Showing 171001 words to 174000 words out of 252707 words

Chapter 58 - HAJAR COMPLETE NOVELS By Nafisa Yusuf Nagoda.doc

gidan. Mami tace a kai box din kayan Hajar zuwa room din data zauna lokacin da bata da lfy amma ina tini Noor tasa mai aiki ta kai box din Wakinta don tace anan zata sauka, Bayan sallahr magrib Nurain na zaune palourn Mami, Mami ta fito daga bedroom dinta tana kallonsa tace "sai yaushe zaka wuce Abujan ba flights din dare bane..?", yace "yeah ynxu zan wuce", Mami tace "Ohk kar dai kayi missing flight", yace "kafin time zan isa Airport insha Allah", Mami tace "ka tafi da warm sweater da Jacket don ynxu China wnn snow din ake musu", yace "Tom Our Mami", tace "ka ringa shafa mentholated cream kar sanyi ya kamaka Nurain kasan dai yadda mura yake maka", yace "Tom Mami". Hajar na zaune kan prayer mat bayan ta idar da sallahr magrib a room din Noor, Noor ta shigo tana kallon Hajar tace "kixo inji Yaya..", Hajar tace "tom" ta mi?e tabi bayan Noor suka fita main palour, Hajar ta ringa bin palourn da kallo don bata gansa ba, Noor tace "meet him outside", Noor na gama fadin haka ta wuce can room din da mai mata gyaran jiki ke jiranta, a hankali Hajar ta fara tafiya har ta fita balcony, Tinda ta fito bai Wauke idonsa akanta ba, yana zaune cikin motarsa ya bar door a buWe snn ma legs dinsa ma basa cikin motar kawai dai zama yayi a driver seat din, walking gently yaga ta nufi wajen motar, kallonta yake har ta ?araso bakin motar, ta tsaya daga jikin motar without saying anything, after the silent of about 1mins Nurain yayi ajiyar zuciya yace "you will be staying here for the meantime...", ta Wan kallesa da wutsiyar ido taga ita yake kallo, a hankali ta gyaWa kai, ya waro ido yace "ko saina buWe bakin za kiyi mgana", ta sunkuyar da kanta tana wasa da ?asan hijab tace "Tom", yace "Good... if you need anything don't hesitate to ask Mami", tace "Tom", envelope da ya ajiye kan dashboard ya Wauka ya fito daga motar, ya tsaya daf da ita leaning against her, tini Hajar ta sake mannewa da jikin motar perceiving his pure scent, hannunta ya kamo ya dam?a mata envelope din yace "if you need anything", sai a lokacin Hajar taji wani iri a zuciyarta tana so ta fahimci wani abu, bata fito daga duniyar tunani ba ya Wan janyota kamar zaiyi hugging dinta, ya sunkuyo a saitin kunnenta yace "be good Hajar", sosai mganarsa tayi hitting eardrum dinta tare da kai electric shock brain dinta, ba tasan lokacin da ta lumshe idonta ba tana jin breathing dinsa, After a while ya matsa daga kusa da ita yace "you can go", ko 1sec bata ?ara ba ta wuce ta bar wajen, Nurain yabi bayanta da kallo har ta shiga ciki, rubbing face dinsa yayi da palm snn ya shiga motar. Sosai Hajar taji daWin zaman gidan, sosai take comfortable bbu abinda ta nema ta rasa, yau kwananta na shida knn a gidan, shirye shiryen bikin Noor ake a gidan ka'in da Na'in, WaiWaikun ranaku ne Sakeena bata zuwa su fita tare da Mami, ita dai Hajar tana kallon ikon Allah taga ya masu kudi suke nasu bikin, ita dai tasan an Satar da kuWi wnda zata iya kiransu da mazaje. Da yamma Hajar ta gama cin abincin da ba taci da rana ba sai ynxu, da plate a hannunta ta fito zata kai kitchen, turus tayi ganin ba?i a palour, Anty Zulaihah ce sai Khausar wnda zuwansu knn, Sakeena dake zaune palourn tin bayan dawowarsu da Mami daga kasuwa ce tare dasu, Hajar ta ?arasa cikin palourn ta du?a ta gaida Anty Zulaihah da ladabi, Anty Zulaihah na kallonta da kyau tace "lfy lou alhmdllh" sai kuma ta dubi Sakeena tace "Matar Nurain ce ko...?", Sakeena ta gyaWa kai tace "Eh Anty", sai a lokacin Khausar dake danna waya ta dubi Hajar sai kuma ta Wauke kanta, though ta taSa ganinta sau Waya ranar da aka kawota amma kuma bata san haka take ba, Hajar ta mi?e ta wuce kitchen da plate din. Noor ta sauko daga upstairs, hugging juna sukay da Khausar, Noor ta gaida Anty din ta ta da ladabi, bayan sun gaisa Anty Zulaihah ta wuce part din Mami, Noor na kallon Khausar tace "banga box naki ba hajiyata..", Khausar ta mata nuni da jakar kayanta tace "gata can ai nazo knn", room din Noor suka wuce tare Khausar na gaya mata ydda suke tsarin cocktail party da friends dinsu, Noor ta zuge closet ta saka jakar Khausar ciki, Khausar tace "ki saka min a Waya side din mna nafi more aware and comfortable with it", Noor tace "Oh box din Hajar ne a wajen", Khausar tace "Ohk... wai waccar farar da ta shiga kitchen itace matar Ya Nurain..?", Noor tace "dman baki santa ba..?", Khausar tace "Nope kawai dai ban ganeta ba", a lokacin Hajar ta shigo Khausar ta bita da kallo, Noor tace "Ehmm Hajar meet my sisto Khausar..", Hajar tace "sannu ko", Khausar ta mi?e daga gefen gadon da ta zauna ta kalli Hajar tace "Hi" sai kuma ta nufi door tana cewa "zanje mu gaisa da Mami". after 10mins Khausar ta dawo, Hajar ganin suna firarsu wcca bata shafeta ba ta dubi Noor tace "zanje palour nayi kallo sai kin taho", Noor tace "Ohk". Da daddare Noor ta zubo musu abinci su uku, da farko Khausar cewa tayi baza taci ba sai kuma ta tashi ta fita sai gata ta dawo da plate ta Webi nata ta koma gefe tana ci, Noor ta bita da kallo tace "Au you like to eat alone", Khausar tace "yeah you know bana cin abinci sama da mutum biyu", Hajar ce ta tattara plate din da suka gama cin abinci ta fita dasu, tana dawowa ta shiga bathroom don yin wanka cause da wuri take so ta kwanta, Khausar tace "Noor amma the bed will not be enough", Noor tace "sai kace wasu elephants even 4 people can sleep on this bed comfortably", Khausar ba ta sake cewa komai ba ta haye gado bayan ta saka nities dinta, wani irin bararrajewa tayi ta kwashe rabi da quartern gadon, Hajar na fitowa wanka ta bude box dinta ta dauki kayan bcci ta saka, kallon position din da take kwanciya tayi taga Khausar tayi Wai Wai tana latsa waya, Noor tace "Khausar matsa zata kwanta ne fa", Khausar ta matsa kaWan, Noor ta tashi daga position dinta tace "Hajar zo ki kwanta anan", Hajar tace "A'a ku kwanta kawai" da haka ta buWe closet ta ciro wani blanket da ta gani tayi kwanciyarta kan carpet, babu yacca Noor ba tayi da ita ba akan ta tashi daga ?asa amma tace she is Okay, Khausar tace "Omo she said it's okay please let her be.. kin san wani yafi son ?asan", Noor dai ta Wan haWe gira ta koma ta zauna, ba ta son wnn acting din da Khausar take gsky, Khausar tace "The bride to be nifa banga Ya Nurain ba, Waxu ma da zanje gaida Mami na biya na gaidashi a room dinsa baya nan", speaking with a repartee Noor tace "ohh he is not around yana China", Khausar tace "Ohk when is he coming back...?", Noor tace "i don't think zai ?ara 1week bai dawo ba", Hajar dake kwance kan carpet duk tana jin conversation din nasu, ita sai ynxu ma tasan tafiya yayi ashe baya ?asar ma, shiyasa bata ganinsa knn. washe gari Hajar ita kaWai ce a gidan, da wuri Mami suka fita tare da Sakeena da alama dai so suke su gama shirye shirye kafin lokacin bikin ya shigo, Noor ma sun fita tare da Khausar ba dai tasan inda zasu ba, duk da Noor tace tazo suje tare amma ta?i sbd ydda Khausar ta nuna bata so a tafi da ita, ita kam daman ba son fitar take ba. Hajar ta shiga Sangaren Mami don yi mata sannu da zuwa kamar yadda ta saba, bayan ta musu sannu da zuwan Mami tace "why are you all alone at home baki bi su Noor ba..?", Hajar tace "Eh", Mami tace "Okay.. je ki kawo mna abinci", Hajar tace "tom" da haka ta tashi ta fita, Sakeena ta fito daga small room din Mami inda suke ajiye kayan da suka siyo, wayar Mami kare a kunnenta tace "You catched cold brother", from the other side Nurain da muryansa ta dashe yace "yeah", don yana isa China wani muku mukun sanyi ake, daga airport kafin ya isa masaukinsa anan yayi catching cold, sosai mura ya kamasa ya ri?e masa murya shiyasa bai kira kowa ba, though ya yiwa Mami message yace mata ya sauka lfy, sai ynxun ne da muryan nasa ya bude ya samu ya kira, Sakeena ta mi?awa Mami wayar tace "Nurain ne", Mami na jin muryansa ta haWe gira tace "ba kayi abinda nace ba ko..?", Nurain ya ja pointed nose dinsa don mganar ya fito sosai yace "No Mother wollah nayi abinda kika ce, tin a plane na saka Jacket dina, akwai sanyi ne sosai Mami", Mami tace "Ohk", suna gama wayar Mami ta katse kiran, saida Hajar ta kawowa Mami abincin da lemo da ruwa snn ta koma room din Noor, wayarta da ta ajiye kan mirror ce tayi haske, tana Waukan wayar taga 4 missed calls da number wcca ba ta ?asar nan ba, Hajar ta ringa kallon numbern kafin ta ajiye wayar ta shiga bathroom don yin alwala. Da daddare wajen ?arfe tara Hajar na dur?ushe gaban box dinta zata ciro kayan bacci da zata saka, Khausar na kwance kan bed tayi rub da ciki tana latsa waya, door aka bude Noor ta shigo ta mi?awa Hajar wayarta tace "Yaya ne", Hajar ta ringa kallon wayar bata amsa ba, Khausar ta taso ta amshe wayar a hannun Noor tace "bari dman za muyi mgana dashi" da haka ta kara wayar a kunnenta ta fita, Noor ta bita da kallo hakama Hajar, Noor ta juya ta fita itama, Hajar ta ?arasa ciro kayan baccinta ta saka, daga nan tayi kwanciyarta kan carpet ta rufe legs dinta da blanket, bata daWe da kwanciya ba Noor ta sake shigowa, a hankali Noor tayi tapping dinta tace "Hajar har kinyi bacci", Hajar ta buWe idonta sai kuma ta mi?e zaune, Noor ta mi?a mata wayarta tace "ga Yaya", Hajar na amsar wayar Noor ta tashi ta fita, a hankali ta kara wayar a kunnenta tayi shiru ba tace komai ba, after a while jin shiru ta ciro wayar tana kallon screen din taga seconds sai tafiya suke alamar dai bai katse kiran ba, turo baki tayi ta mayar kunne, ajiyar zuciya taji ya sauke sai kuma yace "Hajar", ji tayi muryansa ya canza amma still tasan shine, ta haWe kanta da guiwa da sanyin murya tace "ina yini"& &
'?

Please Masu neman complete din Hajar toh ku dena whalar da kanku don bbu complete ynxu nake rubutashi, snn kuma a wajena Ni Nafeesah Yusuf Nagoda (Feenerh feeche) kawai zaki samu book din don nawa ne mallakina.

=؛? HAJAR =؛?

{72..}
A hankali Hajar ta daga kanta jin an buWe door, ido huWu sukay da Khausar wacca ta shigo, Khausar ta haye gado ta cigaba da danna wayarta, Nurain yace "ina wayan dana ara miki ba kya picking call ko..?", Hajar ta girgiza kai kamar yana kallonta tace "A'a ban gani ba", yace "ohh All is well right..?", ta gyaWa kai ba tace komai ba, ai kam kamar yasan me tayi ya tsuke ido yace "ohh nodding head kikay ba zaki yi mgana ba, idan na dawo fa bxan buWesa ta sau?i ba, gwara ma kiyi mgana yarinya", Hajar ta kifa kanta a knees dinta tace "Ni fa bacci zanyi..", wani dogon tsaki Khausar taja ta tashi zaune ta jingina da allon gado don tana jiyo mganarsa sosai sbd the room was so silent, Hajar dai ko kallonta ba tayi ba waya na kare kunnenta, Nurain ya ja nose dinsa yace "hmm your lips are aching surely i must brush them when am back..", wani irin turo baki tayi tace "Allah kuwa Ni bacci zanyi", yayi slight smirk yace "nayi gluing eyes dinki ne", kawai dai latsa waya Khausar take amma all her mind yana kan Hajar ne, lokaci guda ta tashi daga kan gadon taje ta kashe fitila, sosai room din yayi duhu sai hasken wayar Khausar da take latsawa, Nurain yayi ajiyar zuciya yace "you know what Hajar..?", ba ta kai ga basa amsa ba Khausar ta kunna wa?a a wayarta ta ?ure volume, bayan song din data kunna har wani bi take tana Waga murya, hakan yasa Hajar ba tajin me yake cewa tinda muryansa ba sosai take fitowa ba, Hajar tace "saida safe" bata jira cewarsa ba ta katse kiran don tasan ko yayi mgana ba ji za tayi ba, snn kuma idan ba Wakin Noor ba taga inda zata iya waya dashi a gidan ba, Hajar ta ajiye wayar a gefenta ta sauke ajiyar zuciya sai kuma ta kwanta, Khausar ta rage volume din wayar bayan ta lura da kwanciyar Hajar, har bacci ya Wauke Hajar mganarsa ta ?arshe take tunawa ko me zai gaya mata. washe gari tinda Khausar ta tashi take wani cin magani, sai wani murtuke fuska take da ?ananun tsaki, har saida Noor ta tmbyeta lfy lokacin da ta kirata yin breakfast, fuska a Waure Khausar tace "nothing am just moody today", Noor tace "Ohk ki fito muyi breakfast", Khausar tace "tom am coming", Noor ta juya ta fita, Khausar na fita palour ta tarar da Noor da Hajar zaune kan carpet ga Variety na breakfast a gabansu, Khausar ta zauna ta haWa shaya a mug, irish da kwai ta Weba ta matsa ketchup snn ta fara ci, Noor tace "ga croissant fa", Khausar na shan shayinta ta girgiza kai, Noor tace "akwai cheese sosai fa", Khausar tace "am not eating sister", Noor bata sake cewa komai ba, daman Hajar tinda Khausar ta fito bata ko kalli position dinta ba, ta lura yau WaWWaga kan nata yafi na jiya, Hajar na gama yin breakfast dinta ta kai plate da cup din kitchen, da ta fito bata zauna a palour ba tayi wucewarta Waki, bai fi 20mins da zamanta ba Khausar ta shigo, ta zauna gefen gado ta Wauki wayarta dake kan bedside tayi dialing number ta kara a kunne, tsaki tayi ta wurgar da wayar kan bed, Hajar ta tashi ta fita ba tare da ta kalli inda take ba, through out the day hka Hajar ta ringa avoiding Khausar, mgnar da ya gaya mata kafin ya tafi ce ta ringa mata yawo a brain wato be good Hajar, idan ta tina saita share lamarin Khausar da take ?o?arin fusata ta. wajen ?arfe biyu Hajar taje kiran da Sakeena ke mata, mai aikin gidan ce tazo kiran ta, Hajar ta shiga room din Sakeena na gidan da sallama, Sakeena dake zaune kan carpet da kaya baja baja zagaye da ita ta amsa, Hajar ta ?arasa ciki ta zauna, wata leda Sakeena ta bata tace "Outfits dinki ne na biki, nasan size din zasu miki tailor Salmah ce ta miki tinda tasan size dinki amma dai ki gwada", Hajar tace "Toh ngd sosai", Sakeena tace "you're welcome dear", Hajar ta koma room din Noor don ta ajiye kayan, Khausar kawai ta tarar Noor ta tafi Wakin da ake mata gyaran jiki, Hajar ta buWe closet ta sauke box dinta zata jera kayan aciki, sosai laces din sukay mata kyau gasu kuma colors din da za suyi fitting dinta sosai, duk kayan da ta zaro saita Waga sai kuma ta mayar ta linke ta saka a box, by doing that har ta gane zasu mata ko bata gwada ba, Khausar tayi pausing Movie da take kallo jikin Laptop jin wayarta na ringing, tini tayi picking call din ta kara a kunne tace "Ya Nurain i have been calling you since morning..", sai kuma ta karyar da kai tace "Okay... hope you are not busy now..", tinda Khausar ta ambaci Ya Nurain Hajar ta dena abinda take na almost 10sec kafin ta cigaba, a handsfree Khausar ta saka wayar don ba ta jinsa sosai wnda hakan yasa Hajar ta tsinkayo muryansa ainun, taji yace "what were you saying yesterday lil sis..?", tini Hajar ta Wauke hankalinta daga kansu ta cigaba da abinda take, ?asa ?asa taji sautin dariyarsa sbd tazarar dake tsakaninsu da Khausar, Hajar na Wago kanta taga Khausar na murmushi sai kuma ta kwanta tace "Am serious fa Yaya", da sauri Hajar ta tutsa ragowar kayan ta dannasu cikin box din, ta mayar da box din cikin closet da haka ta nufi door ta fita kuma har lokacin basu gama wayar ba, Hajar har zata zauna palour sai kuma ta fasa ta tafi wajen Sakeena, ta gaya mata cewa ta gwada kayan kuma sun mata, Sakeena tace "where is Khausar...?", Hajar tace "tana can Waki", Sakeena tace "call her for me", har Hajar ta tashi kirantan Sakeena tace ta barshi, a nan Hajar ta cigaba da zamanta har ta taya Sakeena shirya wasu kaya da aka kawo a cikin Souvenirs box, wajen ?arfe huWu Mami ta shigo don daman bata nan sun fita da Anty Zulaihah, sannu da zuwa Sakeena ta mata Hajar ma haka, Mami na kallon Sakeena tace "har kin gama da wnn shima...?", Sakeena tace "yeah.. ai nafi so na gama komai ydda zan zama free a lokacin biki", Mami tace "su little Abba na wajen grandma dinsu ko...?", Sakeena tace "Eh", Mami tace "Alright please a ware 100 pieces daban", Sakeena tace "Sure", da haka Mami ta juya ta fita, Sakeena ta kalli Hajar tace "je kici Abinci kiyi sallah sai mu ?arasa", Hajar tace "Toh" da haka ta tashi ta fita. the same time daya kira jiya ta wayar Noor yau ma haka ya kira saidai ta wayar da ya bata, shi asuba ce a can nan kuma ?arfe tara na dare, Hajar ta ciro wayar da ta ajiye cikin handbag dinta tin safe jin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login