Showing 129001 words to 132000 words out of 252707 words

Chapter 44 - HAJAR COMPLETE NOVELS By Nafisa Yusuf Nagoda.doc

in the darkness" da haka ya fice daga Wakin ya fita corridor, da gudu ta bisa still tana kuka amma kuma a hankali, bai juyo ya kalleta ba ya cigaba da tafiya yana jinta a bayansa har ya isa ?ofar Sangarensa, yayi sliding door kafin ya juyo ya dubeta yace "yaya dai kike bina young lady...", ita dai ba tace masa uffan ba kanta na ?asa tana jan fingers dinta tana shesshe?a a hankali, from head to toe ya dubeta da ?ar Singilar rigar baccinta iya guiwa, ko ina ta baro hijab din, Calmly yace "don't follow me...", kafin ya shiga ma ita ta rigasa shiga da mugun speed, buWe baki yayi ya haWe thick eyebrows dinsa strictly yace "hey get out before i smash you...", ta sunkuyar da kanta without saying anything, ja da baya tayi ta shiga palourn nasa sosai tana turo baki, ya sauke ajiyar zuciya ya isa kan three sitter ya zauna, sai a lokacin ta Waga kai ta kallesa sai kuma tabi palourn da kallo, duk da ba haske sosai amma tasan tsadadde ne huge and luxury, Nurain ya duba wayar yaga batteryn ta is running down, ajiyewa yayi kan hannun kujera yayi folding hands dinsa, after few seconds yayi slight hiss ya cire slippers din ?afarsa ya kwanta kan kujerar, ba sai kuma yaga yadda za tay idan charge din ya ?are ba, ya lumshe idonsa, nan inda take ta sulale ta zauna kan tiles ta jingina da bango, wani irin sanyi ne ya ringa shigarta, ga sanyin tiles ga kuma na gari da ake ruwa, tanata zaune a haka harta fara gyangyaWi, takure kanta tayi ta kwanta a ?asa, cikin bacci taji ana tapping dinta, a zabure ta mi?e tana zaro ido, ya mata nuni da kujera two sitter yace "hey koma can ki kwanta...", har ta turo baki zata lafta masa rashin kunya sai kuma ta fasa, tashi tayi ta tafi inda ya nuna matan ta kwanta, ko seconds 40 bata ?ara ba baccin ya sake Wauketa, Nurain ya sauke ajiyar zuciya ya koma kan three sitter ya kwanta kafin ya janyo wayar ya kashe fitilar kar yaje ya rasa wcca zai haska da asuba tinda charge din ya kusa ?arewa. ?arfe biyar da minti uku Nurain ya farka, tashi yayi zaune yana karanto addu'ar da ma'aiki ya koyar damu, yayi stretching kansa ya lalubi wayar a inda ya ajiyeta ya kunna torch, slippers dinsa ya zura ya tashi ya shiga bedroom ya wuce toilet ya Wora alwala, bayan ya fito ya saka wata light brown jallabiya ya fita palour, kallon Hajar dake dun?ule kan kujera yayi kafin ya ajiye wayar kan Centre table ya fita zuwa masallaci, koda ya dawo daga mosque a palourn downstairs yayi kwanciyarsa. Hajar ta buWe idonta a hankali sai kuma ta mi?e zaune tana ?arewa inda take kallo, kallon wayar dake kan Centre table tayi, ta Wauki wayar sum sum sum ta nufi ?ofa ta fita, direct room dinta ta wuce, bayan tayi alwala tayi sallah, kan prayer mat din ta kwanta ta du?un?une da hijab Win da tayi sallah. shida da rabi ya shigo Wakin, kallo Waya ya mata ya Wauke wayarsa da ya gani gefenta ya fita, wayar harta mutu da kanta, Sangarensa ya shiga ya Wakko key din mota ya fito, downstairs ya sauka ya fita zuwa compound ya isa parking space, motarsa ya buWe ya kunnata yayi plugging wayar a charge, a kunne yabar motar ya koma ciki ya shiga kitchen ya haWa coffee, saida wayar ta Wanyi chargi ya kira Engineer din da ya haWa wutar gidan. kafin ?arfe goma Engineer din har yaxo yayi fixing komai wutar gidan ta dawo. sai ?arfe biyu na rana Nurain ya fita, hospital ya fara zuwa ya duba patient din da ya yiwa surgery jiya, alhmdllh patient din har ya farka kuma he is healing.

&Ruqayyah na kwance kan gado tunani fal zuciyarta, bude ?ofar Wakin akay, Meema wacca take matsayin cousin dinta kuma age mate dinta ce ta shigo, Ruqayyah ta Waga kai ta dubeta, ?arasa shigowa Meema tayi ta ajiye cup da plate dake hannunta a kan bedside tana kallon Ruqayyah tace "ga breakfast..", Ruqayyah ta tashi ta dafe kanta da ya sara, Meema ta Wauki cup mai Wauke da tea ta mi?a mata tace "ki daure kici abinci sai kisha drugs dinki..", amsar cup din Ruqayyah tayi ta fara shan shayin, sosai ya mata daWi har taji appetite dinta ya dawo, da kanta ta Wauki plate din dankali da kwai ta fara ci tana dangwalar ketchup, baifi rabi taci ba ta ajiye ta cigaba da sipping tea, Meema dake zaune gefenta tana latsa waya tace "yauwa kinga yanzu ai kyaji kwarin jikinki sister..", gyaWa mata kai kawai Ruqayyah tayi, bayan tasha drugs dinta ta koma ta kwanta, kuka ta fara yi a hankali, tin Meema bata ankara ba har ta gane, with care ta Wora hannu akan goshinta tana tambayarta is she okay, Ruqayyah ta girgiza kai da kyar tace "not at All.. zuciyata zata fashe Meema..", Meema tace "please tell me what happened..?", Ruqayyah ta tashi zaune ta jingina da allon gadon tana sauke silent tears tace "Meema bazan taSa dawowa daidai ba indai Dearest bai dawo gareni ba..", da mamaki Meema ke kallonta tace "waye kuma Dearest...?", Ruqayyah tace "Dr..", Meema ta ?an?ance ido tace "wai Dr Uthman wanda aka fasa aurenku..?", Ruqayyah ta gyaWa kai hawaye na zuba idanunta, Meema was very shocked, kan uba anya Ruqayyah kalau take, Meema ta mayar da hankalinta sosai kan Ruqayyah tace "sister ba ke kika gudu sbd ba kya son auren ba..", Ruqayyah ta girgiza kai tace "wllh tllh ba guduwa nayi ba, wai wane mashahurin ma?aryacin ne ya la?aba min wnn sharrin yake yamaWiWi dani wai bana son aure na gudu, nifa bance bana son auren ba wllh Allah..", Meema tayi ajiyar zuciya tace "what are you trying to say sister..?", Ruqayyah tayi shiru ba tace komai ba, Meema na kallonta da kyau tace "toh a fahimta ta yanxu dai so kike ki auri Dr ko..?", Ruqayyah ta gyaWa kai tace "amma ya zanyi sister, na rasa inda zan dosa, Dr ya?i ya kulani, Daddy yace zai auramin Dauda bacogala, har gidan sister Kulsoom naje itama wai tace na ha?ura da Dr, kiji fa wai na ha?ura.. anya kwa ta san mene ne so..", Meema tace "me sister Kulsoom din tace miki..?", Ruqayyah ta share hawayen idonta ta shiga gaya mata ydda sukay da Kulsoom lokacin da taje gidanta, Meema ta jinjina kai tace "gaskiya ta gaya miki wllh, kuma nima na goyi da bayanta, babu ta yadda za ai Dr ya dawo gareki Ruqayyah, karfa ki manta ranar aurenku kika tsallake kika barsa, yanzu dan yace baya sonki ni banga laifinsa ba wllh, ke kika jawa kanki, zan ?ara akan abinda Kulsoom ta gaya miki kawai kiyi ha?uri ki rungumi sorry, Allah ya baki wanda ya fisa...", katseta Ruqayyah tayi da faWin "yaushe kika fara shan wiwi da Sholisho..?", Meema tace "what..?", Ruqayyah ta daka wani uban tsaki tana zabga mata harara tace "ki bari duk ranar da kika ha?ura da justice sai ki gayamin haka..", ta sauka daga kan gadon ta shiga bathroom, Meema ta taSe baki tace "kece za kiyi ta zama a ?oshin wahala..", Ruqayyah ta fito wanka ta shirya cikin uniform dinta, gwara dai ta fita aiki duk da yau ma ba tayi niyyar zuwa ba, handbag dinta ta Wauka ta fita Wakin, Haj Safiyya ta tarar da Meema a palour suna breakfast, Ruqayyah ta dur?usa ta gaidata da ladabi, Haj Safiyya tace "lfy lou Ruqayyatu, ya jikin naki..?", Ruqayyah tace "da sau?i..", Haj Safiyya tace "ba dai fita za kiyi ba..", Ruqayyah tace "wajen aiki zan tafi..", Haj Safiyya tace "toh za dai ki iya zuwa ko..?", Ruqayyah ta gyaWa kai tace "Eh" da haka ta tashi ta nufi door, Meema ta bita da kallo. Ruqayyah na zuwa hospital ta fara aikinta, dan Nurse Jiddah ta gaya mata daf ake da bata query, tana tsaye gaban bed tana shirya post Anesthetic bed, forcep dake hannunta ta ajiye cikin tray tana jin wani jiri na ?o?arin Webeta, duk dai dagewa take tana so tayi aikin, luu tayi baya zata faWa kan suction machine tayi saurin dafe bed, wani Nurse namiji da yake ward din ya iso inda take yace "are you okay...?", ta girgiza kai tace "partially", yace "alright ki wuce station i will handle it..", tace "thank you in 10mins za a kawo patient din daga surgery..", yace "alright..", Ruqayyah ta wuce station ta kwanta a room dinsu na female Nurses dake asibitin.

&Washe gari da yamma Nurain ya isa gidansu, yana shiga main palour ya tarar da Sakeena a zaune, daman yaga motarta a compound, ?arasa shiga palourn yayi ya zauna opposite to her yana kallonta, tace "brka da shigowa brother, ya sister na..?", yace "she's great alhmdllh...", ta gyaWa kai tace "good to yaushe zaka kawo min ita..?", ya Wage thick eyebrows dinsa yace "sooner or later", Sakeena ta gyara zama tana kallonsa tace "brother serious talk how is the girl..? ba wani matsala ko..?", ya sauke ajiyar zuciya yace "i can't say all is well amma dai kinsan she is not my choice and not my type, alfarma kawai nake mata na zauna da ita snn kuma sbd Abba..", babu wani kwana kwana ya fadi hakan don yadda suka saba da Sakeena baya iya Soye mata komai kuma baya mata ?arya, Sakeena tayi jim don tinda yace mata haka tasan hakan ne, shi kam wayarsa ya ciro yana dannawa, Waxu ne suke mgana da Mami shine Mami tace ta tmbayesa tinda tasan ydda suke dashi, dan Mami tana suspecting kamar auren is not stable, Sakeena tace "brother..", still yana latsa wayarsa yace "Na'am", shiru tayi ba tace komai ba, ya Wago ya kalleta ganin kallonsa take ya waro ido yace "yess..", ta mayar da attention dinta kacokan kansa tace "why are you saying that... the words choice and type bai kamata ka ambace su ba, gwara ma dai favor din, brother idan fa baka saki jiki da ita ba babu ta yadda za ai ku saba, kaga ita maca ce zata ringa shakkarka ko kuma ta?i sakin jikinta da kai as her husband, kaga dai ba tada wani aibu physically and she is beautiful masha Allah, halinta kawai zaka karanta shknn fa kuma am very sure she must be a good girl with that innocent face..", wani murmushi yayi jin abinda ta faWa, wai she must be a good girl with that innocent face, chab lallai ba tasan wace ce yarinyar nan ba, Calmly yace "Ohh yeah really..", Sakeena ta haWe gira tace "bafa joke nake a nan ba..", yace "yeah nima ai ba wasa nake ba, wollah alfarma na yiwa yarinyar nan kuma sbd Abba nake zaune da ita, ni a yanzu ma aka bani pen da paper tsaf xan yankar mata ticket... ammafa sai Abba ya yarda.. kinga da zaki temakamin ki masa mgana ya yarda na saketa da na baki tukuici.." yana gama faWin haka ya tashi ya nufi stairs yace "i have something to do..", Sakeena ta bisa da kallo tace "hey come back here am not done with you..", ya juyo yana kallonta sai kuma yayi murmushi yace "saidai ki canza topic bansan maganar wollah", Sakeena was shocked tace "ita kwa zamu cigaba..", bai ce mata uffan ba ya wuce zai hau stairs sai kuma ya fasa ya dawo palourn yana kallonta yace "where is our Mami..?", ta juya hannu alamar ban sani ba, Sangaren Mami ya shiga, after like 10mins ya fito ya haura sama, babu jimawa Mami ta fito, tana kallon Sakeena tace "nan kika zauna daughter..?", Sakeena tace "dana fito wajen Abba shine na zauna nan kawai..", Mami tace "Ohk" lokacin da ta zauna, Sakeena ta buWe wayarta ta shiga message ta haskawa Mami credit alert daya shigo 30mins back tace "from Abba", Mami tace "keda partner din naki za a bari knn..?", Sakeena tace "yeah, nasan damuwar Abba grandkids dinsa kuma fa da can wajen paternal grandma dinsu zan kaisu, nayi shirina mu keta haxo, amma yace nan da 5 months insha Allah sai mu tafi da Nurain with his wife..", Mami ta gyaWa kai tace "Ohk", Sakeena tace "Mami i talk to him fa, in my view ba wani matsala insha Allah..", Mami tace "are you sure..?", Sakeena ta ?ir?iri fake smile tace "Sure", Mami tayi ajiyar zuciya tace "toh alhmdllh, bana san wata tangarWa ta faru a auren ne..", Sakeena ta sake yin wani fake murmushin tace "ba abinda zai faru sai alkhairy insha Allah". kafin magrib Sakeena ta tafi, as usual Nurain bai bar gidan ba saida ya yiwa Maminsa sallama. washe gari da safe Nurain na zaune palourn downstairs yana shan coffee, Hajar ce ke sakkowa daga kan stairs, saura step biyu ta kai ?asa sai kuma ta dakata tana kallon palourn, Nurain ya sauke cup of coffee da ya kai baki ya dubi stairs din, da sauri ta sauke idonta ?asa sai kuma ta juya a hankali zata koma sama, lower lip dinsa ya cixa painlessly, daga throat maganar ta fito bayan ya runtse idonsa ya buWasu a hankali yace "Hajar..", cak Hajar ta tsaya amma bata juyo ba tana ri?e da railer, a hankali ta juyo ta kalli palourn sukay ido huWu, ta juyar da kanta tana wasa da hannunta dake ri?e da railer, Nurain ya tashi daga kan sofa walking towards the stairs yace "let's work together", ta zuba masa lulu eyes dinta tace "work together as in how..?", yace "young lady nasan ba kya san zama anan ko..? i mean ba kya son auren..", gyaWa masa kai tayi tace "sosai ma kuwa" ta haWe girarta mai kyau tamkar wcca aka zana mata ita, ya jinjina kai yace "same here, as i said let work together, kina jina yanzu ki kawomin jotter da pen dana baki..", tsuro tayi tana kallonsa lokaci guda kwanyarta ta amsa, biro da takarda, da sauri ta juya ta haura sama, babu jimawa ta dawo da jotter with pen ri?e a hannunta, yana zaune kan exclusive sofa ta dawo, tunani yake is he doing the right thing, ajiye masa pen da jottern tayi ta koma gefe ta harWe hannayenta, ya Waga kai ya dubeta yace "then listen, abinda nake shirin yi yanxu shine zanyi ending komai dake tsakaninmu, zan rubuta miki saki, ni da ke kowa yayi rayuwarsa munyi freeing juna, kin fahimta..", tinda ya fara magana take kallonsa, da sauri ta gyaWa kai tace "da kwa ka kyauta idan ka sauwa?e mana", yayi ajiyar zuciya yace "but idan na rubuta duk abinda ya biyo baya kece za kiyi bearing consequences din...", without thinking twice tace "na amince..", daman abinda take so knn, wani nishadin daWi ne ya tsarga mata zuciya, Nurain ya dauki biron da jottern ya Wora kan Centre table, buWe jottern yayi ya Wora pen ya fara rubutu.....
'?

Masu comments a ringa yi kullum Please ku sani ba doc ne a ajiye ba, sai nayi typing nake posting, snn kuma am occupied kawai dai ina squeezing inayi ne, plxx be patient... more love >?p?
=؛? HAJAR =؛?

{58..}
A hankali yake rubutun, Hajar na tsaye ta ?urawa hannunsa idanu, Alla Alla take ya gama ya mi?o mata, shknn tinda safiya ce sai ta fara haWa kayanta da wuri, Allah ya rabata da wnn jarababben auren ta ruwan sanyi, Nurain ya dakata da rubutun ya ?urawa papern ido, ya sauke numfashi lokaci guda ya Waga takardar ya fara yayyagata, Hajar ta zaro ido ganin abinda yake tace "meye haka kuma..?", bai ce mata uffan ba ya cigaba da yaga papern, saida ya mata gutsi gutsi ya watsar da ita nan kan Centre table din, with speed ya tashi ya haura sama, Hajar tabi bayansa da kallo wasu hawayen ba?in ciki suka ciko mata idanu, bata san lokacin da ta fashe da kuka ba, ita taga samu kuma taga rashi, shknn ya yaga shedar da zata nuna cewa babu aure a tsakaninsu, to wace shaida ma ai bata saku ba ma tinda ba taga me ya rubuta ba, jar uba knn dai auren yana nan daram ko girgiza bai yi ba, zubewa tayi a ?asa ta shiga rafsa uban kuka sai kace wacca akaiwa mugun duka, saida taci kukanta ta ?oshi sai kuma taja jiki ta matsa kusa da Centre table din tana kallon pieces din takardar, shesshe?a take a hankali ta fara ?o?arin arranging din papern wai ko zata gane mai ya rubuta, saidai fa abin yafi ?arfin ?wa?walwarta don kwata kwata ta kasa gane farko ma bare aje ga tsakiya ballantana ?arshen rubutun, har alphabets din ma bata iya ganewa sbd yadda yayi rubutun sai kace prescription, takaici yasa ta tattare pieces din takardar ta shiga kitchen ta kunna gas ta barbarWa takardar ta ?oneta, fitowa tayi daga kitchen din tana cika tana batsewa, still ta tsaya a bakin ?ofa sakamakon amsawar da brain dinta tayi, gsky tayi ragon azanci, da ba saita ajiye pieces din in yaso ta nunata a matsayin shaida, sai tace itace ta yaga amma ba a cikin hayyacinta ba, da sauri ta koma kitchen din ta matsa gaban gas, ta ringa kallon tokar papern tana jin haushin kanta, tamkar wacca kwai ya fashewa haka ta fito ta haura sama, tsaye tayi tana kallon huge sliding door din shiga Sangarensa, ta koma ta jingina da bango still tana kallon ?ofar, after like 10mins saiga shi nan ya fito, he changed into sweat pant and white shirt irin dai shigar da yake ta zaman gida, har wani coiled black hair dinsa yake sbd yadda yaji oil yana shining, kallo Waya ya mata ya dauke kai ya rufe ?ofarsa, ya zura hannunsa a pocket ya wuce zai sauka downstairs, da sauri tace "kace fa zaka rubutan takardar kuma fa baka bani ba...", cak ya tsaya kafin ya juya yana kallonta, ganin yadda idonta ya haura ya taSe baki don yasan tabbas halin nata tayi, ya Wage gira yace "wace takarda kike magana akai..?", ta haWe rai ta buWe baki da nufin


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login