Showing 192001 words to 195000 words out of 252707 words

Chapter 65 - HAJAR COMPLETE NOVELS By Nafisa Yusuf Nagoda.doc

masa da kuka tace "wayyo Allahna na shiga uku..", jikinta har ya fara karkarwa don da gaske ta tsorata dashi, ya zaunar da ita gefen gado to calm her down ya du?a gabanta, ya kamo shaking hand dinta ya ri?e a tafukan nasa yace "look at me Baby wife", kaudar da kanta tayi ta?i ta kallesa duk da yacca ya ringa le?a fuskarta yana so suyi ido huWu, yace "Hajar..", ta Waure fuska samm ta?i ta kallesa, murmushin kan lips yayi yace "wai har ynxu fushi kike Baby wife, After tough punishment din da kike min, you left me yesterday all alone, i couldn't even sleep comfortably..", ita dai ba tace komai ba, yace "sorry bazan sake ba sai kin gama healing Baby girl, i promise...", fashewa tayi da kuka sosai, wani irin sai tayi healing kuma, shi da zaice ya dena gaba Waya sai yace sai tayi wani healing, ta fara ?o?arin fincike hannunta amma ya?i sakinta, murmushi mai sauti yayi don ya gane kukan na mene, yasa palm dinsa ya share mata hawayen yace "i promise you this Baby wife", ledar da ya shigo da ita ya dauka ya dora mata kan laps, ta ringa kallon ledar bbu ko ?iftawa, yace "Open it", a hankali ta ciro kwalin tsaleliyar wayar daga cikin leda, tin daga kwalin ma kasan wayar me tsada ce, yace "you like it...?", ta gyaWa kai a hankali sai kuma ta Wago ta Wan kallesa, saukar da kanta tayi tace "Thank you.." ta Wanyi jimm kafin tace "Allah ya saka da Alkhairy", ya ringa kallonta yana jin wani abu mara misaltuwa na figarsa, zamm yarinya nan ta juye irin yacca yake mafarkin matarsa ta kasance, ba tin yau ya fara lura da hakan ba, ta Wago kanta taga har lokacin kallonta yake, suna haWa ido ta saukar da kanta, ya kamo hannunta yayi pecking for almost 10secs, a hankali ya ringa murza hannun nata yace "you need anything...?", da sauri ta gyaWa kai, yace "tell me what is it..?", kanta a ?asa tace "ina so naje gidanmu dan Allah", yayi ajiyar zuciya yace "Is that what you like..?", ta gyaWa kai, yace "Ohk then insha Allah on Saturday sai nayi dropping dinki kiga Umma ko..?", ta Waga kai ta kallesa, ya sakar mata murmushin da tayi nadamar Wagowa jin wani abu ya cakar mata zuciya, yace "yeah... Umma da ake kira daga anji wuya mna", turo baki tayi, ya Wauke kwalin wayar daga laps dinta ya mi?e tsaye sai kuma ya ri?e hannunta ya Wagota, rumgumeta yayi yana sauke ajiyar zuciya yace "missed you soo much yesterday..", a tare suka lumshe ido, ta kwantar da kanta sosai a ?irjinsa. Sosai Nurain yayi keeping promise dinsa don bai sake taSata ba, amma kuma bai sake barin sun raba shimfiWa ba don baya ma iya bacci sai yayi Cuddling abarsa, itama ?ar farkar tafi jin daWin bacci a jikinsa, kamar yadda ta saba a da yanzu ma haka take zata dafa abinci ta ajiye masa nasa a warmers, sai dai yanxu ba da kansa yake zubawa ba sai ya kirata ta zuba masa, Abu Waya ne yake sukar zuciyarta daga ta tuna cewa favor ake mata, wnn abu sosai ya tsaya mata a rai, ranar Saturday kamar zata zuba ruwa a ?asa tasha don murna yau zata je gida, kafin ?arfe goma ta gama duk wani aiki da za tayi, tana komawa Wakinta ta faWa bathroom ta fesa wanka, kayan da bata taSa sakawa ba ta saka cikin na fitar bikin Noor da aka Winka mata, ta saka ?aramin hijab dinta wanda yake tsaya mata a guiwa da kuma Charger din sabuwar wayarta a ?aramar hand bag da ta fitar, sosai tayi kyau kamar a saceta, ta kalli door jin an buWe, bai shigo ba ya tsaya daga waje ya waro ido yace "Hey ina zaki da sassafen nan", ta marairaice murya tace "yau ne fa zanje gida", yace "Ohk Okay... Amma dai ba ynxu ba", ta langwaSar da kai tace "toh Ni yaushe zan tafi ?arfe goma fa ya wuce", Nurain yayi slight smirk yace "where is my breakfast... bring it to my room". haka nan Hajar ta shiga kitchen ta hada masa breakfast sharp sharp ta kai masa Sangarensa, ita da ta shirya tin goma da wani abun amma basu bar gidan ba sai sha biyu, Alla Alla take taga sun shiga unguwarsu don yau ma sai taga kamar gudun da yake bai wadaceta ba, Saida ya tsaya wani super market yayi shopping snn suka cigaba da tafiya, wani sanyi ne ya ratsa Hajar lokacin da yayi parking a daidai lungun gidansu, da sauri ta fara ?o?arin buWe motar sai ta jita a kullu, ta juya ta kallesa ba tace komai ba, ya Wauki envelope din daya ajiye kan dashboard ya mi?a mata, ta girgiza kai tace "Akwai tin wnda ka bani ranar nan", bai saurareta ba ya janyo jakarta ya zuge zip ya saka mata ba tare da ya lura da abinda ke cikin jakar ba, yace "idan na dawo zan shigo na gaida Umma", ta gyaWa kai a hankali, da haka ya buWe motar ya sauka, itama sauka tayi taga ya buWe back seat ya fara ciro shopping bags, yara uku ya biya yace su Waukar mata kayan, Hajar ta saki baki tana kallonsa don ba tayi zaton gidansu za a kai ba, saida Hajar ta Sacewa ganinsa snn ya koma mota yabar unguwar. Nabilah dake bakin rariya tana wanke wanke ta dena abinda take tabi yaran da suka shigo da kaya da kallo, Maama da ta fito daga bayi knn itama kallon yaran tayi baki a sake, Umma na zuba ?ullu cikin gwangwanaye Sabrah na shafa mata manja suma suka dubi yaran, duk cikinsu aka rasa wnda zai yi mgana, walking gently Hajar ta shigo tare yin sallama cikin murya mai sanyi, Umma dai tini ta Wau muryar ?arta ta, Sabrah ta micincina ido lokaci guda ta fasa ?ara tace "Addah.." sai kuma ta tashi da gudu taje ta rumgume Hajar, wani kukan farin ciki ne ya tahowa Hajar ta rumgume little sister dinta, Maama ta saki butar hannunta Nabilah kuma ta saki kwanon da take wankewa don sai ynxu suka gane Hajar, da farko sun sha wata balarabiyar ce tayi shigar hausawa, Maama ta dafe ?irji murya a sama tace "wai Hajara ce", Hajar ko kallon inda take ba tayi ba ta wuce wajen Ummanta ta du?a ta rungumeta, sai kuma ta fara hawayen farin ciki tace "Umma.. Ummanmu", Umma tayi murmushi tace "Hajara", Hajar na Wago kai taga Sa'adatu da Maimuna sunyi cirko cirko a bakin ?ofa suna kallonta sai kace tsofaffin mayu sunji yunwa, Maimuna tayi wani ba?i fuska duk ?uraje sai wata uwar rama da tayi gayau ha?ora sun fito sai kace za tayi cixo, tini Umma ta rufe ?ullun alale taja ?arta sukay Waki, gani kake yuuu Maama da ?a?anta suka bi Hajar da idanu, Sabrah ce ta ringa kwaso ledojin ta shigar dasu Waki, Hajar was more than happy da taga Ummanta, Umma taji daWin ganin ?arta ta data canza matu?a, Hajar dai ta zama wata tauraruwa abar kallo a wajen Maama da ?a?anta, da ta fita yin alwala za tayi sallah har saida tayi tuntuSe tsabar kallo, ita kam ko bi ta kansu ma ba tayi ba don bbu wnda ta kula, da yamma Baba ya shigo gida, Hajar na jin muryarsa ta ji wani mugun dadi, saida ya shiga Wakinsa snn ta tashi ta fita ta tsaya bakin labule tayi sallama, da sauri Baba ya juya ya kalli labulen don ya gane muryar favorite din ?ar tasa, har ?asa Hajar ta du?a ta gaida mahaifinta wnda ya amsa mata gami ta saka mata albarka bayan ya dafa kanta, farin cikin da Hajar tayi a ranar bazai misaltu ba don rabonta da yin farin ciki kamar na yau har ta manta, bayan sallar magrib ne kiran Nurain ya shigo wayarta, dman contact biyu ne a wayar daga tasa wacca ma ko saving ba tayi ba sai na Umma, ita throughout the day ma bata bi takan wayar ba tana wajen Sabrah sai game take, basu wani jima suna wayar ba kawai ce mata yayi yana kan hanya zaizo ya Wauketa, tace masa toh Allah ya kawosa lfy, after 15mins kam ya sake kira yace mata yaxo yana ?ofar gida, Hajar tayi wani murmushin gefen baki sai kuma ta saka veil dinta ta fita, bata wani jima ba ta dawo, Hajar ta du?a gaban Umma wacca take zaune kan darduma tana jan carbi tace "Umma yace wai zaku gaisa", daga bakin ?ofar Wakin Umma Hajar ta shimfiWa darduma guda biyu, gashi kuma anyi sa'a yau an kyallaro wutar Nepa, Hajar ta fita soro bayan ta gama shimfiWa darduman, tare suka shigo dashi ya zauna kan Waya daga cikin darduman, Umma ta fito suka gaisa kansa a ?asa, da haka ya tashi ya nufi soro, Maama dai wuyanta kamar zai karye sbd le?e daga Waki, lokaci guda ta koma gefen gado ta zauna sai kuma ta fashe da kukan ba?in ciki. Hajar ta gyara yafen mayafinta tayi hanyar soro, ta tsaya gami da tattaro courage don abinda za tayi sai da courage, ta ajiye numfashi a hankali, walking gently ta ?arasa inda yake kanta a ?asa, har ta isa kusa dashi kallonta yake, dukkansu shiru sukay bbu wnda yace komai, shi yayi breaking silence din da faWin "shall we..?", ta jingina da bango speaking calmly tace "Thank you", ya tattare thick eyebrows dinsa yace "for what..?", ta kallesa a karo na farko tace "for everything... from the beginning till now that is the end", ya gyara tsayuwarsa yana kallonta da kyau, tace "A watanni huWu da muka zauna tare nasan cewa na maka laifi dan Allah ka yafemin, i know i wronged you many times please forgive me.. however it seems i won't be able to do any of that now, bxn sake zama burden a kanka ba, ngode da favor din da kayimin na good 4months, nsan cewa Babana yamin aure amma ba auren Alfarma ba", Nurain ya tsuke piercing eyes dinsa yace "Hajar", ta haWiyi wata ball da ta tsaya mata a throat tace "yess, kace zaka nunamin am your wife and you did that, still dai it won't change the fact that you are doing me a favor", kallonta yake bbu ko ?iftawa, tace "ban san me yasa kake min favor ba ko don sbd ni ba choice dinka bace ko kuma sbd background dina ne i don't know, ngd da ka dawo dani inda ba favor ake min ba...", ta Wan ja da baya ganin zai ri?o hannunta, ya ajiye numfashi yace "what are you saying Baby wife...?", da kyar tace "Nurain let me go, i will also let you go, from now on we won't own each other anything", tana gama faWin haka ta juya ta shiga gida.....
'?
=؛? HAJAR =؛?

{79..}
A tsakar gida Hajar ta tsaya tana jin wata ball ta tsaya mata a throat, har lokacin akwai ragowar pure scent dinsa da ya bari, lokaci guda idonta ya ciko da ruwa, after a while ta juya ta kalli ?ofar soro sai kuma ta saukar da kanta ta shiga Wakin Umma, wayarta ta amsa a hannun Sabrah ta dannata a Airplane mode ta mayar mata ta cigaba da game dinta, ta cire veil dinta ta koma gefen gado ta zauna, Umma ta kalleta tace "ya kuma naga kin zauna karfa ki barsa a tsaye yana jira", Hajar ta kwakwalo murm???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ushi tace "Laaa ai ya tafi Umma", da mamaki Umma ta dubeta tace "ya tafi kuma...?", Hajar ta gyaWa kai tace "Eh... ni anan zan kwana", Umma ta haWe gira tace "bana son sakarci wane irin anan zaki kwana, tin tini baki zo da shirin kwanan ba saida kika zo nan za wani kice a nan zaki kwana, toh maza tashi ki bi mijinta tin kafin ma ya tafi..", Hajar ta marairaice tace "Umma shi yace fa na kwana wllh... kinga daga nan ma Airport zai wuce wani aiki ne ya taso masa, shine yaxo ya gaya min snn ya tambayi ra'ayina yace ya mayar dani gida ko kuma zan zauna a nan, shine nace masa a nan zan zauna, Umma yaushe rabona da ganin ku wllh nayi missing dinku over..", da kyar ta ?arashe don muryarta har ta fara rawa kar a rafko jirginta, Umma tayi ajiyar zuciya tace "Amma baki taho da komai wnda zaki bu?ata na kwana ba", Hajar tace "ba komai Umma, i will manage...", Umma bata sake cewa komai ba, Hajar ta tashi ta buWe wardrobe inda take ajiye kayanta kafin aure taga kayan Sabrah ne aciki, Hajar tace "Umma an bayar da kayan dana bari ne...?", Umma tace "A'a duba ?asa zaki gansu..", Hajar ta dur?usa tana duba ?asan wardrobe din taga kayanta wajen set 7 da ta bari, sosai taji daWi na ganin kayan, tini Hajar ta cire kayan jikinta ta linkesu ta Wauki wani material mai laushi cikin kayan ta saka, wajen ?arfe tara Hajar ta jiyo muryar Mu'azzam a tsakar gida suna mgana da Umma, tashi tayi ta fita tsakar gidan ta tsaya daga bakin ?ofa tace "Yayana...", Mu'azzam ya juya ya kalleta sai kuma ya tsuke ido yace "Wnn kuma daga ina..?", Hajar ta waro ido tace "Yaya ni din ce baka gane ba..?", yace "Eh kwarai..?", Hajar ta turo baki tace "knn ma ba kayi missing dina ba Yaya..", yace "Toh na sanki ne", Umma tayi murmushi tace "shiga ki Wakko masa kwanon abincinsa wataqila ya tuna wace ce ke", Hajar ta shiga Waki ta Wauko warmer din abincin nasa ta kai masa, ya amsa yace "toh yawwa ngd yar ?anwata..", Hajar tayi murmushi tace "daman nasan tsokanata kake..", yace "Toh ykk..?", tace "lfy lou Yaya", yace "Toh masha Allah haka ake so" da haka ya shiga Wakinsu. Washe gari wajen ?arfe bakwai Hajar ta fita tsakar gida, tinda tayi sallar asuba ta kasa komawa bacci shine da taga Umma ta fita tsakar gida itama ta mi?e tabi bayanta, tasan aikace aikace za tayi don haka ita dai bazata kwanta ta bar Uwarta na aiki ba, tini Hajar ta kama aikin da Umma za tayi, ta share tsakar gida snn ta haWa kwanuka tayi wanke wanke, Charcoal ta hura ma wuta ta dora ruwan shayi, yana tafasa ta juye a flask ta koma Waki ta tarar da Umma na tsince wake, zama tayi tana tayata tsintar waken, Sabrah na tashi Hajar ta ciro kuWi a jakarta ta bata tace ta siyo musu bread da kwai, murna a gun Sabrah ba'a cewa komai ta tafi siyowa, Hajar na zaune kan kujera gaban Mangal tana soya kwan da Sabrah ta kawo, Maimuna ta fito daga Wakin Maama tayi zugum tana kallon wainar kwan yawunta na tsinkewa, cikin bacci taji ?amshin kwan ai kam a duniya taji shi kawai take son ci, Maama ta fito daga Wakin itama da Waurin ?irji, wani irin yamutsa fuska tayi ta kalli Hajar sai kuma ta zubawa Maimuna wani mugun ran?washi ta ?unduma mata ashar tace "Shegiya wuce Waki kona Sarar dake, yau kika fara cin wainar kwai da zaki fito ki tsira mata idanu sai kace tsohuwar mayya, da wata ?onanniyar fuskarki", Maimuna ta juya ta shige Waki da sauri tana sosa inda Maama ta rankwasheta, babu ranar da rana zata fito ta faWi Maama bata rankwasheta ko kuma mintsili ba, wataran har marinta take ko kuma ta fasa mata baki, Maama ta ja wani dogon tsaki tamkar tsohuwar tsaka tana hura hanci tace "ko wa za'a nunawa wata shegiya wainar kwai" ta shige Wakinta tana baza zani, Hajar na gama suyar kwan ta tashi ta shiga ciki, Shayi mai kauri ta haWa musu da kayan shayin data zo dasu jiya. Da yamma Maama na tsaye a soro sun keSe da Balaraba da tazo, Balaraba tace "ke ni wata fa na gani kamar balarabiya a ciki", Maama ta taSe baki tace "hmm ba wata balarabiya wnn shegiyar yarinyar ce yar wajen FaWima..", Balaraba tace "wai Hajara ce yar kishiyarki..?", Maama tace "Uhmm itace wllh tllh... nima da tazo jiya ban ganeta ba", Balaraba tace "jar uba amma dai ba'a ?asar nan suke da zama ba ko..?", Maama ta taSe baki tace "Wllh a ?asar nan suke anan garin ma kuwa", Balaraba tace "ChabWi jam ai ?afarta na gani kamar bata taka ?asa wata irin fara ?al ?al ?al sai kace tumatir", Maama tace "gidanta fa sama da ?asa tayal ne, ga lantarki ta ko ina kamar zata fasa fitilu ba dole ki ganta kamar daga ?asar waje ba, yoh gidan nata ma kika shiga ydda kika san a ?asar wajen", Balaraba ta gyaWa kai tace "Wnn dama malamin makarantar ta aura wllh tllh..", Maama ta sauke ajiyar zuciya tace "Ni hankalina ma duk ya tashi tsaye cur wllh, so nake na haWa kuWin nan muje a Sarar da cikin jikin Maimuna kona samu nayi bacci da munshari, snn kuma zan koma wajen malamin nan na tsamiya da ?udi masu kauri don so nake yayi min aiki mai kyau, wnn shegiyar yarinyar a kaWota daga gidan mijin sai a manna Maimuna a wajenta, ni dai ynxu burina a fige cikin Maimuna kar ya bayyana na shiga uku", Balaraba tace "Gsky dai kiyi da jiki ?awata tin kafin lokaci ya ?ure miki, kamata yayi ma tin ynxu a cire cikin don ya haura wata Waya, snn kuma baki da labarin Malamin tsamiya ya haukace watanni biyu da suka wuce..", Maama ta dafe ?irji tace "na shiga uku ynxu wa zai min aikin kaWo wnn yarinyar daga gidan mijin..?", Balaraba tace "Oho can ta matse miki a matsematsin matsalarki, ina ruwana duk inda zaki ki nemo malami sai kije ki nemo, nida ke anyi ta yanke anyi ta gille indai akan harkar malami ce, wancan karon ma haka kika wula?antani kika tijartani kika yagani sbd kince aikin da akay miki bai ci ba, ynxu ni ba ruwana dake akan wnn lamarin wllh" ta ?arashe da jan guntun tsaki, Maama tace "Toh shknn... ynxu dai bazaki temaka min ba Balaraba, kina gani


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login