Showing 24001 words to 27000 words out of 252707 words

Chapter 9 - HAJAR COMPLETE NOVELS By Nafisa Yusuf Nagoda.doc

ciki sunyi bugun sunyi kukan har sun gaji, muryar Maimuna taji tana kuka tana cewa "dan girman Allah Baba kayi ha?uri wllh bazan sake ba, wayyo Maamana na shiga uku na lalace, wllh kunama ta harSeni dan Allah a buWe mu, Sa'adatu ta yanke da ?arfen langa-langa", Hajar ta kyalkyale da dariya tana wankinta, Maama ta fito daga Wakinta zuciyarta busu-busu ta shiga Wakin Baba, Baba ya gama shiryawa tass zai fita aiki, Maama tace "mal fita za kay?, yaran nan fa har yanzu ba a buWesu ba", Baba ya gyara wuyan rigarsa yace "sai aka yi yaya da ba a buWesu ba?", tace "daman naga ko sallar asuba basu yi ba gashi rana ta fito", yace "Au daman kina damuwa idan basuyi sallah ba?", ta fara ?in?ina tace "dan girman Allah mal kayi ha?uri, a yi musu afuwa", Baba ya gyaWa kai yace "za a yi musu, amma in tambayeki mana?", tace "toh mal", yace "waye uban Sa'adatu da Maimuna?", ta saki baki sai kuma tace "kaine mana mal", yace "ni mijinki ne ko A'a?", tace "kai mijina ne mana", yace "idan kina so igiyar aurenki ta cigaba da rayuwa to ki gyara tarbiyyar ?a?anki, idan kina son ?a?anki to ki gyara tarbiyyarsu, kar Sa'adatu ta sake barin gidan nan, Maimuna karta sake fita da daddare, Nabilah ta fito da miji na aurar da ita", Maama ta gyaWa kai tamkar tsohuwar ?adangaruwa tace "tom", ya ciro mu?ulli daga aljihunsa ya bata yace "ki buWesu idan na dawo ina son ganinsu", Maama ta karSi mu?ullin tana harararsa ?asa-?asa tace "toh" ta fita a Wakin, ruSaSSen kichen Win ta buWe Sa'adatu da Maimuna suka fito wujiga-wujiga, zafi ya dakasa ga kuma jikinsu da yayi tsami.

&Nurain ya fita masallaci sallar la'asar, bayan ya dawo ya tsaya suna gaisawa da Garba da yake bawa flowers ruwa, Nurain yace "wace motar ka wanke min?", Garba yace "farar na wanke maka", Nurain yace "Ohk, ka amso min takalmana daga wajen polish", Garba ya dukar da kai yace "toh alhaji ?arami", Nurain ya wuce ciki, har zai zauna a balcony sai ya fasa dai ya shiga main palour ya zauna a kujera, remote ya Wauka ya canza channel, bayan few minutes ya mi?e ya shiga kitchen ya buWe fridge ya Wauki Apple guda uku ya Wora akan plate ya dawo palour ya zauna yana ci, Noor ta shigo palourn tace "Yaya Mami is calling", yace "Ohk", ya mi?e ya Wauki plate Win Apple Winsa ya shiga part Win Mami, Mami ta ringa kallonsa har ya zauna a kujerar kusa da ita, ya Wan rame kaWan amma kuma fuskarsa babu wata damuwa, Mami tace "where is your phone?", ya shafa kansa yace "Ta fashe ne", tace "Ohk, toh dan ta fashe shine ba za ai amfani da ita ba, saika zauna haka ba waya", yace "zan siyo wata ne", tace "good do that fast", yace "yeah" tace "when are you resuming work?", yace "next week, daman na Wauki leave na two weeks", ta gyaWa kai tace "Son, why not go towards Khausar", yace "Khausar?", tace "yess Khausar"..........
'?
=؛? HAJAR =؛?
by Nafeesah Yusuf Nagoda

~~(Feenerh_feeche)~~

{14...}
Nurain ya ajiye Apple Win hannunsa yace "Mami i don't get you", Mami ta Wauki remote ta danna mute tace "Nurain, ga Khausar nan ?ar uwarka, me zai hana ka nemi aurenta, kasan yarinyar nan kuma kasan iyayenta, duk wani qualities da ake so a wajen mace Khausar na dashi, asali, ilimi, home training and what majority of men are after to, beauty right?, she's beautiful..", Nurain ya sauke ajiyar zuciya yace "but Mami I don't have such feeling for her, i only see her as my lil sister", Mami tace "Alright, tinda kace haka shknn, you may leave", ta Wauki remote ta canza channel snn ta buWe volume, Nurain dai bai sake cewa komai ba yana nan zaune ya cigaba da cin Apple Winsa, bayan 20minutes ya mi?e yana jan shirt Winsa ya nufi door, har ya murWa handle Mami ta kira sunansa, ya juyo yace "Na'am", ta nuna masa plate Win da ya shigo dashi, ga apple nan guda daya da bai cinyeba akai, ya shafa kansa ya dawo ya Wauki plate Win ya fita, Mami ta bisa da kallon gefen ido. room Winsa ya wuce yayi abinda zai yi snn ya sakko down stairs hannunsa ri?e da car key, compound ya fita ya wuce parking space, farar motarsa ya buWe ya shiga, saida yayi warming snn ya gangara ya fita daga compound Win bayan mai gadi ya buWe masa gate, a daidai wani katafaren wajen siyar da waya yayi parking, ya kashe motar ya buWe door ya fita, ya shiga building din da akay molding Winsa da kirar waya, few minutes ya fito hannunsa ri?e da ?ar leda, yana komawa gida aka kira sallar magrib, yayi using tap din compound yayi alwala ya wuce mosque, bayan ya dawo daga masallaci ya bude car ya Wauki ledar ya wuce ciki, direct a room Winsa yayi branching, ya Wauki wayarsa da ta tashi daga aiki akan mirror, sim cards dinsa ya cire snn ya farke sabuwar wayar da ya siyo, ajiyar zuciya ya sauke yana kallon wayar tana booting bayan ya danne switch dinta, bai Waukesa wani lokaci ba ya gama setting wayar, kira ne ya shigo wayar, Nurain yayi murmushi ganin me kiran nasa video call ya Wauka, Farooq ne cousin dinsa da yake Russia, Nurain yace "why the call dude", daga Wayen Sangaren Farooq da ya sha wata jibgegiyar sweeter yace "I can't reach you since last week, what was the problem?", Nurain ya jingina da allon gado yace "look, wnn wintern ta garin ku ai bazata bari kayi reaching mutane ba", Farooq ya Waga gira yace "decline, look for another way", Nurain yace "Ohk", Farooq yace "ya Mutan Niger?, ya su Mami", Nurain yace "All lafiya", Farooq yace "looks like you lost some weight Dr, ko dai Ruqayyah bata iya girki ba, i forgot to asked about her, how is she?", Nurain yace "she is great", Farooq yace "good", Nurain yace "when are you coming?", Farooq yace "nanda 2weeks insha Allah, kuma a gidanka zan fara sauka naci girkin Amarya Ruqayyah", calmly Nurain yace "Ruqayyah is not my wife and she will never be, i don't think ma zaka tarar dani a Nigeria", yadda Nurain yayi maganar without joke yasa Farooq fahimtar something has happened, Farooq yace "bro what...", Nurain ya katsesa yace "don't ask me, zan gaya maka later, after my heart is healed", Farooq yace "Ohk, amma ina zaka da kace bazan sameka a Nigeria ba?", Nurain yace "India", Farooq yace "Ohk, ynxu ka yarda zaka koma ka ?aro karatun kenen", Nurain yace "yeah", Farooq yace "Ohk, i understand, i gotta go, good night", Nurain yace "Ohk, good night" ya katse kiran yana sauke ajiyar zuciya.

&Da daddare Baba yana zaune a Wakinsa Maama tayi sallama ta shigo, tana daga bakin ?ofa tace "mal kace kana son ganin yaran nan?, toh su shigo yanzu ko sai anjima?", Baba yace "ki kirasu yanzu nan, kema kizo", Maama tace "tom" ta juya ta fita, Wakinta ta shiga tana kallon ?a?an nata tace "kuzo inji Babanku", Maimuna ta tashi daga kan kayan wanki tace "na shiga uku na, Maama dan girman Allah kice nayi bacci, wllh har yanzu harbin kunamar nan bai bar jikina ba", Maama tace "A'a dole ki taso, ko baccin ma ki kai tashinki zanyi", ta kalli Sa'adatu da Nabilah tace "kunji dai me nace ko?, ku taso", Sa'adatu ta mi?e tana gunguni ta fita tsakar gida, Maama tabi bayanta, Wakin Baba suka shiga suka zauna, suna zama Nabilah ma ta shigo, Maimuna ce ta shigo a ?arshe, tana ?o?arin zama Baba yace "karki zauna Shiga wajen Umma ki kiramin ita da kuma Hajara", Maimuna ta kalli Maama, Maama ta Wauke kanta, haka Maimuna ta fita ta tsaya a ?ofar Wakin Umma tace "Baba yace kizo keda Hajara", Maimuna ta koma Wakin Baba ta zauna kusa da Nabilah tace "na kirasu", Maama ta haWe rai tace "mal naji kace a kira waccar matar da ?arta, to mene dalili?, mene haWinsu da zamanka da ?a?anka?", Baba yace "Toh haka dai nace a kirasu", Maama bata sake cewa komai ba, Umma ce tayi sallama ta shigo Hajar biye da ita, suka haWa ido da Maama wacca take harararta ?asa-?asa, Umma ta zauna tace "mal gani", Hajar ta zauna kusa da Umma, Baba ya ?are musu kallo duka yace "Nabilah!!", Nabilah tace "Na'am", Baba yace "acikin samarinki ki fitar da wanda yayi miki kice masa ya fito, aurar dake zanyi, idan kuma baki da wanda kike so toh zaSi yana wajena, na baki nanda sati biyu..", Nabilah ta marairaice fuska tace "Baba aure fa..", ya katseta yace "Ba cewa nayi kiyi magana ba, tashi ki ban waje", Nabilah ta mi?e ta fita zuciyarta na zafi, Baba ya juya kan Sa'adatu yace "Sa'adatu!!, Sa'adatu!!, Sa'adatu!!", Sa'adatu ta haWe gira tace "Na'am", Baba yace "sau nawa na kiraki?", tace "Uku", ya gyaWa kai yace "gargaWi na ?arshe kenan da zan miki, zunubin ki mai kauri ne, wllh wllh wllh tsattsauran mataki zan Wauka akanki, tashi ki bani waje", Sa'adatu ta mi?e ta fita zuciyarta na tafarfasa, Baba yana gamawa da Sa'adatu ya juya kan Maimuna yace "ke kuma duk abinda Sa'adatu tayi shi kike yi ko?, kin ?i makaranta kin zaSi yawon dare ko?, toh ranar Litinin Mu'azzam zai mayar dake makaranta, Sacemin daga gani", Maimuna ta mi?e ta fita ranta na soyewa, wai makaranta za'a mayar da ita. Baba ya dubi Hajar da take zaune kusa da Umma yace "saura ke Hajara, uwar rashin ha?uri, Nabilah, Sa'adatu duk yayyenki ne, Maimuna ce sakuwarki kuma itama Win gaba take dake, karki sake yi musu rashin kunya", Hajar tace "toh Baba", yace "toh tashi ki tafi, Allah yayi miki albarka". Maama ta hura tukubar hancinta tace "suma Allah yayi musu Albarka su da ba ?a?an so ba", Wakin ya rage daga Baba sai Maama sai kuma Umma, Baba yace "Rabii", Maama ta mi?e tace "Allah ya tashemu lfy, ba sai kace komai ba mal, ai naji abinda kace da safe" ta fice a Wakin tamkar zata tashi sama. Rayuwar gidan ce ta canza zuwa wani fannin daban, babu ruwan kowa da kowa, yau sati guda kenan ba ai hargitsi ba, sosai Maama tayi ladaf ta hana ?a?anta fita, daman suma sun tsorata da Baba shiyasa ko ?o?arin fitar ma basuyi ba. Sa'adatu ta le?a kwanon Wumamen tuwon da Maimuna ta shigo musu dashi matsayin breakfast tace "chab wllh bazan ci tuwo ba", Maimuna tace "ga koko nan", Sa'adatu ta zabga tsaki ta Wauki jakarta ta ciro kuWi ta saka hijab ta fita tsakar gida, Maama da take ri?e da kofin koko tace "ina zaki Sa'adatu", Sa'adatu tace "ba nisa zanyi ba, wajen mai shayi zanje na siyo biredi da shayi, ni bazan ci tuwo ba", Maama ta zaro ido tace "kin san dai Babanku ya hanaki fita ko?", Sa'adatu tace "ai ba ko wace fitar yake nufi ba, nifa nan nan wajen mai shayi zani ba wata uwa duniyar ba", Maama ta girgiza kai tace "A'a, kawo kuWin na le?a waje idan na samu yaro sai ya siyo miki", Sa'adatu ta mi?awa Maama duba Wayar data rage mata, Maama ta bata kofin hannunta tace "shigarmin dashi ciki, bari na aika yaron", Sa'adatu ta amshi kofin ta koma Waki, Maama tayi hanyar soro kamar da gaske, tana zuwa soro ta laSe a bayan ?ofa ta Waure kuWin a haSar zaninta ta koma ciki, Sa'adatu tace "Maama har an samu yaron", Maama tace "Eh yanzu zai kawo miki, Wan gidan Munkaila ne", Sa'adatu tace "yawwa, ga kokon ki". Maama ta zauna tana kurSar kokonta tana kallon Maimuna da Nabilah da suke kwarfa lomar tuwo. Shiru-shiru yaro zai kawo Shayi da biredi amma ma?atau ba labari, yunwa sai kartar ?ar hanjin Sa'adatu take, Sa'adatu ta le?a soro a karo na bakwai ta dawo ciki tana gunguni ta kalli Maama dake bakin murhu tace "har yanzu fa yaron bai kawo ba, yunwa nake ji", Maama ta tura mata kwanon tuwon data rage tace "ki rage hanya da wnn kafin ya dawo", Sa'adatu tace "tuwon ne fa bazan ci ba", Maama ta gyaWa kai tace "yo ba yunwar kike ji ba, shknn saiki jira shayin". ?arfe sha biyu da rabi Sa'adatu ta fito ta wafci kwanon tuwon da Maama ta bata Wazu tace bazata ci ba, loma huWu tayi masa ta tashi dashi, ta ringa suWe hannu tana muzurai don ko tsarga mata beyi ba.

&Momy ta Shiga palourn Daddy hannunta ri?e da tray, sallama tayi, Daddy dake zaune kan kujera shallow in thoughts ya amsa mata, Momy ta ajiye trayn akan center table kana ta shiga making tea, thick tea ta haWa cikin Mug ta dire a gaban Daddy, ta buWe warmer da ta shigo da ita mai Wauke da chips, plate ta Wauka ta zuba chips Win with omelette egg a gefe, ta matsa ketchup a wani ?aramin bowl, ta jera in front of Daddy kana ta koma kusa dashi ta zauna, a hankali ya fara cakar chips din da fork yana dangwalar ketchup yana ci, kaWan yaci ya ajiye fork ya Wauki tean ya fara sipping, keenly yace "have you eaten?", Momy tace "I'm not hungry", yace "Tom", calmly tace "Alhaji yarinyar nanfa bamu san inda take ba har yanzu, yaufa kwana sha biyu babu ita babu dalilinta..", yace "so", tace "do something", yace "something like what?", Momy was speechless kawai kallon Daddy take, ya ajiye Mug din hannunsa yace "lokacin da Ruqayyah ta saka ?afa ta fita na sani ne?, ajikin lettern da ta ajiye ma tace kar mu nemeta zata dawo, to kinga kuwa me zai sa na Sata golden time Wina wajen nemanta..", Momy tayi ajiyar zuciya tace "har yanzu fa ba a samun wayarta, ai dole hankalina ya tashi", yace "toh maza ki Wauki haramar saka damuwa a ranki, wai yarinya nan ba da kanta ta fita ba, dan ba a sameta a waya ba ai ba wata matsalar bace, tana sane ta kashe wayar, what Ruqayyah did really hurts me, idan tanada wata damuwar why not ta sameki ta gaya miki, and she can talk to me if there is any problem, am i not a free Father?, plxx don't ruin my mood this morning akan maganar Ruqayyah", da haka Daddy ya mi?e ya shiga bedroom Winsa, Momy tabi bayansa da kallo sai kuma ta tashi ta fita a palourn, bedroom Winta ta shiga ta Wauki wayarta tayi dialing numbern Kulsoom, saida ta kusan yankewa snn Kulsoom tayi picking, Momy tace "saiki ringa nesa da wayarki", Kulsoom tace "Momy ina kitchen ne", Momy tace "toh kina jina Daddy ya?i saurarata, anjima da yamma sai muje police station mu shigar da report", Kulsoom tace "toh Momy, har yanzu babu wanda ta kira", Momy tace "Eh", Kulsoom tace "toh ina gama abinda nake zan shirya na taho", Momy tace "toh shknn saikin zo" ta datse kiran.

&Hajar ce zaune a Wakin Umma tare da Zainab, Zainab tace "kefa ?ar rainin hankali ce wllh, yanzu saida kika tattagoni, ?iri ?iri kin ?i hawa online", Hajar tace "kuma inada data isasshiya wllh, duk sati ya sayyadina sai ya sakomin credit da data", Zainab ta taSe baki tace "toh ai kin kyauta da kike masa asara, idan baki yi amfani da ita ba ai tayi expire a wofi", Hajar tace "ya mutan gida?", Zainab tace "lfy wllh, kin san kwa me ya kawoni", Hajar tace "inafa zan sani, ai sai kin sha?amin", Zainab tayi ?asa da murya tace "kin tuna wnn katafaren gidan da kika rakani?", Hajar tace "katafaren gida?", Zainab tace "Eh mna, wanda muka je har kika yiwa wani mai mota rashin kunya..", Hajar tace "Au, wnn mutumin da bai san darajar Wan Adam ba, kinsan kwa na sake ganinsa?", Zainab tace "A ina?", Hajar tace "A hospital, likitane", Zainab tace "okay, yanzu dai kina jina?, Wan gidan ne yace na bashi digits Winki, wllh ya takuramin, ni kuma na?i bashi nace saina sanar dake..", Hajar tace "yawwa gwara da baki basa ba..", Zainab tace "sbd me?", Hajar tace "toh meya haWana dashi da zaki bashi digits Wina?", Zainab ta harareta tace "malama karki raina min hankali, kinfa gane me nake nufi", Hajar ta langwaSar da kai calmly tace "So, kinsan dai akwai wanda muke tare dashi, kuma har yazo gida", Zainab tace "yess nasani, toh ai ba baiko akai muku ba", Hajar ta juyar da kanta tace "kya yi kuma". can dai Zainab ta mi?e tace "toh zan tafi", suka fito tare da Hajar zata rakata ?ofar gida, Zainab ta yiwa Umma sallama suka wuce hanyar soro tare da Hajar, Sa'adatu ta fito daga bayi ta tsaya tana kallon Hajar da Zainab da suka nufo hanyar fita, Sa'adatu ta dire butar hannunta, daman yau ranta a Sace yake neman wanda zata huce akansa take, Zainab ta marairaice tace "dan Allah Hajar ki sauraresa, zan bashi numbern..", Hajar tace "zanyi tunani.", Hajar ko kallon inda Sa'adatu take ba tay ba, Zainab tana zuwa wucewa Sa'adatu ta saka mata ?afa. Zainab ta faWi a ?asa, Sa'adatu ta nuna Hajar da yatsa tace "kema baki isa ki kawo ?awayenki gidan nan ba su fita lfy", Hajar da zuciyarta take tafarfasa ta dur?usa ta kamo Zainab ta taimaka mata ta mi?e tsaye, Hajar ta tsugunna kamar zata Wakko jakar zainab dake ?asa, ta saka iya ?arfinta ta kwashi ?afafuwan Sa'adatu ta nakata da ?asa, a lokacin Baba yayi sallama ya shigo gidan, ya tsaya yana kallon Hajar.......
'?
=؛? HAJAR =؛?
by ~Feenerh_feeche~

{15....}
Wani ihu Sa'adatu ta kurma tace "Hajar kashe ne za kiyi?, nifa ?ar uwarki ce", Hajar ta kasa cewa komai sbd kallon da Baba yake mata, Sa'adatu ta mi?e tana dafe bayanta, Baba baice komai ba ya wuce cikin gida, Umma ce tayo hanyar soro sbd ihun da ta jiyo, kaciSus sukay da Baba tace "sannu da zuwa Malam", Baba yace "yawwa", ya wuce ?ofar Wakinsa, ya ciro keys a aljihunsa, ya buWe padlock Win ya shiga, Sa'adatu ta cafki wuyar Hajar tana ?unduma mata ashar, Hajar tace "wllh badai nawa ba,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login