Showing 42001 words to 45000 words out of 252707 words

Chapter 15 - HAJAR COMPLETE NOVELS By Nafisa Yusuf Nagoda.doc

zata saka daga wardrobe tace "ke ta aiko knn?", Hafsa tace "A'a wai bazata iya gaya miki ba", Anty tace "toh shknn, sai ta saukesa a sitting room, akwai semosa a fridge", Hafsa tace "tom" ta mi?e ta fita. Anty tana gama shiryawa ta Wauki handbag dinta ta fita, Wakinsu Hafsa ta shiga tace "toh sai Allah ya dawo dani", Hajar tace "Allah ya tsare", Hafsa tace "sai kin dawo". Biyar da rabi na yamma Hajar ta fito daga wanka, ta shafe jikinta da sabon cream Winta mai daWin ?amshi, riga da skirt ta saka na atamfa ta tsaya gaban mirror tana cakare Wauri, Hafsa ta shigo tace "uhmm kinyi kyau, na gama soya semosan", Hajar na zizara kwalli a fatar manyan idanunta farare ?al tamkar madara tace "nagode". wayarta dake tsuwwa ta Wauka ganin me kira tayi murmushi tace "ina jin ma ya iso", kara wayar tayi a kunne tace "okay, gani nan fitowa", mayafin da ta fitar ta Wauka ta yafa, Hafsa tace "laa ya naga kinsa mayafi ba Hijab ba, ko ba ustaz bane?", Hajar ta zabga mata harara tace "chab wai dan yana malamin islamiyya shine zai zama ustaz, wllh ba ruwansa indai zaki saka abinda zai rufe miki jiki to shi bashi da damuwa", Hafsa ta kalleta sama da ?asa taga dai ruf mayafin da ta saka ya rufe mata jiki kuma ba shara shara bane, Hafsa tace "Eh, kinsan mazan ma kowa da ra'ayinsa, wani yafi son Hijab wani kuma mayafi wani kuma duka, wani kuma babu ruwansa indai za kiyi decent dressing is okay", Hajar tace "that's my Man shima decent kawai yake so", Hafsa tace "yana fa jira", Hajar tayi wasa da kwayar idonta tace "ai ya saba" ta Wauki turare ta fesa sama sama. slowly Hajar ta fito compound ta nufi gate, ta bude ?ofa ta fita, yana tsaye jikin fillelen sabon motorbike dinsa yana danna wayarsa, yana ganinta yayi murmushi ya mayar da wayar aljihu, kallonta ya ringa yi ba ?iftawa har ta ?araso, sosai silent kwalliyar da tayi da kuma decent dressing Winta ya tafi da imaninsa, sunkuyar da kanta tayi tace "sannu da zuwa", baice komai ba kawai kallonta yake, shirun da taji ne yasa ta Wago kanta ai kam sukay ido huWu, tayi sauri ta sunkuyar da nata tace "Bismillah ka shigo", yace "A'a nidae bazan shiga gidan mutane ba", tace "toh nan fa kan hanya ne", ya dubi street Win yaga akwai mutane yace "toh amma dai ansan da zuwa na dai ko?", childishly ta hararasa tace "Bismillah" ta juya ta koma ciki ba tare da ta jira cewarsa ba. bayanta yabi har suka shiga gidan tayi leading Winsa har sitting room. a kujera one seater ya zauna ita kuma ta zauna a two seater dake gefensa, Calmly tace "ina yini", ya ringa kallonta, Wago kanta tayi jin bai amsa ba sukay ido huWu, tayi pouting lips ta rufe fuskarta da palms Winta tace "dan Allah ka barii", murmushi mai sauti yayi yace "me fa?", tace "why are you staring at me?", yace "because i missed you so much and you look beautiful", murmushi tayi tana wasa da yatsun ?afarta, yace "ba ki rubuta Jamb ba ko?", ta gyaWa masa kai tace "Eh neco kawai na zana", yace "Ohk, suma yanxu school of Nursing suna amfani da jamb, gashi baki rubuta ba amma ba damuwa saiki rubuta next year ko?", tace "Admission din bazai samu ba saida Jamb result knn?", yace "Eh, ai da nasan sun canja tsari da sai kin zana jamb, kamar yanxu ne zaki ji an fara registration, and you're still young kinada enough time", tace "Ahh I'm not young", yace "ohk sai ki gayawa wanda bai sanki ba to me you're a little girl kuma you know akwai certificate of birth Winki a wajena", sallama akai a bakin ?ofa Hajar ta amsa, Hafsa ce ta shigo tana sanye da hijab hannunta ri?e da tray mai dauke da bottle water da drinks sai kuma plate Win semosa, a hankali ta ajiye trayn akan Centre table ta zauna kusa da Hajar, Hafsa tace "sannu da zuwa, ina yini", Nura yace "mun yini lfy?", tace "alhmdllh", yace "masha Allah, ya karatu?", Hafsa tace "alhmdllh", a hankali Hafsa ta mi?e ta basu waje tana fita Wakin akay knocking gate, bakin gate Win ta wuce ta buWe ?ofa, ita tasha ma Humaira ce ta dawo daga islamiyya amma me sai taga wani yaro, tace "ya akai?", yaron yace "wane mutum ne yace wai ana sallama da Hajar", Hafsa tace "yana ina?", yaron yayi nuni da wata jugunanniyar mota dake gefen titi a parke, Hafsa ta kalli mutum da ya fito daga cikin motar, zaro ido tayi sbd ta ganesa, shine mutumin da suka hadu jiya a supermarket, Ahmad ya ?araso bakin gate Win yana kallon Hafsa da itama take kallonsa cike da mamaki.......
'?
=؛? HAJAR =؛?
by Feenerh_feeche

{ 22..}
Ahmad ya shafa kansa yana kallon Hafsa yace "Assalamu alaikum", har lokacin mamaki bai bar face dinta ba tace "wslm, ina yini", yace "lfy lou, kinyi mamakin gani na ko?", tace "dole, ince dai lfy bawan Allah?", numfashi ya sauke a sau?a?e yace "Ammm lfy", tace "Ohk" ta juya zata koma gida, da sauri yace "amm Hajar fa?" ya fada yana shafa kwantaccen beard Winsa, ta juyo tace "what about her?", yace "i came for her, help me by informing her", hannuta na ri?e da ?ofa tace "ohh, amma Hajar ba ta nan", mood Winsa ne ya canza lokaci guda yace "bata nan?", Hafsa ta gyaWa masa kai cause that was the only way, yace "I'm sorry to invade her privacy, tana ina?", ta saukar da kanta ?asa tana tunanin abinda za ta faWa, few seconds passed amma ba tace komai ba, ya ringa kallon fuskarta with his cool voice yace "girl.., where is your sister?", ta Wago ta kallesa sbd yadda yayi pronouncing girl Win tace "amm sunje unguwa da Babarmu", yace "Okay thank you, ai naga yamma ma tayi sosai, bari kawai na jirata...", ta katsesa tace "A'a karka jirata, ba yanxu zasu dawo ba", yace "toh sai yaushe?" yana kallon cikin idonta da rashin gaskiya ya bayyana ainun, hade gira tayi tace "A'a, nace fa ba yanxu zasu dawo ba, may be ma acan zasu kwana", Humaira ce ta Sullo ta layin dake gefen gidan ta dawo daga islamiyya, sosai gaban Hafsa ya faWi ganinta da tayi, Humaira ta tsaya tana kallonsu ko ?iftawa babu sai kuma ta ?araso ta shiga gida, Hafsa ta sauke ajiyar zuciya tabi bayanta da kallo, rediyo me jini knn, tasan tabbas saita zayyanawa Anty abinda ta gani, Hafsa tace "sai dai ka dawo gobe", yace "No zan dawo anjima dai", tace "toh idan kuma basu dawo ba fa sun kwana acan", yace "No problem sai na dawo gobe, she worth it", tace "alright" ta juya zata shiga gida yace "wait", ta tsaya ba tare da ta juyo ba, yace "kinga kwa Cousin dinki tana bani wahala kema kina tayata ko?", tace "kamar ya?", yayi slight smirk yace "kin ?i faWamin whereabout Winta, and my heart keep saying that my Hajar is inside the house", Hafsa can't help it dole tayi slight smile ta juyo tace "really", ya gyaWa kai yace "sure, young lady do you believe in fate?", sosai tambayarsa ta bata mamaki tace "Yess Noo", yace "hmmm, toh yess ne or No?", ta karyar da kai gefe tace "toh nidae a nawa view Win is No, a view din wasu kuma zance yess", yace "toh a ajiye naki view din a gefe a dauki na wasun, kema nasan bazaki so ki zama silar datse fate ba", kallonsa tay tace "sure bazan so hakan ba, abu guda Waya i promise you ni da kaina zan fito maka da Hajar amma not today, zanyi hakan ne dan na nuna maka cewa bazan datse fate ba..", kallonta ya ringa yi kafin yace "then when?", tace "sooner or later", ya gyaWa kai yace "amma taya zan san lokacin?", tace "where is your phone?", wayarsa ya ciro a aljihu, a hankali ta fara karanto masa number yana lodawa, tana gama gaya masa tace "sau Waya zaka kira, idan lokacin yayi zan kiraka..." da haka ta shige gida ta rufe ba ta jira cewarsa ba. Ahmad yayi murmushi yana sauke ajiyar zuciya ya shiga motarsa, saida ya kira layin Hajar wajen sau uku amma bata shiga, tin Wazu abinda ake ce masa knn. ?arfe shida da minti sha biyar Nura ya mi?e daga kan kujera, ya ciro bandir Win ?an 200 ya ajiye a hannun kujera, Hajar na ganin haka tace "kaga ka Wauki kuWinka", yace "toh ai ba ke na bawa ba, na Hafsa ne", ya fita a Wakin tabi bayansa, a bakin gate ya tsaya yana kallonta yace "toh sai munyi waya", ta gyaWa kai tace "toh", yace "toh shiga gida", ta juya ta shiga gida a hankali ta rufe ?ofa, sitting room ta shiga ta Wauki kuWin da tray ta fita, kitchen ta fara shiga ta ajiye trayn ta Wauki glass cup mai Wauke da ragowar lemon da ya rage tana murmushi, a hankali ta kafa kai ta moWe lemon snn ta fito ta shiga Wakinsu Hafsa, rafar kuWin ta ajiye akan cinyar Hafsa dake gefen gado tana operating wayarta, ga Humaira a gefenta sai zaro idanu take tamkar Sera a buta, Hafsa ta dube Hajar da mamaki tace "meye wnn?", Hajar na warware Waurin dankwali tace "cewa yayi na baki", Hafsa ta zaro ido tace "na shiga uku Hajar shine kuma kika amsa", Hajar tace "tinda yayi niyya wllh ba yadda na iya", Hafsa ta Wauki kuWin tana juyasu tace "amma sunyi yawa wllh, ni ya zanyi dasu?", Hajar tace "nima ban sani ba", Hafsa ta kalli Humaira ta galla mata harara tace "na dai gaya miki, wllh kika kuskura kikai wata magana a gaban Anty sai na kira miki IT, yadda ya cinye wnn yaron acikin kwata kema haka zai miki", a rikice Humaira tace "dan Allah kiyi ha?uri wllh bazan ce komai ba", Hafsa ta hade gira tace "yawwa kin temakin kanki, tashi ki tafi palour ki kunna cartoon", a hankali Humaira ta mi?e tana murza ido ta fita, Hajar tace "ji muguwa, me yasa kike threatening dinta?", Hafsa tace "guess what?", Hajar "what?", Hafsa tace "wnn mutumin da muka hadu a supermarket ne yazo", Hajar tace "ban gane ba", Hafsa tace "Wazu ne kina tare da Nura, bayan na fito daga wajenku naji ana knocking gate, ina buWe gate na tarar dashi a ?ofar gida, ke ba kiga dagar da mukay dashi ba kafin ya tafi, toh shine Humaira ta ganni dashi a ?ofar gida, kinsan rediyo me jini ce yanxu saita rattaSawa Anty a yimin wata fassarar ta daban", Hajar ta taSe baki tace "toh taya ya san gidan nan?", Hafsa tace "ke zan tambaya", Hajar ba tace komai ba ta canza kayan jikinta ta fita Wakin zuwa kitchen ta Wora dinner.

&Washe gari da safe Umma ta hadawa Baba breakfast Winsa, tana zaune gefensa yana cin abincin a hankali tana masa fifita, ledar drugs Winsa ta janyo ta Salli wanda zai sha ta basa, Baba yace "Allah yayi albarka", tayi murmushi tace "Ameen", ya jinginar da kansa ga bango yace "wai ina Hajara ne?", Umma ta ajiye maficin hannunta tace "tana gidan Jamila", ya gyaWa kai yace "toh ta dawo gida haka nan", Umma ta gyara zama tace "malam na fi son ta cigaba da zama a can, wllh yanxu gidan nan kunnenmu ?an?anra ba hatsaniya, Hajara ba hakuri gareta ba, kamar dage take indai aka taSata saita rama, zamanta acan shine zaman lfy", Baba ya ajiye numfashi a hankali yace "a wnn marrar bazaka Wauki nauyinka ka rataya a wuyan wani ba, ai a rayuwar nan zama inda Allah ya ajiyeka da kuma ?ar?ashin wnda Allah ya Waurawa nauyinka shine daidai, idan kana so ka zauna lfy da mutane to ka guji abin hannunsu. Hajar ta dawo gida yau Win nan", Umma tace "amma malam...", katseta yayi yace "kiyi abinda nace", a hankali tace "toh, insha Allah zata dawo", Maama ce ta bankaWo labule da ?arfi ba ko sallama ta antayo Wakin, hannunta ri?e da wani kantamemen kofi da cokali, daga tsayen da take tace "malam ya kufan jiki?", ba tare da ya dubeta ba yace "alhmdllh", ta gallawa Umma harara tace "madara zan Wiba zamu karya kumallo nida yara", Baba yace "toh ina kika ga madarar?", Maama ta geSare baki tace "Auu malam jiya fa naga an kawo maka manya manyan gwangwanaye na madara da milo, kayan marmarin ma sai sun ruSe ba za a kasafta ba, ya kamata a raba a bawa kowa rabonsa", Baba yace "an?i a raba", hangame baki Maama tayi tace "toh ai shknn, toh a bamu madarar mu karya kumallo", yace "suma an hana, mai neman auren Hajara ne ya kawo, ita kuma da kike kira da shegiya toh wnn arzi?inta ne....", Maama ta gyara hular kanta da ta wani waskace gefe tace "toh shknn.." ta fita fuuu a Wakin sai kace wata kububuwa. Wakinta ta shiga tana hucii, Maimuna da take tsefe kitson attachment tace "Maama ina madarar?", Maama ta wurga mata ?aton kofin hannunta a fusace tace "madarar gidanku, malama ki cire kuWi a ?ugunki ki siya, uwar tsimilmila kawai", Maimuna ta taSe baki ta cigaba da tsefe kitsonta, Nabilah dake haWa kayanta masu datti da zata wanke tace "toh Maama ina kuWin da yaya Naseer ya baki ne?, ki bayar a siyo mana ?osai da gasara", Maama tace "baki da hankali, toh ?osan Wari biyar ma yayi mana kaWan", Nabilah tace "toh wainar gero fa?", Maama tace "wllh an wula?anta ni, ina Sa'adatu na", Maimuna tace "ta fita", Nabilah tace "wane Wan abu kazan kasan ne ya wula?antaki Maama?", Maama ta sauke ajiyar zuciya tace "wai akan wata mushiyar madara ake min gori", Nabilah ta yamutsa fuska tace "daman ai saida nace miki kar kije amma kika biyewa Maimuna ?ar san banza, ai ga irinta nan", Maama tace "ke Maimuna wai ina Alhaj Win naki ne shi bazai kawowa mahaifin naki kayan dubiya ba?, ko baki gaya masa ba?", Maimuna tace "chab na gaya masa mana amma bana son yazo ruSaSSen gidan nan gaskiya, da ace ma har yanxu Baban na asibiti da sai yazo, ko da yake baya nan ma ya tafi Abuja", Maama ta wangale baki tace "Allah, wato har Habuja yana zuwa?", Maimuna na taje figaggen gashinta wanda ya gama tsiyacewa tass sbd yawan saka attachment tace "uhmm ai yace idan ya aureni acan zamu zauna", Nabilah ta kwashi kayan wankinta tayi waje tana cewa "bamu gani a ?asa ba". Maimuna ta Waga murya tace "oho miki dai, ?ar ciki ba?i kawai", Maama tace "muna fatan Allah ya mayar da ?o?o masaki". Maimuna ta mi?e ta tattara gashin attach Win da ta gama tsefewa tace "Ameen". Umma na fitowa Wakin Baba ta shiga nata, wayarta ta Wauka ta fara kiran ?ar uwarta, bayan sun gaisa Umma tace "ya yaran ya Wawainiya?", Anty tace "alhmdllh Adda", Umma tace "Hajara ta shirya ta taho gida..", Anty tace "to sbd me Adda?", Umma ta sauke ajiyar zuciya tace "wllh malam ne yace lallai lallai yau ta dawo gida, ba yadda banyi ba akan ya ha?ura amma ya kasa fahimta, kuma wllh ni wani abun ma sbd shi nake, yanzu fa ba isasshiyar lfy garesa ba, idan Hajara ta dawo gidan nan sai anyi hatsaniya, ita fa ba a mata ta kyale, ga mu?arrabanta nan suma duk suna nan", Anty tace "toh shknn Adda, nida kaina zan dawo da ita, kuma zan ja mata kunne, amma dai nidae tinda tazo gidan da nake banga wata matsalar ba", Umma tace "uhmm ai hakuri ne yayi mata ?aranci", Anty tace "ba damuwa zan mata nasiha, insha Allah da yamma zan kawota tinda mahaifinta yace ta dawo gida", Umma tace "toh sai kinzo Allah yayi albarka, a yiwa Kabiru godiya da Wawainiya", Anty tace "laa ba komai Adda muma fa masu ri?e Hajar ne, sai anjima" ta katse kiran.

&Da misalin sha biyu da minti uku Anty na zaune palour Hajar ta fito daga Wakinsu Hafsa ta shiga kitchen, fridge ta buWe ta Wauki ruwa ta sha snn ta fito, har zata koma Waki Anty ta kirata, dawowa tay ta zaune kan carpet tace "Anty gani", Anty ta Wakko sababbin ?an Wari biyu dake gefenta ta mi?a mata tace "toh kema ga naki", Hajar ta Waga kai ta kalli kuWin ta girgiza kai tace "A'a na Hafsa ne", Anty tace "ba zaki amsa ba", Hajar ta sunkuyar da kanta tace "ai Hafsa ya bawa", Anty tace "Eh naji Hafsa ya bawa, ita kuma Hafsa ta baki, ki amsa tin kafin rai na ya Saci", a hankali Hajar ta sa hannu ta amshi kuWin ta ajiye kan cinyarta tana ganin aukinsu, kamarma gida biyu aka raba su aka bata rabi, Anty ta gyara zama tana kallonta da kyau tace "Hajar", Hajar ta Wago kai tace "Na'am", Anty tayi softening voice tace "Ha?uri shine babbar ribar zama da mutane, duk wani mai ha?uri yana tare da waraka da kuma wadata shiyasa hausawa suka ce maha?urci mawadaci, akwai laifin da za ai maka ka rama akwai kuma wanda za ai maka ka ha?ura, ammafa wanda za kayi ha?urin ya fi riba, Hajar ki zama mai ha?uri daidai mitsali ba wai wanda zaki zauna a cutar dake ba, kinsan me yasa nace ki zama mai ha?uri", a hankali Hajar ta girgiza kai, Anty tace "yawwa, nasan kinada ha?uri daidai naki amma ina so ki ?ara akai, Wazu mukay waya da Adda tace Babanki yace ki koma gida yau Win nan, toh anjima da yamma zan mayar dake, kinsan dalilin da yasa mahaifiyarki ta ha?ura da zama dake ta kawo ki nan dai ko?, ki ringa jin duk abinda mahaifiyarki ta gaya miki, tin kina ?ar tatsitsiya take ha?uri da kishiyarta a haka dai rayuwa take gara mata cikin zaman doya da manja, babu abinda ya cita dan tayi ha?uri, amma ke kin ?i ha?uri ki zauna lfy, kimin al?awarin cewa bazaki shiga gonar ?an uwanki ba,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login