Showing 162001 words to 165000 words out of 218311 words
Chapter 55 - AJIYA A DUHU BOOK 2 By Billyn Abdull.txt
ne sukai wani masifar kaɗewa kamar an kunna harwashin wuta a cikinsu. Ga azabar ƙafa da hannunta da keta sake kumburi raunuka na ƙara tsami. Su Maman Saheeba kam sunyi jigun-jigun abin duniya ya ishesu babu bakin magana tunda basu kaɗai bane. Ga Nuratu an danna mata allurar barci ita dai sun ɗan huta da ita. A haka doctor da zai duba ciwukan jikin Mamy ya iso. Auntynsu tace ai dolene a gayawa Abah kafin likitan ya shigo tunda ba kamar mace ba dai. Dan haka tace Mamy tai kiransa a wata da kanta.
Cikin tsanin azaba Mamy tace wlhy bazata iya ba, tsoro take ji, dan shirun Aban ba ƙaramin girgiza mata zuciya yayi ba. Jiba fa a yanda ya ganta jiya, amma bai nuna damuwar komai ba, ga shi yau har ƙarfe kusan sha biyu koma tace ana neman ɗaya amma bai leƙo ba, kai wani a cikin ma ahalinsu bai leƙo sashenta ba. Sai da Mariya ta fita tana naɗo musu gulma ta shigo tana ƙara sanar musu halin da gidan yake a ciki na farin ciki a yau. Sai ta fahimci hankalin kowa yana a can kenan.
Dai-dai sanda ake jajen kiran likita su Hajiya Majdiya ke shigowa sashen kuwa. Sosai ganin su Hajiya Majdiya ya saka su Maman Saheeba a shock, sai dai sun san kuma dai babu damar hanasu shiga ɗakin Mamyn. Haka dai suma daure aka gaisa sukace Mamyn na ciki. Da yake daga ita sai doctor da Aunty kawai a ɗakin su duk suna a falo ne, wasu a falon ƙasa wasu a falon sama.
Turus su Hajiya Majdiya suka ja suka tsaya ganin fuskar Mamy tamkar wadda tai accident, accident ɗin ma bana wasa ba, dan fuska a kumbure komai ya ninka kansa sau uku, ga hannu da ƙafa ɗai-ɗai suma a kumbure. Cikin tashin hankali sosai suke tambayar miya faru haka? Miyasa ba'a sanar Mamyn babu lafiya ba? Ai ko Abah basa jin ya sani farin ciki ya ɗauke hankalinsu a sashen Ajwaad.
Cikin ƙarfin hali Aunty ta ce, “Faɗuwa tayi jiya da dare a stearcase, ruɗanin da suka kwana suka tashi a ciki yasa basu sanar ma kowa ba. Yanzu haka ma doctor yazo zai duba mata ƙafarta da hannun dan suna tunanin akwai rauni a ciki”. Ba dai ta faɗi na shayi ba daya sale Mamyn a majalissa. ALLAH yayi ma ahalin Darma tausayi da ɗaukar nasu a nasun, tuni Hajiya Majdiya ta manta da iya shegen data zo da niyyar yima Mamyn ta juya ta fita tana faɗin, “Ai dole a sanar kuwa, bari taje a shigo da likitan”....
Lokacin da Hajiya Majdiya ke fitowa domin sanar ma su Oum halin da Mamy ke ciki Momyn Nibras kuma ke ƙoƙarin shiga ita da ƙawayenta su uku. A kallo ɗaya zaka fahimci a matuƙar fusace suke. Dan har ɗan bangaje ta sukai. Mamaki sosai abin ya bata dan haka ta bisu da kallo, dan da farko ma ita bata gane Momyn Nibras ɗin ba sam saboda abinda ta shafa a fuska. Ashe wai duk a cikin shirin bala'i ne. Sashen Abah ta nufa da sauri, suna tare da Umma da Mah-mah sai Gwaggo Khadijah da Mammah suna tattaunawa ne akan batun Ajwaad a tsakaninsu manyan sai su Uncle Mahmud dake tare da su an kira Baba Sardauna, da Baba, da Abbah video call. Shigowar Hajiya Majdiya yasa duk suka kalleta. Kafin ma wani ya iya yin magana a cikinsu ta ce, “Kuyi haƙuri gidan nan fa babu lafiya. Ga Aunty Kamila can cikin mummunan yanayi daren jiya ta faɗo daga saman stearcase, taji ciwo kuma sosai. Yanzu kuma zan fito ga wasu riɗa-riɗan mata can fitsararru sun shiga sashen daga ganinsu kasan basa tare da alkairi.”
A tare su Uncle Hussain suka miƙe, hakama su Umma. Amma Abah bashi da niyyar yin hakan. Baba Sardauna da suke jin komai duk da ba ganin Hajiya Majdiya suke da ƙyau ba ya ce, “Kutashi kuje ku duba mike faruwa. Kuma ku dama duk bidirin da kuke baku sanar musu ba ne?”.
Da mamaki Umma tace, “Sun sani fa gaskiya, sai dai in ƴar uwarsu bata sanar musu ba. Dan tun ma ana duba yaran nan kamar cousin sister ɗinsu ce yarinyar nan Mariya tazo sashen Ajwaad ɗin. Tare da ita ma likita ta sanar mana komai ai. Amma dai bara muga mike faruwa to”.
Dama su Uncle Mahmud har sun fice, dole shima dai Abah ya tashi yabi bayansu......
_______★
Su RK basu san mike faruwa ba, suna can sashen AA jira kawai suke ya farka musamman Yaya Fawzan da aka ƙara bama labari kaf. Shi kansa dai Babban Yaya yau bakinsa akwai magana. Dan a hakan ma sai jehota yake ɗai-ɗai su RK na dariya. A haka su Maimoon da aka saka gyaran sama suka sakko, sun share ko'ina tas sun saka ƙamshi mai daɗi, dai-dai nan Oum itama ke fitowa a ɗakin Maanal tare da Hajiya Shuwa data shigo gidan yanzu babu daɗewa saboda kiran da Oum tai mata ta mata bayani. Ba ƙaramin shock kuwa itama Hajiya Shuwa ta shiga ba. Matuƙar tausayin Maanal ya kamata, dan harga ALLAH data san yarinyar nan virgin ce da batai mata kalar gyaran can ba, dan ko'a hakan dama tana tausayama yarinyar saboda gyaran datai mata ko mace mai haihuwa uku iyaka kenan. Amma ita tayi ne dan samar da nutsuwa a zamantakewar auren. Shi rashin samun mace a cikakkiyar budurwa a daren farko nada wata illa ne koda ace mijin ne ya santa a mace kafin aure. Sai ya dinga sakama namiji zargi da wasu-wasin bayan shi akwai wani ƙila a gefe. To wannan ƙofar ce suka shirya toshewa gaba ɗaya a zamantakewar Ajwaad ɗin da Maanal.
Ta tabbatar ma Oum da kafin ma ayi ɗinkin ne ta sanar mata da bazata bari ayi ba. Akwai magungunan da zata haɗa mata da ganyayyaki ta dinga sit bath cikin ƴan kwanaki zata warke komai ya koma normal, amma ko yanzun ma bata ɓaci ba in sha ALLAHU zata tsaya akan Maanal ɗin. Da wannan zancen suka fito zataje gida ta haɗa kayayyakin ita kuma Oum tace zata kira Ammie itama a sanar mata wannan daddaɗan labari har ma da su Shahidah. Sai dai me suna sakkowa hayaniyar da gidan ta ɗauka ya shiga rige-rigen shigewa cikin kunnuwansu. Da sauri suka ƙarasa sakkowa dai-dai suma su Babban Yaya na fita dan ganin mike faruwa...........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖8️⃣0️⃣
______________
........Tofa babbar magana. Dambe ne fa ya harƙume tsakanin Mariya da ƙawayen Momyn Nibras. Dan suna shiga sashen basu kula kowa ba suka haye sama Momyn Nibras ɗin na ƙwalama Mamy kira. Mamaki yasa duk ƴan uwan nata ƙoƙarin tsaida su amma basu saurarensu ba sai ma hankaɗe duk wadda ta nema taresu suke cike da bala'i suna faɗin ba dasu zasuyi ba Mamy ce daidai da su. A haka suka ƙarasa hawowa falon saman. Sai kuma duk suka ja tunga ganin su Aunty Rufaidah dake jiran dawowar Hajiya Majdiya, suna a ɗakin Mamyn ne kwakwazon su Momyn Nibras ya fito da su. Jinin Darma manyansu da yaransu jinin girma ne da kamun kai, ALLAH kuma ya musu kwarjini wannan tamkar a jininsu ne.
Aunty Siyama ce ta ce, “Lafiya kuwa haka Hajiya su wanene ku?”.
Ji sukai sun kasa mata da hargagin da suka shigo. Momyn Nibras ta ce, “Wajen Kamila muka zo”.
“Amma ko wajenta kuka zo bayin ALLAH ya ƙyautu ku shigo mata gida a haka kenan? Kar ku manta nan fa sirrinta ne, inama laifi ku jira a down stairs amma har upstairs babu wani excuse. Wannan take hakkin ɗan adam ne, sannan babu girma sam”.
Mariya dake hawowa ta ce, “To dama wannan suna da girma ne in ba na jikinsu ba. Wai baku ganeta bane, uwar waccan yarinyar ce fa matar Fawzan da akama kishiya”.
Da mamaki kowa ke kallon Momyn Nibras a karo na farko. A fusace Momyn Nibras ɗin ta ce, “Ke kuma a suwa ana magana da manyan gida kina saka baki ƴar a jira aci a wanke kwanika. To ahir ɗinki da saka baki anan. Dan ke baki isa ba ita Kamilar ce dai-dai dani. Idan kuma ba tsoro ba ta fito nan muyita naji dalilin yima gudan jini na kishiya bada saninta ba, dan an ga munyi kawaici mun kauda kai kuma yau ƙaton banza ya ɗaga hannu ya mata har mari uku dan ta nema sakinta. To ina son naji ita ta saka shi yay marin ko kuwa raɗin kansa ne?”.
“Ikon ALLAH yau naga masifa. Yo ita ƴar taki har wacece da baza'a mata kishiya ba. Juyar da bata haihuwa sai dai taci takai masai kullum. To mu ƴan duguy-duguy muke son gani dan gidan Darma gidan ƴaƴane kema kin sani.” Mariya ce da wannan murtani a jarabe. Aiko kalmar juya da aka kira Nibras da tafi komai yima Momyn Nibras ciwo yasa Mariya na rufe baki ta sauke mata mari. Tace manyan matan da tazo dasu wai ƙawayenta wai suma Mariya dukan tsiya su saita mata bakinta, dan duk duniya babu mai kira mata ɗiya da juya ya kwana lafiya wanan gangan ne. Yo ALLAH na tuba Mariya dama ƴar daru ce. Aiko kafin kace mi ta fara musu dukan kan uwa da wabi. Tuni ta kaɗosu ƙasa dan tace suje filin tsakar gida wasan zai fi musu dai-dai ita nan ya mata kaɗan. Shine fa suka fito har compound ana dambe. Duk kuma abinda ya faru a kunen Mamy ne dake fama da kanta. Ga azabar ƙunar cikin zani ko ƙafa bata iya haɗewa da ƙyau ga kuma ta ƙafar da hannu ga raunikan fuska. So take kuma tai kuka amma sam yau hawaye sun ma ƙi su zubo mata sam. Ji take a ranta ashe kuka rahama ne ga bawa. Ita fa duk wannan ba shine damuwarta ba ma, hankalinta na'akan Abah ne, so take ya shigo sashen ko zazaginta yayi zataji sanyi a ranta. Dan Wlhy UBANGIJINTA ne kawai yasan iyakar soyayyar da zuciyarta kema Abah. Zata iya ɗaukar komai amma banda fushinsa ya mata girma. Musamman a mihalin shiru, dan tasan wanene Abah kai masa laifi ya maka shiru, sai ka gwammace ya maka duka ma an wuce wajen....
Da ƙyar da ƙyar aka raba Mariya da ƙawayen Momyn Nibras. Zuwa sannan itama Nibras ɗin ta fito. Ƴar zubama juna ashariya manya-manyan aka koma yi, yayinda Momyn Nibras ke faɗin, “In har Fawzan ya cika ɗan halak ya sakar mata yarinyarta, tace bata auren ko dolene. Yanda ta birkice sai kuma ya tada hankalin Nibras, dan ita ba haka take so Mom ɗinta tayi ba. Idan kuma ta ɓata da ƴan family ɗin taya in Fawzan ya saketa zata dawo ta auri AA ne. Ƙoƙarin riƙeta take tana faɗin, “Mom Please kiyi shiru mana. Bafa sai kin zagi kowa ba kibi komai a hankali”.
Ina sam bata jinta. Fawzan da ransa ya ɓaci ya daka wata mummunar tsawa yana isowa tsakkiyar faɗan. Cikin wani irin fushin da kowa zai iya rantsuwar bai taɓa ganinsa a ciki ba ya ce, “Badai saki take buƙata ba, to kije da ƴar taki ni Fawzan Aliyu Abubakar Darma na......”
Tsawa shima Abah ya daka masa. Tare da faɗin, “Kull ka furta Fawzan, kai da nake kallonka ne haƙuri a gidan nan. To ban yarda ka saki matarka ba, suyi duk abinda sukaga zasuyi mugani. Babu abinda ya dameka da rikicinsu can suje su ƙarata tunda babu wanda yasan lokacin da suka ƙulla. Ko ka sani?”.
Kai Fawzan ya girgiza. Sai kuma cike da girmamawa ya ce, “Kayi haƙuri Abah, raina ne ya ɓaci, kaga fa irin zagin da sukema mutane na rashin mutunci”.
“Zagi suyi tayi ai baya tsiro a jiki. Kuma ba ƙurji bane bare idan yayi ruwa ya fashe warinsa ya addabi kowa. Tunda da suka zo bakai suka nema ba ka barsu da wadda suka nema ɗin ita ta sakar musu ƴar”.
Babu wanda kalaman Abah basu girgiza ba. RK ya saki wani makirin ɓoyayyen murmushi, zuciyarsa na faɗin anya Abah kuwa bai san halin Mamy ba pretending kawai yake. Kai wannan al'amari da mamaki yake. Ƙoƙarin barin wajen kowa ya fara musamman su ahalin Darma ɗin ma saboda suna respecting maganar na sama dasu matuƙa sai Hajiya Majdiya ta dakatar da su. Cikin damuwa ta tuna musu halin da Mamy take ciki.
Wani irin zabura Oum tayi tana faɗin, “Suhanallahi shine kuma duk bamu sani ba. Wane kuma jiran umarni ake likitan ya shigo kawai ciki.” baiwar ALLAH jikinta har rawa yake ta nufi sashen Mamy. Sai suma su Babban Yaya da su Umma suka rufa musu baya. Suma dai su Momyn Nibras ɗin jin batun rashin lafiya yasa ta shanye komai. Dan ita wlhy wannan bala'in yanzu ne aka farashi su da Mamy har sai an sakar mata ƴarta. Ai sanda Mamyn taje tana roƙarta a aurama Fawzan Nibras ta tabbatar mata sufa ahalinsu ba'a musu kishiya. Mamyn kuma ta tabbatar mata suma haka suke, itace kawai tsautsayi da soyayya ya sata shiga gidan mai mata. Dan haka Fawzan da Nibras kishiya ko'a mafarki babu ita, shine dan rainin hankali kuma za'ai mata yanzu. To wlhy sai inda ƙarfinta ya ƙare kuwa.....
★Babu wanda halin da Mamy ke ciki bai girgiza ba a cikin su Oum. Ransu kuma ya ɓaci da rashin sanar da su da akayi. Aiko Umma ta fara faɗa sosai musamman akan ajiye Mamy gida da sukai maimakon su wuce da ita asibiti tun dare. Sannan ko babu komai sun san ai Rafeeq likitane, koda ba likitan fannin halin da Mamyn ke ciki bane ai zai kira wani ko. To dama suka ajiyeta a gida su basu sanar musu ba basu kaita asibiti ba mi suke nufi da hakan ne?.
Aiko nan fa hankalinsu ya tashi, suka shiga rantse-rantsen son kare kansu suna kallon Abah ko zai yi magana dan wlhy tsoronsa da ganin da yay musu ya hana su sanar da mutanen gidan ya kuma hana su kaita asibitin. Amma abin mamaki bawan ALLAHn nan tamkar ma bai san mi ake tattaunawa ba. Zaki rantse bai san komai ba. Haƙurin dai da dattijan ciki suka babbada da amsar laifinsu yasa Umma tai shiru. Duk fitowa sukai a ɗakin aka bar doctor da RK sai Babban Yaya da Fawzan a ciki. Shi dai RK yana ganin ƙafar yasan dole akwai karaya, amma bai ce komai ba yabar likitan da suka kawo ya dubata. Likitan nan na gama dubata sai cayay ba sai anje asibiti ba gocewar kashi ce kawai da ɗan targaɗe zai dubata kawai a gida. Haka suka bashi dama ya fara aikinsa. Hannun ya fara taɓawa, aiko hajiya Mamy ta tsandara ihu sai da su Babban Yaya suka riƙeta, ashe wasa farin girki. Sai da akazo kan ƙafa harda fitsarinta, gashi shima fitsarin wata azaba ce idan yana fita dan waje dai ya ƙone kuma taƙi magana. Sosai ta wajigu, ba ita ba hatta su Fawzan suma sunyi sharkaf da zufa. Harda sumanta kafin a gama. Ana gamawa dole akai mata allurar barci....
Lokacin salla yayi, dan haka kowa ya nufi yin tashi, dangin Mamy suka fara shirin wucewa kamar yanda Maman Saheeba ta nuna musu dama Saheebar. Dan sun samesu sukace ya kamata su tafi haka nan tunda anci biki an cinye, kar suga waɗan can basu tafi ba sufa dangin maigidan ne. Bayin ALLAH badan sun so ba sukace to. Aiko suka fito suna murmushin samun nasara, dan sunyi haka ne saboda Mariya, sun kula in dai tana a gidan bazasu sami yin rawar gaban hantsi ba yanda suke so.
Cike da taƙama Saheeba ta nufi sashenta dan tun jiya har yanzu bata samu komawa ba saboda yanayin da suka kwana suka tashi, mizai faru ta samu ƙofa a rufe. Ta koma ta hanyar kitchen nan ma a rufe. Mamaki ne ya kamata, dan ko fita zasuyi basu taɓa kulle ƙofa ba koda duka gidan ne kuwa. Sai zuciyarta ta bata kodan Babban Yayan yaga da baƙine shiyyasa. Sashen Mamyn ta sake komawa wai har ya dawo massalacin....
_________★
Bayan dawowar su salla kaɗan AA ya farka. Lokacin RK na tare da shi dan yana saka ran farkawar tasu dama kusan a yanzu. Babu kowa a sashen sai yara ma da aka saka sukazo suka sake gyara ko'ina tsaff. Sai Hajiya Shuwa da Oum dake ɗakin Maanal suma yanzu suka shigo babu jimawa. Dan Oum nacan ta saka ama su AA ɗin abinci mai rai da lafiya. Da kanta taso tayi ma sai ga Hajiya Shuwa. Sai tace Hajiya Majdiya tayi. To tana fitowa Mah-mah tace Hajiya Majdiya ɗin ta barshi itama bari ta musu ita. Dan abu na musamman take son shiryama ƴan jikokin