Showing 186001 words to 189000 words out of 252707 words

Chapter 63 - HAJAR COMPLETE NOVELS By Nafisa Yusuf Nagoda.doc

hair dinta, few minutes kam ta koma bccinta deeply in his arms. Da Asuba Hajar ta farka ta buWe idonta a hankali, ta ringa bin room din da bbu wani haske sosai da kallo, sai kuma ta juya ta kalli both sides dinta taga ita kaWai ce a makeken gadon, da kuzarinta ta yun?ura ta mi?e zaune gami da zuro ?afafuwanta ?asa, tana taka ?afarta a ?asa taji wata azaba data shallake tunaninta wccca ta ratsa har brain dinta, ta fasa ?ara a gigice sai kuma ta tafi luuu ta faWa kan gadon da baya, ji tayi kamar ana mata ruwan allurai a laps dinta, lokaci guda brain dinta tayi booting on hawaye suka fara sakko mata, tafi minti biyar a kwance kafin zugin da jikinta yake mata ya ragu still dai bata dena hawaye ba, tana ji aka buWe ?ofa aka shigo amma bata motsa ba, Nurain ya ?arasa shigowa Wakin yana kallon position dinta, a yacca take kwance gefen gadon yasan cewa ta farka ne, yana isa kusa da ita ya tabbatar sbd hawayen da ya gani kwance cheeks dinta, ya du?a ya kalli lumsassun idanunta da tinda taji shigowarsa ta rufe yace "Hajar", haWe fuska tayi gami da turo baki sai kuma ta kawar da kanta, murmushi yayi cause yasan fushi take kuma baiga laifinta ba don tayi fishi dashi, ya rage murya yace "let me take care of you baby girl" da haka ya fara tattare hannun button down shirt da ya saka da zai fita mosque sai kuma ya nufi bathroom, ruwan zafi ya tara a tub ya sirkasa kamar na daren jiya. This time around Hajar ji tayi kamar a ruwan jajjagaggen tattasai ya sakata, though ba taji azaba kamar na daren jiya ba amma dai ta WanWana shima, saida ya tabbatar ta gasu snn ya fito ya barta a bathroom din don tayi alwala, walking slowly Hajar ta fito daga bathroom da rigarsa dake jikinta wcca ta tsaya mata a rabin cinya, yana zaune tsakiyar gado yana operating laptop, suna haWa ido tayi saurin janye nata zuciyarta ta buga da ?arfi, ji take kamar ta nutse a wajen, bai Wauke idonsa daga kallonta ba yana lura da yanayin tafiyarta har ta ?araso cikin Wakin, hijab dinta ta Wauka ta saka without looking at him for the second time ta kalli qiblah, yana ganin ta kabbara sallah ya tashi ya nufi door, after 15mins ya dawo ya tarar har ta idar da sallar tana zaune kan darduma, inda take ya nufa ya du?a ya ajiye mug din hot chocolate da ya shigo dashi, da sauri ta haWe kanta da guiwa don bazata iya haWa ido dashi ba ga kuma azabar tsoronsa da ya cikata, ya kamo hannunta da taushin murya yace "yau ma ba gaisuwa...?", sai kace an ?unduma mata zagi haka ta fashe masa da kuka bil haqqi, ya waro ido yace "Laa me aka miki..?", ita dai ta?i mgana kawai kuka take kamar an aikota, ganin har ta fara jan shesshe?a yace "stop crying and tell me what happened... ko masquerade din ya sake zuwa ne..?", mganar ma bata fita sosai sbd muryarta ta dashe tace "Ni gidanmu zan tafi... i don't like it here, i want to go home please", yayi blushing don shi da tayi mgana ma daWi yaji yace "where are you going from your husband's house Silly girl..?", a hankali tace "i don't have one..", ?o?arin Wago fuskarta yayi ya kalli cikin idonta amma ta?i Wagowa, ya jingina kansa a nata gami da mgana in a whisper yace "you don't have one After last night", turo baki tayi ba tace komai ba, yace "yesterday's night was so amazing, super sweet, i really enjoyed it.. i hope today's night will be more sweeter", yana gama fadin haka ya janye kansa a nata sai kuma ya fara ?o?arin Wago kanta, firr ta?i yarda don har wani shivering take, da kyar yayi nasarar ri?e haSarta tana jin haka ta faWa ?irjinsa snn ta rufe fuskar a nan, tini ya sauke ajiyar zuciyar da bai shirya mata ba, gaba Waya sensory nerves dinsa saida suka kai electric shock brain dinsa, mug din hot chocolate din dake gefensu ya matsar sai kuma ya dafe bayanta yana daWa shigar da ita jikinsa sosai, tayi lamo a jikinsa ita dai she don't care indai za tayi avoiding eye contact dinsa, patting bayanta yke with one hand yace "Thank you for yesterday's night... Sorry for the pain..", ita dai ta lafe a jikinsa sai kace anan aka halicceta perceiving his pure scent, after 5mins yace "baby wife here is your free breakfast" da haka ya zameta a jikinsa, sam bata bari sun haWa ido ba, mug din chocolate din ya dauka ya kamo hannunta ya dam?a mata, ya ajiye numfashi ya tashi ya nufi door ya buWe ya fita palour, kan sofa ya zauna yayi resting yana sauke ajiyar zuciya, so yake ya bata hutu don ?arama ce baya so ya sake taSata sai tayi healing, iya hugging dinta da yayi ynxu har lissafinsa ya fara kwancewa shiyasa ya bata space snn shima yayi calming kansa down, sai after 1hour ya koma Wakin, ya tarar ta sha rabin chocolate din ga ragowar nan ta ajiye, ta koma baccinta nan kan carpet, kan gado ya mayar da ita ya rufa mata duvet sai kuma taSa goshinta to feel her body temp, yeah temp dinta ya Wanyi high amma ba sosai ba dman dole sai hakan ta faru.

&Maama ta saki baki har miyau na shirin zuba tana kallon Maimuna da ta shigo Waki tana yamutsa fuska tace "wai Aman kika sake yi..?", Maimuna da tayi wani lakwam ta faWa kan gado tayi rub da ciki tace "Eh", Maama tace "gsky ba lfy.. ko dai wnn cutar da ake ta amai da gudawa ce ta kamaki", Maimuna ta girgiza kai tace "Amai kawai nke fa..", Maama tace "na kawo miki kunun tsamiyar za ki sha..?", Maimuna ta girgiza kai tace "A'a na ?oshi...", Maama tace "wane irin kin ?oshi iyeeh, yau tinda garin Allah ya waye ubanki kika sakawa cikinki salon dai cutar ta miki muguwar illa", Maimuna da take mgana tana yamutsa fuska tace "zan sha anjima..", Maama tace "Allah ya kaimu anjiman" ta tashi tana baza zani ta fita, wajen ?arfe sha biyu Maimuna na farkawa daga bacci Maama ta ciko kofi da kunu ta kawo mata, ai Maimuna na yiwa kunu kurSa Waya ta toshe baki sai kuma ta zura da gudu ta fita waje, nan bakin rariya ta dur?ushe ta ringa kakarin amai, Umma tayi sauri ta janye robar gwangwanayenta da take wankewa, Nabilah tayi kasa?e da tsintsiya a hannu tana kallon Maimuna da har lokacin take kakarin amai, Nabilah ta ajiye tsintsiyar ta zuba ruwa a buta ta ajiye gefen Maimuna sai kuma ta koma ta cigaba da tattare tsakar gida, Maimuna ta kuskure bakinta ta tashi sai kace wcca ta shekara tana jinya ta shiga Waki, Maama ta tarar ta sauya kayan jikinta tana shirin saka hijab, Maama tace "kar ma ki kwanta saka mayafinta na kaiki Chemist", Maimuna ba tayi musu ba don itama lfyr take nema ta canza kaya, Maama tace "Akwai kuWi a hannunki..?", Maimuna ta girgiza kai, Maama tace "Au tsimilmilar ma har kanki za ki yiwa, toh ki fito da kuWin da za'a siya miki mgana dan nidae Wari biyar ce kawai a wajena", Maimuna tace "wllh Allah ba nida ko kwandala", Maama tace "ina kuWin da Alhaj din naki yake baki..?", Maimuna tace "Ni yau sati biyar knn rabona dashi wllh, ko na kira wayarsa ma bata shiga", Maama ta ringa kallonta don ta lura gsky take gya mata ba tada kuWi, Maama tace "dena Waukar wayarki yayi...?", Maimuna tace "Eh dman yace min aiki ya masa yawa bxn ringa samunsa ba", Maama ta gyaWa kai tace "Au toh", tsakar gida suka fita Maama na kallon Nabilah tace "zan kai Maimuna chemist tana fama da masassara", Nabilah tace "toh sai kun dawo", Maama tace "yawwa" da haka ta nufi soro tana ri?e da Maimuna wcca take tafiya a hankali, suna isa chemist Maimuna ta zauna kan benjin dake cikin Chemist din, mai Chemist na gamawa da mutumin da suka tarar ya waiwaye su, ?an tambayoyi ya yiwa Maimuna ta ringa basa amsa, ya kalli Maama yace "A kaita asibiti su mata gwaje gwaje kawai", Maama tace "kai bazaka iya mata gwaje gwajen ba anan, masassara ce fa take damunta", yace "A'a aje dai asibiti, ni Strip kawai zan iya baku", Maama tace "meye kuma sitirif..?", Strip din ya Wakko yace "gashi", Maama ta amshi ledar Strip din tace "kai da zaka bani magani sai kuma ka mi?omin robar banza", mai Chemist ya amshi Strip dinsa yace kawai suje asibiti, Maama na sababi suka bar Chemist din tace su tafi wani, Chemist biyu suka je bayan wnn shima dai abinda ake ce musu knn, Maimuna kam har ta jigata ta dawo jan ?afa, jingina tayi da bango tace "Maama dan Allah mu tsaya gidan Balaraba na huta", Maama ta haWe fuska sai kuma ta saki fuskar bayan ta tuna har gida Balaraba tazo ta bata ha?uri, gidan Balaraba suka wuce wcca ta saukesu a tsakar gida, Maimuna ta sheme kan tabarma zuciyarta na wani irin hautsinawa, bayan Balaraba sun gaisa da Maama tace "lfy dai na ganku da ranar Allah..?", Maama tace "uhmm tinda kika ga haka ai ba lfy", nan ta gaya mata ai Maimuna ce ba ta jin daWi shine suka fito Chemist, Balaraba tace "Ayyah Allah ya bata lfy", a kasale Maimuna ta yun?ura tana toshe baki ta nufi gaban rariya, ba tayi aman ba ta dawo ta kwanta, Balaraba ta ringa kallonta kafin ta jinjina kai ta kalli Maama tace "Rabi kawai kuje asibitin", Maama tace "toh idan munje asibitin shekaruna zan lalo na basu, kuma da rana tsage tsage zamu tafi asibitin ma'aikatan lfy da basu da kirki ai sai su kaWomu..", Balaraba tace "inada kuWin da aka kawomin ajiya sai na ranta miki ai, ita lfy ai yar sarki ce gwara a nemeta", dubu biyar Balaraba ta rantawa Maama da wajewar nan da sati Waya zata biyata kuWinta, Maama tace "ba zai ma kai sati ba ko gobe sai na kawo miki kuWinki don ubanta na dawowa zan amso kuWin a wajensa, amma dai ynxu wani asibitin za mu nufa..?", Balaraba tace "nan nan ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ma asibitin gangare zasu dubata.. bari na raka ku", haka nan Balaraba ta raka su Maama can wani karamin asibitin gwamnati, kuma suna zuwa aka Webi jinin Maimuna za'a mata test din abinda ake zargi, Balaraba na zaune kan benci tare da Maimuna a inda suke jiran result, Maama ta tafi siyowa Maimuna ruwa don tace ?ishi ruwa take ji, wata Nurse ce ta fito da takardar result din test din ta kira sunan Maimuna, Balaraba tace "gata nan", Nurse din ta isa inda suke ta bawa Balaraba takardar tace "nasan dai ku manya ai kun san me yake damunta kawai dai kunxo nan ne dan ku tabbatar", Balaraba tace "me yake damunta..?", ba yabo ba fallasa Nurse din tace "Ciki ne da ita na tsahon sati uku... Allah ya raba lfy", Balaraba da ta gasgata zarginta ta saki fuska kamar ba komai tace "toh Alhmdllh mun gode likita", Nurse din bata daWe da tafiya ba sai ga Maama nan da ledar pure water biyu, Balaraba ta ringa kallonta har ta iso, Maama ta tashi Maimuna da bacci ya kwasheta don ko zuwan Nurse din bata sani ba ta bata ruwan tasha, duk Balaraba na kallonsu saida ta gama shan ruwan snn tace "mu tafi gida kawai", Maama tace "ai bamu gama ba", Balaraba ta nunawa Maama takardar tace "gashi nan sun rubuta mta magunguna muje gida kawai na miki bayani", haka dai suka sake runtuma suka wuce gidan Balaraba, Maama ta fixge hijab dinta snn ta tuge Wan kwalinta tana kallon Balaraba da idonta kamar zasu faWo, ?iris ya rage ta kurma ihu ta ?undumawa Balaraba wata mummunar ashariya tace "?arya kike billahillazi la'ilaha illa huwa", Balaraba ta wurga mata takarda tace "toh duba ki gani da idonki idan karya nake ?arki bata kwaye zani an Wirka mata ciki ba, dman shiyasa nace mu taho gida don nsan tsaf zaki tonawa kanki asiri a cikin jama'a", kafin kace me gumi ya ji?a Maama har yana Wiga, habawa ai da Maama ta wani zabura sai kace wcca aka kaWo daga dawanau tayi kan Maimuna ta ringa loda mata hannu tana fatali da ita, Balaraba ta ringa ?o?arin kwace Maimuna tana cewa "ki rufamin asiri kar kiyi kisan kai a gidana na shiga uku", ina saida Maama ta yiwa Maimuna lilis har ita kanta ta gaji da duka snn Balaraba tayi nasarar amsheta ta wurgata banWaki, mala mala Maimuna tayi a ?asan dauWaWWen banWakin don ba tada maraba da sumammiya, Maama ta Wora hannu bibbiyu a ka ta kurma wani uban ihu sai kuma tayi rimi tayi zaman ?an bori a ?asa ta fara tumami, wiwi ta ringa kuka irin na takaicin nan don ko hawaye bbu sai wata azaba da ma?ogoronta ke mata, Balaraba ta juyar da kai tana dariya ?asa ?asa don yacca Maama ta zaro harshe tana kuka sai kace Akuya mai na?uda ba ?aramin dariya ta bata ba, saida Balaraba ta gama dariyarta wcca Maama bata lura ba snn ta matsa kusa da ita tace "?awata ki bani hankalinki nan, mu tone ?asa mu rufe sirrin nan bbu wnda yaji bbu wnda ya gani kamar yacca muka saba".

&Hajar bata farka daga baccin da ta koma ba sai sha Waya da minti goma, a hankali ta mi?e zaune tana mamaki da ta ganta a gado, da kyar tayi shahada ta zuro ?afafuwanta ?asa amma kuma sai ta?i taka ?asa don tsoro take ji kar taji zafi, ta lallaSa ta mi?e tsaye sai kuma taga ba taji zafin ba, walking slowly ta nufi door ta murWa handle, wata ajiyar zuciya ta sauke jin ?ofar ta buWe, ai kam tini ta nufi ?ofar fita daga Sangaren tayi sliding ta fita, sai kace mai tafiya akan ?aya har ta isa room dinta, wani sanyi ne ya ratsa mata zuciya sai kace wcca ta shigo inuwa daga rana, ta mayar da ?ofar ta kulle ta jingina da ita, turo baki tayi don ?amshinsa kawai take ji duk da cewa ta baro room dinsa, lokaci guda ta kalli kanta taga shirt dinsa ce fa a jikinta, bathroom ta shiga ta cire rigar ta daura pink towel, wanka tayi da warm water ta fito, bata iya zama kan stool ba ta zauna gefen gado tayi rubbing lotion, ta ringa kallon inda box din kayanta suke taga basa nan, kamar da wasa ta bude wardrobe ai kam sai ga kayan a jere intact, she was very shocked haka dai ta fitar da wata gown mara nauyi da hula ta saka, lipbalm ta goga a pink lips dinta da sukay pink sosai, sama sama ta fesa perfumes masu sanyin ?amshi, gyara arrangement din kayan kan mirror din ta fara duk da cewa basu wani hargitse ba, door aka buWe ya shigo tare da yin sallama, ai ko da wasa bata kalli ?ofar ba, lips dinta suka motsa lokacin da ta amsa ciki ciki sai kuma ta haWe fuska, ya ?arasa shigowa ciki ya ajiye ledar hannunsa kan chest of drawers, tini ?amshinsa ya baza room din, kallonta yake bbu ko ?iftawa and he was so happy da ya ganta a hka, tinda ya shigo ta kasa cigaba da jera cosmetics din cause hannun nata ma rawa yake, gaban mirrorn ya ?arasa ya tsaya daff da bayanta har jikinsu na gogar na juna, a bazata ta Wago kanta sukay ido huWu ta cikin mirrorn, da sauri ta saukar da kanta tana jin kamar ta nutsu a wajen, zagaye flat tummy dinta yayi yana kallonta ta cikin mirror yace "how are you feeling now..?", ba tace uffan ba ta ringa kallon hannunsa daya ritsa cikinta, Wan girgizata yayi yace "uhmm ynxu kin dena jin pain din...?", a hankali ta gyaWa kai tana turo baki, yace "Good, i bought your breakfast.. eat alot kinji baby girl", nan ma kai ta gyaWa masa, lips dinsa ya kawo saitin kunnenta har tana jin breathing dinsa, ba shiri ta lumshe idonta tana jin kamar an kwara mata ruwan ?an?ara, yayi pecking cheek dinta lokaci guda ya saketa yace "Sai na dawo" da haka ya fita daga Wakin, after few seconds da fitarsa Hajar ta sulale ?asa ta ajiye numfashi. Shi kam direct downstairs ya sauka ya shiga motarsa ya bar gidan zuwa gidansu zaije wajen Abba da yake kiransa, with minimum speed yake jan motar time to time sai yayi blushing a haka har ya isa gida, yana shiga gida dman direct Sangaren Abbansa ya shiga, suna gama mgana da Abba ya fito da envelope a hannunsa ya wuce wajen Mami, a bedroom dinta ya sameta ya zauna kan carpet ya gaisheta, with care ta amsa masa kmar ba ita bace ya sha faWa a wajenta jiya ba, ita da Abba hka suke daga sunyi faWa toh a wajen suke barinsa basa sake tayar da zancen ko kuma su ringa canzawa mutum fuska, No idan abu ya wuce toh ya tafi knn a wajensu, tace "how is my daughter...?", Nurain ya shafa kansa yace "She is great", Mami tace "Masha Allah", sai kuma ta kalli envelope din hannunsa tace "where are you taking that..?", yace "house of assembly", ta gyaWa kai tace "Ohk baka je work ba..?", yace "yeah", Nurain beyi tunanin zai daWe a wajen da Abbansa ya aikesa ba, sai yamma li?is ya dawo gidansu in a hurry kawai zai bawa Abba abinda ya amso ya wuce gida, gaba Waya hnkalinsa yayi kan Hajar da ya bari a gida, sharp sharp ya fito daga Sangaren Abba har zai fita sai kuma ya juya ya shiga wajen Mami don mata sallama kafin ya tafi, ko zama ma beyi ba ya tsaya ta bayan kujerar da take zaune yace "Our Mami saida safe..", Mami ta juya ta kallesa tace "Ohh

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login