Showing 195001 words to 198000 words out of 218311 words
Chapter 66 - AJIYA A DUHU BOOK 2 By Billyn Abdull.txt
ita balle ma Ammie da bata saka rai ba. Sai ko Yazeed ya zabura ya biyota yana kira kamar zai faɗi dan sauri. Hawaye suka zuboma Ammie. Daddy kam sai ya ma kauda kansa gefe.
Ƙannensa da komai ka faruwa akan idonsu cike da baƙin ciki suka nufi sashen su suka sanar ma Hajiya Yaya. Aiko sai gata ta fito kamar zata tashi sama. Kai tsaye sashen Yazeed ɗin ta nufa, tana tura ƙofar kuwa ta buɗe. Ta wani bugata da iya ƙarfinta ta shiga falon. Turus taja ta tsaya hakama ƴaƴanta da suka biyota ganin Yazeed durƙushe a ƙasa yayi kneeling yana bama Nazeefa da tai wani zaman ƙasaita haƙuri. Itako sai danna waya take tana taunar cingum kamar ma bata san da shi ba. Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un.
Sarai Nazeefa taji shigowarsu amma sai ta watsar da su kamar bataji ba, sai ma cike da rashin mutunci ta dakama Yazeed tsawa. “Dalla malam yimin shiru, shashasha kawai dabai san ciwon kansa ba. Kai ko kunya bakaji ba zagam-zagam ka tafi gaida ubanka sai kace wani uban kirki. To wlhy ka jama kanka yau sai kaji a jikinka a gidan nan. Dalla tashi ka mana shara kana ganin waje duk datti”.
Jiki Yazeed har rawa yake ya miƙe kuwa. Ko kallon su Hajiya Yaya baiyi ba ya nufi inda suke ajiye kayan shara ya ɗibo...........✍️
Tofa Hajiya Yaya da alama anzo dai-dai wajen🥱.
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖9️⃣6️⃣
______________
.......Muryar Hajiya Yaya na rawa ta ce, “Yazeed!”.
Yanzun ma baiko kalleta ba sharar sa ya fara ma. Ta ƙara kiranshi cikin tsawa. Ko gezau baiyi ba. Dariya Nazeefa ta shiga tuntsurawa. Sai kuma ta wani miƙe cike da gadara da raini taje gaban Hajiya Yaya ta tsaya, kallon sama da ƙasa tai mata fuskarta da murmushin ƙularwa ta ce,. “Kima daina wahal da kanki, dan in dutsen arfa zaki hau kiyi ihu bazai taɓa ya jiki ba. Dan yanzu shi ɗin ba naki bane, nawa ne nan, dama kin rainar min shine Hajiya Sadiyya”.
Ta kira ainahin sunan Hajiya Yaya.
Hannu Hajiya Yaya data gama kaiwa wuya ta ɗaga ta ɗauke fuskar Nazeefa da mari. Marin daya farfaɗo da sauran ƴaƴanta da sukai sumar tsaye tunda akace yayansu yay shara. Gigitaccen ihu Nazeefa ta fasa da kiran sunan Yazeed. Bawan ALLAH tamkar ƙyaftawar ido har yazo inda suke. Yay ƙoƙarin kama Nazeefa yana tambayar miya sameta? Hankaɗashi tai baya ya tafi taga-taga zai faɗi saboda a bazata ta turesan. Ta kallesa hannunta riƙe da kuncinta ɗayan ta nuna Hajiya Yaya da yatsarta manuniya. “Wannan jakar ce ta mareni, kuma wlhy idan baka rama min ba sai na tafi gidanmu yau....”
Ai baki ma Nazeefa bata gama rufewa ba Yazeed ya zabura tare da ɗaga hannu zai sauke ma Hajiya Yaya a fuska. Ammie da ihun Nazeefa ya sata nufo sashen saboda sashen su Yazeed ɗin shine kusa da nata, duk tana iya jiyo hayaniyar tasu caraf ta riƙe hannun Yazeed ɗin. ALLAH sarki Hajiya Yaya harta rufe idanu tana jiran saukar marin ɗanta a fuskarta😥. Abinda zai baka mamaki suma sauran yaran kowa ya kasa yunƙurin komai sai idanu kawai suka rufe dan suma su Sabuwa ba ƙyalesu sukai ba😂👍.
Kai Ammie ta shiga girgiza masa hawaye cike da idannunta. Muryarta na rawa ta ce, “Karka sake ka taɓa wannan gangancin Yazeed. Komu da muke matan uba bama fatan ALLAH ya jarabceka da aikata hakan a kammu balle ita. Yazeed bakai data haifa ba, ko mu da muke ƙarƙashin miji ɗaya bazamu so taɓa kwatanta haka ba gareta kodan shekarun da ALLAH ya bata a kanmu. Haba Yazeed Mamma ce fa...”
ALLAH sarki, a mamakin kowa sai Yazeed ya risinar da kansa a hankali. Itama Ammie sai ta sakar masa hannunsa. Sum-sum ya wuce yabar wajen kansa a ƙasa ya koma ya ɗauka tsintsiyar daya yarda ya cigaba da shararsa. Ko kaɗan ba haka Basariyya dake laɓe jikin window tana leƙe taso ba. Sai taji wani irin haushi da takaicin Ammie ya sake kamata. Cikin ƙus-ƙus tace, ‘Munafuka ta hanamu kallon show. Ai mu irin wannan wasan muke so’.
Ko kallon Nazeefa dake cika tana batsewa Ammie batai ba. Sai ma hannun Hajiya Yaya ta kama. Cike da lallashi da kwantar da hankali ta ce, “Yaya kiyi haƙuri muje”.
ALLAH sarki rayuwa, Hajiya Yaya ko musu bataima Ammie ba. Ta sake kallon inda taga Hajiya Basariyya dake laɓe tun ɗazun ta janye idanun ta dake cike da hawaye. Suma yaran Ammie tace, “Ku wuce muje”. Suma babu wanda yay musu. Har falo Ammie takai Hajiya Yaya, ta taimaka mata ta zauna sannan ta dubi yaran ta ce, “Ku bani ruwa mai sanyi”.
Amrah ce dake hawaye taje ta ɗauka mata. Koda ta kawo Ammie ta buɗe ruwan Hajiya Yaya ta ba, nanma bata musa ba ta amsa ta sha, dan ji take tamkar zuciyarta zata fashe mata a cikin ƙirji. Sosai tasha ruwan, dan ɗan kaɗan ta rage. Kamar dama ruwan take jira tasha kawai ta saki kuka. Yaran duk sunyo kanta a zabure zasuyi magana Ammie tai musu alamar suyi shiru. Duk komawa sukai suka zauna, sai da Hajiya Yaya tai kuka sosai sannan Ammie ta ciri tissue ta bata ta kuma sake bata ruwan tasha. Bayan wasu mintuna ta sake natsawa Ammie ta fuskanceta.
“Yaya kuka ba shine mafita ba, na barki kiyisa ne dan ki samu nauyin zuciyarki ya ragu. Kiyi haƙuri idan na shiga hurumin daba nawa ba. Amma Yazeed ba kuka ko biyema yarinyar nan ai rikici al'amarinsu ke buƙata ba. Hasalima ɗauke idanu daga garesu shine yafi alkairi, idan ba haka ba komai zai iya faruwa, saboda Yazeed baya a cikin hayyacinsa gaba ɗaya. Yanzu shi yana a wani matsayine da baya banbance fari da baƙi sai wanda yarinyar nan ta nuna masa kawai. To idan muka ce ta ƙarfin tsiya zamu sakashi ya gane akwai babban matsala, dan maimakon ya gane ɗin sai ya sake rikice mana ne kawai, idanunsa su sake makancewa daga ganinmu. Dan haka dole zamuyi haƙuri da kauda kai na wani ɗan lokaci, mu shanye zafi da radaɗin da muke ji akan wannan sabon yanayin nashi tunda mun san bayin kansa bane. Ita kanta yarinyar mu barta ta rinƙa jin tamakar ta gama samun dukkan nasarar da take buƙata sai mu samu damar gayama ALLAH damuwar ya warware mana ita cikin sauƙi kuma. Amma tankawa da nuna damuwar kai tsaye a yanzu tamkar sake zaburar da ita ne ta cigaba da sabon shiri a kansa, shi kuma dama illar sihiri ɗaura wani aikin akan wani, yakan sa asha wahala sosai kafin a raba mutum da shi. Wannan shine mataki na farko da zai taimaka mana. Mataki na biyu addu'a, Yaya Addu'a Yazeed yake buƙata daga garemu baki ɗaya. Kuma taki ita ce mafi ƙololuwar daraja a gareshi, itace kuma tamkar yankan wuƙa. Kasancewar ta a hakan kuma bazai samu ba sai kin daure kin sanyaya zuciyarki, kin yafe ma Yazeed kurakuransa. Ki rage barci, ki tashi cikin dare ki gayama ALLAH damuwar ki masa kuka ki masa bagiya shi mai ji ne mai gani, kuma shine ke raba abinda duk duniya babu mai kwatantawa. Yaya da zakiji wahalhalun da na fuskanta a rayuwata data zuri'ata da kince wannan na Yazeed ba komai bane ba. Amma wlhy ban taɓa zuwa gaban wani na duƙa nace ya taimakeni da garin magani ba. UBANGIJINA na fuskanta, shi kaɗai na amince zai yaye min damuwar da ƙuncin. Na ajiye maganar barci gefe, na sadaukar da rabin nema na a sadaƙa, na maida harshena da laɓɓana a ambaton UBANGIJI ne a koda yaushe. Na rungumi ƙishirwa da yunwa a kowane yini. Na sakama zuciyata jarumta da tunatar da kaina akwai fa wanda suka fini shiga ƙuncin rayuwar, akwai wanda idan zanga halin da suke a ciki nawa ba komai bane ba. Na dinga tuna ANNABAWAN ALLAH ma an jarabcesu. SAHABBAN MANZON ALLAH sun sha gwagwarmaya da jarabawoyi kala-kala. Amma da sukai haƙuri wace irin riba ce basu samu ba. Ƙarshen dai wahala da faɗi tashin bawa shine ya samu makoma mai ƙyau ta aljanna. To su tun ma suna duniya akama mafiya yawansu albishir da aljannar, sakamakon ayyukansu na alkairi da sadaukarwar yaƙi a bayan MANZON ALLAH. Wannan abubuwan sun ƙarfafani matuƙa, na kuma saka yarana suma suka dage, dan nasan yanda tasirin addu'ar uwa take akan ɗa haka addu'ar yara nada tasiri matuƙa. Dan haka Yaya ki jure, ki gwada ki gani in sha ALLAHU zakiyi dariya nan bada jimawa ba, al'amarin Yazeed zai zama tamkar labari ne. Muma kuma ba zama zamuyi ba in sha ALLAHU. ALLAH ya baki haƙuri ya sanyaya ranki.” ta juya ga yaran suma da duk suka nutsu suna saurarenta.
“Kuma ina muku nasiha da ku kauda kanku akan al'amarin Yayanku, komi zaku gani tsakaninsa da matarsa dan ALLAH ku daina zuwa kuna faɗawa mahaifiyarku. Ba wannan Yazeed ke buƙata ba, addu'a yake buƙata, idan ba haka ba maimakon mu tsamoshi a wannan masifar sai dai mu sake bada hanyar sakashi a cikin wani. Kunga dai abinda yaso faruwa. Da taci nasara ya mari mahaifiyarku kunga ya sake shiga wata masifar ne ai ko. Ku kwantar da hankalinku mu haɗu mu tayashi da addu'a, sadaka, komai zai wuce”.
Daga haka Ammie ta miƙe abinta. Harta kusa kaiwa ƙofa Amrah dake kuka sosai ta ce, “Ammie!”.
Tsayawa Ammie tayi, tare da juyowa tana kallon ta, sai kawai Amrah ta taso da gudu ta rungumeta tana sake fashewa da kuka da faɗin, “Mun gode Ammie, mun gode, in sha ALLAHU ke ƴar aljanna ce. Dama nace ke mai ƙaunarmu ce da zuciya ɗaya amma ba'a fahimtata.....”
Murmushi Ammie tayi, tare da ɗagota, cikin katseta ta ce, “Amrah ya isa haka kinji, mu dukanmu in sha ALLAHU ƴan aljanna ne. Kuma ba fahimtarki ne ba'ayi ba. Kowace rayuwa da nata ƙalubale ne kinji”.
Amrah zata sake magana Ammie ta hanata, sai ma share mata hawaye datai tas sannan ta maidata ta zaunar ta fice...
★Baki Hajiya Basariyya ta ƙyaɓe. Tare da faɗin, “Kai wannan kilakakkiyar mata anyi munafuka. Ita adole gata ALLAH. Yannn! yannnn! yannnn! Tana wani zabga wa'azi. Sai dai kuma a gayama wasu amma wlhy bamu ba. Ubanwa ye zai yarda wani kin tsaya a addu'a ne da azumi da mima tace. Waye wawa an gama tsaface mana miji, da samarin ƴaƴanmu sun aure ƴaƴanki”.
Haka dai ta gama surutanta sai kuma ta gyara yanayinta ta nufi cikin falon Hajiya Yayan a ɗan rikice. Har wani neman yin tuntuɓe take zata faɗi. Tadai dafe kujera tana kaiwa zaune kusa da kujerar da Hajiya Yaya ke zaune. Sudai kallonta suke kawai. Cike da makirci ta fara faɗin, “Mun shiga uku, ina wanka yanzu Jannah ke sanar min abinda ke faruwa. Kai wannan yarinya anyi ibilishiya, ita yanzu dan bata da mutunci sai ta saka Yazeed ya mareki, kai ALLAH wadan naka dai ya lalace. Amma gaskiya dai ya kamata a kira Sabuwa a gaya mata wannan ɗanyan aiki tazo tai mata faɗa dan ba halin arziƙi bane ba. Yanzu haka ƙawayen banza ne suka ɗorata a wannan hanyar mara ɓullewa. Yo mara ɓullewa mana kasa ɗa ya mari suruka ina arziƙi. Ita bata tunanin zata haifa tunda ga cikin nan a gabanta itama za'ai mata wataran. Ai ni yaran nan baku ƙyauta min ba da baku haɗu kun lakaɗama shegiya duka ba, har sauran ƴan uwanku duk basai ku kira ba damu mu haɗu mu ci ubanta ai daɗi gidan yawan kenan dama ko”.
Amrah da surutun ke ƙonama zuciya ta ce, “Ai hakan baida amfani Ummi. ALLAH kawai ya shiryeta. Jarabawace watarana sai labari.”
Kasare Hajiya Basariyya tai tana kallonta, ta zata wani zai sake magana ta samu point, sai taga kowa bai tanka ba. Hajiya Yaya ma miƙewa tai abinta ta nufi bedroom. Sai suma yaran suka fara miƙewa.. ganin fa zataji kunya sai itama ta miƙe tana faɗin, “To ALLAH dai ya ƙyauta. ALLAH kuma ya kiyaye gaba iyakarta kenan”. Daga haka ta fito tana tsine musu a zuciya. Ganin nan babu nasara sai ta nufi sashen Ammie, Sakina da Waleed kawai ta samu, sukace mata Ammie na sashen Daddy. Nan ma ta fito cike da baƙin ciki, amma sai itama ta nufi sashen Daddy ɗin duk da kuwa ɗazun taje ya korota..........✍️
🤣Itafa Hajiya Basariyya tafi dacewa da haihuwar Saheeba. Kai ALLAH ya rabamu da munafunci gaskiya☹️.
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖9️⃣7️⃣
______________
.........Maanal na kwance barcin wuya ya ɗauketa dan oga da kansa ne ya gama wajigata. Itako sarkin raki tasha kuka har ta godema ALLAH. Sam ta kasa sabawa, gabanta har faɗuwa yake ya nuna buƙatarsa a gareta. Zata biye masa a shan minti amma da anzo fagen fama ta fara kuka da roƙo. Shi ko ya zama kurma ya zama makaho har sai ya samu yanda yake so dan bai san ɗanɗani haukaci ba bai kuma san haƙuri ba. Kwana biyun nan har ƴar rama ta fara. Ko kuma ta gudu sashen Oum sai yata zarya ko Oum ɗin ta korosu sannan. Gaba ɗaya ta ƙagara weekend ɗin nan ta ƙare, idan aka koma aiki ta samu sauƙinsa ai tunda da rana babu dama.
Oum data fahimci matsalar Maanal dan ramar da yarinyar ta fara ta fara tsaya mata a rai sai ta shiga haɗa abubuwa, ta kuma amso wasu hannun Hajiya Shuwa. Itama ta fuskanci irin wannan yanayin a hannun Abah, dan shima akwai fitina kamar AA ɗin, kai bama su kaɗai ba kusan duk mazan family ɗin Darma haka suke sai dai wani yafi wani. Gasu kuma ALLAH ya jarabcesu da son zama da mata ɗai-ɗai, shiyasa matan ke jigatuwa a hannunsu kafin su saba..
Kiran da Oum tama Maanal ɗin a waya ne ya farkar da ita, dan AA ya fita shi da Yaya Fawzan shiyyasa sai ita kaɗai. Muryarta kawai Oum ɗin taji ta fahimci mike faruwa. Dan dama tana anan sashen suna hirarsu AA yay kiranta a waya ta kawo masa wai fruits dan shi yana sashen Abah suna meeting shi da su babban Yaya. To daga kai fruits ɗin ne fa ya samu ya matseta a sashen sai da ya sauke damuwarsa sannan yay shirin fita da zasuyi da Yaya Fawzan ɗin. Ita kuma wahala ta hanata tashi dan barci ne ya ɗauketa sama-sama ma taji fitarsa. Cike da tausayi Oum ta girgiza kai, sai kuma ta ce, “Barcin yamma kike Baby?”.
Cikin sanyin murya Maanal ta ce, “Eh Oum, amma na ma tashi gani nan zuwa sashen.”
“Okay sai kinzo”.
Oum ta faɗa tana yanke kiran. Itama Maanal tashi tai ta shiga bayi ta gyara jikinta yanda ya kamata, koda ta fito gashinta ta busar ta shirya cikin atamfa doguwar riga tai sallar la'asar da ake kira sannan ta gyara gadon da suka yamutsa ta fita. Ta nufi sashen Oum motar Momyn Nibras ke shigowa gidan. Maanal bata tsaya ba tai shigewarta, dan yanzu kusan kullum Momyn Nibras ɗin sai tazo gidan. Jiya da yamma har sabuwar rigima suka tafka da Mamy.
Wani haɗaɗɗen gashin nama mai ruwa-ruwa Oum ta bama Manaal taci ta ƙoshi, sannan ta bata abubuwa na musamman data haɗasu da kanta kuma ita tasan sirrinsu dan sune take amfani da su. Har sai da Maanal taji kamar zatai amai sannan ta ƙyaleta. Daga haka suka cigaba da hirarsu. Su AA basu dawo gidan ba sai bayan sallar isha'i. Anan suka yada zango sashen Oum sukai dinner aka ɗora da hira, hirar gaba ɗaya akan yanda bikin Fawzan zata kasance ne dan shi aka fara shirye-shirye, amma suna saka rana a haɗa dana Babban Yaya, sai dai ba'a yanke hukunci ba sai gobe idan ALLAH ya kaimu su Baba Sardauna zasuje Katsina domin ganawa da dangin mahaifin su Ameerah.
Koda AA yace Maanal tazo su tafi catai ita anan zata kwana. Shiru kawai yay yana kallon ta, Oum kuma taƙi saka musu baki. Yanda AA ya tsaya yana kallonta mi Yaya Fawzan zai yi inba dariya ba. Harda ƴar waƙarsa ta neman tsokana. Aiko AA ya wuce ya tafi kawai ransa a ɓace. Babban Yaya daya bisa da kallon ƙasan ido ya ɗan murmusa a zuciyarsa. A zahiri kam fuskarsa babu alamar wasa ya kalla Maanal da itama ta kumbura baki ta kwanta a cikin kujera. A dake yace, “Lilly!”.