Showing 57001 words to 60000 words out of 218311 words
Chapter 20 - AJIYA A DUHU BOOK 2 By Billyn Abdull.txt
Ta shagala sosai a bazata ya waiwayo suka haɗa ido, cike da borin kunya ta kauda nata gefe tana ɓata fuska. Shi dai baice mata komai ba, kuma bai daina kallon nata ba har sai da wayarsa ta motsa alamar shigowar kira. Ɗauka yay ya duba, babban yaya ne. Dan haka ya ɗaga tare da kai yatsansa ya gyara zaman bluetooth ɗin kunnesa baƙi, cikin yanayinsa na rashin son ɗaga sauti yay sallama... Tsabar yanda yake magana can ƙasa su kansu su AS dake a gaba ba jinsa suke ba. Ita kanta Maanal dan kawai ta nutsu ne ta maida hankali a kansa duk da ba kallonsa take ba. A haka suka iso airport dan gudu sosai sukayi.
Bai motsa domin fita ba, ita kuma ya riƙe hannunta bai bata damar ta fitan ba. Magana suke da AS. Ita Maanal ma tayi zaton bada shi za'a ba. Sunja kusan mintuna biyu a haka sannan aka buɗe musu. Juyawa yay ya ɗan kalleta, kafin ya saki yatsun hannunta dake sarƙale da nashi a hankali sannan ya yunƙura ya fita yanzu ma jacket ɗinsa da bai saka ba har yanzu a hannu. Itama ɗin fitar tayi, dai-dai driver na rufe side ɗin data fito ɗin AA ke isowa wajenta. Yayinda AS daya fiddo akwatinsu da wani da bata san na waye ba ya tura su yay gaba. Shi kuma da yake binta da wani kallon ƙasa-ƙasa hannunsa ya miƙa mata. Hannun ta zubama ido, sai kuma ta ɗan ɗago ta kallesa. Ita ɗin dai yake kallo idanunsa na komawa ƙanana. Yau dai ta fahimci kurumtar ce ta motsa ta miskilanci, dan haka ta ɗaura hannun nata a hankali saman nashi, shiko ya haɗesu da ƙyau sannan suka fara takawa a tare.
Dole duk wanda ya kallesu su burgesa, dan kallo guda zai tabbatar maka da su ɗin ma'aurata ne. Sun matuƙar dacewa da juna kuma, duk da ita ɗin ƴar ƙarama ce a gabansa, dan koda take da tsaho tsahon nata gaba ɗaya bai wuce kafaɗarsa ba. Arba da ma'aikatansu su Yaqub ya sakata jin nauyi da kasancewar a yanda suke. Shi ko ko'a kwalar rigarsa. Sai ma amsa musu gaisuwar da suke masa yake ta hannyar jinjina kai. Itace ke amsawa cike da jin nauyin da su kuma suke fassarawa da jan ajinta. Dai-dai nan kuma aka fara shelar neman matafiyan da zasu tashi a jirginsu zuwa Qatar. Gaba yay riƙe da hannun nata su AS da su Yaqub da yaƙi yarda ya kalla ko inda Maanal take biye da su. Sai da sukai ƴan abubuwan da suka kamata kafin wucewa inda jirginsu yake. A haka yana riƙen da ita suka shiga, su sun wuce vip ne.
Ganin hakan sai da yasa Maanal sauke ajiyar zuciya a ɓoye. Duk da ya jita bai nuna yaji ba, sai ma taimaka mata da yaya ta zauna a nata sit ɗin kafin shima ya zauna a nasa dake kusa da ita. Ta inda suken keɓantaccen waje ne madaidaici zaman mutum biyu tamkar wani falo ko ɗan ɗaki, zaka iya maida kujerun gado idan kaso. Ga television da kayan dai ƙawa yanda ya kamata. Tuni Maanal ta zama baƙauya, dan ita kam bata san akwai hakan a jirgi ba. Kai masu kuɗu na sha'aninsu. Bata tsinke da al'amarin ba sai da AA ya danna wani ɗan bottom ta gefen kujerar belt ya saka kansa da kansa a jikinsu. Dai-dai jirgin na tashi zuwa sama dole ta lalubo hannunsa a cikin nata. Kallonta yayi, sai kuma ya buɗe tafin nasa ya maida natan a ciki ya sargafe yatsunsu cikin na juna. Sosai ta sake ƙanƙame masa hannun har tana kafa masa ƙubunanta da ba wani tsahone da su ba dan bata wasa da yankewa a kan fatarsa. Aiko sai da ta fasa masa fata abinka da ba'asan wahala ba. Bata fargaba kuma sai da jirgin ya gama dai-daita ta buɗe idanun, hannun nasu ta ɗan kalla tana sauke ajiyar zuciya, har zata janye sai kuma tai saurin sake kallo. Sosai taji gabanta ya faɗi, babu shiri ta juyo da shi ganin yana ƙoƙarin juyarwa dan karta gani. A sanyaye cike da damuwa ta ce, “Ya ALLAH na ji maka ciwo”.
Komai bai ce ba, ya dai ɗan kalli hannun ya kauda kansa. Yayinda ita kuma ta buɗe yatsun nata tana matso da hannun saitin bakinta ta shiga wura masa iska da baki kamar wanda ya kone. Ai ba ƙaramin ratsa jijiya da jinin AA hura hannun nan yay ba, a take ƙofofin gashinsa suka shiga bubbuɗewa. Dole yay ƙoƙarin janyewa yana faɗin, “It's okay”.
Kanta ta jinjina masa idannunta na cika da ƙwalla, sai kuma taja tissue ɗaya dake ajiye a kwalinsa ta shiga goge jinin daba wani zuba yake ba ya dai nuna alamar fita ne kawai. Dai-dai nan ma'aijaciyar jirgin ta shigo bayan tai ɗan knocking, tray ɗin hannunta mai ɗauke da coffee ta ajiye, sai kuma ta dubesu domin jin ko suna buƙatar wani abu ne. Cikin harshen turanci Maanal tace suna buƙatar First aid box.
“No...”
AA ya faɗa yana ƙoƙarin dakatar da ita, amma sai maanal ɗin tace taje ta kawo. Itama ganin jinin yasata fita, babu jimawa ta dawo da wata matashiya kamarta da first aid ket ɗin a hannu. Kai tsaye inda suke tayo, ta ajiye box ɗin tana ma AA sorry. Shi ko kallonsu ma baiyi ba. Maanal ɗin da duk ta rikice kawai yake kallo ƙasa-ƙasa. Mata ta kawo hannu zata kama hannunsa Maanal tai mata tsawa batare da ita kanta tasan mi tayin ba. Cike da masifa tace ta bata zata masa. Karo na farko AA yay wani ɗin killer smile na gefen baki ya lumshe idanunsa kawai. Sai dai yana kallon yanda take goge masa jinin a ɗofane tana kuma hurawa da baki wai kar yaji zafin spirit. Sai yaji kawai abin ya masa suger. Ƙoƙarin tsokanarta yay, dan haka ya ɗan ja hannun baya kamar wanda yaji zafin.
Ai da sauri Maanal ta kallesa a raunane ta ce, “Da zafi ko, I'm sorry”. Yanda tayi kamar zatai kuka yasa shi ƙara girman idanun nasa a kanta yana kallonta ciki-ciki. Kansa ya girgiza mata ganin yanda ta zuba masa idanun dake tara ƙwalla. Kan nasa ya girgiza mata kaɗan, sai kuma ya juya nasa hannun nata ya koma sama, ya matso da shi tare da ɗan duƙowa ya sumbata. A hankali ta lumshe nata idanun tare da jan ajiyar zuciya.
Su dai ma'aikatan jirgi sun shagala suna kallon ikon rabbu, wannan al'amari kamar a film, dama a baƙaƙenmu akwai masu irin wannan shagaltacciyar ƙaunar, dan wannan ta wuce soyayya sai tsantsar ƙauna mai zafin gaske da sam bata ɓoyuwa a idanun masoyan. Da ƙyar ɗaya tai ƙarfin halin miƙama Manaal plaster ɗin data yanko tare da ƴar audiga. Maanal ɗin ta amsa ta sanya masa sannan tasa plaster ɗin a sama. Tattarwa sukai suka wuce suna waigensu..........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖2️⃣8️⃣
______________
.......Matuƙar saka rayuwar Huznah gaba Sageer yayi a wannan tsakanin da buƙatunsa. Tabi kowacce irin hanya na bijirewa amma ya nuna mata namiji yake. Sai dai taci kukanta da zaginsa a zuciya dan tsoronsa ALLAH ya dasa mata. Ko fita yay da zarar taji motsin dawowarsa zuciyarta ke fara dukan uku-uku. Gashi yanzu ya hana kowa shigowa gidan dan kullesu yake ta ciki, mutum ya ƙaraci bugunsa dole ya haƙura. Wayarta ya amshe ya kashe tun ranar da sukai waya da Hajiya Basariyya. Girki kam tunda tayi sau ɗaya ta ƙwaɓa musu hauka ya koma yi da kansa. A rana ta uku yasata shiga kitchen ɗin ya fara koya mata. Dan ya tabbatar mata yana da mata bazai dinga zuwa gidansu cin abinci ko saye ba. Idan zata zage ta zage babu abinda za'a fasa. Tako tabbatar da babu abinda za'a fasa ɗin kuwa. Dan tako ina baya raga mata yanzu. Hatta da gyaran gidan tsaye yake mata akai sai tayi komai yanda yake so.
Sau biyu tana satar wayarsa ta gwada kiran Hajiya Basariyya sai taji tata wayar a kashe itama. Ba ƙaramin tashi hankalinta yay ba da rashin jin uwar tata. Shiko sarai yana sane da ita, abinda bata sani ba yaji komai akan abinda ya faru da Hajiya Basariyyar a kwanakin nan Daddynsu na faɗa ma Babanshi saboda haƙurin daya bashi akan ya barsu su koma ɗakinsu suyi azumi. Shine yake sanar masa abinda Hajiya Basariyya ta aikata, da idonsa ya ganta shi da ƴaƴanta a wani ƙauye bin malamai, su kuma sunje cinikin gona ne a kusa da ƙauyen. Amma yay masa alƙawarin maida Hajiya Yaya idan tayi azumi koda goma ne a gidansu.
Sosai Huznah tai ramar dole a wannan gaɓar, ga shi kota kulle ƙofar ɗakin ma yanzu a banza ama wofi zai buɗe da wani key ɗin ne. Gida kuma in zai fita ta baya yake kulleta. Tun tana masa girman kai harta fara tunanin saukewa ta bashi haƙuri kozai taimaka ya bincika mata Umminta, dan tana son sanin wane hali take. Kamar kullum yau ƙarfe biyar ya dawo kasuwa. Tana falo zaune idonta a tv sai dai bata fahimtar komai kallon kawai take yi. Shigowarsa ta sata zabura tana masa sannu da zuwa. Sosai ya zuba mata ido dan mamaki. Amma sai baice komai ba ya gyaɗa mata kai kawai. Kitchen tai saurin nufa, a wani mamakin nasa bata jimaba sai gata ta fito da ruwa ta ajiye gabansa. Badan ruwan leda bane ALLAH sai ya tsargu wani abun mutuwar ta zuba masa. Amma yasan bazai yiwu ba tunda fure water ne....
“A kawo abinci?”.
Ta faɗa cikin katse masa tunani. Sai ya samu kansa da sakin murmushi. “Kina lafiya kuwa Huznah?”. Ya faɗa yana tsatstsareta da idanu.
Kanta ta jinjina masa alamar eh.
Iska ya ɗan furzar, sai kuma ya gyaɗa kansa da miƙewa yana faɗin, “Okay bara na watsa ruwa to, kibar abincin sai nayi sallar magrib tukkunna.”
Murya a ƙasa ta ce, “To”.
Nan ma sai da ya sake kallonta kafin ya wuce ciki abinsa yana kwasar dariya a zuciyarsa.....
Ni kaina dai abin ya bani dariyar Man Sageer 🤣😜
_________★
Gaba ɗaya Oum kewar yaranta take ji, dan ma babban Yaya da Fawzan sun ɗauke mata kewarsu. Nibras ma da farko ta shigo, amma jin hirar da su Fawzan keyi akan tafiyar su AA ɗin saita miƙe tsam kamar ma wadda jikinta ke rawa. Sallama tai musu cikin danne kukan dake neman zuwa mata tace zataje ta kwanta ta gaji. Da kallo kawai Oum ta bita. Hakama babban Yaya da tuni shima ya fahimci take-takenta. Amma a mamakinsu shi Fawzan ɗin da suka ji tausayinsa ya kama su shi hankalinsa ma nakan waya abinsa sai zabga murmushi yake dan charting yake da Najma.
Sai sukai tunanin ai bai fahimci matar tasa bane saboda sonta ya rufe idonsa. Sai dai abinda basu sani ba Fawzan ya riga kowa fara fahimtar matar tasa da inda haukanta ke ɗawainiya wajen kaita. Ya barta ne kawai bisa wasu dalilai dan yasan wane Autansu. Sannan yafi son kowa ta fahimta da kansa musamman Mamy data haɗa auren nasu. Dan yayi alƙawarin in sha ALLAHU da bakinsa dai bazai cema kowa a gidan ga halin da yake zaune da Nibras ba, har sai idan sune suka gani sukai magana....
Kuka sosai Nibras ta shiga yi a sashenta, ba komai ya kawo hakan ba sai jin matsanancin kishin AA akan Maanal. Yanzu ita har rashin muhimmancinta a gidan nan yakai AA ya shirya tafiya da wannan ƴar iskar yarinyar amma bata sani ba har sai bayan tafiyarsu. AA ɗinta, sanyin idaniyarta. Aiko har abada bazata yafe ma Maanal ɗin wannan tafiyar ba, sai ta mata hukunci dai-dai da hakan....
A ɓangaren Mamy ma dai ranta a jagule yake ita da muƙarrabanta su Nuratu. Dan Nuratu ma tun bayan tafiyar su Maanal data shige bedroom bata sake fitowa ba. Ita kanta Mamy sai da Abah ya fahimci bata cikin walwalarta. Koda ya tambayeta sai ta nuna masa kawai yanayi ne sannan kamar kanta zai mata ciwo take ji tasan kuma zafin gari ne dake sirkawa.
Sannu yay mata tare da bata magani yace tasha ta kwanta yau yama yafe mata zuwa sashen nasa kawai. Aiko wannan freedom ɗin data samu kusan raba dare sukai suna waya da yayarta da maman su Saheeba. Sun tsara yanda zasu tarwatsa Oum da Maanal sosai a gidan. Daga ƙarshe suka birkice zuciyar Mamy musamman akan AA. Tare da tunzurata akan batun ƙara auren Fawzan wai dan a tantance waye baya haihuwa shi da matar tasa tunda idan sunje asibiti sai ace musu duk ƙalau suke lokacine kawai baiyi ba. Su dai sam basu aminta da hakan ba dole akwai lauje cikin naɗi.
Tsaf kuwa zuciyar Mamy duk ta hau akan shawarwarin nasu. Duk da ita dai Aunty Babba har cikin ranta tana yaƙine da kishin ƴar uwarta wato Mamy, yayinda Maman Saheeba ke komai da zuciya biyu, dan itafa fatanta ƴaƴanta su kasance a gidan su mamaye komai na dukiyar su Babban Yaya ta hanyar baza ƴaƴa. Kunga ko komai ai ya dawo tafin hannunsu. Dan ita kanta Saheebar ido a rufe maganin haihuwa ake neman mata tunda tun daga cikin Anum shiru kake ji bata sake ko ɓatan wata ba ga Anum na neman cika 5years.
Ita ko Mamy ɗauka take duk sonta suke yi musamman ma Maman Saheeba, dan wasu lokutan ita Aunty Babba kan ɗan faɗa mata gaskiya shiyyasa tasu bata tsaho a tare.....
_________★
Bayan sallar magriba da isha'i da su Maanal suka gabatar ita da AA da har yanzu bai sake ba wajen zamansu suka koma. Ganin ya buɗe laptop itama sai ta ciro novel a bag ɗinta kawai ta hau karatu. Koda aka kawo musu abinci daga ita har shi babu wanda yabi takai duk da shine da kansa ya bada umarnin a kawo ɗin. Ɗan ɗagowa yay ya kalla Maanal jin kamar ta daina motse-motse, aiko dai gyangyaɗi take. Shi sai ma taso bashi dariya, yo tun ba'aje ko ina da tafiya ba, Chaina fa suka nufa tafiya mai nisan awanni.
Wani ɗan bottom ya danna a gefen kujerar a take ta wani kalar buɗewa ta zama gado, abinda ya raba tsakkiyarsu mai kama da hannun kujera ya naɗe kansa wajen shima ya zama flat. Laptop ɗin ya matsar gefe ya kwantota a jikinsa tare da zare novel ɗin hannun nata ya ajiye. Fuskarta data fito so cute a zagayen rolling ɗin veil ɗinta ya zubama ido, sai kuma ya janye cikin lumshewa ya kuma buɗe a lokaci guda. Veil ɗin ya shiga warware mata a hankali bayan ta cire pin ɗin data riƙe da shi. Yana ko gamawa ta gyara kwanciya tana sauke ajiyar zuciya. Shima sai ya samu kansa da sauke ajiyar zuciyar acan ƙasan maƙoshi. Ɗan takurewar da tai waje guda ya sashi ɗaukar lallausan farin mayafin dake gefensu kaɗan ya lulluɓa mata har a kafaɗa, sai kuma ya zare ribbons ɗin data kama kanta da su a tsakkiya gashinta ya tarwatse masa a hannu, kamawa yay ya tattaresa cikin hannun nasa ya shiga tufkewa a hankali ta yanda bai tsamke tushen ba balle taji zafi. Veil ɗin ya ɗauka ya ɗaura mata a kan kamar ɗan kwali cike da dabara, daga haka ya ɗan ranƙwafa ya sumbaci kan nata sannan ya ɗauka laptop ɗinsa ya cigaba da aiki duk da kuwa wani ɓangare na jikinta yana a jikinsa ne...
Sosai ya raba hankalinsa biyu a kallon fiskarta da aikin, dan yanda ta ɗam tsuke baki zaka fahimci kamar tayi barcin ne da faɗa a zuciyarta. Yasan halin mutuniyar tasa ba rabo take da masifa ba har a cikin barci tanayi faɗa. Kawai dai kura ce tai lafiyar dole. Eh lafiyar dole mana tunda dai risinar ta dole ce ai....
★Barci sosai Maanal tasha, dan bata tashi farkawa ba sai kusan 9:30, zuwa sannan awa ɗaya da rabi ce ta rage musu su sauka cikin ƙasar Qatar domin yin canjin jirgi. A hankali ta shiga motsawa, sai kuma tai juyin daya bata damar komawa tana fuskantar lafefen cikin AA, rashin nauyin rigarsa da yanda ta kwanta masa a jiki har yana jin saukar nunfashinta a kan fatar cikin nasa. Sosai tsigar jikinsa ta fara tashi. Cikin wani irin motsawar zuciya ya lumshe idanunsa a slowly sakamakon sake motsawa da tai ta kife ƙirjinta da ƙyau a cikin nasa tare da zagayo hannayenta ta bayansa. Daga ganin yanda tai ɗin ka tabbatar ta ɗauka filo ne ta rungume. Cigaba da saukar numfashin nata mai ɗumi a jikinsa ya sashi jin ina bafa zai iya ba. Da ƙyar ya iya jawo busashen yawun da ke neman suɓucemasa a baki ya haɗiye, maƙoshinsa yay wani irin yin