Showing 63001 words to 66000 words out of 252707 words

Chapter 22 - HAJAR COMPLETE NOVELS By Nafisa Yusuf Nagoda.doc

sha biyar, ko wani uzirin ne ya ri?esu..", Bappa ya gyaWa kai yace "ai ba jiran bane damuwa, jama'ar da suka taru kuma ba a rasa masu wani appointment din bayan wnn ba", Naseer yace "insha Allah yanxu zasu ?araso". Bappa yace "toh Allah yasa kar abar mutane a tsaye", kai har minti sha biyar da Baba ya ambata babu alamar dangin ango, tuni mutane suka fara canza fuska harda masu cewa su sauri suke, a yanxu kam hankalin Baba ya kai ma?ura wajen tashi, Mu'azzam kam tinda ya koma gefe yake kiran lambar Nura. Naseer yanata duba agogon wayarsa, Bappa ya sharce zufar da ta wanke masa fuska sbd zafi, soron a cike yake da mutane gashi kuma ba a aiwatar da abinda ya tara jama'ar ba. kai abu fa ya fara wuce jira domin har an fara sidetalks, Huzaifa ne ya fito daga cikin gida ya dur?usa gaban Bappa yace "ko muje gidan nasu a jiyo lfy tinda nan gangare ne bamu da nisa", Bappa ya karkaWa Wan yatsansa yace "samm, ba zamu zubarwa da kanmu mutunci ba, a cigaba da jiran nasu, ai idan matsala ce waya zasu bugo", Huzaifa ya tashi ya koma kusa da Mu'azzam yana tambayarsa ko ya samu lambar. Daga ta cikin gida kam gidan biki ya Wau harami, Umma sai warkajaminta take cikin riga da zani na atamfa mai shegen kyau, ta kashe Waurinta ture kaga tsiya, Hajar kam tana Wakin Baba tare da ?awayenta, kai kana kallonta kasan itace Amarya, tayi kyau harta gaji, abinda yafi birgeni da kwalliyarta shine yadda tayi maintaining natural beautyn ta, ba wata make-up da akay mata, Hafsa ce ta gyara mata fuska, powder mai tsane gumi kawai ta shafa mata sai zizaren kwalli da kuma colourless lip gloss wanda yasa pink lips Winta shining matu?a, sassanyar kyau tayi kam ba ?arya, ko nanda shekara ashirin ba a kalli hoton bikinta ayi dariya ba, dan wnn make-up Win ta zamani canja kamanni take ainun. Zainab ta kalli agogon wayarta tace "uhmm yaci ace an Waura fa, Hajar ta kusa zama matar ya sayyadi Nura", murmushi Hajar tayi tana jin wani daWi har cikin ranta, hannunta da yaji zanen ?unshi ta saka ta janyo wayarta, mesaage din da ya turo mata yau da safe ta binciko, ta karanta fuskarta ?unshe da murmushi sai kuma ta sauke ajiyar zuciya tana juya lulu eyes Winta da yayi wani fari sol tamkar madara sbd kwallin da aka zizara masa, Hafsa tace "ko na zubo mana abinci ne?", Zainab tace "Eh kam gwara muci yanxu don nasan bayan Waurin aure sha'anin yini zamu shiga", Hafsa ta fita tsakar gida ta fara neman Anty tinda itace incharge of abinci, a Wakin Umma ta sameta tana zuba tuwo sinasir wainar shinkafa da gurasa a mabanbantan warmers, Hafsa tace "Anty zan zuba mana abinci", Anty tace "tom ga plates can, idan kin gama zuba muku ki fita ki kiramin Mu'azzam ko Abdallah su fitar da na ?an daurin aure gashi nan na fitar musu da nasu", Hafsa tace "tom", ta dauki plate ta zuba musu waina da sinasir, wani plate Win ta Wauka ta zuba miyar taushe da isasshen tantakwashi, saida ta kai abincin Wakin da suke snn ta fito ta doshi soro, le?awa tayi waiko zata hango Mu'azzam amma bata ganshi ba, juyawa tayi kawai zata koma gida sai kuma ta tsaya tana sauraron wasu maganganu, cikin gida ta koma ta tarar da Anty ta fito tsakar gida, wajenta ta isa ta rage murya tace "Anty, kinji wai har yanxu dangin Angon basu zo ba", Anty tace "kamarya basu zo ba ai na Wauka ma an gama Waura aure shiyasa nace ki fita kira Mu'azzam", Hafsa tace "A'a wllh ba a Waura ba", Anty tace "ikon Allah ko mene ya makarar dasu". Hafsa tace "bari naje muci abinci" da haka ta shige wajensu Hajar. wata shegiyar dariya Maama ta Sarke da ita ta mi?awa Balaraba hannu suka kashe, Maama tace "ga dukkan alamu aiki yayi kyau, kinga har yanzu mirsisi banji maro?i ya ambaci cewa an Waura aure ba", Balaraba tace "hmm ke dai bari, yanxu kawai tashi mu fita tsakar gida yadda zamu sha kallo muga ?an bori", Maama ta tuntsure da dariya zuciyarta wasai tace "wllh kam ?an bori, dan wllh tllh idan aka fasa auren nan tsaf faWima za tayi bori", su Nabilah dai kawai binsu suke da kallo don basu rafko jirgin ba, mi?ewa Maama tayi ta fita tsakar gida Balaraba biye da ita, kawai kallon Umma take tana yamutsa fuska cike da tsantsar tsana. A hankali yake shigowa cikin lungun yana ratsa mutane da suke basa hanya da kansu sbd shigarsa ta kamala, hehehe akace kuWi ?umbar susa, yana zuwa ?ofar gidan nan ma aka bashi hanya, ido huWu sukay da Baba da ya kafe ?ofa da ido yana fatan dangin ango su shigo, Baba ya goge fuskarsa da handkerchief ya mi?e tsaye yace "Muktar, barka da isowa", Alhj Muktar yace "Amma Adam jiya fa muka haWu da kai amma baka sanar min da abin arzi?in nan ba", Baba dai baice komai ba sbd hankalinsa baya jikinsa, Alhj Muktar ya gaggaisa da mutanen soron snn ya samu waje ya zauna.

&Wata zufa ce mai shegen yawa take tsattsafowa Nura, tamkar ?aramin yaro haka yayi dafa'an gaban Hajiyarsa, fuskarta a murtuke tamkar ba?in hadari, Nura da zuciyarsa ke wani irin tafarfasa gami da dagargajewa yace "dan girman Allah Hajiyarmu kar ki min haka, kiyi ha?uri dan Allah", Hajiya dake zaune bisa kujera ta wani harWe ?afa tace "Nuraddeen", yace "na'am Hajiyarmu", with seriousness in her tone tace "matu?ar ni na kawoka duniya, matu?ar ni na Wauki cikinka na wata tara, matu?ar ni na shayar da kai, matu?ar ni na raineka, matu?ar ina da daraja da kima a idonta to nace bana son auren nan, nace a fasa yin sa bazaka auri yarinyar ba", wata gudumar tashin hankali ce ta doka a kwanyarsa, kansa ya Wau zafin da ya saka jinin jikinsa tafarfasa wanda ya linka tsiyayar gumi a sassan jikinsa, tamkar wanda aka sharawa ruwa haka gumi ya ji?asa, farar Sabuwa shaddar jikinsa mai kyalli ta ji?e sharkaf, idonsa da ya rine yayi jajur ya Wago yace "Hajiyata, karki min haka dan Allah, me yasa.....", tsawa ta daka masa tace "tambayata kake Nuraddeen, akan wata zaka zo ka titsiyeni kana min tambaya sai kace sa'arka, wllh tllh indai baka tashi daga gabana ba yanzun nan saina tsine maka, kaji mu da mara kunyar yaro, daman an haifi wata yarinya a duniyar nan da zaka zauna a gabana ina fada kana fada akanta, to wllh kar a kuskura a Waura auren nan na gaya maka", shi dai kawai kallonta yake sbd canzawar da tayi, kamar ba Hajiyarsa ba, wacca bata masa tsawa, wacca kullum cikin saka masa albarka take, sai kace wacca aljanu suka shafa, sai ranar Waurin aure za tace a fasa, to me yake faruwa ne, kamar ba ita bace ta daWe tana jiran wnn rana, guiwa a sace ya mi?e ya fita daga palourn nata, Babban palourn gidan ya shiga inda Uncles da kuma Aunties Winsa ke jiransa, tin Wazu da Hajiya ta tubure aka kasa shawo kanta shine yace zaije da kansa ya bata ha?uri, shimfiWar fuskarsa ma kaWai amsa ce, kallonsa suka ringa yi kafin Uncle Winsa Saminu yace "ta ha?ura Nuraddeen", Nura ya haWiyi wani yawu wanda ya gagara wuce ma?ogoronsa yace "A'a, tace tsine min za tayi", baki buWe Saminu yace "A haba dai, ina zuwa", ya mi?e ya shiga palourn Hajiyar, haj Yahanasu ?anwar Hajiya ta mi?e itama ta shiga palourn Hajiyar, Nura da kansa ke juya masa ya koma da baya ya tsaya a bakin palourn, duk abinda suke cewa yana ji a inda yake tsaye daga bakin ?ofa, Hajiya har ?warewa tayi tana kumfar bala'i ita Nura ba zaiyi aure ba, haj Yahanasu ta sauke wata Soyayyar ajiyar zuciya tace "Haba dan Allah yaya ki yiwa yaron nan adalci mana, mene dalilinki da zaki ce ba zai yi aure ba?, ki dubi Allah kuma kiji tsoronsa karki Wauki ha??in yaron nan dan kina matsayin mahaifiyarsa", Hajiya tace "dakata Yahanasu karki min wata maganar banza a nan, cewa nayi kar yayi aure, ni ban hana Nuraddeen aure ba, abinda nace shine ba zai auri yarinyar can ba", haj Yahanasu tace "Yaya karki datse soyayyar dake tsakanin yaran nan dan girman Allah...", a matukar hasale Hajiya tace "Yahanasu karki kaini bango, dan wllh tllh zan iya zazzabga miki marii, kuma zan tsinewa Nuraddeen Albarka", sai a yanxu Saminu ya tanka yace "Hajiya ayi ha?uri, Nura fa ba yaro bane, tinda har yace aure zaiyi to ayi masa...", hannu Hajiya ta Waga masa tana karkaWa ?afa tace "wai ku me yasa baku da hankali ne, nifa ban hana Nuraddeen aure ba, amma tinda har kun Wauki haramar fassarani baibai, bari na kashe bakin tsanya, ka aura masa ?ar wajenka Maryam yanzun nan, ai yarinyar na sonsa shine ya ?i yace wai ?ar gidan gini yake so, ai aure dai aure ne ko wane iri ne, na yarda a aura masa Maryam a maimakon ?ar gidan gini", Nura ya jinginar da kansa a bango ya lumshe idanunsa da suke masa zugi, a zuciyarsa ya furta "innalillah wa'inna ilayhirraji'un", wai shine zai rasa Hajar Winsa, wnn wace irin mummunar ?addara ce, shekara sama da goma ya rayu da soyayyar Hajar Winsa, tin tana ?ar yarinya yake sonta har lokacin da ta mallaki hankalinta ta gane kuma Allah ya haWa zuciyoyinsu, ya sake furta kalmar "innalillah wa'inna ilayhirraji'un" a fili. Saminu ya shafa tsigaggen gemunsa yace "anyi haka kuwa Hajiya, karfa ayi abinda zai Sata zumunci", Hajiya tace "wnn abu ai saidai ya gyara zumunci Saminu, idan ka amince ka bayar da Maryam magana ta ?are, na gaya maka Maryam tana sonsa, tin tini nasan da hakan har maganarta nayi masa kwanaki", Saminu ya sauke ajiyar zuciya don sosai ya aminta da hakan, barin ma da yaga Nura ya fara tara abin duniya. cikin mintinan da basu wuce ashirin ba aka Waura auren Nura da Maryam a babban palourn gidan, Nura da already ya fara ganin ba?i ba?i ya tashi yana haWa hanya ya shige Wakinsa. daga nan kuma wani ?anin Hajiya ya bada shawarar cewa aje gidansu Hajar a sanar musu cewa an fasa auren, su uku ne suka shirya suka nufi gidan. wajen da aka bubbuWa musu a soron suka zauna, wani sanyi Baba yaji a zuciyarsa, Bappa kam kallonsu yake ganin hannunsu si?am babu goron Waurin aure, ?anin Hajiya wanda shine Babba a cikinsu ya fara koro bayani, rufa rufa yayi ya musu bayani mai cike da nutsuwa ta hanyar da bai bayyana ainahin abinda ya faru ba, sarawa kan Baba yayi ya mi?e yace "ku dai ba mutanen kwarai bane wllh, baku san darajar al?awari ba, kunsan baku shirya aurar da dan naku ba kuka nemi da a basa auren yarinya....", sar?ewa maganar tayi ya fara tari, da sauri Naseer ya mi?e ya ri?osa yana ?o?arin zaunar dashi, Bappa ya gyaWa kai cike da takaici yace "Allah ubangijj ya musanya mata da wanda yafi Wan ku Alkhairy a gareta, muma mun fasa aura muku ?ar mu", Saminu yace "Ayi ha?uri, dan Allah idan an nutsu kuje ku kwashe kayanku da ku ka zuba a gidan yaron mu, muma wanda muka kawo muku ku dawo mana da abin mu, ai da sulhu muka zo", Bappa yace "karku damu za a dawo muku da komai tsinke ba za a bari ba". Saminu yace "Allah ya haWa kowa da rabonsa", da haka suka bar soron, ?an Waurin aure suka fara tashi da nufin tafiya, wasu na jajantawa yayinda wasu suka samu abin gulma, tamkar saukar wahayi daga zama haka soron ya amsa ?uwwa da kalmomi shida da suka fita daga bakinsa "ina nemawa Wana auren wnn yarinya", Bappa ya dubi Alhj Muktar da yayi wnn furuci, Baba ma da yake cikin tashin hankali ya dubesa, mutanen da suka fara tashi da sauri suka koma suka zauna, Alhj Muktar ya mi?e ya isa gaban Baba yace "Adam ina nemawa Wana auren ?ar wajenka da aka fasa aura yanxu", wani Waci ne ya kauraye bakin Baba wanda yake jin tamkar an musanya masa miyau da ruwan maWaci, expression Win fuskarsa bazai misaltu ba, kasa cewa komai yayi, Bappa ya girgiza kai yace "A'a, ba zan iya aura mata wanda bansan koshi waye ba, ban san komai a kansa da ya kamata na sani kafin aure ba...", Alhj Muktar yace "nine mahaifinsa, amma nasan bana daga cikin jerin mutanen da za a tambaya shaida a kansa, koda ba za a tambayeni ba amma zan faWa cewa Wana nagartacce ne, halayensa masu kyau ne saidai kuma ko wane Wan Adam tara yake bai cika goma ba, a matsayina na uba kuma mahaifi wanda bazan so abinda zai cutar da ?a?ana ba toh haka zalika bazan cutar da ?a?an wasu ba, ba nida wata manufa na nemawa Wana auren wnn yarinya face manufar alkhairy". Bappa ya sake girgiza kai, Naseer ma dai girgiza kan yayi kuma har cikin ransa bai aminta ba, Baba ya dubi fuskar aminin nasa Alhj Muktar snn ya dubi ta ?aninsa Bappa, ajiyar zuciya yayi yace "Muktar na amince maka, Bappa a Waurawa Hajara aure da Wan gidan Muktar".........
'?
=؛? HAJAR =؛?
by Feenerh_feeche

{32..}
Bappa ya ringa kallon Baba kafin yace "kace na daurawa Hajara aure da yaron da ba musan waye shiba?", Alhj Muktar yayi murmushin manya yace "naji daWin wnn furuci naka, tabbas kanada gsky sosai, nima hkan zanyi idan na samu kaina a matsayinka na yanzu, kuma nima na taSa shiga irin wnn yanayin da Adam ya shiga yanzu, na sake faWa cewa Wana nagartacce ne, amma idan zuciyarka ba ta aminta ba shknn ba damuwa", Baba ya dubi Bappa yace "A Waura mata aure da Wan gidan Muktar, ba nida shakku ko kaWan a kalamansa, na yarda dashi...", Bappa yayi ajiyar zuciya yace "tom, Allah ubangiji ya tabbatar da Alkairi" sai kuma ya dubi Alhj Muktar yace "fatan dai akwai sadaki a kusa", Alhj Muktar da walwala ta bayyana ?arara a fuskarsa yace "akwai, bani minti uku", wayarsa ya ciro daga aljihu ya kira drivernsa, da sauri driver ya Wauka, Alhj Muktar ya umarcesa da ya Wakko masa kuWi a mota, bayan minti bakwai driver ya bayyana a soron, ya dur?usa gaban Boss dinsa ya ciro wasu ma?udan kuWi daga pocket ya ajiye, Alhj Muktar yace "zauna ka zama shaida", ba musu ya zauna ya tankwashe ?afa, Alhj Muktar ya Wauki uwar kuWin ya ajiye gaban Bappa, Bappa ya dubi kuWin ya girgiza kai yace "wnn kuWin sunyi yawa", Alhj Muktar yace "ba suyi yawa ba, sadaki ai baya yawa saidai yayi kaWan", ( Ehennnn a zamanin nan sai kaji mutane suna cewa wai ba a tsawwala sadaki ai ba siyar da yarinya za ai ba, to ga point of correction ba wani siyar da yarinya, shi fa sadakin aure baya yawa a musulunce, matu?ar kanada ikon bawa matarka zunzurutun dukiya mai yawa matsayin sadaki toh ba matsala, tauye sa shine matsala, wllh idan ma kanada arzi?in raba kano gida biyu ka bata rabi matsayin sadaki hakan daidai ne). An Waura auren Hajar da Wan gidan Alhj Muktar bisa sadaki mai tsoka, Waurin auren ya samu shaidu masu yawa, Baba ya lumshe idonsa ya furta "alhmdllh", maro?i ya Waga murya yana sanar da jama'a cewa Waurin aure ya kammala, muryarsa har cikin gida ta ratsa, wani mugun bugu zuciyar Maama tayi jin muryar maro?i ta daki dodon kunnenta, ta juya ta kalli Balaraba da ta hangame baki har ?uda na ?o?arin afkawa ciki, Wasila ta Waga zureren hancinta sama ta rangaWa guWa, murmushi mai kyau Umma tayi. Maama da idonta ya kisfe tsabar takaici tace "wllh sai malamin nan ya biya ni kuWi na, kadan ba sai ya biya ba", Balaraba tace "abin fa da mamaki, tinda nake dashi bai taSamin aiki baici ba, wllh a tarihin aikinsa ma baya faWuwa, gaskiya akai abinda ya faru Rabii", Maama tace "Eh ai kam ga aiki nan na gani", Balaraba ta dafe kai tace "Rabii akwai lauje cikin naWi, mu tsaya dai muyi kallo". Mu'azzam ne da Huzaifa suka ringa firfita da abinci, walima aka baje a soro ana kwasar dabge. Alhj Muktar da Baba suka fita daga soron zuwa can inda babu taron jama'a, godiya Alhj Muktar ya ringa?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? yiwa Baba, shima Baban godiya yake masa domin kwa ya fitar dashi kunya, Alhj Muktar yace "insha Allah da yamma zasu zo", Baba yace "bana ganin Waukar yarinyar nan zai yiwu a yau, a bari zuwa gobe, kaga dai yadda lamarin ya jirkita, shima yaro ai sai an sanar dashi...", Alhj Muktar yace "toh ba damuwa da yau da gobe ai duk Waya ne, karka damu yaro a shirye yake", Baba yace "nagode fa, kaxo domin mu gana sai kuma wnn batu ya gifta bamu samu lokacin ganawarba", Alhj Muktar yace "daman nazo ne domin naga inda kake Adam", Baba yace "Allah sarki", Alhj Muktar ya mi?a masa hannu sukay sallama snn ya tafi. saida rurumar ?ar Waurin aure ta tsagaita snn Baba ya samu shiga gidan nasa, nan fa akay masa caa da gaisuwa da kuma fatan alkhairy, da sakakkiyar fuska ya ringa amsawa yana neman Umma da idanu, daga Wakinta ta fito fuskarta ?unshe da walwala, Baba ya dubeta yace "Wakinsu Nasiru a buWe yake?", tace "bari na duba", ta wuce ?ofar Wakin ta tura taga a buWe take, tace "Eh a buWe take", ya ?arasa ?ofar Wakin yace "ina son ganinki" ya shiga ciki. afujajan Maama ta fito daga Wakinta jin muryar Baba, wuwwurga idanu ta fara yi duk ta ji?e da gumi, hangosa tayi lokacin da ya shiga Wakinsu Huzaifa, da sauri ta wuce har tana ?o?arin bangaje Umma ta shiga Wakin, kallonta Baba da yake shirin zama yayi, Umma dai ta shigo ta samu waje ta zauna, daga tsaye Maama tace "tin safe ka hana mu kudin abinci a gidan nan mal", yace "kuWin abinci kuma Rabii?, ga abinci nan ku zuba kuci", tace "a ina yake abincin?, ni bangani ba", ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login