Showing 153001 words to 156000 words out of 218311 words
Chapter 52 - AJIYA A DUHU BOOK 2 By Billyn Abdull.txt
kirata saboda jinta shiru amma ta kasa. Knocking ƙofar da akai ya sata kallon wajen. Aka ƙara na biyu sai ta bada izinin shigowa. A mamakinta Babban Yaya ne ya shigo bakinsa da sallama. Taɗan zuba masa ido, sai kuma cikin ƙarfin hali ta ce, “Kai kuma lafiya a daren nan?”.
“Lafiya Lau Mamy, Saheeba ce tace kin kirata a waya, na ji shiru kuma shiyasa nai tunanin ko babu lafiya”.
A zuciya Mamy tace (Saheeba kuma...?) a zahiri kam rasa ma abin cewa tayi, sai kuma ganin yanda ya zuba mata ido ta ce, “Yanzu Fadeel dan na kira matarka shine ka taso ka biyo ta?”.
“Lah Mamy ki fahimta mana, nace najita shiru shiyasa nai tunanin koba lafiya ba. Yanzu fa magana ake ta sha biyu ta wuce. Kinga dole nai tunanin akwai damuwa. Amma tunda lafiya ai Alhamdullah sai da safe”.
Daga haka ya juya ya fice abinsa. Da kallo ta bisa kawai abu uku na mata kai-kawo a zuciya masu ɗaci. Na farko miyyasa Saheeban zatai ƙarya cewa itace ta kirata? Sannan ina taje a daren nan to?. Na biyu yanda sam su Fadeel basu damu da ita ba, yanzu ace a yanayin nan daya ganta bazaiyi tunanin bata da lafiya ba, ta inda Ajwaad ya ɗarasu kenan, ko yaya yaga canji daga gareta sai ya gane. Hawaye suka ziraro mata. Tamkar wadda aka bama ƙarfi sai gashi ta yunƙura ta tashi. Dolene taje ta duba Saheeban da Nana ma da taji shiru babu ita babu Ajwaad ɗin. Da ƙyar take tafiya saboda ƙafafunta da suka kumbura suntum, ga ciwon kai gana ƙirji da yake mata kaɗan-kaɗan shima. Shiru tsakar gidan babu kowa, haka ta dinga tafiya cike da ƙarfin hali tana haɗa hanya, tama rasa ina zata dosa, shawarar da zuciyarta ta bata na zuwa sashen Ajwaad tabi, dan gwara ta fara duba Nana tasan halin yaron nan ba ragama ƙanwar tata zaiyi ba.
Ta ƙofar kitchen tabi itama, tunda dama tannan ta bama Maman Saheeba shawarar bi. Itama sai da tabi komai na kitchen ɗin da kallo tana taɓe baki, kafin ta shige sai dai falon ƙasan shiru ne babu kowa. Amma fitula a kunne. Kuka-kuka da kiran sunan kamar Nuratu da taji anayi yasata nufar upstairs ɗin da ƙyar dan ƙafafunta sun mata nauyi sosai. Ai kamar jira ake ta gama hawowar kunnuwanta suka jiye mata abinda ya sakata tsayawa cak a firgice. Dai-dai nan kuma su Maman Saheeba suma suka ganta duk sai suka ƙara firgicewa. Jikin Mamy rawa yake sosai, takai hannu ta toshe kunnenta amma abinda take gudun jin tamkar a ƙwaƙwalwarta ake zayyanawa. Idanu a rufe tai wani irin juyawa gaba ɗaya domin komawa a bisa tsautsayi tai tsallaken taka step ɗaya, sai kawai ji kake rikicaaaa manyan mata sun kife.
A wani irin mugun tashin hankali Saheeba da Mamanta suka bar Nuratu suka kai kan Mamy da har ta fara mulmulawa tana yin ƙasa. Da shegen gudu suka shiga binta, tana gab da ƙarasa direwa ƙasa gaba ɗaya suka samu nasarar riƙota. Sai dai ina aikin gama ya riga ya gama dan gaba ɗaya jini ya wanke mata fuska, kuma sam bata numfashi.
Anya Saheeba da uwarta sun taɓa shiga irin wannan tashin hankalin kuwa a rayuwarsu. Dan Maman Saheeba bama tasan ta fashe da kuka ba tana kirama kanta ta shiga uku. Saheeba da itama jikinta ke rawa kaf-kaf ta ce, “Mama mun mutu, yanzu yaya zamuyi, wlhy idan bamu fitar da su a sashen nan ba akwai matsala. Kada fa ki manta duk ƴan kano suna a gidan nan. Sannan wlhy Ajwaad baida mutunci komai zai iya yi idan yazo ya gammu da uwarsa kwance a wannan halin, zai ma iya cewa mune muka turota. Mama aurena, dan ALLAH ki taimaka ni bari na tafi wlhy suka ganni anan zasu saka Fadeel ya sakeni, kuma shima nace masa Mamyn ce ta kirani.....”
Itama Maman kukan ta fashe da shi, “Yanzu Saheeba sai ki tafi ki barni cikin wannan bala'in? A tunaninki idan ni sun zo sun sameni auren naki zai tsira ne. Ki kamata mu kaita sai mu dawo mu ɗauki Nuratu itama”.
“Mama tayaya zamu iya? Ta yaya bayan kin san dai matar nan itama ba laifi ƙatuwa ce. Gwara-gwara ma Nuratun. Mafita ɗaya garemu kawai ki kira Aunty”.
“Baki da hankali Aunty kuma?”.
“To wlhy itace kaɗai mafitarmu, idan ba haka ba ni dai zan tafi gaskiya. Dan wlhy ina son mijina da ƴaƴana. Bazan so barin gidan nan ba, yo ko kishiya bana fata balle barin gidan kina dai ganin sun haɗa kai an aurama Fawzan ƴarsu shima Fadeel ɗin zasu iya yin haka”.
Ran Mama ya ɓaci amma sai ta danne. Da ƙyar ta iya lalubo number Auntyn su, cikin barci ta ɗaga wayar, roƙonta kawai Maman Saheeba ta shiga yi akan tazo sashen Ajwaad ta biyo ta kitchen akwai matsala.
“Sashen Ajwaad kuma? Ke kuwa miya kaiki sashen Ajwaad a wannan daren Nana?”.
“Bani kaɗai bace ba fa harda Aunty Kamila”.
Kamar dai Aunty bazata tanka ba sai kuma ta yanke wayar, ita kanta lokacin da take isowa falon saman abinda ya fara shiga kunnenta duk sai taji ta gigice. Ta ƙoƙarin juyawa Maman Saheeba daketa sheƙama Mamy ruwa taƙi ta farfaɗo ta riƙota. Cikin ɓacin rai Aunty ta zubama Maman Saheeba mari. “Ku daƙiƙan inane zakuzo ma yara sashe a irin wannan lokacin, ƙarfe biyu saura fa. Mike damunku ne? Kun haukace daga ke har Kamila ne”.
Duk da Maman Saheeba taji zafin marin nan matuƙa ta ce, “Ni dai dan ALLAH Aunty kiyi haƙuri, ko kamata mu fita da ita karma yaron nan ya fito ya gammu, ko wani a gidan nan ya fahimci muna nan. Nuratu ma tana a sama a sume”
Rasama abin cewa Aunty tayi, dan sai lokacin ta iya hango Saheeba dake wajen Nuratu ɗin a yanzu. A fusace ta ce, “Ai gara ma asan kuna nan ɗin, wannan ai jahilci ne da rashin sanin mutuncin kai, ya ALLAH na shiga uku na, wai mi kuke son ku zama ni kam Nana?”. Aunty ta faɗa tana nufar hanya, cike da magiya da roƙo Maman Saheeba ta kamota, Aunty ta watsa mata wani mugun kallo. Da ƙyar dai ta yarda suka kamata suka fita su ukun. Aunty taja ƙofar kitchen ɗin ta rufe. Sun zo kusan tsakkiyar gidan kawai sai sukai ido biyu da Abah. Gaba ɗaya rikicewa sukai, suka saki Mamy a ƙasa babu shiri. Aiko sai gashi ta farfaɗo, taja wani wahalallen numfashi, sai kuma ta fashe da kuka tana kiran, ta shiga uku.
“Shiga uku? Ai da sauran lokaci”.
Abah ya faɗa yana sakarma Maman Saheeba da Aunty wani murmushi ya juya zai bar wajen. Sarai kuma abinda ya faɗa a kunnen Mamy. Ai ko sai ƙirjinta ya shiga dukan dubu-dubu jikinta na rawa sosai gashi bata gani da ƙyau saboda jini daya ɓata mata fuska. Aunty kuwa cikin sauri ta ce, “Aban Fadeel wlhy ban san komai ba, yanzu suka kirani a waya ina barci ma”.
Juyowa Abah yay ya kalleta, sai kuma yayi murmushi kawai ya cigaba da tafiyarsa. Mamy da ke jin kamar zata sake suma muryarta na karkarwa ta ce, “Na shiga uku da gaske shine?”.
Banza Auntyn tai mata, dan harga ALLAH murmushin Abah ya matuƙar dakarta. Ita kanta Maman Nana jitai murmushi na girgiza mata zuciya, balle Saheeba da tun cin karo da Aban tai saurin juya baya dan ita ta fara sakin Mamy a ƙasa ma. A karo na biyu Mamy da jini ke rinjaya ta sake sume musu. Aunty da bata fatan bayan Abah wani ya sake zuwa ya gansu kuma, dan gara shi idan tai masa bayani maybe ya fahimceta a zafafe ta ce, “Sai ku kamata muje, kuma wlhy sai dai ku dawo ku ɗauki Nuratu”.
A wahale suka kaita sashenta, Haule da motsinsu ya sakata leƙowa ta bisu da kallon mamaki, ganin fa abun mai girma ne zaram ta fito. Gaba ɗaya sunma manta wacece ita sukace ta taimaka musu dan Mamyn ta musu nauyi sosai. Haka ta kama suka haura da ita sama. Suka shimfiɗeta a ƙasa, Aunty sai zagin Maman Saheeba take, ita kuma tanata rantse-rantse Mamy tace ta rakata zatama Ajwaad magana.
“Ai kin rakata, kunje kuma kun jiyo abinda kuke buƙatar ji, kun kuma samo sakamakon daya dace daku. Yanzu sai ku jira shima randa yaron zai san su wanene ku marasa hankali kawai tunda ubansa yau ya sani. Kuma sai dai ku koma ku ɗakko Nuratu wlhy bazan koma ba”. Daga haka ta jawo kwalin tissue dake a table ta fara goge ma Mamy jinin daya wanke mata fuska har ya fara jiƙa gaban rigarta. Ashe rauni taji a goshi da haɓarta sai gefen idon dama. Haule ta aika ta kawo mata first ald box tai mata ɗan abinda zata iya ta saka mata audiga da bandage dan a samu jinin ya tsaya kafin dai safiya...
Dai-dai nan su Saheeba suka dawo ɗauke da Nuratu, a falo suka ci karo da wata cousin sister ɗinsu Mamy. Motse-motse ya sata fitowa. Da mamaki take duban Maman Saheeba da Saheebar sai Haule data fito da kayan da aka gama gogema Mamy jini. Sai kuma ta kalla wanda suka ɗako da alamu suka nuna kamar bata numfashi.
“Subahanallahi. Nuratu kuma? Nana daga ina haka?”.
Hawaye Maman Saheeba ta share, tana kaiwa zaune kusa da Nuratu da suka shinfiɗar anan falon, zatai magana caraf Saheeba ta karɓe. “Aunty Mariya yanzu drivern gidansu ya kawota, wai ta matsa ya kawota nan shine ta suma a hanya. To ya kirani a waya da wayarta na fito sai ga Mama itama shine muka shigo da ita”.
Matar da yake akwai kwakwazo ta ce, “Innalillahi... Amma miyasa Hajiya Turai zata barta ta fito a wannan tsohon daren? Koda motar gida ce ai akwai haɗari. Haule kawo ruwa”.
Da sauri Haule ta wuce kitchen, babu jimawa ta dawo da gorar ruwa masu sanyi a hannu. Saheeba ce ta amsa ta shafama Nuratu. Amma ko gezau, sai da Aunty Mariya nan ta bata shawarar a watsa mata da ƙarfi sannan Saheeba ta zuba da yawa a hannun ta ta watsa mata. Aiko wani irin nannauyan numfashi ta ja mai ƙarfi sai kuma ta sake komawa lagaf. Hankalinsu ne ya ƙara tashi. Saheeba ta ce, “Kodai za'a duba Rafeeq ne”.
Da sauri Mamansu dake sharar hawaye ta ce, “ALLAH ya kiyaye, jini Fateema bazai taɓa min yarinya ba wlhy”.
Rasama abin faɗa kowa yayi suka sake watsa mata ruwan mai yawa sai gashi ta sake farfaɗowa. Kuka ta fashe da shi tana wani irin zaburowa zata tashi Maman ta maidata, zatai magana nan ma ta rufe mata baki. “Basai kince komai ba dan ALLAH Nuratu, kiyi shiru baki da lafiya”. Kuka ta sake fashe wa da shi mai ƙarfi, wannan kuka ne ya farkar da mutane da yawa duk suka shiga fitowa suma. Nan fa aka zagaye Nuratu.
Caraf wata dattijuwar mata ta ce, “Kai yarinyar nan ba lafiya ba tanada iska.” ai jin wannan batu sai su Maman Saheeba suka laƙe, nan fa kowa ya shiga mata tofi, wani ma babu abinda yake karantawa motsa bakin kawai yake yi ya tofa yawu hankalinsa kwance🤣.........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖7️⃣6️⃣
______________
.........Ganin hankalinsu ya raja'a akan Nuratu Haule ta zame jikinta ta fita. Ƙasan bene ta maƙale tai kiran Sille. Bugu biyu ya ɗauka, yanda taji muryarsa kuma ya tabbatar mata da wata macen yake tare. Kishi ne ya turnuƙeta, amma tasan ko giyar wake tasha bata isa yin magana ba, kaɗan daga aikinsa yasa taje har gida yay mata dukan tsiya. Sai kawai ta fara masa bayani cikin rawar murya..
“Dear ya kamata ka baro Lagos ɗin nan tunda ka gama aikin daya kaika ka dawo Abuja, dan abubuwa nata faruwa. Kaga dai anci biki an gama yau ango ya shiga ɗaki ga Nuratu can taje ta jiyoma kanta abinda ya dame ta. Hakama Hajiya Kamila kaca-kaca suka shigo da ita cikin jini, ban sani ba ko itama daga sashen AA ɗin ne oho. Dan Mamar Saheeba da Saheebar sun kima ƙarya.
“Naji”.
Ya faɗa a taƙaice yana wani shiii da baki na iskanci ya yanke wayar. Duƙewa Haule tai a wajan ta sanya kuka......
__________★
Iskar sanyin asuba ce ta farfaɗo da AA, dan yana kaiwa border shima ya sume. A hankali ya shiga buɗe idanunsa da suka masa wani irin nauyi na masifa. Bishi-bishi ya ke kallon Maanal, sai kuma a hankali ta fito masa a cikin ido. Gabansa ne ya faɗi, ya zabura duk da bashi da wani ƙarfi ya matsa daga jikinta. Hannu ya kai ya kunna lamp ɗin dake side drawer, kafin ya kai yatsarsa sai tin hancinta amma babu numfashi, zuciyarsa ta shiga tsitstsinkewa da rarrabewa, gefen wuyanta ya maida ya taɓa jijiyar wajan, nan ma babu motsi. Ji yay kamar shima zai ƙara sumewa. Sai ya ɗora kunensa a saitin zuciyarta... Bugun da tashi zuciyar take ai tamkar zata faso ƙirjinta ta fito a yanzu. A karo na farko ya yunƙura zai tashi, amma hakan ya gagara saboda wani irin ɗaurewa tamau da cikinsa yay masa. Ga jiri yana ji ga ciwon kai mai tsannanin gaske da bai taɓa fuskanta a rayuwarsa ba. Kan ya dafe da hannu ɗaya, ɗayan na riƙe da cikinsa. Ba irin ciwon cikin jiya bane ba, yanzu ji yake tamkar an ajiye masa dutse ne. Sai da yaja fin minti biyu kafin ya sake yinƙurawa cike da ƙarfin hali da jarumta. Aiko ji yay kamar ya fasa ihu dan azaba, amma ina bazai iya zama yana kallon Maanal a haka ba. Da ƙyar ya miƙe a galabaice ya nufi bayi, ruwa masu zafi ya daidaita ya sakarma kansa na shower. Yafi mintuna biyar a haka sannan yay wanka yay na tsarki cikin ƙarfin hali ya fito yana dafe da cikin nasa, dan ko iya miƙewa da ƙyau baya yi ma. Ga idanunsa kamar zasu faɗo idan ya buɗe saboda ciwon kai. Bashi da kaya a ɗakin, sai dai in wanda ya cire zai maida. Ba kuma zai iya haka ba. Haka ya daure ya fita cikin haɗa hanya ya koma ɗakinsa, jallabiya kawai ya ɗakko ya dawo. Yana ƙoƙarin zama dan ya ɗago Maanal duk da shi yasan da wahala ya iya hakan saboda cikinsa yaga wayarsa na haske. Kamar zai share sai kuma ya tuna Rafeeq yace zai kirashi da asuba. Da ƙyar ya iya kai hannu ya ɗauka, Rafeeq ɗin ne kuwa. Ɗagawa yay batare da yay magana ba, daga can RK ya ce, “Ajwaad!”.
Ƙasa magana AA yayi, sai da ƙyar ya ce, “Uhmm”.
“Babu dai wata matsala ko?”.
Nan ma ya daɗe kafin ya iya furta, “Akwai, bata numfashi sam. Nima kaina da cikina na ciw....”
Ya kasa ƙarasawa saboda kansa dake kamar ana bugawa da wani ƙarfe.
“Wannan sakamakon dama shi nake tsoratar maka tun jiya. Yanzu dai bara muyi salla gani nan zuwa gidan”.
“Uhmm”.
Kawai yace ya kife wayar batare daya yanke kiran ba, sai RK ɗinne ya yanke daga can. Duk yanda yake tunanin taimakawa Maanal bazai iya ba, ga salla ana ƙoƙarin shiga. Kuma har cikin ransa bazai iya kiran kowa ba. Dama ace cikin ƴan uwanta akwai wani ko Amaal zai iya sawa tazo ta taimaka mata. Baya son wasa da salla, dan haka ya tashi ya gabatar da ita a zaune. Yana zaune ya jingina da gadon idanunsa a lumshe sai dai bai rufesu ba duka yana ɗan kallon Maanal kiran RK ya sake shigowa wayar. Hannu kawai ya kai ya ɗauka, yana ɗagawa RK ya ce, “Zaka iya buɗe ƙofar?”.
“Ko sakkowa bazan iya ba”.
“Okay ina zuwa, bari na samo keys wajen Aunty. Ka ɗan daure kaɗan saka mata kaya masu kauri, dan zamu shigo ne koda Aunty haka”.
“No! Rafeeq kar kai min haka Please ”.
“Dole ne ayi hakan Ajwaad, dole ne laifin da kowa ke kallonka da shi na tsawon shekaru ya shafe a yau....”
Kafin AA ɗin ya sake magana ma RK ya yanke wayar. Idanunsa ya lumshe tare da cije lips da ƙarfi. Fahimtar babu wani isasshen lokaci ya sashi mikewa cike da ƙarfin hali, closet ɗinta ya nufa,