Showing 84001 words to 87000 words out of 252707 words

Chapter 29 - HAJAR COMPLETE NOVELS By Nafisa Yusuf Nagoda.doc

jikin ya tashi", yace "tom ina zuwa" ya koma cikin Wakin nasa domin Waukar wasu abubuwan, definitely yasan haka saita faru tinda ta?i bari yay mata allura, yana gama Waukar abinda zai Wauka ya fito, yabi bayan Mami suka wuce part enta, yana shiga Wakin ya Wauki ledar da ya bari kan chest of drawers, ya zu?i injection dose en da zai mata a syringe, ya isa inda take jingine da gado yana kallon hannunta da yaji zanen ?unshi, Mami ta ringa kallonsa ganin yayi tsaye bashi da niyyar yi mata allurar, har ya kai hannu zai ri?e hannunta sai kuma ya fasa, ya farke ledar hands gloves da ya shigo da ita ya saka gloves en a hannunsa, Mami da Noor dai suka bisa da ido, ita kam baiwar Allah Hajar ko iya buWe idonta ba tayi sbd haske linka mata ciwon kan yake, a damtse yayi mata allurar, ta motsa kaWan lokacin da ya zare empty syringe en daga muscle enta, ya saka mata drip da bai sa mata Wazu ba, deeply in his mind saida yayi dana sanin da yasa akay dischaging enta, wai shi gudun liability na asibiti yayi, sai gashi bai tsira ba, yana gama mata duk wani abin da ya dace yace "Mami you should get back to sleep, itama bacci za tay", Mami na kallon Hajar tace "gobe da sassafe sai mu koma asibiti gsky", yace "No, insha Allah she'll be fine", Mami tace "toh Allah yasa, Allah yay albarka", yace "Ameen" kafin ya fita, bayan minti goma da fitarsa Mami taga jikin nata har yay sauqi, ta koma baccinta kuma babu zazzaSi a jikinta, Mami ta kashe musu fitila kafin ta bar room din, washe gari kam jikin Hajar saidai nace alhmdllh cause kamar ba ita bace ta cikin dare jiya, har Waki aka kawo mata breakfast, daga wayewar gari zuwa yanxu da ake maganar 10 na safe Mami ta shigo dubata sau uku, Noor kuma ta wuce school tinda ranar Monday ne.

&Hakima Ruqayyah ta ajiye wayarta a kan mirror bayan ta gama tura text message, ta gyara wuyan rigar kayan baccin jikinta wando da riga kafin ta fita daga Wakin nata, kitchen ta shiga ta fara preparing breakfast, omelette roll da toasted bread saita tafasa black tea mai kayan ?amshi, tana gama haWa breakfast din ta Wakko Oat meal ta damawa kanta, ta zuba isasshen powdered milk da sugar kaWan, ta zuba 4pieces na omelette roll ta Wauki oat meal din ta fita, a palour ta zauna ta ci abincin, tana gama ci ta kai plate da cup en kitchen ta wanke, ta koma room enta ta shiga wanka, ta fito ta tsaya gaban mirror ta gama shafe shafenta tana humming song da tayi setting enta matsayin ringtone na dearest, well ironed uniform Winta ta Wakko ta saka, as usual ta Wora black Abaya saman uniform en, tsaf ta shirya snn ta Wauki wayarta ta zura a jaka ta fita ta rufo Wakin, room din Momy ta shiga don ta sanar da ita ta fita, Momy ta amsa gaisuwar da ta mata tace "kuma kika ce yau night ne dake?", Ruqayyah tace "Eh, exchanging nayi da wata collegue dita ita tamada abinda za tay da safe", Momy tace "ohk, toh sai kin dawo", Ruqayyah tace "uhmm, nayi breakfast na ajiye muku a kitchen", Momy tace "Okay", Ruqayyah ta mi?e zata fita, har ta kai ?ofa Momy ta kirata, dawowa tayi ta zauna, Momy tace "kinsan dai lokacin da Daddy ya Webar miki ya kusa ?arewa ko, ya maganar Dr tinda kince kun sasanta idan ya dawo daga tafiyar komai zai daidaita, ya ake ciki ya dawo en ko bai dawo ba, don na gaji da kareki a wajen Daddy zanyi shiru na zuba idanu ya aura miki Daudan tinda dai bashi da wata matsala...", Ruqayyah ta sauke wata Soyayyar ajiyar zuciya tace "Momy, har yanzu bai dawo bane, daga ya dawo shknn, dan Allah ki cigaba da bawa Daddy ha?uri, wllh bana son Dauda bayan mata biyu da yake dasu gashi gajere kamar a kife da kwando, kuma fa Wingishi yake wllh sai a zata gurgune..", tini idonta ya kawo ruwa, Momy ta taSe baki tace "Au lallai Ruqayyah har kinada bakin kushe wani ko, toh ke da kike ba nakasasshiya ba ai ba finsa kikai wajen Allah ba, toh kwa ki san inda dare yayi miki wllh, haba kin bi kin nace sai Dr, Doctorn da kika tozarta kika gudu kika barsa ranar Waurin aure, daman ni jinki kawai nake da kike cewa ai kun sasanta, ai ba zuciyar kare ne dashi ba da zai yarda dake bayan cin amanar da kikai masa, wani chance en sau Waya yke zuwa a rayuwa, ki tsaida hankalinki ki fuskanci reality, ki na dai da manema ba babu ba...", Ruqayyah dai gaba Waya guiwarta ta saki, ta goge kwallar da ta zubo mata, Momy tace "you may leave na gama dake", Ruqayyah ta tashi tana goge idonta tace "zan biya gidan ya Kulsoom", Momy tace "kar kiyi dare", tace "tom" kafin ta buWe ?ofa ta fita, slowly take tafiya a street en gidansu tana sa?a da warwara a zuciyarta har ta fita babban titi, ta tsayar da Napep ta gaya masa inda zai kaita, har cikin asibitin ya shigar da ita, ta sauka ta buWe jaka ta bawa mai napep kuWinsa, a hankali take tafiya tana kallon parking spaces, wani irin harbawa zuciyarta tayi, hope din da take dashi ya zagwanye gami da tsiyayewa ta guiwarta ganin babu motar Dr Uthman a wajen parking ensa, direct hanyar office ensa ta nufa, tayi zaman jira kan silver chair dake ?ofar office en nasa, nace wasa farin girki hakima Rukky, almost one hour tana jira amma babu alamarsa, ta shiga aikin da ta saba na kiransa da tura masa text message, ta ciro handkerchief ta fara share hawayen dake sauka idonta, ji tayi ance "A Nurse are you okay?", ta Wago kanta sukay ido huWu da Khaleel, tayi fake smile tace "Oh Dr am fine..", ya tsuke ido yace "are you sure?", tace "sure", ya kalli ?ofar office en Dr Uthman yace "but what are you doing here all alone?, aren't you suppose to be in nurse station?", ta sake yin wani fake murmushin tace "yeah, yanzu nake shirin tafiya can en", yace "ohk see you later.." da haka ya bar wajen ya barta zaune, ta dafe kanta a hankali tana tunanin what next, ga dukkan alamu dai wanda tazo Hospital en dominsa bazai zo ba, daman yau sai dare take da duty amma sbd shi ta ?uma uban sammako, gashi kuma bai zo ba, tamkar wacca aka zarewa spine haka ta tashi ta bar bakin office en, wani irin nauyi zuciyarta tayi mata, haka ta sake saSa ta fito daga asibitin, ta tsari napep zuwa gidan Kulsoom.

&Sosai Hajar ta ware, she really appreciate yadda mutanen gidan suke they were so humble and caring, duk abinda take bu?ata an mata shi, lunch ma har Waki mai aiki ta kawo mata, ga Mami wacca take dubata akai akai, da daddare Hajar ta idar da sallahr magrib knn tana wrapping prayer mat Noor ta shigo, tace "Alhmdllh jiki yay sauqi, ai zaki iya fitowa ko?..", Hajar ta ajiye darduman kan stool ta girgiza kai a hankali, Noor ta jingina da jikin ?ofa tace "na shi gangaWe...", da farko kamar Hajar ba zata tambaya ba sai kuma tace "me ya faru?", Noor ta shafa forehead dinta tace "wllh iron lady ce, nace mata kin samu lfy amma duk bayan minti talatin saita ce nazo naga ya kike, wai ?afarta ke ciwo bazata iya tafiya sosai ba, ta hanani ma kallon stuff ena gashi i hate watching it on phone or computer, i prepare watching it on TV...", Hajar dai ba tace komai ba, Noor tace "dan Allah kizo muje ta ganki in yaso saiki dawo, Allah bazata barni na huta ba", Hajar dai tayi shiru ba ta san me za tace ba, ita kam bata son ma ta Wara ko ina, kawai dai dagewa take tana so ta zama comfortable which was very hard on her, ta kalli expression en fuskar Noor wacca take kallonta da pleading eyes tana jiran amsa, da kyar ta iya cewa "tomm", Noor tayi clapping hands enta wanda hkan ya bada sound kaWan tace "thank you, muje ko, tana ganin dai you are fine saiki dawo abinki, rigimar tsufa ne..." da haka ta buWe ?ofa, Hajar ta gyara wuyan dogon hijab din da ta idar da sallah kafin tabi bayanta, ba kowa a huge palourn Mami, itama Mamin ta shiga bedroom enta daman idan ta shiga sallar magrib bata fitowa sai after isha'i, Hajar tayi surveying palourn da idanunta tana biye da Noor, Noor ta buWe ?ofar fita daga part en kafin suka wuce long corridor suka fita main palour, nan ma dai saida Hajar tayi surveying ensa, wani nervousness ne ya rufe ta, ta fara tambayar kanta to wane ne wnn abokin na Baba ita dai bata sansa ba, tinda take bata taSa ganin palour mai girma da ?awatu kamarsa ba, ita bata tsaya ?arewa gidan kallo ba jiya da aka kawota, ko lokacin sallah da agogon room enda take ciki take amfani cause bata gane dare da rana sbd komai na gidan equal yake, safe rana dare duk akwai wuta, Noor ta wuce hanyar da zai leading zuwa part en Hajiya, Hajar dai was following her like one living statue, buWe ?ofan part en Hajiya Noor tayi da sallama, Hajiya dake zauna kan lallausan carpet ta mi?e ?afafuwa ta kalli door tace "waye anan?", Noor ta matsa gefe Hajar ta shigo da sallama, Hajiya ta sake cewa "nace waye anan...", Noor ta tsugunna gabanta ta Wauki glasses enta ta saka mata tace "da me yasa kika cire glasses dinki..?", Hajiya tace "yo idon ne yake min ?ai?aiyi shine na cire zan sosa, ban kai ga sosawar ba naga inuwa akaina", Noor ta dubi Hajar tace "?araso mana", Hajar ta ?arasa shiga cikin palourn ta zauna can ?arshe carpet, Hajiya ta bita da ido, Hajar tace "ina yini..", Hajiya tace "wace ce wnn?", Noor tace "Au keda glasses din ma idon naki sai a slow, wacca fa kika takura naje na dubo miki ce fa", Hajiya tace "O oho matar Usuman din ce?", Noor tace "daman nace miki taji sauqi, toh gashi dai yanxu idonki ya gani", Hajiya tace "matso kusa mana ?ar nan saiki raSe can ?arshen buzu sai kace wata bare ba ?ar gida ba", Hajar ta matso a hankali ta shigo kan carpet en sosai ta sake tisa gaisuwar da tayi mata, Hajiya ta amsa tana dashare wawulon bakinta tace "tubarkallah masha Allah, yarinya ta saSe jiki yayi kyau alhmdllh", Noor tace "ai na gaya miki", Hajiya tace "ita ta zaunar dani a gidan nan, yo inba larura ba mai zaisa na baro mijina na zo nan na zauna, hankalina ne ya?i ya kwanta wllh tin jiya da naga yadda muka kaita asibiti, ace ana kawo mna yarinya sai kawai ta kwanta ciwo sai kace an kawota wajen mayu, kinga kwa gobe in Allah ya kaimu saina kira Umaru yazo ya Waukeni na koma gidan tsamiya..", Noor ta haWe gira tace "nan ma ai gidan tsamiya ne", Hajiya tace "nan fa Waya, ba miji a gida ta ina ya zama gidan tsamiya", Noor ta mi?e tana kallon Hajar tace "bari nayi leading enki ki koma ko..?", Hajar ta gyaWa kai, Hajiya tace "ta koma ina kuma, rabu da ita anan tayi zamanta tinda ba tace ta gaji ba, haka kurum ki ?ugata a Waki", Noor ta koma kan kujera two sitter ta zauna, remote ta janyo ta canza channel, tayi murmushi don yanxu ne ake taken next Cdrama da take so, ta fara cin coconut macaroons da ta ajiye nan tare da popcorn, Hajiya ta micincina idanu tana kallon Tvn tace "ji mutane sai kace aljanu, fuska kamar anyi Sarin filawa, anya ma kwa akwai ji a jikinsu?", Noor dai an riga da an bada amanna ba ta ji ma sosai, a hankali Hajar dake wasa da laushin carpet ta Waga kai ta kalli TV, ko minti goma ba ai da fara film en ba ta ji ya Wan birgeta sbd margic da ake zubawa, Hajiya sai mita take a mayar mata da makka, Noor kam tayi mata shiru tinda ita ta nace saita zauna a wajenta don haka sai ta gama kallonta kuwa, Hajiya ta sa?a hannunta ?ar?ashin kujerar da ta jingina da ita ta ciro kwalbar man zafi (Aboniki), ta buWe kwalbar ta shiga lakuta tana laftawa a sangalale, tini Noor ta toshe hanci sbd har yaji ya bulale palourn, saida ta lafce ?afufuwanta tasss da Aboniki, sai shining suke da she?i, can wajen yatsun ?afar ne kawai bata shafawa ba sbd hannunta bazai kai ba kuma bata iya tankwashe ?afar, ta lakuto wani lafcece kafin ta dubi Hajar da already idonta ya kawo ruwa sbd yaji tinda tafi kusa da ita tace "shafa min daga nan saman makyangyamar..", ba musu Hajar ta mi?a hannu Hajiya ta lakuce mata uban man Aboniki a tafin hannu, a hankali Hajar tayi rubbing dinsa a palm kafin ta fara shafesa a toes en Hajiya da suke a yamushe kuma a tattare sbd tsufa. juyowar da Noor za tay kenan taga Hajar na aikin da ita da Aysha ke gudu, Noor tayi murmushi ta kuma toshe hancinta ta cigaba da kallonta, door aka buWe aka shigo, scent ensa ne ya mamaye palourn, yay sallama yana ?arasa shigowa sai kuma ya tsaya cak, Hajar ta Wauke hannunta daga legs en Hajiya gami da mayar dashi cikin hijab ta juya ta cigaba da kallonta, and that gives him the full access to saw her face completely, and he realized her, automatically ya juya ya fita a palourn tare da banging door......
'?

_Dear HAJAR fans, sai fa kun yiwa Feenerh feeche uxuri, a tsakani ga Allah wllh ni kadai nasan irin stressing kaina da nake wajen typing, 3 to 4 hours nake Wauka kafin na gama one chapter banda editing, ku kuma a minti biyar zuwa goma kuke karanta shi. you know ni sabuwar writer ce speed en typing dina ba mai yawa bane, plxx be patient with me, insha Allah together we'll see the end of this book. my pleasure. ina yinku wujiga wujiga mutane na. =?
? >?p?
=؛? HAJAR =؛?
by Feenerh_ feeche

{40..}
Hajiya tabi ?ofar da Nurain yayi banging da kallo tace "ikon mai duka, cewa nayi fa zanyi magana da kai shine zaka zo ka nunamin wata fuskarka da na rasa dalilin sauyawarta ka fita", Hajar ta runtse idonta tana haWiyar wani kwallo da ya tsaya mata a throat, ta wutsiyar ido ta gansa shine ta maze, gaba Waya taji ta tsani zaman nan en so take ta koma inda ta fito, a hankali ta mi?e tana jan fingers, Hajiya ta dena sababin da take ta Waga kai tana kallon Hajar tace "lafiya kika mi?e sai kace wacca aka zubawa mugun mintsili?..", Hajar tayi kasa da idonta tace "zanyi sallah ne..", Hajiya ta nuna mata qibla tace "buzun tsaftatacce ne, kiyi sallar ki", Hajar dai tayi shiru don ba haka taso ba, ita so take ta bar nan din kawai, Hajiya tayi kasa?e tana kallonta ganin bata kalli qiblar ba kuma ba tada niyyar kabbara sallar da tace za tay, Hajiya ta dubi Noor tace "?ar nan, kee", ina Noor sai blushing take tana tura coconut macaroons a baki, gaba Waya mind dinta na kan TV, Hajiya ta Wauki trow pillow ta wurga mata, sai a snn Noor ta juyo tana wuri wuri da ido tace "mene ne iron lady?", Hajiya ta mata da?uwa tace "wnn wane irin masifar kallo kike ne, nayi ta miki magana amma kin saki baki da hanci kin zubawa wasu ?odaddu idanuwa a talabijin", Noor ta ajiye coconut macaroons da take ci tayi folding hands tace "Allah ya baki ha?uri, banji bane", Hajiya tayi tsaki tace "kinga ?ar nan matar Usuman tace zatay sallah nace tayi anan tinda buzun tsaftatacce ne amma ta?i yi, toh inajin dai tsaftarsa ba tay mata ba, ki tashi ki Wakko mata wani acikin Waka sai ta Wora akan wnn tayi sallar", Hajar tayi ?asa da murya kanta a ?asa tace "A'a zan koma can din ne sai nayi sallar a can", Noor ta tashi tace "alright muje na rakaki..", da haka Noor ta nufi door Hajar tabi bayanta walking slowly, Hajiya ta bisu da kallo tana taSe baki tace "Au wnn aka aurawa Usuman, da gani bata son mutane, ta zauna a cikin mutane amma ta?i ta gwammace ta ?ursuma a Waki, Allah dai ya kyauta...". har sun kama hanyar part din Mami sai kuma Noor ta dakata, ta juyo tana ?arewa main palourn kallo, taji scent dinsa amma kuma bata gansa ba, yana zaune a edge of executive two seater yana operating Mac phone, Noor ta buWewa Hajar ?ofar shiga part en Mami tace "go ahead am coming", Hajar ta shige ciki, Noor ta koma main palourn ta isa kusa dashi ta tsaya daga gefen kujerar tace "Yaya ina yini?", ciki ciki ya amsa mata ba tare da ya kalleta ba kawai danne dannesa yake jikin Mac phone, tace "Yaya don Allah zan turo maka da project dina ka duba min kafin nayi submitting na gama..", sai a lokacin ya Waga kai ya kalleta kafin ya mayar da idonsa kan abinda yake yace "Ohk, Allah yasa ba shirme kike rubuta ba, don naga yanzu ba kya karatu sai kallon shirme kika iya, keep this in front of your mind idan shirme kika rubuta am going to punish you", ta sosa forehead dinta tace "shknn ma, yaya Farooq zan turawa ma kar nayi stressing dinka", yace "kafin 9pm naga mail dinki in my inbox Noory", ta gyaWa kai a hankali tace "Sure Yaya" ta bar wajen ?irjinta na bugawa, tasan dai bata rubuta shirme ba cause saida tayi research kafin ta rubuta komai, amma dai dole sai an mata gyara, ta shiga part en Mami, a tsaye ta tarar da Hajar a


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login