Showing 105001 words to 108000 words out of 252707 words

Chapter 36 - HAJAR COMPLETE NOVELS By Nafisa Yusuf Nagoda.doc

zuciyarsa wondering yake who is this patient with a damage lungs. Hajar ta sake sakkowa ?asa don yunwa take ji sosai, plain Noodles ta dafa ta juye a plate, tinda ta shigo kitchen din take kallon Cup din dake cike da Coffee, bayan ta gama tafasa tea ta juye a cup ta zuba sugar da lipton, har zata fita da shayi da Noodles dinta a hannu sai kuma ta dawo da baya, ta ajiyesu kan kitchen island, store ta shiga ta Wakko ledar gishiri ta fito, farke ledar tayi ta Wauki spoon ta matsa wajen Coffeen, ta zuba cokali biyar cikakku na gishiri a Coffeen tana murmushi, ta mayar da gishirin store ta fito tana kakkaSe hannunta tace "Asha shayii lfy.. counting from today..." kafin ta Wauki plate din Noodles da kofin shayinta ta fita. Nurain ya shigo kitchen din bayan fitar Hajar da minti biyu, direct Coffeen sa ya Wauka, ya ringa kallon coffeen ganin kamar ya ?ara yawa, gashi kuma it is not hot but warm, tinda it is warm he can take it, Sipping yayi domin yaji temp din dai a bakinsa, guntse wanda ya kurSa yayi ya yamutsa fuska, lokaci guda ya isa gaban sink ya zubar ya kunna tap ya wanke bakinsa, har lokacin wani irin taste yake ji a bakinsa wanda ya kasa gane masa, ya ringa kallon Coffeen kafin ya she?ar dashi ya bar kitchen din, yana zuwa Wakinsa ya wuce bathroom ya shiga wanke bakinsa da mouth wash har saida yaji taste din ya ragu sosai.

&Tin daga soro Sa'adatu ta fara zabga sallama harta shiga cikin gida, wani kallon hadarin kaji ta watsawa Umma dake zaune kan ?aramar kujera tana shafa manja jikin gwangwanaye, Wakin Maama ta shiga, Maimuna dake zaune kan gado ta bita da kallo tace "kin dawo..?", Sa'adatu ta saki baki tana kallon Maimuna kafin ta yakice hijab din da ta zumbula a jikinta, wasu irin matsattsun kaya ne jikinta wanda ya bayyana shape din bom bom dinta da ?irjinta, ta zauna kusa da Maimuna ta sake ?are mata kallo tace "ke kuma wa ya mayar dake wnn mummunar halittar, babur ne ya bigeki...?", Maimuna ta shafa goshinta tace "idan na gaya miki Allah yasa ki yarda.., wai fa Mu'azzam ne yamin haka..", Sa'adatu ta hangame baki tace "Mu'azzam din ne ya miki haka...?", Maimuna da takaici ya kuma ma?ureta tace "shifa..", Sa'adatu tace "chaSWi jamm, wato har dasu kaza acin dan?o, ke me ya haWani da wnn jakin har yayi miki haka...?", Maimuna ta kwashe kaf abinda ya faru ta gaya mata, Sa'adatu ta ringa jinjina kai tana hura bubble da chewing gum din bakinta, Maimuna ta kwashe cinya tace "kinga walmukalafatun da Baba yayi min..", Sa'adatu tace "karki yarda wllh tllh, toh aiko shinkafar Seran kika zuba iya abinda za a miki knn, karki ha?ura wllh..", Maimuna tace "ke ko ce miki akai zan ha?uri zaki yarda ne, dan na rantse da zabbatin Ubangiji bazan yarda ba..", Sa'adatu ta karyar da kai tace "wllh karki ha?ura wannan halittar da ya mayar dake ai ya cuce ki, fuska duk ta suntuma, ji fa yadda idanunki suka koma ciki sai kace fuskar biri bukka, kibi dare idan ya kwanta ki rusa masa taSarya a ka..", Maimuna tace "A'a ni bazan taSasa da hannuna ba, dafa kuWina a ?ugu, ?an daba zan biya su lakaWa masa duka su sassara banza su jefar a layii", Sa'adatu ta she?e da dariya tace "hakan yayi... wai ina Maama da waccan mai kai a tukunyar...?", Maimuna tace "Maama ta fita bansan inda taje ba, Nabilah kuma ta fita auno shinkafa...". babu jimawa Maama ta shigo gidan bayan ta dawo daga gidan Balaraba, ganin Sa'adatu Maama ta ya?e ha?ora tace "Sa'adatun Maama kin dawo...?", Sa'adatu tace "nadawo Maama..", Maama tace "ai kinga haka yafi kin cika al?awari, kinga gobe ma sai nasan ?aryar da zan shiryawa malam idan ya tambayeki, ina ?an albarkar ?awayen naki kuwa...?", Sa'adatu tace "suna nan kalau Maama sunce ma na gaisheki..", Maama ta washe ha?ora tace "Ahh ina amsawa kuwa..", Nabilah ta shigo hannunta ri?e da ba?ar leda, kallo daya ta yiwa Sa'adatu ta Wauke kanta, hijab dinta ta cire zata fita Maama tace "haba Annabilatuwa biki ga ?ar uwarki ba", Nabilah ta juyo tace "Au sannunta toh" da haka ta fice a Wakin, gawayi ta zuba a kurfotu ta tashi wuta, tana fifita wutar Naseer ya shigo, ta masa sannu da zuwa ya amsa a ta?aice, Maama ta le?o tace "A'a Nasiru sannu da zuwa..", Naseer ya ajiye doyar da ya shigo da ita ya russuna ya gaisheta, Maama tace "lfy lou, ya wajen aikin..?", yace "Alhmdllh an gode Allah..", bai tambayi Baba ba sbd yasan dai a wnn lokacin Baba ya fita aiki, ganin haka yasa Nabilah tace "Yaya Baba yana nan fa..", yace "toh" ya shiga Wakin Baban da Sallama, Maama ta zabgawa Nabilah wata harara tace "naga ranar da wnn munafikin canjin naki zai Wore..", bayan Naseer sun gaisa da Baba yace "Baba ko dai jikin ne..?", Baba ya numfasa yace "Nasiru duk ranar da kuka wayi gari bani toh mahaifiyarku ce sila..", Naseer ya kasa cewa komai tsabar ydda mgnar Baba ta dakesa, can dai yace "Ayi ha?uri Baba, Allah ya huci zuciyarku..", Baba yace "ha?uri ai ya zama dole tinda ta gama zubamin virus ta haifeku...", Naseer dai kawai ha?uri ya ringa basa duk da cewa bai san me ya faru ba.

&Kamar yadda Nurain yace kafin 12noon zai iso hospital, 11:40 ya isa hospital din, yana shiga office dinsa yasa Haleema ta kira masa his team members, har zai wuce sai kuma ya dawo yace "exclude A Nurse, call Nurse Amina instead..", Haleema tace "yess sir", ta Wauki landline ta shiga kiran members din, babu jimawa kam All of them suka hallara a office din, Nurse Amina ce kawai ba tazo ba, briefing dinsu Nurain yayi akan surgeryn da zasu shiga, daga nan suka fita to get ready, Nurain na wanke hannunsa kafin ya shiga surgery room din Khaleel ya da already dressed up in surgeon gown da nose mask a fuskarsa amma bai rufe hancin ba ya iso wajen yace "Boss everyone is here banda Nurse Amina, kuma i informed her tace tana zuwa..", Nurain na cigaba da wanke hannunsa yace "lets wait for her since the surgery is not yet started...", Khaleel yace "sure..", Nurain na gama wanke hands daman already ya sanya surgical Scrub. Surgery room din ya shiga, wani Nurse dake ri?e da surgeon gown ya ?araso kusa da shi helping him to wear the gown, Nurain ya saka nose mask da hand gloves kafin ya isa position dinsa na head of the surgery ya tsaya, patient din daman tintini aka masa anesthesia. Ruqayyah na zaune Nurse station duk abin duniya ya isheta, tinda tazo babu wani aikin arzi?i da tayi kawai safa da marwa take tsakanin Nurse station da Office din Nurain, taje office din yafi sau biyar saita tarar baizo ba, Nurse Amina ce ta shigo station din in a hurry tace "please Ruqayyah ki kulamin da ward C ina dawowa..", Ruqayyah tace "ina zaki haka..?", Nurse Amina ta dafe goshinta tace "Dr Uthman ne yake nemana a surgery room..", mi?ewa Ruqayyah tayi tace "surgery zaiyi knn..?", Nurse Amina tace "eh..", wani irin Waci Ruqayyah taji ya taso mata daga zuciya, she is part of the team toh me yasa ake neman wata Nurse din bayan gata, Nurse Amina tace "Please Rukky..", Ruqayyah ta girgiza kai tace "A'a gaskiya bazan kula miki da ward ba saidai ke ki zauna in shiga surgeryn", Nurse Amina tace "ai kwa da na fi son hakan ma, nagode sosai..", Ruqayyah tace "don't mention" da haka ta bar station din walking fast, surgery gown ta Wora kan uniform dinta ta saka nose mask da gloves kafin ta shiga surgery room din kanta a ?asa, with respect ta Wan russuna tace "sorry Dr..", Khaleel yace "come closer..", ta ?arasa ciki tana satan kallon Nurain, surgery tray ta dauka ta tsaya position dinta, ta Wauki Scalpel ta mi?awa Nurain, da haka aka fara surgeryn, kawai aikinsa yake cike da nutsuwa yayinda Ruqayyah ta kafa masa idanu tamkar zata cinyesa, wani sa'in ma sai yace ta basa instrument snn take basa sbd rashin nutsuwa, a haka dai har suka gama surgeryn, bayan an fita da patient din sauran doctors din ma sun fita Nurain ya cire hands gloves yayi disposing, sauke nose mask din fuskarsa yayi ya wuce zai bar room din, Ruqayyah tace "Dr...", ya juyo yace "yess Nurse Amina...", idonta yayi rau rau ta kai hannu ta zame nose mask dinta....
'?

Chapter 47.... Arewabooks @ feenerhfeeche02
=؛? HAJAR =؛?
Feenerh feeche ce

{47..}
Da mamaki Nurain ya ringa kallonta dan bai taSa tunanin da ita akay surgeryn ba Nurse Amina ba, Ruqayyah ta sauke idonta ?asa a hankali tace "the surgery was a success, alhmdllh..", baice mata ?ala ba ya juya ya fita daga surgery room din ya barta tsaye, tabi bayansa da kallo hawayen da suka taru idonta suka fara bin kuncinta, fita tayi daga room din bayan ta gama matsewa, ta cire surgeon gown kafin ta wuce Nurse station, bag dinta ta buWe ta Wauki black Abaya ta Wora saman uniform dinta, daga haka ta sa?ala jakarta a shoulder ta yiwa colleagues dinta sallama ta bar hospital din, tana fita titi ta tari napep ta gaya masa unguwar da zai kaita, shiga napep din tayi bayan sun gama ciniki, tafiyar minti ashirin ce ta kaisu unguwar, ya shiga da ita har layin da ta masa kwatance, sauka tayi daga napep din ta buWe handbag dinta ta ciro kuWinsa ta basa, ya mi?a mata chanjinta yaja machine dinsa, wani gida mai brown paint da black gate ta dosa ta fara knocking, almajirin gidan ne ya buWe mata, bayan ta shiga ya gaisheta ta amsa a takaice kafin ta nufi entrance din gidan, ta buWe ?ofa ta shiga palour da sallama, ?arewa palourn dake tashi da ?amshin turaren wuta gauraye da na freshner kallo take sai kace wani ba?onta, ta sake yin wata sallamar kafin ta zauna kan kujera, ?ofar wani room dake palourn aka buWe, Kulsoom ta fito da 2months old babyn ta goye a baya tana jijjigasa, ganin Ruqayyah tace "Ruqayyatu kece kika ta sallama sai kace wata ba?uwa..", Ruqayyah ta cire ?aramin hijab dinta tayi resting da kujera tace "ina wuni sister..", Kulsoom ta ?araso cikin palourn tana jijjiga babyn dake ?ishi ?ishin kuka tace "mun yini lfy...", Ruqayyah tace "alhmdllh..", Kulsoom na kallon fuskar ?ar uwarta ta da ta lura tayi duhu tace "kin kwaso rana..", Ruqayyah tayi ajiyar zuciya tace "kawosa naga kamar kuka zaiyi..", Kulsoom ta kwanto babyn ta mi?a mata tace "rigimamme ne wllh.." da haka ta wuce kitchen, Ruqayyah ta ringa kallon Babyn kafin ta lakuce masa hanci tace "shine kake wa sister na kukan banza ko, tubarkallah ga ka dai narkeke sai kace ba watanka biyu ba bare ace yunwa kake ji", ta ringa patting soft cheeks dinsa, deeply in her mind taji dama babyn ta ne, da anyi aurenta da Dearest da tini itama ta kusa haifar baby, Kulsoom ta fito kitchen da tray a hannunta, ajiye trayn tayi kan Centre table tace "toh ga ruwa kisha kafin na gama girki na ga kinyi wani wujiga wujiga...", Ruqayyah tace "na gaji ne, kuma gashi na shiga surgery yau na 3hours", Kulsoom dai ta gyaWa kai tace "Okay", a ?asan ranta tasan bayan gajiya akwai damuwa a tattare da Ruqayyah, Ruqayyah ta zuba ruwa tasha tana jin yadda sanyin ruwan ya sanyaya mata ma?oshi, bayan kamar 15mins Kulsoom ta tashi ta shiga kitchen, babu jimawa ta fito da plate da bowl a hannunta, Ruqayyah ta ringa kallon abincin tana jin appetite dinta na dawowa, lafiyayyen dambun shinkafa ne wanda yaji attaruhu da albasa da gyaWa yana bayar da wani ?ayataccen aroma, sai kuma coleslaw a bowl, Ruqayyah ta janyo abincin tana ci a hankali, kallonta Kulsoom ta ringa yi tana feeding babyn ta, saida taga ta ture plate din alamar ta ?oshi tace "kin gama....?", Ruqayyah tayi gyatsa tace "alhmdllh, godiya dubu..", Kulsoom na shafa kan babyn ta looking at Ruqayyah tace "now tell me, me yake damunki sister...?", Ruqayyah ta zaro ido tace "Ni.. me kika gani..?", Kulsoom ta saka serious face tace "haba Ruqayyah nifa ?ar uwarki ce na sanki ciki da bai, wllh there most be something troubling you, ji fa yadda kika rame kuma kinyi duhu ai ba haka hasken ki yake ba..", Ruqayyah bata san lokacin da hawaye ya fara zuba cheeks dinta ba, Kulsoom ba tace komai ba kawai kallonta take, Ruqayyah ta share hawayen tace "tin lokacin da na dawo Daddy ya yankamin warning cewa na fito da miji shi aurar dani zaiyi idan kuma banyi hakan ba zai aura min Dauda, Dauda fa wnn mai bacogalar ?afar, da kyar da ma?yar?yata na shawo kan Momy ta shigemin a wajen Daddy bayan na shirga mata ?arya nace ai mun sasanta da Dr, idan ya dawo daga tafiya za a Waura mna aure, da haka na samu abubuwa suka lafamin a wajen Daddy, sister wllh na gama sakankancewa ina tutiya da irin son da Dr yake min kawai jira nake ya dawo na basa ha?uri, and now he is back almost 2weeks da dawowarsa, nayi kiran a waya na tura text message amma duk a banza, babu kalar ha?urin da ban rubuta a message na tura masa ba amma he didn't respond to any of it, ke na ?ar?are miki mgana jiya har office dinsa naje ina basa ha?uri amma ya?i saurarata, daga ?arshe ya kiramin security, yau kam he kick me out of the surgery team..", Ruqayyah ta fashe da kuka tace "wllh Allah ina sonsa, i can't live without him Allah kuwa..", Kulsoom ta jinjina kai ta kwantar da Babyn da ta gama feeding tace "gsky kinyi babban kuskure da kika yiwa Momy ?arya Ruqayyah..", Ruqayyah tace "toh ya zanyi sister dole ce tasa na mata ?aryar nan, da banyi haka ba da tini an wuce wajen an auramin Dauda bacogala..", Kulsoom tace "ke kika fusata Daddy shiyasa ya kafe sai ya aurar dake, Ruqayyah yau inda ace baki aikata abinda kika yi ba wllh kinji dai har na rantse babu abinda zai sa Daddy ya miki auren dole, zai dauka cewa Allah ne bai kawo lokacin aurenki ba, amma akazo akay komai da komai ranar Waurin aure kika kwashi ?afa kika gudu...", Ruqayyah ta kastseta da faWin "wllh ba guduwa nayi ba..", Kulsoom ta haWe gira tace "let me land malama, idan ba guduwar ki kay ba toh uban me ki kai, yanzu dai ina baki shawara kije ki gayawa Momy cewa ?arya kika shirga mata snn kuma ki ha?ura da wani Dr, yo Allah na tuba mazan yanzu har wasu abin so ne, an gaya miki in this era ana yiwa namiji makahon so ne, namiji ya soka ma yaka ?are da wula?ancin sa ballantana wanda ya fito ra'ayil aini ya nuna baya sonka, idan Dr ya soki a baya toh yanzu ba hakan bane, ai kin masa narkakken wula?anci ba ?arya duk abinda ya miki ke kika siya da kuWinki, so wake up malama ki san inda yake miki ciwo, kin zauna kina wani Sare baki kina kuka shaSa shaSe akan wani namiji.... ehen ki ajiyesa a gefe ko shine autan maza", tinda ta fara magana Ruqayyah ta saki baki hanci kunne tana kallonta tamkar wata psycho, idonta har wani wul?ilewa yayi tsabar yadda take kallon Kulsoom cike da ruWin abinda ta gaya mata, Dearest din zata ajiye a gefe, da kyar ta iya cewa "wai doctorn zan ajiye a gefe..?", Kulsoom tace "yhap shi din mna tinda kinyi loosing opportunity tin farko...", Ruqayyah ba ta sake cewa komai ba ta fara haWa kayanta, ta saka wayarta a jaka, hijab dinta ta sanya kafin ta mi?e ta fara zura Abaya, Kulsoom ta bita da ido, Ruqayyah na gama saka Abayar ta Wauki handbag dinta tace "sai anjima", Kulsoom ta taSe baki tace "mu jima da yawa..", ficewa Ruqayyah tayi daga gidan fuskarta a haWe, da badan Kulsoom ?ar uwarta bace da babu abinda zai hanata dan?ara mata ba?ar magana, kuma taci sa'a elder sister dinta ce yau da ace itace gaba da Kulsoom to babu abinda zai dakatar da ita daga kwalla mata marii, wai ta ajiye Dearest a gefe wato ta rabu da shi, never ever babu abinda zai sa ta rabu da shi sai mutuwa, tana isa bakin titi ta tari napep zuwa gida.

&Hajar ta gyara Wakinta fes bayan ta gama cin Noodles da ta dafa, ta rufe Wakin ta sauka downstairs zata kai plate da cup din da tayi amfani dasu kitchen, gaban sink ta tsaya tana kallon liquid soap dake wajen, ta kunna pampo ta matsa liquid soap din a plate ta tashi foam, sponge ta dauka ta fara wanke utensils din da ta Sata, tass ta wankesu ta kife a inda ta Wauka, duk da kitchen din babu datti amma saida ta sake gyarasa, tayi drying hannunta da towel kafin ta fita daga kitchen din, room dinta ta koma tayi zugum sai kace wata prisoner, can dai ta gaji da zaman da?in ta tashi ta fita, ta kitchen tabi ta fita daga gidan zuwa backyard, through out the day anan tayi zamanta kamar dai jiya sai idan za tayi sallah ne take komawa ciki, bayan ta idar da sallar la'asar ta birkito kayan da ta saka set biyu sai nities da hijab biyu, toilet ta shiga da kayan ta zazzaga detergent a bucket ta shiga wankesu duk da cewa ba suyi wani datti ba, tana gama wankewa ta Wauraye toilet din ta fito da kayan cikin bucket, can backyard din ta wuce ta shanya kayan jikin flowers, tana cikin shanyar saiga mai gadi da watering can a hannunsa zai bawa flowers ruwan yamma, dan russunawa yayi ya gaisheta ta amsa kafin ta Wauki bucket din tabar wajen dan ta gama shanyar, tana shiga palour taji kamar ana buWe main door din gidan, ta ringa kallon ?ofar har aka buWeta, Nurain ne ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login