Showing 6001 words to 9000 words out of 252707 words

Chapter 3 - HAJAR COMPLETE NOVELS By Nafisa Yusuf Nagoda.doc

riga Tshirt duk ta jeme, gyatsine tayi ta mulmulo ashar tace "kai me za a baka kake mana ihu??", yaron yace "yaji za'a zuba min a kulele", Sa'adatu taja wani dogon tsaki tamkar tsohuwar tsaka tace "kawo na zuba maka", ya mi?a mata kwanon, ta buWe tana kallon kulelen da aka shanana masa manja gwanin sha'awa, ta taSe baki ta tsugunna ta duntsi ?asa cikin hannu ta barbaWe kulelen da ita tas, ta rufe ta mi?a masa tace "jeka an zuba yajin", yaro yayi kasa?e yana kallonta da mamaki, taja tsaki ta fara kwashe kayan shanyarta akan igiya, Hajar ta fito daga bayi taga yaro tsaye da kwano a hannunsa tace "yaji za'a zuba ko??", ya nuna Sa'adatu da hannu yace "waccan ce ta zuba ?asa a ciki", Hajar ta zaro ido waje tace "?asa?" ta karSi kwanon ta buWe, ai kam dai kulelen nan bazata ciyu ba saboda tasha ?asa harda tsakuwa, wani ?ululu ne ya tsaya mata a ma?oshi gashi umma ta mata gargaWi, dole ta hakura ta zubo masa wata sabuwar kulelen ta juye waccan, ta koma kan kujera ta cigaba da yanke farce, gani tai bazata iya yin shiru ba kawai anyiwa baabarta asara ta Wari biyu, ta kalli Sa'adatu da take kwashe kaya jikin igiya tana bigesu saita linke ta Wora a kai tace "Sama fanta ?asa coca cola, fuska fara ?afa ba?a", Sa'adatu ta ?yal?yale da dariya amma a zuciyarta ji take kamar ana zuba mata dalma, Hajar kam kamar ta sani harma kamar wa?a take haka ta cigaba da cewa "Sama fanta ?asa coca cola, fuska fara ?afa ba?a", Sa'adatu da haushi ya gama turnu?eta gashi Hajar ko kallonta ba tay ballantana tace da ita take ta shiga Waki tamkar zata tashi sama.

&Zaune take cikin wani jugunannen palour wanda ya ?ure lambar haWuwa, hannunta ri?e da wani tsadadden bowl tana shan fruit salad, damSasheshiyar Tvn palour sai aikinta take, wata ?ar budurwa ce ta sakko daga kan stairs Win da ya kewaye makeken palour, ta zauna kan sofa tace "Mami yaya Nurain bai dawo ba har yanzu??", Mami ta shanye fruit Win bakinta tace "Eh bai dawo ba", Noor ta ta?une fuska ta kalli agogo sai kuma ta jingina da kujera ta fara latsa tsaleliyar wayarta, Mami ta kalleta tace "is there any problem dear??", Noor ta ajiye wayar tace "No Mami", Mami tace "ohk" ta cigaba da shan fruit salad Winta tana kallon Tv, few Minutes after that wani sassanyar ?amshi ya fara karaWe palourn da yake ?amshin breath taking freshner, Noor ta kalli door jin ?amshin na yayanta ne, ai kam dai shi Win ne, yayi sallama ya tako a hankali hannunsa ri?e da briefcase, Mami ta ajiye bowl Win hannunta a hannun kujera bayan ta amsa sallamarsa, a kan soft carpet Win dake malale a palourn ya zauna yace "Mami barka da gida", Mami tayi murmushi tace "An dawo lafiya Nurain", yace "lafiya alhmdllh" ya koma kan kujera ya zauna. Noor tace "yaya sannu da dawowa", ya kalleta yace "yawwa Lil sis", Mami tace "a kawo maka abinci ko sai anjima", yace "amm yanzu zanci, Noor ta shirya min kafin na dawo", ya Wauki briefcase Winsa yabi stairs, saida yayi wanka ya shirya cikin ?ananan kaya ?an ubansu sannan ya sakko down stairs, already Noor ta gama shirya masa lunch, zama yayi yana ci peacefully, Mami tace "yauma kayi surgery ne Nurain??", ya ajiye spoon Win hannusa yace "yeah Mami, amma banje hospital da nufin yin surgery ba, wata patient aka kawo emergency tana bu?atar aiki in not less than 24hours, a rayuwar nan ta yanzu nothing goes without money, gashi asibiti sun bu?aci su kawo kuWi mai yawa kuma basu da hali ga surgeon Win da zaiyi aikin yace sai an biya sa, ni kuma naga aikin is inside my field shine nayi surgeryn free", Mami ta jinjina kai tace "Allah ya saka maka da alkhairy, i know baka zama likita saboda neman kuWi ba sai don temakon al'umma". yace "Mami akwai rashin temako a ?asar mu sosai, masu temako basu da yawa". Mami tace "idan ka temaki wani Allah zai temake ka, Nurain Allah kaima ya dafa ma cikin lammuranka", yace "Ameen". glass cup ya Wauka da lemon kwali, har zai buWe lemon sai kuma ya fasa ya kalli Noor yace "plxx change it with chivita orange", ta mi?e ta amsa ta shiga kitchen ta buWe damfareren fridge ta Wakko masa chivita orange, ta dawo ta ajiye masa a gabansa sai kuma ta tsaya tana kallon rigar jikinsa fara tass, tsuke ido tayi tana nuna rigar tace "yaya wai rigar nan ta rannan da ka shafo taSo ajiki yauma itace ka saka??", Nurain ya kalli rigar jikinsa yace "hey get out" ya saita mata hanya........
'?

=؛? HAJAR =؛?
by Feenerh_feeche

{ 5...}
Noor ta koma kan kujera tana murmushi tace "Allah kam sai naga kamar rigar ce", shiru yayi mata ya buWe lemonsa ya zuba a glass cup ya fara sipping, Noor ta tashi ta haye stairs ta kara wayarta a kunne tana murmushi. Mami ta kallesa tace "Nurain", ya Wago yace "na'am Mami", Mami ta sauke ajiyar zuciya ta mayar da hankalinta kacokan akansa tace "you have to move on dear, me ake ciki ne maganarka da Ruqayyah??, ka riga da ka gama gini to mai kake jira, gaskiya ya kamata ka motsa kar iyayenta su Wauka playing daughtern su kake", Nurain ya sauke sassanyar ajiyar zuciya ya dire cup Win hannunsa yace "yeah Mami daman ina so na gaya miki ki sanar da Abba, I'm ready a kai kuWin, kuma..." sai yayi shiru yana shafa lallausar sumarsa, Mami tace "kuma me??", yace "kar a saka lokaci mai tsaho tinda dai mun gama fahimtar juna, kuma maganar lefe shima ba wata matsala Insha Allah", Mami tayi murmushi tace "idan kai a shirye kake toh iyayenta fa, nima kaina ban shirya ba", yace "Amma nasan kafin lokacin kin shirya aii", tace "maganar lefe mai za a ?ara nasan dai akwai wasu kayan wajen zulaiha, abinda ya rage bashi da yawa", yace "yeah munyi maganar da ita tace 2million sun isa a cike ragowar kayan", Mami tace "toh shknn zan sanar da Abbanku idan ya dawo", Nurain yace "ohk, bari na fita masallaci", ya mi?e ya fita daga palourn. Da daddare Mami ta tari Abba da maganar ta sanar dashi komai, Abba yana zaune a palournsa ya kalli Mami yace "ohk, kika ce yace he is ready??", tace "uhmm haka yace", yace "ohk then, bawai na rabu da Nurain yayi komai na aurensa yana nufin bana sonsa bane, abinda yasa ina son ya martaba matarsa ne kuma ya kula da ita, nafi so yayi aure da dukiyarsa yadda zaifi kula da matar da ha??o?inta, though banida doubt akan Nurain amma i have to do this", tace "na fahimceka my prof". Abba ya Wauki wayarsa yayi dialing numbern Nurain ya kara a kune, Nurain a lokacin yana balcony yana waya da Ruqayyah, ganin kiran da yake shigowa wayarsa yasa yace "ina zuwa bari na Wauki kiran Abba zan kiraki if I'm done", Ruqayyah tace "ohk" ta katse kiran, yayi picking kiran Abba, ba tare da Sata wani lokaci ba Abba yace masa ya samesa a palourn sa ya katse kiran, Nurain ya sakko down stairs ya wuce part Win Abba, ya murWa tsadadden handle Win ?ofar palourn ya shiga da sallama, Mami ce ta amsa ya ?araso ciki ya zauna kan carpet yace "Abba gani", Abba ya nuna masa sofa yace "zauna", ba musu ya koma ya zauna inda Abba ya nuna masa, Abba yace "naji sa?onka wajen Maminku, naji daWin hakan, kace kar a saka lokaci mai tsaho amma baka tunanin Sangaren ita yarinyar zasu iya cewa lokacin ya musu ?aranci, kamar month nawa kake so ayi fixing date??", Nurain yace "Amm kamar three months haka", Abba ya jinjina kai yace "ohk, kaine ai me aure shiyasa nake tambayarka, amma bazan yi assuring dinka three months ba idan sun nemi a ?ara musu lokaci za a mayar five months, idan kuma basu nema ba za a barshi a three months din da kake so, Insha Allah gobe zan samu uncles Winka next tommorow sai aje gidan nasu", Nurain yace "okay", Abba yace "ka iya tafiyarka".

&Umma na fita bakin titi ta tari napep ya kaita har ?ofar gidan Anty Jamila dake a unguwar Goron dutse, Umma ta shiga Wan madaidaicin gidan mai Wan ?aramin gate da wajen parking mota Waya matsayin tsakar gida, Anty Jamila baki har kunne ta tarbi ?ar uwarta cike da murna, suka zauna a Wan matsakaicin palourn Anty Jamila da yasha ado ba laifi, Hafsa ce ta shigo wacca itace second born Win Anty Jamila da jug mai Wauke da zoSo mai sanyi da ruwa ta ajiye a gaban umma, Umma tace "kai alhmdllh jiki yayi sau?i, Allah ya ?ara afuwa", Hafsa tace "umma ina wuni, ya baki tahomin da Hajar ba?", Umma tace "lafiya lou, Hajar tana nan tafe zata zo aii", Hafsa tace "tom Allah ya kawota" ta fita ta basu waje. Anty Jamila tace "wllh Adda dama baki wahalar da kanki ba ai na gaya miki Hafsa taji sau?i, amma naji daWin zuwanki", Umma ta tsiyayi zoSon a cup ta ajiye gefenta tace "akwai wani dalilin da ya kawoni bayan duba Hafsa aii", Anty Jamila ta gyara zamanta ta Wauki remote ta kashe ?arar Tv tace "ai da kin gaya min sai nazo can Win ma Adda ba sai kin wahalar da kanki ba", Umma ta sauke ajiyar zuciya tace "babu komai nan Win yafi", Anty Jamila tace "toh Adda Allah yasa dai lafiya", Umma tayi sipping zoSo tace "Jamila babu abinda baki sani ba akan rayuwar gidan da nake, toh a da dai abin bai fiya damuna ba sai yanzu da Hajara ta fara mallakar hankalinta, yanzu fa gidan kullum cikin tashin hankali ake, ga Hajara ba zata taSa gani ta kyale ba, in ?ar?are miki zance har dambe ake yi dani", Anty Jamila ta ri?e baki ta zabga salati tace "Adda dambe..", Umma tace "da zarar sun tsokani Hajara saita rama, to sai su haWu su lakaWa mata duka, ni kuma idan naga zasu kassaramin ?a saina shigar mata a haka abin yake zama dambe, babu irin faWan da ban yiwa Hajara ba akan ta dena biye musu amma kuma ta?i ji saboda na lura da ita tanada zuciya kuma bata son wargi, toh yanzu gaba Waya lungun mu an riga da an canfa mana gida wai mu ?an bala'i ne kullum cikin dambe muke, kinsan mutane wallahi harda nasu gishiri da magin suke ?arawa, ni dai yanzu na yanke shawara zan mayar da Hajara wajen Iya ko a samu sau?i, jira nake suyi sauka a islamiyya saita koma gaban Iya, ko ya kika gani??", Anty Jamila tace "Eh toh me zai hana ki kawomin ita nan saina haWasu da Hafsa", Umma ta girgiza kai tace "gara dai na kaita wajen Iya kinga ta ringa taimaka mata da wasu abubuwan, amma kuma bansan ta yadda zan shawo kan Mal ba kinsan yadda yake jin Hajara duk cikin ?a?ansa", Anty Jamila tace "indai kikai masa bayani ai zai gane". Umma bata baro gidan Anty Jamila ba sai bayan sallar la'asar.

&Wata numfasasshiyar Mota ce tayi parking a daidai lungun ?unshi, saida motar tayi minti ashirin da tsayuwa sannan Sa'adatu ta buWe ?ofar mai zaman banza ta fito, hannunta ri?e da ledoji ta fara tafiya tana rangwaWa ta shiga lungunsu, Naseer na zaune akan benci gaban shagon Iliya kuma akan idonsa aka sauketa daga mota tazo ta wuce, iliya da Munkaila suka haWa ido suka kasa cewa komai saboda kasancewar Naseer a wajen, ita kam Sa'adatu bata ma lura da yayan nata ba saboda duhun dare na damuna, saida Naseer ya bari tayi nisa sannan ya biyo bayanta, tana shiga soro shima ya shiga ya sakawa ?ofa sakata, ya saka ?afa ya kwarfeta ta zube a ?asa har saida bayanta ya amsa, beyi wata-wata ba ya zuge belt Win wandonsa ya fara zabga mata ta ko'ina, Sa'adatu ihu take tana neman ceto gashi ta kasa tashi ?ugunta ya ri?e, da iya ?arfinsa yake sauke mata ruwan belt ajiki. Maama da Maimuna da kuma Nabilah da suke tsakar gida suka jiyo ihu a soro, Maama ta mi?e da sauri tana gyara zaninta da yake shirin kwancewa tace "ke Sa'adatu ce fa" tayi hanyar soro cikin sauri Maimuna ta bita a baya, Nabilah kuma ta rarumo wayarta keypad tana ?o?arin kunna fitila wayar ta suSuce daga hannunta ta tawarwatse a ?asa. soron duhu dunWum Maama cewa take "Nasiru ka rabu da ita nace maka", Naseer kam dukan Sa'adatu yake da iya ?arfinsa yana cewa "uban waye wancan da ya ajiyeki a mota??", Sa'adatu da azaba ta hanata magana sai gunji take, Maama ta kwalawa Nabilah kira tace "ki Wakko min kyandir a Waki", kafin Nabila ta kawo kyandir ai Sa'adatu ta faWawa ?an garinsu, a matu?ar fusace Naseer ya wuce cikin gida Maimuna da take kan hanya itama saida ta samu rabonta, domin kuwa saida ya cije ya zabga mata belt Win hannunsa ta Waureta ya zuge mata ita ajiki tayi mata wankan jego, da mugun gudu Maimuna ta kyalla cikin gida tana soshe-soshe, batama san lokacin da ta bangaje Nabilah ba kyandir Win hannunta ya li?e mata a wuya har saida fatar wajen ta kwaile, Nabilah da zafin wuta ya ratsata ta mulmulo ashar ta dan?ara mata, a banza dan Maimuna batama san me ta aikata ba ji take tamkar an zuba mata tafasasshen ruwan zafi a fatar baya. Maama ta tallafi Sa'adatu ta shiga da ita cikin gida, gaba Waya jikinta yayi ruWu-ruWu da shatin belt, ga wani shaWi da yayi mata a fuska wajen har ya kwaile, Nabilah ce ta tsaya Wakko ledojin da Sa'adatu tayi wurgi dasu tin lokacin da Naseer ya kwarfeta, shawarma ce da pizza gaba Waya sun gama baWewa da ?asa babu ta yadda za ai su ciyu, ice cream kam kifewa yayi a ?asa. Maama ta shiga Wakinsu Naseer tace "Nasiru banyi maka gargaWi akan dukar min ?a?a ba?", Naseer ya dafe kai yace "Maama dan Allah ki barni da yaran nan, wllh a wata ?watuwar mota aka sauketa, ki duba fa irin suturar jikinta sai kace ?ar arna", Maama tace "nima tashi ka dakeni Nasiru tinda har agaban idona kake kiran ?ata arniya", Naseer ya fice ya bar Wakin yayi soro da sauri. Washe gari tinda Hajar tayi sallar asuba bata koma bacci ba, tana zaune tana tilawar Al'qurani har saida gari ya fara washewa sannan ta rufe karatun ta matsi toothpaste a brush Winta ta fita tsakar gida, saida ta kusan wurgi da brush din hannunta ganin Sa'adatu da take fitowa daga Wakin Maama da Wingishi, fuskarta ta kumbura idonta na hagu ya lume da taruwar jini a gefensa, gefen kumatunta ya kumbura suntum sai kace ta ajiye kwallon goruba a baki, duk da irin saSanin da suke samu saida ta tausaya mata, jiya da daddare tana jin lokacin da Naseer ya lakaWa mata na jaki, Hajar ta taSe baki ta saka slipers dinta ta wuce gaban tukwanen ruwa, ta Webi ruwa a buta ta saka kujera ta zauna ta fara goge bakinta, kamar daga sama taji saukar wani mugun WaWe a gadon bayanta, ta gantsare saboda azaba brush Winta ya suSuce daga hannunta..........
'?

=؛? HAJAR =؛?
by Feenerh_feeche

{6...}
Da sauri Hajar ta mi?e daga kan kujera ta juya taga wane ne yayi mata wannan azababben WaWen na rashin imani, Maama ta gani tana mata wani kallo mai cike da tsantsar tsana, Hajar ta ja da baya idonta na kawo ruwa tace "me nayi miki??", Maama tace "uwarki kikay min, uban waye yace ki zauna min a kujera?, ko so kike ki shafamin ba?in fentin da ke tare dake", Hajar bata ce komai ba darajar Naseer da Huzaifa yasa take ragawa Maama, Sa'adatu ta Wingiso tana ?o?arin buWe idonta na hagu da ya kanne tace "chaS wannan Wan dukan, ai da kin sani dundu kikay mata wanda shegiyar za tay aman wahala", Hajar ta tsotse kumfar bakinta ta tofar ta zabgawa Sa'adatu harara tace "ke dalla malama ja can da ruSaSSen bakinki, wllh kika sake magana saina naushi Wayan idon kinyi duka babu", umma daga cikin Waki ta jiyo muryar Hajar ai kam ta fito da sauri, tana ganin Hajar tsaye ta ri?e ?ugu ga Maama da Sa'adatu tasan ba lafiya, daga bakin ?ofa ta tsaya tace "Hajara zo nan yanzun nan", Hajar ta Wauki buta ta kuskure bakinta ta Sallawa Sa'adatu harara ta shiga Wakin umma. Maama ta kalli fuskar Sa'adatu tace "keda nace karki fito, me za kiyi a wajen?", Sa'adatu tace "bayi zan shiga ne", Maama tace "toh ina Maimuna da nace ta taimaka miki kafin anjima a karSo miki magani a chemist", Sa'adatu tace "uhmm Maimunan ce zata temaka min" ta Wingisa ta Wauki butar da Hajar ta ajiye mai ruwa ta shiga bayii. Maama ta bita da kallo sai kuma ta nufi ?ofar Wakin su Naseer, bubbugawa ta shiga yi da ?arfi, Mu'azzam ya buWe, ta Salla masa harara tace "ban hanya", ba musu ya matsa mata ta tura kai Wakin, Naseer da yake kwance a katifarsa ya rufa har ka ta tsaya tana kalla, ta yaye rufar tace "Nasiru tashi", ya buWe idonsa da kyar ya mi?e zaune yace "Maama lafiya??", tace "ka gaida babanku kuwa?", ya juyar da kai yace "Tin asuba muka gaisa aii", tace "toh maza yanzu ka fito ka sameni a tsakar gida karka Sata lokaci" ta fita a Wakin. Umma ta kalli Hajar tace "waike Hajara mai yasa kike da kunnen ?ashi ne iyee, ba nace ki dena shiga sabgar su ba", Hajar tace "Allah umma ban shiga harkar su ba, kawai fa ina zaune ina goge baki shine Maama tayi min WaWe a baya wai na zauna mata a kujera", ta kwashe rigarta tace "kinga wajen", Umma ta zabga wani uban salati ganin yatsu biyar cif raWa-raWa a bayan ?arta, wajen yayi Jajur tamkar ka taSa jini ya fito abinka da farar fata, Umma tace "wllh Allah ya isa ban yafe ba", Sabra da take shafa Vaseline a ?afafuwanta ta mi?e

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login