Showing 123001 words to 126000 words out of 252707 words

Chapter 42 - HAJAR COMPLETE NOVELS By Nafisa Yusuf Nagoda.doc

yayi ya nufi stairs din.....
'?
Join my WhatsApp group =?G?
=؛? HAJAR =؛?

{55..}
&Washe gari Monday Nurain na zaune office dinsa yana duba patient, yana gama duba patient dake office din kira ya shigo ta wayar landline, picking yayi yace "yess", Secretaryn sa Haleema tace "sir A Nurse tana son ganinka..", yace "i thought it is something important, next patient ya shigo.." bai jira cewarta ba ya katse kiran, Haleema ta ajiye landline din tana kallon Ruqayyah da tayi tsuru tsuru a gabanta, duk ta rame kamar ba Nurse Ruqayyah ?ar gayu ba, yanzu gayun ma baya amsarta ko tayi, Haleema tace "A Nurse ki Wan jira a waje yace Patients yake dubawa..", Calmly Ruqayyah ta gyaWa kai tace "Okay", tinda dai yace ta jira ai mgana ta ?are, knn zai saurareta idan ya gama duba patient din, fita tayi daga office din ta zauna kan silver chair dake waje, tanata zaune a wajen har patient din da suke bin layi suka ?are daman su 20ne, wayarta dake cikin scrub pocket ce tayi ringing, ta ciro wayar tana kallon mai kiran kafin tayi picking ta kara a kunne tace "ina ji Jiddah..", Nurse Jiddah tace "haba Ruqayyah ina kika tafi haka, station din fa babu kowa, Amina ta riga tayi miki handing over fa, gashi can ma ward din da kike kula dashi lokacin yiwa diabetic patient din nan insulin ya cika, ya kamata kixo ki masa yaci abinci dan Allah...", Ruqayyah ta lumshe idonta dan kanta ne ya sara tace "Jiddah dan Allah kije ki masa allurar ni na Wan fita ne bana nan, zan jima kafin na dawo in yaso nayi night duty...", Nurse Jiddah ta taSe baki tace "Au haka kika fita bayan ga jakarki nan da Abayarki ina gani, ko dai haka kika fita ?indu ?indu with Scrub...", Ruqayyah tace "to dai bana cikin department din ina can Pediatric department..", Nurse Jiddah tace "Ohk, toh gsky this is the last tsakani ga Allah, ke kaWai kike raSarSashe albashinki..", Ruqayyah tace "thank you..", Nurse Jiddah dai ta kashe wayar tana tsaki, Ruqayyah ta mayar da wayar pocket, ta Waga kai tana kallon ?ofar office din, tashi tayi kafin ta buWe aka rigata ta ciki, Nurain ne ya fito ri?e da briefcase dinsa don ya gama gida zai wuce, Ruqayyah ta dubi hannunsa ganin briefcase tace "are you leaving...?", ko kallonta beyi ba ya wuce zai bar wajen, ta bisa da sauri ta ri?e hannunsa hawaye har ya ciko idonta, wani mugun kallo ya watsawa hannun nata with stern voice yace "hands off..", ta cikasa sai kuma ta sha gabansa tana kallonsa, tace "Do you know how much i love You..?, do you know how long i waited to see you...?, why do you not listen to me...?, i don't want to part from you again, so you must listen to me dearest.." tana gama faWin hakan ta fashe da kuka tana dukansa a chest painlessly, kukan da ta fashe dashi ne ya janyo attention din few mutanen dake wajen, har lokacin bata dena rusa masa kuka ba, janta yayi zuwa office dinsa, Haleema da ta gama shiryawa itama zata tafi ta bisu da ido, Nurain ya ajiye briefcase din kan table ya shafa hair dinsa kafin ya zura both hands dinsa a pocket, juyowa yayi yana kallon Ruqayyah da take kuka bil ha??i, ya sauke ajiyar zuciya yace "damn it.. what are you doing Ruqayyah..", ta zuba masa jajayen idanunta da muryar kuka tace "ai ka ?i ka ha?ura sai ha?uri nake baka Dearest..", ya girgiza kai yace "we already sort it out Ruqayyah, am not keeping any grudge against you, ki dena bani ha?uri ni babu abinda kika min, in ma akwai toh na ha?ura..", tana shesshe?a tace "ka ha?ura toh me yasa kake avoiding dina, ka dena picking calls dina, idan nazo office dinka ba a barina na shigo..", ya dubi ceiling feeling confuse yace "Ruqayyah..", bata amsa ba amma ta zuba masa idanu, yace "Allah ma ya gani am done with you, I don't have any feeling for you now and forever, please let me be, bana so na miki abinda baza kiji daWi ba so stay far away from me, kawai abinda ya wuce ya riga ya wuce, abu Waya na sani yanxu akanki shine kina cikin team members dina bayan haka babu komai... kiyi abinda zai fisshe ki A Nurse.." yana gama faWin haka ya Wauki briefcase dinsa ya bar office din with speed, like one living statue haka Ruqayyah ta daskare a tsaye, tamkar an dagargaza zuciyarta haka take ji, Haleema ce ta shigo tana kallonta tace "amm zan rufe office din..", Ruqayyah ta ja ?afa ta fito, da ido Haleema ta bita tana girgiza kai tace "sai ki ha?ura dai tinda tin farko kin yiwa kanki sagegeduwa..", Ruqayyah ta juyo ta kalleta dan ramm taji abinda ta faWa, sai kuma ta juya ta cigaba da tafiya. Ruqayyah bata zauna a asibitin ba haka nan ta shirya ta tafi gida, Ruqayyah na zuwa gida ta gamu da tashin hankalin da ya shalleke tunaninta domin kwa sa?onta ya isa ga Daddy, daman tin kwanaki biyu da zuwan Ruqayyah kadunan Kawu ya kira Daddy yace yana son ganinsa, Daddy yace masa zaizo insha Allah ranar Litinin, toh yau Monday da wuri Daddy ya shirya ya tafi Kadunan don yaji kiran da ?anin mahaifin nasa ke masa, ba ?aramin fusata Daddy yayi ba, Kawu kawai mgana ya masa ba wata mai zafi ko Wumi ba, shi takaicin Daddy wai har Ruqayyah ce zata kaisa ?ara wajen Kawu, knn ja dashi zatay, tinda ya Wauko hanyar kano bayan ya bar Kaduna nan ya kira Momy a waya, tashin hankalin da ta shiga ba kaWan bane, itama taji haushin abinda Ruqayyah tayi. Momy na zaune palour ta dafe kanta tace "Ruwayyah ki haWa kayanki ki wuce gidan Safiya..", Ruqayyah ta ?arasa palourn zuciyarta na bugawa tace "Momy sbd me dan Allah..?", Momy tace "kinje Kaduna wajen Kawu ko bakije ba..?", Ruqayyah ta sunkuyar da kanta tamkar munafuka, Momy ta daka mata wata tsawa tace "tambayarki nake malama", Ruqayyah ta koma ta manne da bango ta sunkuyar da kanta tace "naje..", Momy tace "innalillah wa'inna ilayhirraji'un, kin kyautawa kanki, ki wuce kiyi abinda nace..", Momy ta tashi ta shiga room dinta ta kira ?anwarta Haj Safiyya ta sanar da ita Ruqayyah zata zo, bayan ta gama wayar ta fito ta shiga room din Ruqayyah, zaune ta tarar da ita kan bedside ta zabga tagumi, Momy tace "kin haWa kayan Ruqayyah..?", Ruqayyah tayi firgigit bayan ta fito daga duniyar tunani tace "A'a", Momy ta gyaWa kai tace "toh kar kiyi sauri ki zauna har ya dawo gidan ya sameki, wllh babu ruwana, dalla malama tashi ki shirya..", Ruqayyah na sharar kwalla ta gama haWa kayanta set biyu a ?aramar jaka, duk Momy na tsaye tana kallonta, da jakar a hannunta Momy ta iza ?eyarta har palour, ganin batada niyyar fita Momy ta turata waje tace "maza ki tafi.." da hka tayi banging door, Momy na sane tace Ruqayyah ta bar gidan, tasan ran Daddy ya Saci matu?a, gwara idan ya Wanyi sanyi ta dawo koma wane hukuncin zai mata ita ta janyo amma dai banda lokacin da ransa yake tafasa.

&Bayan Hajar ta idar da sallar la'asar ta sakko downstairs, kitchen ta shiga ta Wakko abincin da ta dafa tin Wazu, har zata haura sama da warmer din sai kuma ta fasa ta zauna nan palour, tana fara cin abincin saiga ?arar bell, ta ajiye spoon din hannunta tana kallon door, saida aka sake danna bell din snn ta tashi still tana kallon ?ofar, toh Allah yasa dai a buWe take tinda dai tasan kullum a rufe take, da wnn tunanin ta isa kusa da ?ofar ta murWa handle, zaro ido tayi jin a buWe take, tana buWewa tayi arba da Hafsah, Hajar ta gwalo ido don bata taSa tsammani ba, cike da murna tayi hugging dinta tana welcoming dinta, Hafsah dai kawai binta take da kallo ganin yadda ta canza, ta kusa linka ainahin farinta har wani pink pink take, a palour suka zauna Hajar tace "yasu Humairah da Anty..?", Hafsah tace "suna nan lfy wllh.." sai kuma ta ri?e haSa tace "kinyi luf luf abinki, wnn lu?ui lu?ui haka..", Hajar ta galla mata harara tace "ke nan din ya miki kama da wajen da mutum zai wani luf.." tashi tayi ta shiga kitchen ta kawo mata ruwa da lemo, Hafsah tace "ke kullum wayarki a kashe..", Hajar ta taSe baki tace "hmm ta lalace..", Hafsah ta ringa kallon palourn tace "shi bai sayar miki wata ba..", Hajar ta yamutsa fuska tace "shi din wa.. Hafsah knn..", Hafsah ta Wauki lemon ta zuba a cup tasha, after like 40mins Hafsah tace "toh na gaisheki Hajar, tafiya zanyi bazan kai magrib ba, unguwar nan napep wahala yake, kinga ma waccan karon da nazo ban samu napep ba..." sai kuma tayi shiru tana murmushi tace "kinsan kwa wane ya mayar dani gida a ranar..", Hajar tace "sai kin faWa..", Hafsah tace "wnn mutumin da muka hadu dashi a Supermarket, Ahmad din nan..", Hajar tace "ohhh Allah sarki..", Hafsah ta sauka daga napep bayan tazo gida, handbag dinta ta bude ta basa kuWinsa, kallon motar dake parke a gefen titi ta ringa yi, ta dai amshi canjinta ta zaga wajen slapp zata shiga gida, buWe motar yayi ya fito yana kallonta, ya rufe motar yabi bayanta Calmly yace "Assalamu alaikum..", no doubt zamm ta Wauki muryar, amma she was shocked, a hankali ta juya tana ?ir?irar murmushi tace "Wslm..", ya shafa kwantaccen beard dinsa yace "how are you doing..?", tana Waga kanta taga Abdallah yana tsallakowa daga other side din titi, zuciyarta ta buga da ?arfi, Wauke kanta tayi tace "lfy alhmdllh ngd..", yace "masha Allah daman i am passing by nace bari mu gaisa da friend dita tinda bata picking call a gaisa..", daidai nan Abdallah ya tsallako, jimm yayi yana kallonta sai kuma ya wuce cikin gida, Hafsah tayi murmushi tace "toh ngd sai anjima", ta juya ta shige gida da sauri, Ahmad ya bita da kallo bayan wani lokaci ya shiga motarsa ya bar unguwar, Hafsah na shiga gida ta tarar da Anty zaune a palour, Abdallah ma na palourn zaune kan 1sitter yana cin abinci, ta kalli position din da yake sau Waya sai kuma ta dubi Anty tace "Anty na dawo..", Anty tace "toh sannu da zuwa ya Hajar din..?", Hafsah tace "wllh sumul take Anty, tayi kyau abinta..", Anty tace "masha Allah..", Hafsah ta dubi jakarta jin wayarta na ringing, tashi tayi ta shiga room dinsu tana satan kallon Abdallah da ya bita da kallo, Anty ta Wauki wayarta dake gefenta ta kira Umma, bayan sun gaisa Anty tace "ya jikin Mu'azzam..?", Umma tace "jiki alhmdllh ai yaji sau?i sosai..", Anty tace "toh an gode Allah, ai Hafsah na tura taje ta duban ?ar tawa kafin naje da kaina..", Umma ta numfasa tace "ba wata matsala ko Jamilah..?", Anty tace "lfy lou wllh Adda, kinsan ?ar tawa ha?uri wala, idan da gaske ba zaman lfyar da tini ta taho fa, amma tinda kika ga shiru toh lafiya ce gsky..", Umma tace "nima nayi tunanin hka..", Anty tace "yanzu idan an kwan biyu sai naje da kaina..", Umma tace "toh shknn ngd Jamilah..", Anty tace "ba komai Adda, sai anjima.." da haka sukay sallama.

&Bayan tafiyar Hafsah Hajar ta koma room dinta, two hijab sai kayan baccin da ta saka ta Wauka ta shiga bathroom dasu ta wanke, bayan ta gama wankewa ta fito dasu a cikin bucket ta sauka ?asa don ta shanya, ta main door ta fita daga building din, can backyard taje ta shanya snn ta dawo ciki, tana dawowa daman an kira sallar magrib don haka tayi sallarta, can wajen ?arfe tara harta yada pillow zata kwanta ta tina da kayan shanyarta, tashi tayi ta le?a window taga garin akwai hadari, hijab ta saka ta fito daga room dinta Walking like a chameleon ta sauka, tsaye tayi a palourn tana kallon Tv da ta gani a kunne, ga kuma Lap top kan hannun kujera itama a kunne, ta taSe baki ta nufi ?ofa, zagawa tayi can backyard din ta kwaso kayanta, tana tafiya tana kallon gidan in it's night view, fitilu ko ina sai kace rana, tsaye tayi daidai window din kitchen tana kallon ciki, lokaci guda ta matsa gaban windown tana kallonsa, he is in his pajamas making coffee, ta ringa bin duk abinda yake da kallo tana taSe baki, a gabanta ya gama haWa coffeen ya tsiyaye a cup ya fita bayan ya kashe coffee makern, ta zagayo ta buWe ?ofa ta shiga, Nurain ya juya yana kallonta, Wauke kanta tayi ta nufi stairs abinda, ya haWe thick eyebrows dinsa ya cigaba da abinda yake jikin Laptop. washe gari Hajar na idar da sallar asuba ta fito, har lokacin gari baiyi haske ba, tana shiga kitchen ta buWe cupboard ta ciro coffee powder, har wani nishadi take yau zata sha abinda take marmari, switch din coffee maker ta kunna, No milk no sugar da tsurar cocoa powder tayi amfani, tana gamawa ta tsiyaye a cup, harda wani Wan karkaWa cup din wai ya huce da zafi, tana sha ta yamutsa fuska bayan ta guntsesa a baki, wani mugun Waci ne ya kaure mata a baki, da sauri ta tofar da na bakinta acikin sink, ta kunna pampo ta kuskure bakinta, kallon cup din worst coffeen da ta haWa tayi tace "chaSWi jamm nida maWaci..", tini ta sakar masa ruwan pampo ta wanke cup din ta fita daga kitchen din tana gyatsine. ?arfe bakwai da rabi Nurain ya sakko downstairs, yana zaune a palour yana shan sahibin nasa, ya duba time ta faskeken agogon dake manne a palourn, tashi yayi ya fita compound zai sanar da Inuwa ya wanke masa wheels din motarsa kafin ya fita. tinda Hajar ta hango cup din daga sama tayi sauri ta sakko, ehen ai kam sai tasha kuwa, ta isa inda cup din yake ta Wauka, tini ta kwankwaWe tass ta ajiye kofin a inda yake, saidai tana Waga kanta sukay ido hudu dashi, yayi folding hands dinsa yana kallonta babu ko ?iftawa, Wauke kanta tayi ta sha kunu irin ai nawa ne din nan, ta juya zata bar wajen kawai taji saukar muryarsa mai zurfi a kunnenta "Ke.. dan kinga jiya ban miki mgana ba shine ma yau kika aikata ko..?", ta juyo tana Wage gira babu ko nadama a fuskarta tace "Au akan wnn maWacin...", ya tsuke ido irin what, ta juya lulu eyes dinta tace "toh wllh sai nasha wani yace ka ringa ajiyewa", ta galla masa harara ta wuce zata hau stairs, bai bata damar hakan ba dan tini yayi blocking front dinta, ta Waga kai tana kallon how huge he is, gata wata dwarft a gabansa, Calmly yace "yeah no problem tinda kinada abin biya young lady..", da sauri ta Waga kai ta kallesa, lokaci guda brain dinta tayi booting on, ta zaro lulu eyes dinta kafin ta ja da baya tana girgiza kai, a karo na farko da ta taSa ganin murmushinsa amma kuma sai ya mata kama dana mugunta yace "sai kin biya..", da gudu ta koma cikin palourn tana ?o?arin zagayesa ta haura sama nan ma ya hana hakan, ganin zai cafkota ta tsala wani uban ihu ta ruga corridorn shiga guest room, sosai zuciyarta ta buga ganinsa a corridorn ya biyota, ai kam ta murWa ?ofar guest room din ta shige da sauri tayi banging door, saidai fa unfortunately for her taga babu key ajikin ?ofar, ta jingina da jikin ?ofar ta danne with all her strength, sai kace wanda ya tura wani bicycle haka ya tura ?ofar ya buWe, wani uban ihu ta tsala ta koma can ?arshen Wakin tana zaro ido tamkar Sera a buta, ya mayar da ?ofar ya rufe ya tsaya yana kallonta yace "ke da kike da abin biyan bashi young lady mene kuma na tsorata, ohh c^mon ki biya ko na fanshe abina..", ta shiga yarfe hannu tace "na shiga uku".....
'?
********************** **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
************************* **********************

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.

Email > aihausabooks@gmail.com

******* FOLLOW US ******

Facebook: Ai Hausa Novels

Twitter: Ai Hausa Novels

Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels

WhatsApp Number: 08138873799


Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafinmu ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.

********************** **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** **************************
=؛? HAJAR =؛?

{56..}
Ko one step bai ?ara ba daga inda yake tsaye jikin ?ofa yace "mene kuma na shiga uku.. zaki biyani ko sai na fanshe..?", bakinta na rawa sai kace an jona mata shoking tace "zan biyaka..", yace "with what..?", tace "shi shayin naka dashi zan biya ka", yayi nodding kansa yace "alright muje ki bani", ta gyaWa kai da sauri, har zufa ta ji?a mata goshi gashin wajen ya sake kwanciya da santsi akan ydda yake na asali, ganin bata motsa ba sai muzurai take yace "kona fanshe ne..?", ta yarfe hannu ta girgiza kai tace "A'a dan Allah..", ya matsa daga bakin ?ofa yace "toh zo ki wuce..", ta gyaWa masa kai kafin ta fara tafiya a hankali, tana zuwa bakin ?ofar tace "dan Allah karka taSani..", yayi folding hands dinsa yace "wuce nace..", sum sum ta fita daga Wakin yana biye da ita. tana zuwa palour ta fakaici kallonsa ta gefen ido, taga dai biye yake da ita kuma babu distance sosai a tsakaninsu, speed ta ?ara, ai kam yana ganin haka yasan akwai abinda take target, da mugun gudu ta Wiba zata haura sama, tini ya fixgota ai kam ta tsala ihu ta fara kiciniyar kwace kanta, ya tsuke piercing eyes dinsa yace "Ke..! you think am joking ba..", ta girgiza kai tace "toh ba nace zan biyaka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login