mahmoud da yay masa rakkiya. Saheeba ce ta shiga tana faɗa ma Mamy zuwansu. A take fuskar Mamy ta canja, cikin taɓe baki ta ce, “Uwar mi kuma akayi to?”.
“Waya sammusu Mamy, kin dai san in dai kaga tsohon nan to ba alkairi ba ne”.
Kafin Mamy ta bada amsa kira ya shigo mata waya, Abah ne kuwa, tana ɗagawa yace tazo ga Baba. Kafin tace wani abu ya yanke. Kwafa tayi mai ƙarfi, kafin ta miƙe tana tsinema Darma Family gaba ɗaya. Hijjab ta saka sannan ta nufi sashen Abah ɗin hannunta ɗauke da basket na abinci data saka Haule ta haɗa mata. (Munafukai) Ta faɗa a zuciyarta ganin Oum zaune kusa da Baba fuskokinsu cike da farin ciki, dakewa tai itama ta ƙawata tata fuskar da fara'a. Cikin girmamawa ta gaishe da Baba, ya amsa mata da kulawa kamar yanda ya saba. Sai ta koma tsokanar Uncle Mahmoud irin wasan ƙanin miji. Shiko yana ramawa. Haka dai aka gaisa cikin farin ciki kamar babu komai a zukata..
Bayan su Baba sunci abinci sun huta bayan sallar isha'i akai zaman meeting. Baba da kansa yay masu bayani cewar sun shiryama Ajwaad da Maanal bikin tarewa. Sannan batun Nuratu ga yanda suka tsara saboda abinda ya dinga faruwa a tsakanin Maanal da Nuratun da azumin nan. Dan haka yana roƙonsu su basu haɗin kai ayi komai a tashi lafiya, su kumayi fatan zuwan na Nuratun itama da kamar yau ne da an kammala ginin da za'a sakata ciki, saboda haɗasu waje guda bazai haifar da ɗa mai ido ba..........✍️








*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*


*09032345899*






*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
















*_💞AJIYA A DUHU....💞_*








*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*




*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login