Showing 81001 words to 84000 words out of 218311 words

Chapter 28 - AJIYA A DUHU BOOK 2 By Billyn Abdull.txt

sashensa ya dawo compound ɗin ji take kamar taje ta fisge system ɗin daga hannunsa ta hana kowa ganin AA sai ita kawai. Sai dai babu wannan damar. Ita kanta Mamy abinda take rayawa a tata zuciyar itama kenan.
Cike da girmamawa Babban Yaya yazo ya ajiye laptop ɗin a gaban Abah, Mamy da Oum na gefe-da-gefensa daman alamar sun gama shiryawa. Kasa haƙuri da yaran sukai duk sai sukazo suka zagayesu ta baya. Su dai su Saheeba basu motsa ba, amma hankalinsu na wajen, musamman Nibras da Nuratu ji suke kamar su fisge laptop ɗin.
Tar-tar AA ya bayyana a screen ɗin, hakama su Abah sun bayyana masa fes shima. Wani irin bugawa ƙirjin Mamy yayi, dan haka kawai sai zuciyarta ta kissima mata ganin AA ɗin na wani walƙiyar mutumin daya sha angwanci. Abah da Oum kam murmushin da AA ɗin ya ɗan sakin musu suka mayar masa. Cikin nutsuwar nan tasa da rashin hayaniya ya furta, “Assalamu alaikum. Abah, Oum, Mamy barkanku da shan ruwa”.
A tare Abah da Oum suka amsa masa, sai kuma ya shiga gaishesu, dai-dai nan Maanal dake cin abinci a gefensa ta matso jin ya ambaci sunan su Abah ɗin. Dan ita da farko a tunaninta ma aiki zai yi. Ganin su Oum da tayi sai tai saurin komawa baya dan abin yazo mata a bazata. Dariya Abah da Oum suka sanya, shima AA dai murmushi yayi, kafin ya furta, “Tun jiya fa take rigima a kiraku a kiraku, ni kuma ban samu zama ba saboda ɗan fita da mukayi shopping”.
Sosai murmushin Abah ya sake faɗaɗa, cike da tsokana yace, “Haba Babyn Oum mune kuma ake ɓoye mawa, common zo na ganki”.
Sosai kunya ta ƙara rufe Maanal, ta matso kusa da AA kanta a ƙasa, shiko yaƙi ya ɗan gyara ta samu ta zauna yanda ba sai ta raɓu da jikinsa ba. A haka ta gaishesu tare da yi musu barka da shan ruwa. Oum ta ce, “Naga takaina ni Fateema, Baby wannan boye-boyen fuskar na miye?”.
Yanzu ko AA dariya yayi kaɗan, hakan yasa Maanal mintsininsa ta yanda su Oum bazasu gani ba. Fuska ya ɓata yana kallon Oum, “Oum kinga ta mintsine ni ba, na rama kuma Abanta yace na masa ba daidai ba”.
Cikin dariya Oum ta ce, “Gaskiyarka Auta. Aba kama ƴarka magana ta kiyaye mu”.
Murmushi Abah yayi, ransa fes, Mamy dai wani kalar kallo take ma AA da shi kaɗan yasan ma'anarsa, dan haka ma ya ɗan rage kallon sashen da take. Hira Abah ya dinga jan Maanal da ita, tun tana sinne kai harta ware tana basu labarin Chaina shi da Oum. Yanda take yi ɗin sosai farin ciki ya mamaye zuciyar Oum da Abah, yayinda AA ya zama ɗan kallo kawai gashi tana a jikinsa batare data farga ba. Tsaguwar da ƴan hutunsu sukai yasa suka haƙura aka miƙama ƴammatan dake kusa da Oum.
Wani irin waro idanu Maanal tayi na mamakin ganin Najma, Meeno, Maimoon, Jiddo, da Lailah, sauran ƙananun bata ganesu ba. Yanda ta zano sunan kowa babu mantawa ya sakasu a farin ciki sosai. Shi kansa AA sai yaji daɗi, dan son ƴan uwansu a cikin jininsu yake. A dake AA da yaga ko takansa basu bi ba ya ce, “Baku iya gaisuwa ba ko? Auntynku kaɗai kuka sani”. Ai a tare suka shiga faɗin, “A'a Yaya kayi haƙuri!” sai kuma suka shiga gaishe shi da girmamawa. Ɗan mintsininsa Maanal tayi ƙasa-ƙasa tace, “Jealousy”. Kaɗan ya murmusa yana wani kallonta a ƙasan ido. Tasan saboda yaran ya wani kame, sai taji ya bata dariya. Dan AA akwai tsare girma. Daƙyar suka miƙama samarin suma, a mamakin AA suma duk Manal ta ganesu, dan babu wanda bata kira sunansa ba, tafa yi mugun sanin ƴan family ɗin Darma ɗin nan dan haihuwarta ne kawai ba'ai a cikinsu ba. Suma da ƙyar suka iya daina ma AA surutu dan sunata roƙonsa su dawo suna missing ɗinsa, sannan kowa yana lissafa masa abinda za'a saye masa. Lokacin da laptop ɗin takai gaban Nuratu, Nibras da Saheeba sai da sukai wani ɗan shock. Gashi hakan yayi dai-dai da AA ya ɗan duƙo a jikin Maanal yana mata magana a kunne, ita kuma ta irin juyawa da saurin nan ta saka yatsarta a saman lips ɗinsa alamar yay shiru. Shi kuma batare daya lura an ajiye laptop ɗin a gaban wasu ba dan ita tama juya baya tunda shi take fuskanta ya kama hannun nata ya tura yatsar nata a cikin bakinsa kai kace wani lollipop ya samu. Da sauri ta fisge hannun tana wata ƴar dariya da kai masa mintsini shi kuma yana murmushi da ƙoƙarin riƙe hannun nata zai maida a bakin. A bazata tana ƙoƙarin ƙwacewa da juyowa a lokaci guda saboda tsoron kar wani ya gansu idonta ya sauka a kansu duk kamar sunyi sumar zaune. Ba shiri ta ankarar da shi ta hanyar faɗin, “Besty su aunty fa”.
Sai lokacin ALLAH ya bashi ikon ganin nasu, maimakon ya saketa sai ya basar kawai yama sake mannata da ƙirijinsa hannun nata dai da take son ƙwacewa bai sakin ba ya dai haƙura da sakawa a bakin. Dole ta haƙura dan tasan ba sakin zai ba. A haka ta shiga gaishesu, Saheeba ce kawai ta iya amsawa da ƙyar, Nuratu kam a bazata sai hawaye, dan numfashinta har ja yake kamar zai fice a ƙirjinta, sai ma ta miƙe tabar wajen kowa ya bita da kallo musamman sauran da basu san abinda ke faruwa ba, Nibras kam hannunta sai rawa yake tana ƙoƙarin riƙesa da ɗayan.
A dake AA ya amsa gaisuwar Saheeba. Sai itama Nibras ɗin ta shiga gaisheshi muryarta na ƙoƙarin ƙwacewa tana riƙota da ƙyar. Maimakon ya amsawa Nibras gaisuwar a wani irin daƙile ya furta, “Ita matata laifi ta miki kika ƙi amsa tata gaisuwar?”.
Kanta ta girgiza da dauri. Cikin zaro ido Maanal ta juya tana kallonsa tare da ɗamƙe rigarsa, irin (miye haka kake yi ɗin nan) shiko yaƙi kallonta. Dole ta juya tana amsa gaisuwar da Nibras take mata fuskarta da murmushi dan harga ALLAH bata ji daɗin abinda AA ɗin yay ba. Dai-dai nan Yaya Fawzan yazo ya ɗauke laptop ɗin daga gabansu. Ya wani ware idanu da faɗin, “Inye kaga amarya da ango”.
Ai ba shiri Maanal da maganar ta sata jin kunya tai saurin duƙewa, ƙoƙarin kamota AA yayi ta zille tama tashi gaba ɗaya. Tana jiyo dariyar Fawzan cike da shaƙiyanci. A gado ta naɗe bata sake zuwa wajen ba balle gaida Yaya F. dan tasan halinsa na tsokana, yanzu haka ma tana jiyo yanda ya saka AA a gaba shi kuma ya kasa bashi amsa.....


Zamansa a kusa da ita bayan ya kammala wayar ya sakata ɗagowa ta kallesa, gira ɗaya ya ɗan ɗage mata yana wani ƙanƙance idanu. Idannunta ta kawar, tana ɗan tura baki gaba. Murmushi ya ɗanyi tare da ɗan taɓe baki, sai kuma cikin taushin sauti ya ce, “Kinga Besty zo kiji wata magana”.
Shiru kamar bazata tashi ba, sai kuma ta yunƙura a hankali zata zauna. Kamota yay ya kwantar a jikinsa, sai taji tsigar jikinta na tashi, ga wata kunya mai kassara jiki. Agogo ta kalla, gudun karsu shiga lokacin gama sahur. Tsaf ya lura da yanayin nata, sai yay ɗan murmushi a zuciyarsa. A fili ya furta, “Kwantar da hankalinki, awa kusan ɗaya ce damu gaba”.
Hannu tasa ta rufe fuskarta kawai. Shi ya san tun Maanal na yarinya ta musamman ce, hakan yasa ɗabi'unta da yawa suke sakashi kallon mata da yawa a basu iya komai ba. Ganin yanda ta rufe ido ya sashi kai yatsarsa manuniya a kansu ya fara sosa mata samansu. Dole ta buɗe idanun a hankali, suna shiga cikin nashi tai ƙoƙarin janye wa amma sai ya hana hakan. Kaɗan yaja mata hanci tare da faɗin, “Yarinyar nan ke da kunyar nan taki ko......”
Kauda fuskarta tai tana murmushi. Shima sai ya ɗan murmusa hannunsa riƙe da fuskrta cikin raɗa ya furta, “Na tambayeki wani abu?”.
Kanta ta jinjina masa kawai.
“Mi doctor yace miki jiya a asibiti?”.
Ai da gudu tai ƙoƙarin tashi a jikinsa amma ya riƙeta, magana tai ƙoƙarin yi kamar zatai kuka yace, “Relax! Tunda baƙya son na sani. Amma kin yarda ni na faɗa miki wata magana?”.
Shiru kamar bazata amsa shi ba sai kuma ta jinjina kai. Hannunta da take matsewa waje guda ya kamo cikin nashi, cike da lallashi da son kwantarta mata da hankali ya cigaba da magana da sanyin murya da tausasa lafazi. “Besty! Ina son ki kwantar da hankalinki tsakanina dake. Nasan akwai abubuwa da yawa da kike buƙatar ji daga gareni amma ban faɗa ba, nima akwai wanda nake buƙatar son ji daga gareki amma ban tambaya ba. Lokaci nake jira, akwai gaɓar da zamu zo wannan matakin ne in sha ALLAHU. Abu na biyu nasan a baya bamu taɓa kallon kammu a wannan matsayin ba, ko nace daga ɓangarenki, dan ni dai a gareni wannan shine burin rayuwata na farko daya fara ginuwa tun ma ban fahimci wanene ni ba.....”
Karo na farko Maanal ta kallesa, wani irin lumshe mata idanu yayi ya sake buɗewa. “Kada kiyi mamaki, kada kuma ki tambaya, kada ki damu da son sani game da jin hakan domin ba yanzu ba. Abinda nake so daga gareki a yanzu kawai haɗin kai, kwantar da hankali, ki kwantar da hankalinki dani, bazan taɓa aikata wani abu a gareki ba bada yardarki ba Maanal! Duk yanda zan tsinta kaina a matsuwa ta buƙatar jiki kota rayuwa ki sani ke kinfi hakan muhimmancin da bazan fifitasu a kanki ba. Domin su na wuccin gadi ne, zasu iya samuwa su wuce sai wani lokaci a buƙace su, ke kuma ta har abada ce, akoda yaushe kece kaɗai Ajwaad, kece kaɗai nake iya buɗema zuciyata, ke ce kaɗai nake iya buɗema damuwa ta, kece ƙawa! Kece ƙanwa! Kece aboki! Kece aminiya! Kece abokiyar dariya! Kece abokiyar magana! Kece abokiyar kuka! Kece abokiyar karatu! Kece abokiyar sirri! Ko duk kin manta? Kin manta haka saboda nisa da ratar da ƙaddara ta bamu ne? Kin mance haka saboda jarabawa da UBANGIJINMU yay mana dan yaga ƙarfin imaninmu? Kin manta saboda a yanzu tunaninki na baki komawarki mace matancin naki ne kawai zan iya buƙata? Noo Manaal! Noooo! Wannan Ajwaad ɗin na nan a naki tun na waccan rayuwar, bakuma zai taɓa canjawa daga hakan ba domin a matsayin da dama na gina kenan tun fil azal. Ki sani tubalin ginin da kayan ginin an samar da su ne daga himmar aiki mai ƙarfafa ƙwanji tun daga ƙarƙashin zuciya da bigire na fitowar TSIRRAI daga HUKUNCIN UBANGIJI. Wallahil azim inda zaki ce Ajwaad bazan taɓa baka kaina ba mu rayu a haka yanda muke ni mai riƙe miki wannan ALƘAWARIN ne dan ba wannan nake kallo ake ɗin ba, ke! Ke! Ɗin nake kallo a matsayin Ke! Kawai Maanal.....”✍️




Hummmmmmm













*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*


*09032345899*






*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
















*_💞AJIYA A DUHU....💞_*








*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*




*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_My TikTok account 👇_*


https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1


*_Instagram👇🏻_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_Arewabooks_*


Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


*_WhatsApp channel_*


https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R




_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_


*_BOOK 2_*
🅿️➖4️⃣0️⃣




______________


.........Gaba ɗaya sai Maanal taji ta sake rikicewa, hawaye kam gudu suke wasu na bin wasu dan sunanta kai tsaye a bakin Ajwaad babbar magana ce, jikinta na wani irin tsuma zuciyarta na rawa da sake rauni. Bata san sanda ta zabura ba lokacin da AA ya cigaba da faɗin, “Maanal! Har yanzu ke yarinya ce, shekarunki basu kai na fara banbance ƙarfin ikon zuciya dana ƙwaƙwalwa ba. Amma ina son daga yau, daga yanzu kisa a ranki, Ajwaad Aliyu Abubakar zai iya FANSARKI da kansa a kowanne irin TARNAƘI. Sannan zai iya MALLAKA miki kansa da komansa domin biyan buƙatar ki. Zai iya ƙwata daga hannun wani domin FARIN CIKIN KI. Zai iya bayarwa ga wani domin MUTUNCINKI. Zai iya sadaukarwa ga DUNIYA domin ɗaga DARAJAR KI. Koda kuwa kina kallon komansa a matsayin AJIYA A DUHU bazai damu ba Maanal, bazai karaya ba Maanal. Domin rauninki ne kawai ke iya karya lagon Ajwaad a bayyane da raunana shi har ya iya kaiwa ƙasa wanwar. Na rantse miki da ALLAH babu abinda ke iya dukan wannan zuciyar ya sata risina da sallamawa akan komai sai ke Maanal.....” yay maganar yana ɗaura hannunta a dai-dai saitin zuciyarsa, kafin a wani irin ƙaramin sauti ya sake faɗin, “Manaal...”
ji tai bazata iya jurewa ba, dan sautin kukanta har ya fara bayyana waje, da sauri takai hannunta ta dafe masa baki jikinta na rawa sosai, idannunta a jikin nashi tana mai girgiza masa kai. Sosai nasa idanun shima sukai wani irin kaɗewa suka koma jaaa matuƙa, ƙyallinsu ya sake zama mai ƙyalli sosai tamkar wanda hawaye suka tararma a ciki. Ji yake tamkar ya tsaga jikinsa ya sakata kawai a ciki duk inda yaje akace ina Maanal yace tana a cikin jikina. Ganin yanda idannunta ke wani tafiya luuu-luuu kamar zata suma sai kawai ya jawota gaba ɗaya a jikin nasa ya rungume tsam-tsam hawayenta na sauka masa a kan ƙirji. Sun fi minti biyar a haka kafin ya kai lips ɗinsa kan kunnenta ya sumbata, ta ƙanƙame jikinta dan har tsakkiyar kai taji al'amarin, cike da raɗa ya furta, “Shagwaɓaɓɓiyar AA minti biyu fa doctor yace ki ringa rungumeni kawai in ba haka ba zan iya BOƘAREWA a tafi step 2 kin san ba mata bane kawai boƙararru”.
Ƙaramin ƙulli (dundu) ta masa a baya tana ƙwace jikinta fuskarta da murmushi. Siririyar dariya ya saki shima yana biyota zai sake kamowa ta zille. Ganin ya tsare ko ina cikin shaƙƙaƙiyar muryarta irin ta mai kuka batare data kallesa ba ta ce, “Kasan dai na iya duka a ciki ko”.
Yanda tai maganar tana dunƙule hannu kamar zata kawo naushin ya saka shi matsawa baya yana waro idanu. Sai kawai ta wani ƙyaƙyƙyale da dariya tana faɗin, “Matsoraci kawai Oum's boy”. Takai kwance tana masa gwalo.
“Kinci bashi”.
Ya faɗa yana ɗaukar wayarsa da kira ke shigowa. Ganin Āhōng Chen (Sheikh Chen) ne yasa shi miƙewa a wajen ya koma wajen kujeru. Ita kuma sai kawai ta kwanta ta zuba masa idanu. Wani irin dawo mata kalamansa keyi a zuciya, so take ta fasa komai dalla-dalla amma nauyinsu yay mata yawa. Sai ma wani irin barci mai ɗan karan daɗi daya fara fisgarta. Kafin kace mi ta lula a cikinsa cike da mafarkin AA.
Bayan kammala wayar yazo ya tasheta dan lokacin sallar asuba yayi....

_________★


Huznah dai azumi ya gagara kaiwa yamma, dan anayin azhar tiɓis ta zama. Tsoron kar Sageer ya dawo batai komai ba ta miƙe cike da lallaɓawa tai gyaran gidan ita da Khadijah ƙanwarsa da tazo tayata aikin, sannan ta fara hada-hadar ɗaura girki dan ya tabbatar mata yau da ɗan yawa zatai abincin akai gidansu shiyyasa ma ya turo mata Khadijah, dan yana son iyayensa suyi buɗa bakin farko da abincin gidansa, baya son ta kwafsa shiyyasa yace Khadijahn tazo tunda har yanzu hannunta bai wani gama faɗawa da girkin ba. Haka ta lallaɓa sukai komai, abu na ƙarshe data bari yin farfesun kifi da yace yana so duk da bata son ko sunan kifin a kira. Ca tai Khadijah ta ɗaura ita bara taje tai wanka. Khadijah bata kawo komai a ranta ba tace to ganin komai an tanada haɗawane kawai. Abu kamar almara tayo wanka tana shiryawa kifin da Khadijah tasa a wuta ya tafaso sai ga ƙamshinsa har cikin bedroom ɗin da Huznah take. Wani kalar harmutsawa cikinta yayi, kafin kace mi tai bayi a guje sai amai. Kakarin aman nata Khadijah ta jiyo ta shigo a guje. Sosai tsoro ya kamata ganin yanda Huznah ke amai, gashi sai magiya take mata wai taje ta kashe gas ta fita da kifin. Ina ita Khadijah bata fahimta ba, sai da Huznah ta gama birkicewa da galabaita sannan tai hankalin kiran yayanta a waya ta sanar masa. Mamaki ne ya kamashi jin wai Huznah na amai saboda ƙamshin kifi, dama dai shirin tahowa gida yake, dan haka ya taho, ya sameta kwance duk ta saki, ya shiga mata sannu da tambayarta mike damunta. Idannunta cike da hawaye tace, “Dan ALLAH yaya Sageer bana son kifin can kace ta sauke shi”.
Kallonta kawai ya tsaya yi, sai kuma ya juya ya fita zuwa kitchen. Ya samu Khadijah na kwashe kifin, sai kawai baice komai ba ya fice. Babu jimawa ya dawo tare da Nurse ɗin yarinyar dake makwaftan su, dan yayarta ce ta duba Huznah ranar first night ɗinsu yanzu kuma yayar na asibiti sai ƙanwar. Tambayoyi ta fara ma Huznah ɗin dake wani yatsine-yatsinen fuska, ita dai yarinyar bata kulata ba dan suna ganin irinsu Huznah har ma wanda suka fisu a iya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login