Showing 201001 words to 204000 words out of 218311 words
Chapter 68 - AJIYA A DUHU BOOK 2 By Billyn Abdull.txt
a tsakanin nan. Ita kanta Maanal yau gaba ɗaya bata huta ba. Sun shiga meeting har sau kusan huɗu kafin break. Sun fito na ƙarshe ne lokacin salla yayi, AA yaja ra'ayinta suka je office ɗinsa sukai alwala. Sannan suka fito zuwa yin salla. Ana idarwa suka dawo, a hanya ne suka haɗu da CFO. Sai tai saurin ɗauke kai kamar bata gansu ba. Murmushi Maanal tayi a ranta tace (ƙyaji da shi dai) a fili kam yitai kamar bata ganta ba. Dan taga dama wani ɗacin rai da take a wajen meeting. Shi kam AA baima ɗauka abinda CFO ɗin keyi a komai ba. Dan yanda ta iya takunta yasa bai wani fahimci take-takenta ba har yanzu. A office ɗinsa sukai zaman cin abincin data shiryo musu sukazo da shi. Suna nishaɗinsu da soyayyarsu. Bayan sun kammala Maanal ɗin ya haɗe komai waje guda ta koma nata office ɗin. Bata wani jima da zama ba suka sake fita yin meeting, sai dai yanzu babu AA yana ganawa da baƙi, AS ne ya zauna a madadinsa. Meeting ɗin ya jasu lokaci mai tsayi kafin su fito. Dan lokacin ma la'asar tayi........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖9️⃣9️⃣
______________
🥱🥱 Nace ba, na fara saida GUMAMA ta yara data manya mai so yayi magana kafin ta ƙare. Dan na sakata a farashi mai RAHUSA da ARHA, karku damu tana ƙamshi yanda ya kamata😆🤌.
Hhhhh Haba hajjaju ya da fara maida murtanin faɗa bayan WASAN bama a farashi ba. Banning number Bilyn Abdull tamkar an kashe MACIJI ne ba'a sare kansa ba wlhy😂. Dan ko mutuwa Bilyn Abdull tai in sha ALLAHU ina ji a raina zan cigaba da zama a zukatan masoyana zasuna min addu'ar kwanciya lafiya a kabari. Karki kuskura kice zakiyi wannan wasan, dan wlhy mamaki zan baki keda ƴan jagaliyar taki. Ke reporting kika sa akayi a WhatsApp ni kuma dare zan raba ina reporting naki ga babban sarki. Kinga maimakon Banning a WhatsApp ke a media ɗin gaba ɗaya ma UBANGIJINA zai yi banning ɗinki, (Wayaga ruwa zai ƙarema ɗan kada, dama kuma da ruwan muka dogara😜😆🤭).
Wannan Bilkisun da kike ganinta ba ƙyalan bace ƙyalle ce, kawai kafin mu sara ne mu sai mun dubi bakin gatari ALLAH wlhy. Ina ƙara baki shawara karki ce zaki saka Game dani akwai damuwa, ubana har ya rasu albarka yake zuba min, uwata kullum sai tace ALLAH yay miki albarka Bilkisu dan dattijuwar ƙwarai ta kullum goshinta na bisa ƙasa tanama UBANGIJI Sujuda. Mijina kam ai duk motsinsa sai ya ce Bilyn Abdull ALLAH yasa ki gama da duniya lafiya, yo an gaya miki a banza nake ɗaɗara shi a littafin🤪, gata yake bani iya gata, tsaro iya tsaro, naci shinkafa na kora da ruwan fanfo ga windows ɗin gidana iska tako ina ko ba'a bamu wutar nepa ba bana damuwa. Idan zai fita yanda nake masa addu'a haka yake min shima kaga shalelen Bilyn sa ALLAH yasa muna jone har a aljanna🤏🥰.
To Ladidi banda kankamba😲 ke wacece da kike tunanin zaki nuna min yatsa ban karya shi ba🤣 ina da waɗan nan ƙafofin murhun uku na haye kansu na zauna matsayin tukunya na dafa duk kalar ruwan dana gadama TSAYAWAR ALLAH kenan. To gaskiya ina baki shawara, kawai dai ki daurewa zuciyarki abar kaza cikin gashinta, dan in akace figeta za'ayi wallahi jikinta zai koma ne kamar na BALBELA. Shegen tsuntsu kenan ƙyau iya ƙyau a waje ciki kam ba'a cewa komai. WAJENJI FARI CIKINKI BAƘI KENAN😂.
Nifa a duniya cakwakiya na birgeni kwarai-kwarai da gaske kun ganni nan, ALLAH birgeni take😆, idan akai wasa ana gama AJIYA A DUHU zan saki sabon Update na zazzafan littafi mai suna Ladidi a harhaɗa🤣, alƙalami ɗan albarka, kun san yafi takobi kaifi, balle na Bilyn Abdull har ƴan a leƙa katanga zanowa yake, gashi baya yafiya dalla-dalla yake cika aikinsa🤫.
Bari dai nayi shiru, tsiyar Mamy ma ta ishi al'ummata, ita kuma Sille ya isheta😂, wayaga AJIYA A DUHU.
Kai idan akace ƴar baka za'ai na rantse akku zan koma muku ALLAH dai ya ƙyauta ba shekarar zazzaga bace ta kama😆, dan wata tabarmar idan aka zazzageta babu mai sake ɗora ɗuwawunsa akai saboda ƙazantar da aka zubar a bisanta.
Kudai kuyita salati ƴan uwa karna zare a maimakon labarin na koma muku tatsuniyar gizo-gizo. Dan labarin ƙoƙi dai baya wuce na gizon Update iya Update 😎.
🤔To Kuma su Haƙilah a dai kiyaye dan mun jima da sanin suna kuma mun san numbers, yanzu komai mai sauƙi ne a buga maka sallama a ƙofar gida daga ƴar jagaliyar media ki jawa kanki ai miki tonon leƙa katanga a gaban Rijalu da matan anguwa, ya barki a gida da tunanin ya killaceki ƙarƙashin igiya uku a kira shi ace kina ofishin ƴan doka. Banu taci ƴan a ara a yafa kenan, bamu san tushe ba amma muna rawar takaɗiɗi akan nera biyar-biyar😂. Tab ɗin wayaga goge hadda, kajawa kanka daga karanta HIKAYIYIN su Bilyn Abdull a tuɓale ƴar igiyar auren😮💨 dama lamarin rijalu yanzu ana basu wuta a sama suna bama Nisa'u a cikin gida, yana ƙaraki gaba wlhy galleliya zai santalo, idan dama kuma kina da abokiyar burmi a cikin gidan shike nan ya samu filin shakatawa, yo kunga laifinsa ne, koni na auri mace ta zama ƴar ARE-ARE (Gayyar SHANU) a media walle na kamata zanen yarbawa zan mata a uwawu😌 kafin na saita miki hanya zuwa gidan tsoho.🥳
To kama kanki wannan kokawar ta GIWAYE ce, ke kunama daga neman suna ko na gwajin harbi karki jama kanki ƙafa ta takeki batare da ansan da ke a cikin ƘURAR YAƘIN ba. Idan kunne yaji jiki ya tsira. 👉🙆👈
Dan ni idan na tashi bada gumamar kaya idan ta kama har ZINARI haɗawa nake a ciki🤪😂, yo miye amfaninsa ALLAH na tuba, ƙaryar banzar da wal-wal a kan wuya baya fansata ga walakirin kabari🥱. Oh oh faɗan matsoraci wai wasan sunƙuru, idan mace takai mace ta fito a bamu fili dan ALLAH, Bilyn ce fa, jinin Kanawan dabo da katsinawan dikko kunya gareku badai TSORO ba. Idan kin yarda mu fara wannan game ɗin dan GIRMAN ALLAH gobe naga raddi😏👈 .
Nawa ki ɗaukesa kamar na taba kasa ne na lashi miyau tushen faɗan yara kenan😂, koda yake muma yaran ne bamu wuce ehhhhhhhhh😉 ba, kun dai gane mutane na🤪😂.
LADIDI BISMILLAH🙄🤌 zamu iya fara wasan, ni banda matsala ko ina typing ɗin zan iya😂, yo wani abune ina gama muku posting na koma filin yaƙi💪, kafin safiya nasan koda na ciyo wuya da DUKA wajen zai huce🤣 sai a cigaba da gashi zuwa yammar washe gari a koma filin dagar, wayaga faɗan Kurame, ta AA Darma zan koma, KURMA kuma MAKAHO😆😆🤣Ladiyos bismilla👆🏻😒😣☹️😔🥶🥱🥱🥱.
Kar wanda yace Bilyn yaya akayi, shi saƙon yasan inda aka aika shi😆, waɗanda zasu ƙarɓi saƙon suma sun san nasu ne🥱. Idan kuna son kallo ku jira a maido min raddi ai kune ƴan rakkiyata faɗan🤣🤣👍.
Ina sonki masoyana, ALLAH wlhy sai da ku na Bilyn Abdull, Zafafa family na miƙo muku gaisuwa irin ta girma da mutuntawa❤️❤️❤️❤️🥰🥰🥰🥰😘👏🏻
Bala'i page guda ya tafi a banza Ni balki kumuje jan labari, gulmar ta isa haka dare ya fara yi kuma.😩🏃
____________
......Anan Kaduna kam da ƙyar Ammie ta shawo kan Daddy ya yarda da batun sakawa aima Yazeed addu'a a islamiyyu. Amma da farko yace ta barshi uwar tasa ta ƙara ji a jikinta. Ammie taita masa magiya da nuna masa ba Hajiya Yaya za'a duba shi Yazeed ɗin. Dan yaron kirki ne mai hankali da sanin ya kamata. Kodan ibadarsa da ta samu rauni sa tarosa. Sannan halin da yake a cikin ba Hajiya Yayan kawai yake ƙonawa ba har da su suma. Da nasiha da lallashi dai Daddy ya amince. Dan haka Ammie ta fara fitar da kuɗinta batare data nema komai a wajen Daddyn ba taba Nene akan a dinga abinci ana sadaka. Suka kuma saka ana sauka a islamiyyun yara. Ta kuma shirya da kanta taje Kano ta amso masa ruwan addu'a a gidan Babban malamin nan....
A lokacin da nan su Ammie keta ƙoƙarin ganin sun maido Yazeed hayyacinsa da ƙarfin ikon ALLAH a ɓangaren mijin sabuwa shirinsa ne ya gama kammala akan Daddy, aiwatarwa kawai zai saka Yazeed ya fara masa. Dan kuwa tun randa abin can ya faru Nazeefa ta kirasu tana kuka ta faɗa musu ƙarya da gaskiya. Aiko suka ƙullaci Ammie harda alwashin yin maganinta itama. Suka kuma sake ɗammarar yin sabon shiri akan Yazeed ɗin. Washe gari Sabuwa tazo ta kawo mata komai da zatai amfani da shi. Ko kallon sashen Hajiya Yaya batai ba balle ta shiga su gaisa. Sai yara taji suna hirar zuwan Sabuwar gidan batare da sun san ma taji ba. Dan yanzu suna aiki da nasihar Ammie basa gaya mata komai daya shafi Yazeed ɗin ko sun gani...
Aiko komai Nazeefa ta aikata, sai dai anyi rashin sa'a Sakina taga lokacin da take ajiye na sashen Ammie. Dan tsabar munafunci sashen tazo wai bama Ammie haƙurin abinda ya faru kuskure ne, miye-miye ita ba laifinta bane kaza-kaza.. Ammie bata nuna mata komai tace ta fahimta, sai ma tai mata nasiha akan hakan. Shine a zama ta saƙaka abu a cikin kujerar ta barbaɗa wani a ƙasa. Tana fita Sakina tace Ammie kada ta tashi ta jirata tana zuwa. Zuwa tai ta ɗakko kayan shara ta kwashe maganin tas, ta ciro wanda Nazeefa ta saka a cikin kujera. Sosai Ammie tai mamaki ta kuma jinjina al'amarin. Ta kuma yarda su Sabuwa da gaske suke babu wasa a shirin nasu. Ko Daddy Ammie bata gayama abinda ya farun ba kuwa, balle Hajiya Yaya. Ta dai sake dagewa da addu'a ta kuma gargaɗi su Waleed suma. Kai daga ƙarshe ma ta saka suka dawo sashen ta da kwana suka baro nasu, dan a wannan halin tako ina Nazeefa zata iya ɓullo musu. Aiko Ammie tayi farar dabara, dan kuwa a randa tasa su Hameed suka dawo sashen nata har su Amaal data zo gidan na dariya a daren suma Baban Nazeefar ya aiko abinda za'a sakama yaran. Dan ya fahimci aikin zaima Yazeed yawa sai ya haɗa da su Waleed ɗin....
Hajiya Basariyya dai banda son ina aka tsaya ina aka kwana babu abinda ta saka a gaba. Ta kowane ɓangare kuma taƙi samun damar shiga jikin Hajiya Yayan ko Ammien balle taji. Abin na ƙona mata rai sai take ganin sun haɗe mata kai ne kawai. Gashi Daddy ma yaƙi bata fuskar yimasa batun Yazeed ɗin nan ma. Dan zuwa yanzu dai bisa dagewar Ammie ya haƙura sun koma raba kwana. Daga ita har Hajiya Yayan suna zuwa turakarsa kuma yana cin abincinsu. Basariyyar ce ma ke zumuɗin hakan, ita ko Hajiya Yaya ta kanta take, al'amarin Yazeed ya maidata shiru-shiru ga wata rama da tayi alamar abin na cimata zuciya bana wasa ba. Dan da gaske kuwa lamarin na girgiza mata zuciya, kuma Sabuwa tafi kowa bata mamaki a cikin al'amarin. Ga iyayensu sunce babu ruwansu, sanda suka ƙulla zancen yaran ai basu sani ba batun aure kawai sukazo musu da shi. Musamman ma babansu yafi ɗaukar zafi, dan har tina mata batun Maanal yayi da yanda ta katsatstsare ta dinga aibanta yarinyar da mahaifiyarta. Sai gashi yanzu Ammien ce dai tsaye a al'amarin ɗan nata da ta hana ya auri ƴarta...
Ji Hajiya Yaya tai abubuwan sun mata yawa. Kamar tana jin nauyin Ammie kuma a ƙasan ranta. Amma dai a zahiri bata nuna ba, ba kuma ta furta ba. Sai dai duk shawarar da Ammie ke bata akana al'amarin Yazeed yi take yi. Yayinda Hajiya Basariyya ke bata mamaki.. Duk da kai-kawo gulma da Hajiya Basariyya keyi hankalinta kuma na'a kan Huznah ne, tama Daddy magana akan rashin jin Huznah ɗin ya nuna mata ta shiga hankalinta ta kama kanta, idan ba haka ba kuma zatasha mamaki. Da yake yanzu tana tsoron komawa gidan Kawu Manu sai tai shiru, sai dai abin na damunta a rai matuƙa, musamman daya kasance Maman Yaseerah ta mata bayanin komai har wayar da suka dinga yi da Huznah kwanaki ta kuma daina jinta ma gaba ɗaya......
___________★
KANO.
Anan Kano kuwa abu biyu ne ke shirin faruwa a ɓangare biyu. Bangaren Huznah mahaifin Sageer yace ya barta taje ganin gida dan a tunaninsu Hajiya Basariyya ta risina yanzu zata kama kanta akan al'amarin auren yaran. Yazeed dai zuciyarsa bata so hakan ba. Amma bazai iya jayayya da iyayensa ba ya amince. Amma ya roƙa alfarmar a bari har sai babbar salla dake tunkaro mu. Zuwa lokacin itama ta ƙara jin sauƙi sosai duk da dai Alhmdllh zuwa yanzu ma taji sauƙin. Shi kuma yana samun damar baje hajarsa yanda ya kamata a jikinta, sai dai taci kukanta a ɓoye da jera masa ALLAH ya isa babu damar yi a gabansa dan wani tsoronsa take ji bana wasa ba. A hakan ma sai yaga ta takura kanta da yawa ne yake ɗan sassauta mata. Ko in yaga laulayin ya takura mata, dan wani lokacin takayi lafiya na kwanaki sai kuma jikin ya rikice..
Ga kewar yan uwanta dana mahaifiyarta, dan Alhmdllh a cima babu abinda ta rasa a gidan Sageer. Duk da kasancewarsa talaka yana iyakar ƙoƙarin sa na bata abinda take ci a gidansu. Kuma duk abinda zai sakata a farin ciki yana iyakar ƙoƙarin sa yay mata gwargwadon ikonsa....
_______★
Ɓangare na biyu kuwa su Baba Sardauna da Baba, Abbah, Uncle Mahmud, Hassan, Hussain, Najeeb da wasu aminansu Baba Sardauna uku a yau suka shiga garin Katsina domin ganawa da dangin mahaifan su Ameerah. Kwarjinin Darma a idanun al'umma da yawa daban ne. Ko sunan wannan family kaji alkairansu nasa kaji kimarsu da girmansu a zuciya. Duk irin alwashi da cika bakin da dangin mijin Hajiya Shuwa suka dingayi akan sai sun nuna mata su ɗin sune a bikin Ameerah sai gashi sunyi kurum. Dan kuwa wata gaban ai tafi gaban a taka...
Jikunnansu na rawa suka ma su Baba Sardauna tarba ta mutuntawa, ta girma, ta kuma martabawa. Dan kuwa cikin ikon ALLAH a cikin ƙannen baban su Ameeran akwai mai aiki a ƙarkashin asibitin Abbah. Wato KK HOSPITAL dake garin Kano. Babu wani ja'inja ko kai kawo sukace sun bama Babban Yaya Ameerah, kuma sun yarda a haɗe biki dana Fawzan nan da kwanaki goma kenan.
Matuƙar jin daɗi su Baba Sardauna sunyi da wannan karramawa. A take Uncle Najeeb ya ajiye sadaki daga aljihunsa. Uncle Hussain ya ajiye kuɗin gaisuwa dana mungani muna so dama duk wani tarkacen tsarabe-tsarabe na aure. Akai huɗɗar arziƙi aka kuma rabu cikin mutunta juna da karramawa. Suma sukace suna nan tafe Kano nemawa Ameer auren Maimoon.
Shi halin girma duk mai shi to mai halin girman ne. Sai kawai Baba Sardauna yace in dai haka ne wace wahala kuma. Ai kawai ayi komai anan a gama sun hutar dasu a haɗe ranar ɗaurin aure. Babbar magana. Dangin mahaifin su Ameerah fa mamaki ya sake kamasu da waɗan nan bayin ALLAH. A take sukai kiran Hajiya Shuwa suka sanar mata. Ai sai ta sanya kukan farin ciki, babu wani jeka ka dawo tasa Ameer ya tura ma kawunansa kuɗaɗe. Suma dai a take anan akai hannun karɓa kuma hannun bayarwa. Dan suma dai sun ajiye kuɗin gaisuwar Ameer da sadaki da dukkan abinda ya kamata na aure. Kafin aka sake sabuwar addu'a suka musu rakkiya airport dan dama ta jirgi suka zo. Dan haka komai da komai cikin awanni biyar aka yishi aka kammala tamkar a cikin Kano akayi...
________★
Lokacin da duk su Maanal ke dawowa aiki da wannan farin cikin suka iske Oum a ciki, su Mamy dai basu san anayi ba. Sai da su Oum da ƴayanta da RK da Matarsa dake gidan suka gama farin cikinsu da murna RK da Fawzan harda ma Babban Yaya liƙin kuɗi dan neman tsokana. Abin ya bama Oum da Maanal dariya sosai, AA kam sai murmushi yake, shi kaɗai yasan a irin kalar farin cikin da yake a ciki yau. Yayinda yake sake girmama al'amarin UBANGIJI. Wani gefe na zuciyarsa na addu'a da fatan ALLAH yasa Mamy kada ta ɗaga hankalinta akan wannan al'amari dan itace kawai damuwarsa ba wata Saheebar banza da wofi ba.
Sai bayan sallar isha'i a karo na farko tun bayan bikin AA da Maanal Abah yay kiranyen meeting a sashensa. Tsoro fal zuciyar Mamy kamar tace bazata je ba ita dai, sai dai bazata iya ba, dan koba komai tana matuƙar jin kishirwar rashin ganin Abah na tsawon kwanaki. ALLAH ya jarabceta da son bawan ALLAHr nan kwarai da gaske. Zata iya yin komai akan Abah. Jiki a sanyaye ta kimtsa ta amsa kiran ita da Saheeba. Nuratu nason zuwa Mamyn ta hanata. Sanda suke shigowa kowa ya gama hallara. Abah ne kawai da Oum basu fito ba suna bedroom ɗin Abahn.
Ganin harda RK da Nuwaira abin ya tsayama Mamy a rai. Amma dai batace komai ba ta zauna. Nuwaira bata taɓa damuwa da zuwa gaida Mamy ba a gidan, dan tunda RK ya bata wasu labarai