Showing 165001 words to 168000 words out of 218311 words

Chapter 56 - AJIYA A DUHU BOOK 2 By Billyn Abdull.txt

nata. Ai ko sai Gwaggo Khadijah ta shigo suka jone. Abinka da tsoffi an san takan sirrikan abubuwa, nan fa suka shiga haɗama Maanal haɗin nama da wasu abubuwa na musamman, sai abincin shima irin na tsoffin hannu ya subahannallah.....


Da taimakon RK AA ya tashi, Alhamdullah zazzaɓi ya sauka. Hakama cikinsa da kansa duk komai sai godiyar UBANGIJI. Sai ma wani irin fresh yake jinsa tamkar sabon mutum. Tambayoyi RK ya ɗan masa ya sake tabbatar da komai normal sannan ya taimaka masa zuwa bayi dan yayi wanka. Da kansa ya gyara masa ɗakin, fitowa yay dan bincika ko itama Maanal ta farka...........✍️








*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*


*09032345899*






*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
















*_💞AJIYA A DUHU....💞_*








*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*




*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_My TikTok account 👇_*


https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1


*_Instagram👇🏻_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_Arewabooks_*


Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


*_WhatsApp channel_*


https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R




_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_


*_BOOK 2_*
🅿️➖8️⃣1️⃣




______________




.........Alhamdullah itama Maanal ɗin ta farka. Dan RK na fitowa sai ga Oum ta fito domin kiransa tace masa Maanal ɗin ta farka yazo ya cire mata ruwan da ya ƙare har jini ya ɗan fara komawa ciki. Hajiya Shuwa na zaune kusa da Maanal data ƙi buɗe ido ta kallesu tunda ta farka wai ita kunya. Jin RK kuma ya shigo sai taji kamar ta nutse ma a cikin gadon ta huta. Shi dai ya cire mata ruwan, sai Hajiya Shuwa ke tambayar basu shigar musu aiki ba idan sukama Maanal amfani da magungunan gargajiya wajen sit bath ko. RK ya tabbatar mata in dai an yarda da ingancin su babu wani abu. Fita yay ya barsu dan ya fahimci halin da Maanal ke a ciki. Aiko yana fita Hajiya Shuwa ta tashi ta fita kitchen da kayayyakin tana faɗin Maanal ɗin taje tai wanka tai salla kafin su dahu.
Da ƙyar Maanal ta yarda Oum ta tadata zaune. Sai kuma azaba ta sakata shiga jikin Oum dan bazata iya zama ba. Murmushi Oum tayi, cike da tsokana ta ce, “Babyna raguwa”. Sake ɓoye fuska Maanal tai a jikin Oum. Hakan ya sake bama Oum dariya. Ta ce, “Oh ni Fateema yau ke da mijinki duk kun maida ni surukar ku dai a gidan nan. Haba Babyna, Oum ce fa. Ai ni yau babu abinda zance da UBANGIJI sai godiya, ALLAH yay muku albarka, ya zagaye rayuwarku da farin ciki, ya baku zuri'a masu albarka. Yanda ALLAH ya bayyana gaskiya yau abinda muka daɗe cikin ɓacin ransa ya kasance ba haka bane ALLAH ya shafe mana dukkan zunubanmu. Na kira ƙanwata na sanar mata komai harda kukanta. Na rasa ma miya shiga kammu a lokacin muka gagara fahimtar babu abinda ya faru dake? Koda yake muna cikin ruɗani sosai, kuma ya riga shima ya amsa yayi ashe yaron nan baiyi ba.....”
Karan farko dai Maanal ta ɗago ta kalla Oum, cikin kasa daurewa a wannan gaɓar ta ce, “Oum wai da gaske ne abinda doctor ta faɗa ɗazun kenan?”.
“Da gaske ne Baby na, babu abinda ya faru tsakanin ki da Auta a waccan ranar. Bamu san dalilinsa na amsawa da yayi ba. Mukuma firgici yasa bamu nutsu mumma dubaki ba da kammu a lokacin, kawai jinin dake zuba a jikinki da wanda ke a jikinsa yasa muka aminta yayi. Shi kuma doctor ɗin daya dubaki ban san dalilinsa na yi mana ƙarya ba. Amma yanzu dai kowa Auta yake jira ya tashi muji yaya aka faɗi a ragaya. Aban ku kuma har yasa a bincika masa likitan daya dubaki a waccan ranar muji shi kuma dalilinsa na mana ƙarya.”
Hawaye ne sosai suka ziraro a fuskar Maanal, komai daya faru a waccan ranar ya shiga maimaita kansa a ƙwaƙwalwarta. Muryar Ajwaad da ƙamshinsa da taji, faɗa mata jiki da akayi, fara kissing nata daga haka bata sake fahimtar komai ba, kawai ta farfaɗo akace ai ya mata fyaɗe ne. Abubuwa suka rikice saboda mutuwar baba Haruna suka wuce Giro. Ciwo ya kwantar da Ammie mutanen gida da su Gwaggo suka cigaba da wulaƙantasu harda Babu, hatta mutanen gari ma basu barsu ba aka koma aibantasu ana cewa tayi cikin shege, kai su bama ƴaƴan Babu bane daga waje Ammie ta rorosu. A lokacin bazata iya ƙarar da cewar fyaɗen ne ya sata a halin ciwo ba. Amma tana jin ciwo a zuciyarta idan ta tuna an mata fyaɗe kuma Ajwaad ne. Bestyn ta fa. Bata san ainahin minene fyaɗe ba kai tsaye ko a aikace. Amma yanda al'ummar duniya ke ƙyamatarsa harda ma saɓanin musulmai yasa itama taji ƙyamatar abun a ranta a lokacin ƙwarai da gaske. Amma shigarta cikin matsanancin halin ciwo shine, ƙuncin rayuwa fa suka tsinta kansu, zafin rabuwa da Ajwaad dake cinta a ƙansan zuciya. Abinda ya aikata mata da rashin biyo sahunsu da basuyi ba. Sai firgicin tsorata da tayi a lokacin da take da tabbacin Ajwaad ɗin ne yake ƙoƙarin keta mata mutumcin, tunda a lokacin ne ta suma shiyyasa abin ya zauna daram a brain nata. Koda ta girma ta ƙara hankali ta sake tantance mi ake nufi da tabon fyaɗe ga ɗiya mace sai al'amarin ya ƙara zafafa ta, musamman da shekaru suka cigaba da ja babu Ajwaad babu labarinsa......”
Oum ce ta katse mata tunani ta hanyar share mata hawaye. Cike da lallashi ta ce, “Kuka ya ƙare ai Baby in sha ALLAHU, tashi muje kiyi wanka kiyi salla kema Rafeeq yace shima Auta ya farka”.
Kai Maanal ta jinjina mata, sai kuma kanta a ƙasa ta ce, “Oum shima baida lafiya?”.
Kai Oum ta jinjina mata tana murmushi, ta ce, “Yana taya Bestyn sa jiyya mana”.
Siririyar dariya Maanal tayi saboda yanda Oum tai maganar tana lakace mata kumatu cike da tsokana. Itama Oum ɗin dariyar tayi. Tare da miƙar da ita suka nufi bayi tana takawa a hankali. Dan har yanzu tana jin zafi sosai a wajen, labarin farin cikin nan ne kawai ya sata dannewa. Sai da Oum ta haɗa mata ruwan wanka masu ɗumi sannan ta fito ta barta, haka Maanal ta fara wanka tana sake nazartar abubuwa. Kamar zararriya tana hawaye tana murmushi. Ƙasan zuciyarta kuma na mamakin dalilin Ajwaad na amsa laifin da bai aikata ba. Ashe shiyyasa bai taɓa bata haƙuri ba, kai tunda suka sake haɗuwa bai taɓa tada mata zancen ba. Lallai yanzu ta sake yarda RK ya fahimci Ajwaad matuƙa, dan shine ya ɗan fara mata shaguɓe akan hakan. Amma ita koda ta karanta abinda AA ɗin ya rubuta fassarar data basu daban ce. Jitai ma ta ƙagara ya shigo suga juna. Haka dai ta kammala wankan tai alwala. Cike da dauriya ta fito ita kaɗai, ashe ma Oum na kusa tana jiranta. Itace ta taimaka mata suka ƙarasa, har an gyara ɗakin tsaff an saka kamshi. Oum ta bata doguwar riga tace saka tai salla yanzu Hajiya Shuwa zata dawo, ita kuma ta fita tana cigaba da faɗin “Bara na duba ko Majdiya ta kammala muku abincin”.
Kai Maanal ta jinjina mata, ta ɗauka Abayar ta saka da hijjab, cike da dauriya tai sallar azhar ko zama bata iyayi da ƙyau. A haka Hajiya Shuwa ta shigo da botiki babba yana ta tururin ruwan zafin dake a ciki. Maanal ɗin na idar da salla ta kamata suka nufi bayi.....


_________★


Yaya Fawzan dake fitowa a wanka ya nufi wayarsa dake haske alamar kira ya tsinke ko shigowar saƙo. Wayar nada alaƙa da komai nasa mai muhimmanci ne shiyyasa baya wasa da ita. Ilai kuwa Najma ce ta turo masa message. Zama yay a bakin gado kafin ya buɗe, abinda ta tura masa ya saka shi sakin murmushi, tun shekaran jiya ita ta wuce gida da yamma tare da ƙannenta dan jiya ta fara jarabawa. Idanunsa ya lumshe ya buɗe dan kowannensu ya iya wannan ɗabi'ar AA ne kawai ya ɗara kowa dan shi komai nasa irin na Aba ne sosai. Hasken fata kawai zai nuna masa dan Abah shima fari ne tas kamar su Fawzan. Ƙoƙarin kiranta yay amma wayar a kashe, ya sake sakin murmushi yana kaiwa kwance. Babu abinda ke dawo masa a zuciya sai washe garin ɗaurin aurensu. Dan ranar da aka daura auren bata yarda sun haɗu ba ko a wajen dinner ɗin su AA tana maƙale da Mah-mah saboda shi. Shi kuma sai yay kamar bai ganta ba duk da yana cike da ɗokin kadaicewarsu sai a washe gari.
(To bari mubi tunanin Yaya F muji miya faru shi da ƴar shalelensa a waccan ranar da bamu sani ba😂🙏).
A ranar walimar su Maanal data kasance washe garin ɗaurin auren sa da Najma bayan ya gama wahalar bin duk hanyar da zasu haɗu ta toshe kwatsam sai gata ita da Aunty Rufaidah sun dawo daga gidan Hajiya Shuwa da suka je. Dan aunty Rufaidah na son a mata gyara ita da Nuwaira. To sai Nuwaira ta tashi a safiyar da zazzaɓi abinka da mai laulayi. Shine Oum tace a haƙura da nata gyaran jiki aje ama Najma a maimakonta, ita Nuwaira tunda suna nan a Abuja idan ta samu sauƙi a mata dan RK yace bazata koma Kano ba yanzun. Shine fa sukaje akai musu. Sunyi ƙyau sosai masha ALLAH. Suna shigowar ne shi kuma yana fitowa a sashensu zai shiga mota. Suna haɗa ido da Najma ta wani basar ta ɗauke kai harda ƙara sauri. Aiko sai ya wani dake ya ce, “Najma zonan”. Cak Najma ta tsaya gabanta na faɗuwa, zuciyarta na gudu a ƙirjinta. Basu san raina na gaba da su ba musamman ma yayun nan nasu. Ga Aunty Rufaidah tayi kamar ma bataji mike faruwa ba tayi gaba abinta dan waya take da mijinta. Cike da sanyi jiki kai a ƙasa Najma taje, sai wani sinne kai take gana gaishesa. Ƙin amsawa yay ya buɗe mata mota yace shiga. Idanu ta waro sosai waje, zatai magana yay mata alamar zipping. Dole ta rufe bakin ruf ta shiga ya maida ya rufe ƙofar ya zagaya nasa waje shima ya shiga. Komai baice mata ba ya tada motar ya fice a gidan. Tun tana tunanin zasu tsaya a cikin anguwar ne har taga ya bar ta yankin ma gaba ɗaya, sai da yaje wani waje da babu kowa shiru duk Companys ne ma sannan ya samu ƙasan wata bishiya yay parking. Ita dai kanta a ƙasa tama kasa kallonsa. Shi kuma ya zuba mata ido yana kallon yanda taketa cuɗa hannunta a cikin na juna alamar a tsorace take, nishaɗi sosai abin ya saka shi da dariya amma ya dake. Muryarsa ba wasa ya ce, “Babu gaisuwa”.
Muryarta a ƙasa sosai ta ce, “Kayi haƙuri ina yini”..
“Bazan amsa ba sai da na roƙa! Kuma ai bama haka ake gaida miji ba”.
Fuskarta tai ƙoƙarin ɓoyewa tana murmushi ya riƙota, a bazata ya wani jawota gaba ɗayanta ta koma jikinsa ya rungume ta tsam-tsam. Uhmm su Hajiya Najma ko musu babu akai luff a jikin Yaya Fawzan. Sai ma sauke ajiyar zuciya suke a tare. Dan shi zuciyarsa har wani gudu take a ƙirji, sakamakon hakan ya jima bai faru a tsakaninsa da Nibras cikin salama ba. A farkon aurensu dai komai normal ne, amma tunda Ajwaad ya dawo gidan nan komai ya canja, bukatarsa ma zai biya sai da ƙarfin tuwo balle runguma. Kiss kam ai tun na farkon amarci bai ƙara samu ba. Dan haka tuni ya shiga laluben bakin Najma a lokacin, sai ko bata hanashi ba ta bashi dama harda taimaka masa duk da dai a kunyace take sosai, aiko sai ya rikice mata, ya shiga sumbatar ta tamkar zai cinye mata lips. Daga ƙarshe ma al'amarin ya shiga canja salo sai da ta shiga roƙonsa. Da ƙyar ya iya barinta, dan harga ALLAH shi kansa bai san fitinanne bane irin haka sai tsakanin daren da aka ɗaura aurensu daya kwana da ita a ransa zuwa ranar.......✍️








*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*


*09032345899*






*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
















*_💞AJIYA A DUHU....💞_*








*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*




*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_My TikTok account 👇_*


https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1


*_Instagram👇🏻_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_Arewabooks_*


Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


*_WhatsApp channel_*


https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R




_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_


*_BOOK 2_*
🅿️➖8️⃣2️⃣




______________






........Sun jima shiru fuskarta na ɓoye a jikinsa kafin a hankali ya furta, “Thanks you Love! Na godema UBANGIJI daya bani ke a matsayin mata. Na kuma godema Babban Yaya da Uncle Rafeeq da Ajwaad daya kasance gaba-gaba na ganin kin zama mallakina na har abada. Naso ace an bani ke a yau ɗin nan koma tun jiyan, amma ba komai zanyi haƙuri har ki kammala exam ɗinki maybe dariyan dana dingama Auta ce ta bini nima”. Dariya Najma ta sanya. Fuskarta a ɓoye ta ce, “Ato shiyasa ai tsokana ba ƙyau, gashi shi an bashi tashi kai kuma zaka fara naka zaman jiran”.
Dariyar shima yayi da faɗin, “Oh hakama zaki ce. Ba komai zan rama ne yarinya. Shima kuma ba ƙyalesa zanyi ba. Ɗazun Abah yace min yau zaku wuce dan gobe zaki fara exam”.
Kanta ta jinjina masa. “Eh zan tafi dasu Nah-nah zamubi train zuwa kaduna, Abba zai ɗauke mu dan yana kadunan yace zai jira mu”.
“Amma shine daban ganki ba ma yanzu sai dai naji kin wuce. Gaskiya da sai na hukuntaki kuwa. A kiyaye bana son haka kinji ko. Ina son komi ya shafi matata na fara sani kafin kowa har iyayenmu. Na yafe miki wannan dan na farko ne bakuma ki sani ba.”
“Thanks you Yaya, in sha ALLAHU bazan sake ba kuma kayi haƙuri. Ina jin kunya ne kawai dama. Dan komai yazo min ne a bazata. Amma jiya da naji an ɗaura mana aure bamma san yanda zan musalta abinda naji ba gaskiya.”
Murmushi sosai yayi yana kallonta, ji yake kamar ya haɗiyeta ya huta. Ga wani irin canjawa da jikinsa ke neman yi. Haka dai ya daure ya amshi wayarta yay abinda zai yi, sannan ya saka mata kuɗi masu yawa a account ɗinta ya sake rungumeta ya sumbaci lips ɗinta. Cike da sanyin yanayi ya ce, “Idan kun shirya ki kirani dan da kaina zan kai amaryana station ɗin”.
“Thanks you Yaya”.
Ta faɗa a hankali tana sake lafewa a jikinsa.....
Bugo ƙofa da shigowar da akai ya yanke tunanin nasa, a hankali ya buɗe idanunsa dake a lumshe ya sauke akan Nibras dake wujiga-wujiga yau ko wanka batai balle ai maganar taci wani abu ma. Sai huci take na bala'i, tsabar son bata haushi sai ya sake maida idanun ya lumshe kamar bai ganta ba.....


_________★


Sosai Maanal tasha gashi a wajen Hajiya Shuwa ta kuma sha kuka. Amma harga ALLAH taji daɗin jikinta sosai dan hatta jikin nata Hajiya Shuwa saida ta daddana mata da towel kamar wata mai jego. Baiwar ALLAH sai sauke ajiyar zuciya take. Bayan sun fito ta sata tai tsigunnen turaren wuta na jiki dana ƙasa, harma dana gashi ta kuma busar mata da shi ta gyara mata tsaf duk da tana faman raki. Kafin ta taimaka mata ta shirya cikin abaya mara nauyi ƙirar dubai. Ta ɗan gyara mata fuska aka ƙara gyara ɗakin aka saka masa turare. A lokacin Oum ke dawowa da abincinsu tare da Meeno data ɗakko. Meeno ta gaida Maanal cike da damuwa dan yarinyar nasan Maanal sosai, har catai mata ita bazata koma Kano ba zata zauna a wajenta. Maanal kuma ta mata alƙawarin in sha ALLAHU zata sa a barta dan itama tana son yarinyar, kodan ta ɗanyi duhun fata irin ta AA ne oho, gashi tana kama da shi sosai koda yake kaf family ɗin Darma kama suke da juna na bala'i ma kuwa. Sosai Oum taji daɗin ganin yanda Maanal ɗin tayi ƙyawun gani, sai idanun da har yanzu suke a kumbure dan manyan mata sun sha kuka. Dan ma yanzu Hajiya Shuwa ta saka mata kwalli. Oum bata zauna ba suka fice da Hajiya Shuwa, itama Meeno suka tisa ƙeyarta dan yanzu RK ke sanarma Oum da zata shigo AA fa nason zuwa ya duba matarsa ya damu. Shine Oum tace to bari ta bar musu abincin kawai a tare ba sai an kawo masa ba.
Aiko suna fita bai fi da mintuna uku ba Maanal na kwance da wayarta a hannu zata kira su Didi da taga miss call ɗin su harda Ammie aka buɗe ƙofar. Idannunta ta ɗago a hankali ta kalla wajen jin ba'ayi magana ba kuma ba'a ƙarasa shigowa ba. Ido huɗu sukai da AA, a hankali ta lumshe idanunta ta maida kanta ta kwantar. Shima sai ya lumshe nasan ya buɗe a lokaci guda, sai kuma ya maida ƙofar ya rufe sannan ya shiga takowa ciki. Ƙananun kaya ne a jikinsa da suka masa ƙyau sosai. Kai da ka gansa kaga sabon ango fill a kwali dan sai ƙyallin goshi yake. Lips ɗinsa ya wani koma pinkish sosai alamar ansha shagali da shi daren jiya. Idanun kam sunyi tar-tar da su kamar an watsa madara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login