Showing 12001 words to 15000 words out of 252707 words

Chapter 5 - HAJAR COMPLETE NOVELS By Nafisa Yusuf Nagoda.doc

rigarta da wani irin rainin hankali tace "Baiwar Allah ki iya bakinki, kuma kisan a inda za kiyi zagi kici bulus, ke kin isa ki kalli mahaifina ki gaya masa magana akan idona, shiyasa na gurje bakin fitsarar da ruwan kwata, wllh kaWan ma kika gani", waWannan kalaman su suka dawo da Maama Sa'adatu Nabilah da Mabaruka daga duniyar daskarewa, zeenatu ta sharce kwatar da ta mamaye mata baki dake fitar da jini tana kallon Hajar cike da mamaki, Sa'adatu ta mulmulo wata ashariya tayo kan Hajar a fusace..........
'?

=؛? HAJAR =؛?
by Feenerh_feeche

{8...}
Da sauri Hajar ta tuntsurar da ruwan Waurayar wanke-wanken, ta Wauki bokitin ?arfen ta nuna Sa'adatu da ta yo kanta tace "na rantse da girman Allah kika taSani saina rotsa miki kai", Sabra tana ganin haka ta fita a guje kiran Umma da ta shiga makwabta barka, turus Sa'adatu tayi saboda tasan tsaf zata aikata, maimakon kan Hajar da tayi nufin yi saita juya akalarta zuwa ga zeenatu da take ta faman sharce kwatar fuskarta, Mabaruka ma ta taho da sauri ta kalli fuskar zeenatu tace "chab an tsokano sama da kara", Nabilah ta shiga tafa hannaye tana faWin "mun shiga uku yau ga ?ar daba a gida tana dabanci", Maama tace "innalillah wa'inna ilayhirraji'un, mal kana ganin abinda shegiyar ?ar da kake i?irarin takace ta aikata ko??, tafa fitarwa da ?ar mutane jini", Baba ya nuna Maama da hannunsa mai carbi yace "karki sake kiramin ?a shegiya na gaya miki, Hajara ?ata ce", Maama ta tsaya tana kallon Baba galala tamkar wawuya sai kuma ta hura tukubar hancinta tace "wllh idan zaka shekara dubu kana kiran Hajara ?arka saina ?aryata", Hajar ta ri?e bokitin ?arfen ta gam tana kallon kowa sama da ?asa, Sa'adatu da Mabaruka suka temaki zeenatu ta wanke fuskarta da hannayenta, Mabaruka ta cire yalolon mayafin jikinta taci Wammara ta kalli Nabilah tace "naji kin kirata da ?ar daba ko??, to ga wacca ta dameta ta shanyeta tas a iya dabanci", Baba ya Waga murya yace "Sa'adatu!!, ki kwashi ?awayenki ki barmin gida", Mabaruka ta kaiwa Hajar wata dam?a, babu tausayi Hajar ta kwaWa mata bokitin ?arfe a hannu, azaba tasa Mabaruka dur?ushewa tana yarfa hannu, da gudu Sa'adatu taje ta rarumo taSarya zata jirga mata, Hajar ta kufce, da sauri Baba ya shiga tsakani hakan kuma yazo daidai da shigowar Umma gidan cikin sauri Sabra biye da ita, salati ta fara zabgawa ganin Hajar na huci hannunta ri?e da bokitin ?arfe ga Sa'adatu itama da taSarya, Maama tace "kin haifi bala'i da masifa wllh faWima, ga shi nan shegiyar ?arki ta kassara ?a?an mutane a gidan nan", Sa'adatu tsalle take tana hargowa tana ?o?arin bangaje Baba da ya shiga tsakaninta da Hajar faWi take "kin san kwa su waye waWannan, wllh yau sai kinyi nadamar zuwa gidan duniya", Hajar ta daka shewa tace "ahayye wllh sune za suyi nadamar zuwa gidan nan, dubeki dabba jahila da?i?iya kin tsaya kina hura hanci da ?o?arin bawa hammata iska akan jakunan da suka zagi mahaifinki, asararriya mara mafaWi da tarbiyya....", Umma ta fizgi Hajar tana ?o?arin dannata a Waki, Sa'adatu ta yun?uro tana SaSSarkawa Hajar zagi irin na cikakkun marasa tarbiyya, Hajar da Umma ta kusan cusata a Waki tace "tirr da halinki Sa'adatu, ki Wauki tsummokaran jakunan ?awayenki daga nan ku wuce chemist, gaba Wayansu idan suka ji zugin shanshanbale na ratsasu suka WanWana azaba zasu gane inda ya kamata su nuna rashin tarbiyyarsu", Sa'adatu tace "zaki gani ne ba dai zeen da Mabruk kika taSa ba", Hajar tace "babu abinda zan gani sai alkhairy, sara da sassa?a basa hana gamji tofo, jaka kawai". Umma tayi nasarar danna Hajar a Waki ta rufe ?ofa, wani irin huci Hajar takeyi tana sauke numfashi, Umma ta kalleta cike da takaici tace "ba kya jin magana Hajara, Insha Allah gobe goben nan zaki bar gidan nan", Hajar ta koma gefen gado ta zauna tana huci zuciyarta wasai. Washe gari Umma ta haWawa Baba karin kumallo, Wumamen tuwa da kunun tsamiya, zama tayi har saida ya gama cin abincin sannan tace "yawwa mal daman ina so Hajara ta koma wajen iya da zama tinda zamanta anan gidan ya ?i daWi, idan babu damuwa ta koma gaban iya", Baba ya zuba ruwa a kofin da ya gama shan kunu ya girgije yace "faWima ina ne gidansu Hajara?", Umma tace "nan ne", yace "yawwa, to Hajara babu inda zata agidansu zata zauna", Umma tace "amma mal...", ya Waga mata hannu yace "ya isa haka, kirawo min Hajarar", tace "tom" ta fita a Wakin ta shiga nata, Hajar da take gyara gado ta kalla tace "kije inji Babanku", Hajar ta ajiye bedsheet din hannunta ta fita, Wakin Baba ta shiga da sallama ta tsugunna tace "Baba gani", ya kalleta yace "Hajara banji daWi da kika biyewa fitsararrun nan ba jiya, kin saSa al?awarin da kikai min kwanaki cewa bazaki sake shiga sabgarsu ba, yanzu jiya me kika yi..", ta buWe baki za tay magana ya Waga mata hannu yace "duk nasan abinda ya faru kuma nasan me yasa kika shiga sabgar su, da kinyi ha?uri saiki samu riba, karki sake aikata hakan kinji", tace "tom Baba", yace "tashi ki tafi Allah shiryeki". ta mi?e a sanyaye ta fita, gyaran gadon da take ta ?arasa snn ta share Wakin. ta fito tsakar gida tana kallon Umma da ke bakin rariya, kallo Waya umma tayi mata ta Wauke kai ta cigaba da wanke waken kulele da za a kai markaWe, Umma ta Wauki zafi fishi take da Hajar ainun yau ko gaisuwarta bata amsa ba da asuba, Hajar ta tsugunna a gabanta tace "Umma dan Allah kiyi ha?uri, nadena bazan sake ba", ba tare da ta dubeta ba tace "ai daman kin iya tuban muzuru, ki matsa min a nan wajen", idon Hajar ya ciko tace "dan Allah Ummana ki yafemin nadena bazan sake ba", Umma ta ja tsaki tace "sau nawa akai hakan Hajara, tinda dai kin?i jin maganata ai sai kiyi abinda kika ga dama, duk abinda ha?uri bai samar ba rashinsa bazai yi ba", Hajar tace "wllh Umma nifa bana shiga harkarsu tinda kikai min magana, sau nawa suna takalata bana kulasu, jiya ma fa ?awayen Sa'adatu ne suka yiwa Baba rashin Wa'a", Umma tace "uhmm ai kina ganinsu kinsan basu da tarbiyya dan me yasa zaki tanka masu", Hajar tace "bazan sake ba", Umma tace "da ya fi dai". Maimuna ce ta fito daga Wakin Maama tana rangwaWa, ta saka wasu matsattsun kaya riga da skirt na atamfa, saboda Wamewar da skirt Win yayi mata har shatin panties Winta ana gani, itama ta tsiri fita yanzu kuma bata dawowa gida sai dare da ?an ledojinta na kwaWayi mabuWin wahala, ko kallon inda take Umma da Hajar ba suyi ba tazo ta gama barbaWesu da Harara kana ta fita. Hajar tace "umma dan Allah da yamma zanje gidansu zainab muyi karatu", Umma tace "toh shknn Allah ya kaimu". Bayan Sallahr la'asar Hajar tayi wanka ta shirya cikin doguwar riga ta atamfa, ta kashe mai?on fuskarta da farar huda ta murza lipstick a lips Winta, ta saka hijab da ya zarce mata guiwa, tayi kyau sosai sai kace wacca ta caSa kwalliya, wani flat shoe ta Wakko ta saka ta yiwa Umma sallama ta ?ara gaba, da yake gidansu Zainab Win akwai ?ar tazara daga gidansu, ta tsaya a bakin gate tana knocking a hankali, Zainab ce ta buWe ?ofar ta haWe rai tace "haba Hajar tin Wazu fa nake jiranki amma sai yanzu zaki zo", Hajar tace "ke dalla malama Umma na taya aikin kulele", Zainab ta matsa gefe tace "Shigo mana", a Wan matsakaicin compound Win gidan suka tsaya, Hajar ta kalleta da kyau tace "ke kuma ina zuwa??, naga kinyi shiga sai kace mai shirin fita", Zainab ta gyara yafen mayafinta tace "fita zanyi mana, tinda Allah ya kawoki saiki rakani Ummi ce ta aiken", Hajar tace "ban tambayi Umma ba iya nan kawai nace mata zanzo", Zainab tace "muje ki gaisa da Ummi saina kira Umma a waya mu tambayeta ko?", Hajar tace "Eh hakan dai yafi". cikin gidan suka shiga, Mamansu Zainab tana zaune a palour, Hajar ta tsugunna tace "Ummi ina wuni", Ummi tace "ina gajiya, ya Maman taku", Hajar tace "lafiya alhmdllh", Ummi tace "masha Allah", Zainab tace "Ummi Wan aramin wayarki plxx", Ummi ta lalubi gefe da gefenta taji wayam tace "duba Wakina", Zainab ta shiga Wakin Ummi ta fito da wayar a hannunta ta kalli Hajar tace "taso muje", Wakinsu Zainab suka shiga, Zainab ta mi?awa Hajar wayar tace "saka numbern Umma", bayan Hajar ta Wura numbern tayi dialing, anayin picking Hajar taji muryar Sabra, Hajar tace "game kike mata ko?, maza ki kay mata wayarta", tana jiyo muryar Sabra tana cewa Adda ta bugo waya, Umma tayi sallama ta kara wayar a kunne, Hajar tace "Umma nice". da kyar Umma ta amince kuma tace mata kar ta kai magariba. bakin titi suka fito suka tari napep, unguwar da suka je ta masu hali ce haka ma gidan da suka amso sa?o wajen ?awar Ummi, a clean and silent street Win suka tsaya suna jiran abin hawa.

&Noor na zaune a main palour tare da Khausar da yau kwananta biyu a gidan, wata spicy noodle mai shegen daWi suke ci, gaba Waya hankalin Noor yana ga TV da ake haska wani Kdrama, Khausar ta ajiye fork Win hannunta tace "Noor what is the name of the drama??", ba tare da ta kalleta ba tace "Alchemy of souls", Khausar ta taSe baki tace "ni kam nafi kallon Cdrama, ina yaya Nurain ne?", Noor bata amsata ba her mind was fully on screen, Khausar ta Wala mata duka a cinya tace "hey I'm talking to you", Noor ta zabura tace "ouchh kadan ba saina rama ba" ta mayar da idonta Tv, Khausar tace "wai bazaki ci ba saita sandare", Noor idonta ?ur kan Tv tace "kashe AC", Khausar ta janyo wayarta tace "I'm not your servant". atmosphere Win living room Win ce ta fara canzawa zuwa wani breath taking scent mai daWi, Khausar ta Wago kanta suka haWa ido da Nurain, murmushi yayi mata ya kalli Noor da bata ma san da shigowarsa ba yace "Noor.. Noor.. Noor.." ya kirata sau uku, saida Khausar ta zungureta sannan ta juya tace "what, wai mene??", da ido Khausar tayi mata nuni da Nurain tace "yaya na magana", yace "juicy fruit salad zaki hada min", Noor tace "ohk, amma babu fruit fa, apple and berries ne kawai ya rage", juyawa yayi ya fita daga palourn Khausar ta bisa da kallo, compound ya fita yana neman Garba ya bashi ya siyo masa fruits Win amma ya tarar baya nan, lallausar sumarsa ya shafa yace "shittt", ya shafa pocket Win wandonsa yaji key Win motarsa yace "good", motarsa ya dosa dake parking lot ya buWe bayan ya gama warming ya mirgina ya bar compound Win, a hankali yake murza steering Win motar amma kuma ya take accelerator. Almost 20mis Hajar da Zainab na jiran napep, wasu yara su uku suna wasa da ball daga cikin wani Wan fili, guda Waya ne ya buga ball Win da ?arfi tayo kan road, da gudu yaron ya biyota a lokacin kuma wata dun?ulalliyar mota ta yanko cikin street Win with minimum speed, saura ?iris motar ta bige yaron taci wani uban burki ?iiii ta tsaya gaf da yaron da tsoro yasa ya ?ame, Hajar ta runtse idonta tace "innalillah wa'inna ilayhirraji'un", Zainab kam juya baya tayi ta toshe kunnuwanta da hannayenta, a hankali Hajar ta buWe idonta ta dubi yaron da ya zama froze a gaban motar, da sauri ta isa gabansa ta fara shafa kansa a hankali tace "wake up kiddo babu abinda ya sameka", ajiyar zuciya yaron ya sauke. Tinda ya tabbatar bai bige yaron ba ya kifa kansa ga steering, calming kansa yake yana addu'a a zuci, ajiyar zuciya ya sauke ya Wago kansa a hankali, ta front glass yake kallon yaron da kuma ?ar budurwar da take tare dashi wacca tayi backing dinsa bega face Winta ba. tamkar wacca aka umarta haka ta juya ta kalli glass Win motar da wani irin yanayi, in one sight ?wa?walwarsa tayi booting on ya gane wannan fuskar, one thing came to his mind which is ?ar gidan gini.........
'?
=؛? HAJAR =؛?
by Nafeesah Yusuf Nagoda

~~(Feenerh_feeche)~~.........
'?

{9...}
Da yake glass din motar tint ne yasa Hajar bata ga drivern ciki ba. hannun yaron ta ri?e still dai tana kallon glass din motar, kawai jira take drivern ciki ya fito, few seconds passed amma babu alamar wanda yaso aikata ta'asa zai fito, Zainab da ta toshe kunnuwanta har tayi jarumtar juyowa ta hango Hajar tsakiyar titi tare da yaron, Hajar taja hannun yaron ta tsaya bakin ?ofar driver ta shiga knocking glass, a hankali glass din yayi ?asa ya zuge gaba Waya, wani sanyi da ?amshi suka fara sirnanowa suna dukan fuskar Hajar da ta yaron. Hajar ta haWe gira tana kallonsa tace "malam wai baka san darajar rai bane iyeee?, ya za ai ka kusan bige yaro amma ka wani hakimce a mota bazaka fito ka dubasa ba", Zainab ce ta tsallako kan titin itama tace "zo mu tafi ai Allah ya kiyaye tinda dai bai bigesa ba", Hajar tace "ke kinga mutumin nan fa ko a jikinsa, idan da ace ya bige yaron nan fa sai fa yadda Allah yayi", shi kam Nurain mamaki da firgicin da ya ziyarcesa ne ya hanasa magana, Hajar ta sake kallon cikin motar tace "Allah ya isan sa kuma a ringa sanin darajar Wan Adam", Zainab ta zaro ido tace "Hajar mene haka", Hajar taja hannun yaron ta tsallar dashi titi tace "maza gida kaji", yaron ya kyalla da gudu ?an uwansa suka take masa baya. wajen da suke jiran napep ta koma ta tsaya fuska a haWe, mutanen yanzu basu da kirki ace ka kusan aika yaro lahira amma ka zauna ko a jikinka sai kace wanda ya kusan bige akuya yo ko akuyar ce aika fito ka duba idan kasan darajar rai, Zainab ta dawo gefenta ta tsaya tace "Hajar yanzu me kika aikata haka, Allah ya isa fa kikai masa, dubi fa har yanzu bai tafi ba", Hajar ta kalli motar da har yanzu take tsakiyar titi ta yamutsa fuska tace "me kwa na aikata, ya shekara a wajen kar ya tashi". a hankali ya juya kan motar ya gyara parking a gefen titi, Zainab ta dam?i hannun Hajar ta fara janta ganin ya fito daga motar ya tunkarosu, Zainab tana janta tace "Hajar kizo mu gudu kar yayi mana wani abun", Hajar ta fuzge hannunta tace "wllh bazan gudu ba", Zainab tayi tsam ganin har ya iso gabansu yayinda wani ?amshi mai daWi ya fara busowa a hancinsu, yana kallon Zainab speaking calmly yace "Assalamu alaikum young lady", a Warare ta amsa kana tace "bawan Allah kayi ha?uri dan Allah", Hajar da ta juyar da fuskarta ta juyo ta Salla mata harara jin abinda tace, girgiza kai yayi yace "ba komai, tell your friend itama tasan darajar Wan Adam cause ba tayi hali ko kama da mutanen da suka san darajan mutum ba", da sauri Hajar ta juyo ta kallesa, and that look makes her brain to boot on, she see that calm and charming face familiar, but where and when??, walking fast ya koma ya shiga motarsa ya kunna ya fita daga street Win da reverse. gida ya koma sbd wannan incidence Win da ya faru yasa yama manta da wani batun fruit salad, yana parking motar Garba ya taho wajensa, ko kashe motar baiyi ba ya fito cikin sauri ya shiga cikin gida, Garba ne ya shiga motar ya kashe sannan ya zare key ya fito. har lokacin Noor da Khausar suna zaune a palour, Noor tana kallonsa tace "yaya ina fruit din ko basu ka fita nema ba", shiru yayi mata ya haye stairs, Khausar ta taSota tace "he is weird", Noor ta sauke ajiyar zuciya tace "ina jin an Sata masa rai ne", she knows her brother in and out kuma she is very sure rai aka Sata masa.

&Hajar ta shiga gida sai gunguni take, Mu'azzam da yake alwala a bakin rariya yace "toh jarababbiya", ta zumSuri baki tayi Wakin umma, Maama da take talgen tuwo Nabila na mata tankaWe tace "kin ji ba Wan uwanta ma yasan jarababbiya ce", Nabila ta doka tsaki ta cigaba da tankaWenta, Umma ta kalli Hajar da take ?o?arin cire hijab tace "ke kuma lafiya kike wani cin mur", Hajar tace "wai a duniyar nan Umma mutane basa son gaskiya, wai wani mutum ne ya kusan kaWe wani yaro a titi amma ko a jikinsa, wllh ko fitowa ya duba yaron ?i yayi", Umma tace "Allah ya kyauta bai dai bigesa ba ko??", Hajar tace "saura ?iris fa, amma wllh mutumin nan yadda kika san gunki haka ya zauna a mota ya?i fitowa ya duba yaron", Umma tace "ke kuma shine kike kumbura akan hakan", Hajar tayi shiru kawai tuno abinda yacewa Zainab take wai batayi hali ko kama da mutanen da suka san darajan Wan Adam ba. kiran sallar magrib ne ya fitar da ita tsakar gida tayo alwala ta dawo Waki tayi sallah, bayan ta idar da Sallahr isha'i tana zaune akan darduma Sabra ta ajiye littafi a gabanta tace "Adda ki koyamin", Hajar ta janyo littafin ta duba kana ta fara gaya mata abinda zata rubuta. Umma ta shigo da wata warmer ta abincin da tayi tazarce ta ajiye a gefe guda, Hajar na kallon Sabra tace "yanzu ke Sabra mosquito din ne baki iya spelling ba, ?wa?walwar dusa ne dake ko me??" ta zuba mata rankwashi aka, Sabra ta ri?e kai tace "ashhh Adda fa na iya", Hajar tace "to rubuta mana", Umma tace "kiyi mata a hankali dan Allah". washe gari Hajar taje islamiyya tayi screening dinta na ?arshe, kuma a yau ne aka fayyace musu kuWin sauka da walima, kwanaki uku bayan haka ranar Alhamis da yamma, Baba bai jima da dawowa daga wajen aiki ba yana zaune a ?ofar Wakinsa yana cin abinci, wani yaro ne ya shigo gidan yace "wai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login