Showing 60001 words to 63000 words out of 252707 words

Chapter 21 - HAJAR COMPLETE NOVELS By Nafisa Yusuf Nagoda.doc

amma shine za kice na baki dubu talatin, wllh ban dasu ba nida dalilinsu...", Maimuna da ta tamke fuska tamkar tsohon ba?in hadari tace "yo kema knn, bare ni, wai dubu ashirin", Maama tayi kwafa tace "duk za kuci gidan ku, dani kuke zancen, toh wllh ko kun?i ko kun so sai kun bani kuWin nan, yanxun nan ma kuwa", Maimuna tace "nidai Maama saidai ki yanka ni amma ban dasu eheee", Nabilah dake sauraron su tace "anayi ina cin indomie, ni kam ko ta kaina ba a bi sbd ansan babu, Hajjajai maza ku buWe lalita hajiya Maama na jiran dumuss", Sa'adatu tace "ai kam dai baxa ta ji wani dumuss ba, Maama nidai kin san in ina dashi zan baki", Maimuna tace "nima dai in ina dashi zan.....", katseta Maama tayi da faWin "?arya kike uwar mamma?o, a gidan ubanwa kike ban iyee?, toh bari kuji in gaya muku karku zata ban sani ba, sarai nasan cewa ba makaranta kuke zuwa ba daga zarar kun fita sai ko waccen ku ta wuce shu'uninta, ko ku bani kuWi ko na gayawa Babanku, kuma kun san cewa Nasiru na gida, babu abinda ya shalleni haka zan bada fuska ya zane muku jiki, kai wllh har ziga mal zan ringa yi dan jikinku ya gaya muku, ni zaku mayar yarinya kucemin wai baku da kuWi..", Sa'adatu tace "to ki faWa mana ai nace miki banda su...", Maama tace "haka kika ce ko?", Maimuna tace "Maama ai gaskiyar knn", gyaWa kai Maama tayi ta isa bakin ?ofa ta Waga murya tace "Malammm", da wani mugun zafin nama Sa'adatu ta rufe mata baki, Maimuna kuma ta kama zaninta sai muzurai take, habawa ai Nabilah kifowa tayi daga kan gado sbd dariya, Maama ta kwace bakinta tace "zaku bayar ko a'a?", haWa baki sukay su kace "zamu bayar", Maama ta hura tukubar hanci tace "jikinku ya huta" ta fizge zaninta daga hannun Maimuna. daga waje Baba ke neman ba'asin kiransa da akay, Maama ta sake Waga murya tace "daman cewa nayi barka da hutawa". A take Maimuna ta buWe jakarta ta lalo duba ashiri ta mi?a mata a wula?ance, Sa'adatu kuma ta kira Zeenatu tana mata wata maganar ?irsa tace ta turo mata mutsabbai, da kyar Sa'adatu ta lusar da Maama cewa gobe da safe zata fita Pos ta ciro mata kuWin. Da sassafe kam Maama ta tayar mata da mandiran zuciya, haka ta fita tasha wahala harta nemo pos ta ciro kuWin ta kawo mata, tinda Maama taga dubu hamsin dumuss a hannunta ta fara shirin zuwa gidan Balaraba, ?arfe goma na safe ta fice don saida ta bari Baba ya fita, tana isa gidan abokiyar cin mushen nata ta azalzale ta, sharp sharp Balaraba ta shirya suka saSi hanya, tin ?arfe sha Waya suka fita amma basu dawo ba sai yamma li?is, gidan Balaraba Maama ta tsaya ta huta snn kuma ta amsa mata tambayoyin da take ta ri?onsu tin bayan fitowarsu daga wajen malamin tsamiya, ruwa kawai tasha ta hau surfa mata tambaya, Balaraba tace "kai Jama'a tinda fa yace aiki ya kammala to mgana ta ?are", Maama da idanunta sukay jajur tsabar wahala ta tafiyar mota da ?afa tace "da farko fa cewa yayi tabbas yaga ana biki, kuma aure sai an Waurasa", Balaraba tace "ai kece kika ringa cewa ga abinda kike so ayi, kinga kin ce masa a sawa yaron tsanar yarinyar kuma da ya duba allon bokancinsa yace miki hakan bazai yiwu ba sbd yaron akwai addini, ba za a iya samun galaba dashi cikin sau?i ba, idan kwa aka matsa to lokaci zai ?ure har ranar auren tazo ba a samu galabar ba, shine yace ya sami lagon yaron wanda dashi zaiyi amfani, kuma ma yace aiki ya kammala kawai ki jira lokaci", Maama ta sauke wata gauruwar ajiyar zuciya tace "yanzu dai ba matsala knn?", Balaraba tace "kwarai kuwa, ki saki jikinki ki shiga bidirin biki, daga gefe kuma ki zubawa sarautar Allah ido kiga ta inda Saraka zata Sullo", tin daga wnn moment Maama ta samu peace of mind, daga gefe guda kuma tana jiran ranar da faWima da shegiyar ?arta za suji kunya.

&Wani irin fresh Hajar tayi, fatarta tayi luwai luwai har wani she?i take sbd gyaran jikin da akai mata na sati biyar, ga wani sassanyar kamshi da yake tashi ajikinta, duk inda ta gifta sai ?amshi, ko a waje ta zauna sai ya Wauki lokaci ?amshin bai baje ba, ilahirin jikinta kamshi yake, gashinta kam tamkar gonar furanni masu ?amshi, babu inda take zuwa, ba ta shiga rana shiyasa gyaran yayi armashi, ko kitchen Anty ta hanata shiga, idan ma aikin za tayi iyakacinta palour da Wakuna amma banda gaban wuta da rana, Nura kam kullum yana kan hanyar zuwa, WaiWaikun ranaku ne kawai baya zuwa, ji yake tamkar ya janyo lokacin akay masa ita kawai, wata sha?uwa ce ta shiga tsakaninsu a wnn ta?in, Yau ma dai mai gyaran jiki tazo tayi mata ta gama ta tafi, toilet ta shiga tayi wanka, ta fito tana wani ?amshi na daban wadan ya gauraya da wanda take zubawa kafin shigarta wankan, zama tayi kan stool ta janyo sabon man da take shafawa na gyara fata da saka glowing, a tsanake take tattale fatarta da tayi wani laushi da santsi, ita kanta yaba kyan da tayi take a zuciya, Hafsa ce ta shigo hannunta ri?e da cup, ajiye cup Win tayi kan mirror tace "ki shanye yanxu ki bani kofin na mayar mata", Hajar ta Wauki kofin ta kwankwaWe ta mi?a mata empty, ( Ehen ba fa maganin mata bane, it's not good a bawa budurwa, maganin infection ne da cire dattin golden organs of a woman). doguwar riga ta material ta saka snn ta fita palour, zama tayi kan kujera tana latsa wayarta, tanan suke magana da zainab akan bikin musamman ma walimar da zatay, Anty ta fito da shirin fita da jaka a hannunta tace "ina Hafsa?", Hajar tace "tana kitchen", kitchen Win Anty ta shiga, bayan few seconds ta fito tace "na tafi", Hajar tace "A dawo lfy", tace "Ameen", snn ta fita, su Anty an shiga ruruma don yanxu bikin saura 1week, sha'anin jera gidan amarya suka karkata. A hankali Hajar ta dafe kanta tace "subhanallah innalillah wa'inna ilayhirraji'un" sakamakon gabanta da ya yanke ya faWi ba gaira ba dalili, sau huWu yana mata haka bayan zamanta a palourn, wayar ta ajiye ta mi?e ta tafi kitchen wajen Hafsa, Hafsa tace "Abu zaki Wauka ne?", girgiza kai Hajar tayi tace "nope nagaji da zama ni kaWai", Hafsa tace "kinga ki fita ynxu zan fito bari na gama zuba seasoning a miyar", Hajar tace "kawo na Sare miki maggin", Hafsa tace "A'a zanyi da kaina, Anty fa tace ki dena shiga kitchen", turo baki tayi ta buWe fridge ta Wauki ruwa ta fita, tana ?o?arin zama gaban nata ya sake faWuwa, nan ma dai Addu'ar tayi, har bayan Sallahr isha'i abinda take fama dashi knn, a hankali ta tashi daga kan dardumar da tayi sallah ta nannaWe, wayar tace tayi ?ara wanda ya razanata tsabar rashin sukunin da ya risketa a bazata, ta Wauki wayar tana kallon mai kiranta, ( ya sayyadi na) haka tayi saving, picking tayi ta kara wayar a kunne, ajiyar zuciya taji ya sauke snn yace "Hajar", tace "Na'am", yace "dan Allah fito na ganki, gani nan a ?ofar gida".......
'?

sorry 4d late update.

likes comments and share my novel widely.
=؛? HAJAR =؛?
by Feenerh_feeche

{30..}
Shiru tayi na some seconds kafin tace "tom" ta katse kiran, da dogon hijab din da tayi sallah ta fita, Humaira da Hafsa ne zaune palour, Abdallah ya fita masallaci salla, Hajar tace "Hafsa zan fita ?ofar gida", Hafsa tace "okay zuwa yayi knn?", gyaWa mata kai kawai tayi ta nufi ?ofa, ta ?etare small compound Win gidan ta buWe ?ofar gate ta fita, jingine ta gansa da jikin gate Win, street light ta haska masa fuskarta, yayi ajiyar zuciya yana kallonta sosai, jinginar da kanta tayi jikin gate Win itama tace "ina yini", tini hancinsa ya cika da scent Winta, da cool voice Winsa yace "lfy alhmdllh, ykk?", tace "am fine", ya juyo sosai yana kallon yace "Hajar", kanta a ?asa tace "Na'am", yace "karki bari azkar ya fita a bakinki, kinga dai ynxu zaki shiga ruruma, ki dage da Addu'a kinji", gyaWa masa kai tace "insha Allah", ta Wago ta kallesa tace "amma dai lafiya ko?", yayi ajiyar zuciya yace "alhmdllh", tace "ni kuma sai naga kamar you're not okay", keenly yace "partially", tace "me yake damunka?", murmushi yayi yace "ai tinda na ganki komai ya wuce, na dawo normal", tace "da gaske?", yace "uhmm", shiru ne ya Wauka na wasu ?an sakanni, ya katse shirun da faWin "toh me kika shirya a bikin?", ta girgiza kai tace "ba komai", yace "ba komai, babu abinda za kiyi?", ta gyaWa kai, murmushi yayi ya zaro envelope daga pocket Winsa, mi?a mata yayi yace "take", tace "meye wnn Win?", hade gira yayi yace "i said take", tasa hannu ta amsa tace "nagode", yace "good girl, toh shiga gida saida safe", tace "Allah ya tashemu lfy", har ta juya zata shiga sai kuma ta fasa ta juyo ta tsaya tana kallonsa kamar yadda shima yake kallonta, murmushi yay mata ta mayar masa snn ta shige. Ranar talata da yamma Hafsa ta rakata wajen salon, Anty tace tayi amfani da kuWin da ya bata, wankin kai na musamman akay mata, natural aka bar mata gashin, steaming kawai aka ?ara mata bayan wash and set, sai kyalli gashin yake da she?i, daman ba?i ne siWik shiyasa she?in yay yawa, Hafsa ma aka wanke mata nata, kafin magrib suka dawo gida, da wuri Hajar ta kwanta sbd ciwon kan da ya dameta uwa uba faWuwar gaban da take fama da ita, washe gari da sassafe wacca za tay mata lalle tazo, saida tayi breakfast wanda kawai turawa take snn ta zauna aka fara shaWana mata lallen, jan lalle kawai akay mata banda ba?i, inda za ai ba?in akay mata shi da ja, waoh lalle ya samu inda yake so wato farar fata ga kuma jiki yaji gyara, duk da yadda kanta ke ciwo haka ta jure aka rangaWa mata kunshinta, mai lallen ce ta yarfa mata kitso sirara mai kyau two steps, sha biyu na rana angama mata komai, tayi kyau harta gaji kamar a sace ta, kaf suka shirya suka wuce ainahin gidan biki sbd a ranar akwai ?ar gaWa da ?awayenta suka shirya. lfy ?alau aka gudanar da shagalin gaWa a wani kango da aka gyara tsaf dake bayan gidansu, washe gari Alhamis saura kwana Waya Waurin aure wato ranar Juma'a, a ranar akay walima wacca ta ?awatu matu?a daidai gwargwado, Hajar tasha kyau har ta gaji. Maama kam bata tsoma hannunta aka komai ba haka ?an ci ku bamunta, saidai fa zuciyar nan ba?i ?irin tamkar ta iblus.

&Baba ne zaune bisa bencin mai siyar da dankali da doya a bakin titi, mai dankali dake cin banWashen gurasa yace "mal Adamu gobe ne ko?", Baba yace "insha Allah, bayan Sallahr Juma'a za'a Waura", mai dankali yace "anan ?ofar gidan naka?", Baba yace "Eh", mai dankali ya lu?a wata ?atuwar yankan gurasa baki yace "so samu ayi a masallacin juma'a na unguwar nan, yafi sarari kuma ga albarkar mutane", Baba yace "Eh saidai nafi son a Waura a ?ofar gidana, ?ofar gidansu yarinya", mai dankali ya jinjina kai yace "hakan ma yafi wllh, Allah ya kaimu goben", Baba yace "Ameen". wata shimfiWeWiyar mota mai numfashi ce tazo ta wuce, har tayi nisa sai kuma ta dakata kafin ta dawo da reverse, adaidai saitin benci da Baba da mai dankali ke zaune ta tsaya, tsayuwar motar a wajen ya katse musu firarsu, mai dankali ya suWe hannu ya mi?e ya isa gaban motar sbd a zatonsa siyar dankalinsa ko doya za ai, tsaye yayi bakin motar yana gwalo ido yana jiran a buWe ayi masa ciniki, da yake glass din motar tint ne don haka ba'a ganin wnda ke cikinta, back seat aka buWe a hankali, wani mutum ne ya fito wnda yake sanye cikin wata shegiyar shadda, kawai kallon Baba yake kamar yadda Baban ma ya ?ura masa ido, mutumin ya saSa babbar rigar jikinsa yana micincina idanu, mi?ewa Baba yayi daga kan bencin, mutumin ya tako har kusa da Baba yace "Adam", Baba da shima ya ganesa ainun yace "Muktar", Alhj Muktar ya mi?awa Baba hannu sukay musabaha yace "duniya mai yalwa, Adam daman kana garin nan?", Baba yayi murmushin manya yace "Muktar ai kai zan tambaya daman kana garin nan, tinda nidae a sanina ai kana Abuja", Alhj Muktar yace "shekara ta sha biyar da baro Abuja na dawo Kano", Baba yace "ba masaniya", Alhj Muktar ya gyara babbar rigarsa ya samu waje ya zauna kan benci, Baba ma ya koma ya zauna, Alhj Muktar da yake jin wani daWi na ganin aminin nasa da ya jima yana nema yace "ya bayan saduwa, ya iyali?", Baba yace "bayan saduwa sai alkhairy, iyali lfy alhmdllh an gode Allah, ya naka iyalin Muktar?", Alhj Muktar yace "Alhmdllh, amma dai ba'a kano kake zaune ba?", Baba yace "kano nake zaune Muktar", Alhj Muktar yace "baka koma Yola ba knn?", Baba yace "Eh, nan nake rayuwa da iyalina saidai dangina na can Yola", Alhj Muktar yace "masha Allah" ya faWi hakan yana duba tsadadden wrist watch Win hannunsa, Baba yace "shekara da yawa Muktar, ban taSa tunanin zan sake ganinka ba", Alhj Muktar yace "ikon Allah....", bai ?arasa maganar ba drivern sa ya fito hannunsa ri?e da waya dake tsuwwa, russuna yayi ya mi?a masa hannu bibbiyu cike da girmamawa yace "ranka shi daWe ana kira", Alhaj Muktar ya amshi wayar snn ya Waga kiran, maganar da bata wuce ta minti Waya ba yayi ya katse yana kallon Baba yace "Adam, zan sameka gobe a nan wajen", Baba yace "Eh to, ba damuwa zaka samen", Alhj Muktar yace "ko dai anan unguwar kake da zama?", Baba ya gyaWa kai yace "a nan nake", Alhj Muktar ya jinjina kai yace "to ko bayan nan akwai wani wajen da zan iya samunka, insha Allah gobe fa zan dawo Adam", Baba yace "idan ma baka sameni anan ba, kana tambayar gidan gini shknn", Alhj Muktar yayi ajiyar zuciya ya mi?e, ya bawa Baba hannu sukay sallama snn ya doshi motarsa da driver ya buWe masa ?ofa, mai dankali da ke daskare tin Waxu yaja baya gudun kar a markaWe masa ?afa, saida motar ta Sace snn ya juyo ya kalli Baba, ya ?araso ya zauna yace "mal Adamu, wnn mutumin fa?", Baba yace "mutumin arzi?i wanda ya gaji ainihin arzi?i ba ?an tashi firgigit ba, Muktar knn", mai dankali ya kasa kunne yace "yo Mal Adamu aini a duhu ka sake dulmiyani, ai ban gane me kake nufi ba", Baba ya dubesa yace "hmmmm, Idi knn" daga haka bai sake cewa komai ba.

&Ranar ta yau itace fa Juma'a, ranar Waurin auren Hajar, tin bayan sallar asuba ?an uwan Umma suka Wora sanwa, tuwo suka mullu?a aka WaWWaura shi a leda aka zuba a ?atuwar warmer, dabgen miyar taushe da taji tantakwashi itama aka juye ta a warmer, bayan nan aka shiga tuyar wainar shinkafa da sinasir, ga kuma gurasa da Mu'azzam ya kawo buhu guda. kai Hajar dai mai ?ashin arzi?i ce, tinda aka fara shagalin bikinta ba ai abu na ?aranta ba duba da cewa gidansu ba masu hannu da shuni bane, komai an yisa cikin wadata, wnn magana ake ta masu arziki da yalwar zuci bata masu kuWin banza da basu ciyuwa ba saidai a fito daga gida ana ?ombo, yo wasu masu kudin ma ai gidan su living hell ne. da gyatsine Balaraba ta shigo tsakar gida, duk wanda ke tsakar gidan nan kallon hadarin kaji tayi masa kafin ta faWa Wakin Maama, a karo na farko da Maama ta washe ha?ora tin wayewar gari, Balaraba tace "wai haka aka mayar miki da gida sai kace na mahaukata Rabii", Maama ta taSe baki tace "uhmm, ba?in cikin da nake sha?a yafi ?arfin kwatance", Balaraba ta ?arewa Sa'adatu da Maimuna dake bacci kallo tace "su kuma basu tashi ba", Maama tace "ai jiya ba a barmu munyi baccin kirki ba a gidan nan", Nabilah da ke malelewa ?asan siminti tace "Anty Balaraba ina kwana", Balaraba tace "yawwa". Maama ta matso kusa da Balaraba ta rage murya can ?asa tace "kinga dai babu wani cigaba, anya kwa aikin malamin nan yayi?", Balaraba tayi yadda Maama tayi tace "hmm ai zuwa nayi na tayaki farin ciki, snn nima nasha kallo, don tinda malamin tsamiya yace ba aure to magana ta ?are, kedai kawai mu zuba ido", Maama tayi ajiyar zuciya ta gyaWa kai tamkar tsohuwar ?adangaruwa. Tin daga soro har zuwa ?arshen lungun ?unshi aciki yake taf da jama'a, maza wanda suka zo halartar Waurin aure, ?an uwan Baba na Yola da abokan arziki, ga dangin umma. daga soro kuma waliyyin Amarya da sauransu ne zaune suna jiran dangin Ango, lokacin Waura aure harya gota amma har yanzu dangin Ango basu hallara ba. Naseer da ke zaune soron ya dubi agogon hannunsa, yayi kyau sosai cikin farar shaddar da ya saka ta ankon da sukay shi da Huzaifa da Mu'azzam da kuma mahaifinsu, Naseer yace "lfy kuwa, ya har yanxu basu iso ba", Bappa ?anin Baba wanda shi ne waliyyi yace "Baka da lambar wani daga cikin dangin Angon?", Naseer yace "ba nida ita Bappa", Mu'azzam ya shafa aljihun wandonsa yace "bari ni na kira Bappa", Bappa yace "yawwa, marmaza kira su, jama'a na jira", Mu'azzam ya ciro wayarsa daga pocket ya shiga kiran Nura Ango tinda lambarsa yake da ita, sau uku ya kira tanata ringing amma ba'a Waga ba. tsayawa yayi yana kallon uncle din nasa, Bappa yace "ya akay?", Mu'azzam yace "ba'a Wauka ba"..........
'?
=؛? HAJAR =؛?
by Feenerh_feeche

{31..}
A tare Baba da Bappa suka dubi Mu'azzam, Naseer yace "ka sake kira", Mu'azzam yace "tom" snn ya sake dialing numbern Nura, respond din dai daya ne, Baba da hankalinsa ya fara tashi yace "A Wan jinkirta zuwa nan da minti goma


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login