Showing 195001 words to 198000 words out of 252707 words

Chapter 66 - HAJAR COMPLETE NOVELS By Nafisa Yusuf Nagoda.doc

zan zama abin dariya a bainar nasi..", Balaraba tace "kinga ni tafiya zanyi bani kuWina na ?ara gaba..", Maama ta sosa kanta tace "Wllh bani dasu banida dalilinsu kiyi ha?uri ki Waga min ?afa zuwa wani lokacin", Balaraba ta saki baki tace "ban gane ba, haka mu kayi dake tsakani ga Allah, cewa fa kikai a washe gari ma zaki dawomin da kuWina, kuma na gaya miki kudin nan ba nawa bane na mutane ne suka kawomin ajiya..", Maama ta juya hannu tace "ha?uri za kiyi Balaraba..", Balaraba tace "ni dae ki bani kuWina tin muna shaida juna Rabi", Maama tayi kasa?e tana kallonta kafin tace "Toh shekaruna zan lalo na baki iyee", Balaraba bata sake cewa komai ba ta juya ta fita fuuu kamar zata tashi sama, Maama ta taSe baki ta juya ta koma gida.

&Walking slowly Nurain ya sauko daga stairs da farar Shirt a jikinsa da black sweat pant, kitchen ya shiga ya jona coffee maker, jingina yayi da jikin cabinet yana ?arewa kitchen din kallo, haka nan yaga tana masa gizo a ko wane angle na kitchen din, ya dafe kansa da yayi masa nauyi gami da lumshe idonsa, daren jiya bai rintsa ba even a nap bai samu yayi ba, shi kansa saida yayi mamakin yacca idonsa ya soye ya kasa bacci, sai wajen biyu snn ya Wora alwala ya fara yin sallah ganin bacci ya?i zuwa, har asuba bai rintsa ba haka ya wuce mosque yayi sallah ya dawo, a tunaninsa zai iya bacci da safe ashe ba haka bane, daga karshe shine ya taso zai haWa Coffee ko zai samu relief, ya dauki mug din Coffee ya fice daga kitchen din bayan ya gama haWawa, direct sama ya haura ya shiga Sangarensa ya zauna kan Sofa, after a while ya Wauki mug din Coffeen ya kai baki, yana sipping yaji Waci sai kace ruwan bitter leaf, lokaci guda ya sauke cup din ya kalli Coffee din, sai da yaga ba?in Coffeen snn ya tuna ashe fa bai zuba milk da sugar ba haka nan ya haWa tsura, ya haWe thick eyebrows dinsa sai kuma yayi slight smirk bayan ya tuna ranar da ya Wura mata irin wnn coffeen, yacca ta ringa yamutsa fuska and she cried tace Allah sai ya sakamin da ka bani maWaci nasha... wayarsa dake kan Centre table ya dauka, ya shiga call log ya kira layinta a karo na ba adadi, abinda aka kwana ana gaya masa yaji wato switched off, Nurain bai ?ara ko 2hours a gidan ba ya fita, gaba daya gidan ya zamar masa wani empty, gidansu ya wuce kuma yana zuwa bbu wnda ya lura dashi don haka kawai ya haura upstairs ya shiga room dinsa, sai a lokacin ya samu bacci, ba shi ya farka ba sai ?arfe biyu na rana, abinda ya fara yi shine daukar wayarsa ya sake kiran layinta, ajiye wayar yayi yana sauke ajiyar zuciya murya ?asan ma?oshi yace "Baby wife". wajen ?arfe huWu da rabi Nurain ya shigo main palour ya tarar da Farooq suna gaisawa da Mami, ?arasawa yayi ya mi?awa Farooq hannu sukay musabaha snn ya zauna kan Sofa, Mami ta Wan kallesa tace "ka Wauki Abincin da kace a zuba mka..?", Nurain ya gyaWa kai yace "Eh..", Mami tace "Ohk then..", da haka ta tashi ta nufi Sangaren Hajiya, Nurain ya dubi Farooq yace "kaxo tafiya da Amaryar taka ne...?", Farooq ya gyaWa kai yace "Sure ita ta tasoni fa..", Nurain yace "Ohk" sai kuma ya koma yayi resting da kujera yana shafa kansa, Farooq ya gyara zama yace "That girl.. umm I can't recall her name daughter din sister din Mami..", Nurain yace "what about her..?", Farooq ya shafa kansa yace "what's that her name..?", Calmly Nurain yace "Khausar..", Farooq ya gyaWa kai yana maimaita sunan, after few minutes of silence Farooq ya Wago kansa daga latsa wayar da yake ya ringa kallon Nurain yace "Dude...", Nurain yace "why Punk..?", Farooq yace "you look dull and moody..", Nurain ya girgiza kai yace "Am perfectly alright", yasan idan ya gayawa Farooq damuwarsa toh sai ya masa dariya ma kafin ya basa solution, toh shi a wnn Mood din dariya ce baya so a masa, Nurain na jin alamar Hajiya zata fito ya tashi ya bar palourn ya shiga na Mami, definitely yasan saita masa mganar Hajar shi kuma baya so a ringa taSo weak point dinsa a ynxu, haka nan Hajiya ta bar gidan tare da Farooq da yxo Waukarta, Washe gari Monday da wuri Nurain ya isa hospital, first abinda ya fara yi shine cancelling duk wni surgery da akay scheduling da zaiyi, ina zai iya wani surgery a wnn halin da yake ciki, patient kawai yake attending suma ba wasu da yawa ba ragowar yace Haleema ta sallamesu su dawo gobe, wajen sha Waya da minti hamsin ya gama duba patients din da zaiyi, wajen Haleema ya fita yace ta kira Nurse station yana son ganin A Nurse, da haka ya koma office dinsa ya zauna, after 10mins aka buWe ?ofar office din Ruqayyah ta shigo, walking gently ta ?arasa shigowa ta zauna kan kujera dake gaban table dinsa, Nurain ya taso daga chair dinsa ya ja kujerar dake kusa da wcca ta zauna, saida yayi nesa da kujerarta snn ya zauna opposite to her yana fuskantarta yace "Good afternoon A Nurse", ta Wan kallesa tace "Afternoon" sai kuma ta saukar da kanta tana wasa da ring din hannunta, speaking calmly yace "You wanna to talk to me right...?, nace i will make time for you on Monday ko, so now ina jinki", sosai Ruqayyah tayi mamaki don bata taSa tunanin zai kirata akan hakan ba, ita tasha ma ya manta ashe ba haka bane, A hankali tace "Dr ba sai na tsaya maka wani dogon jawabi ba kasan dai duk akan me nake binka, so nake kayi haquri akan laifin da nayi mka dan Allah", Nurain ya sauke ajiyar zuciya yace "If that's the case toh na ha?ura, please stop disturbing my slumber..", har cikin ranta taji daWi kuma hakan ya nuna a fuskarta, tace "Thank you very much Dearest..", ya girgiza kai yace "Take that name off your mouth Ruqayyah, ki manta da duk wani abu da ya wuce Ruqayyah, ba wai na ha?ura bane sbd don mu dawo da relationship din mu na baya ba A'a na ha?ura ne na abinda kika min, Ruqayyah bana so a ta dalilina kiyi ruining rayuwarki, ni na riga nayi moving on nayi aurena and ina zaune cikin farin ciki da matana, sai a ynxu nasan cewa ban dace dake ba from the start Ruqayyah, ina so kema ki ajiye komai kiyi moving on don gyara future dinki, wollah Ruqayyah I don't have any feeling left for you, kuma har abada bazan sake waiwayenki ba just know that, ki dena Sata golden time dinki wajen yin abinda bazai fissheki ba", hawaye wasu nabin wasu haka suka fara zarya akan cheeks dinta, Nurain ya figi tissue paper ya mi?a mata, a hankali ta amsa ta goge hawayen, tana gogewa wasu na sauko mata, shi dai gsky ya gaya mata gwara tasan inda dare yayi mata tin wuri, After a while ta Wago tace "Thank you for letting me know what is in your mind... ngd da ka yafemin laifin da na mka, tabbas some opportunities comes once in life, nima opportunityn aurenka sau Waya tazomin a rayuwa amma nasa ?afa nayi fatali da ita, insha Allah Ni Ruqayyatu ba zan sake shiga rayuwarka ba Dr..", Nurain yace "Better", a hankali ta tashi ta nufi door har lokacin hawaye bai dena sauko mata ba, ta juya tana kallonsa sai kuma tace "Allah ya baka zaman lfy with your wife..", speaking with a repartee yace "Ameen.. please Shut the door", ta gyaWa kai a hankali tace "Tom" da haka ta fice ta kullo masa ?ofar. ?arfe tara na dare Nurain na kwance kan doguwar kujera a palourn Maminsa, ceiling kawai yake kallo ya Wora left hand dinsa a forehead, thick eyebrows dinsa a haWe thinking of what to do, toh ynxu idan yarinyar ta gayawa parent dinta da wne idon zai kallesu, bama wnn ba Babanta wane irin kallo zai yiwa Abba, shiyasa ya rasa courage din zuwa gidan nasu don bai san me zai tarar ba, kuma shima rashin zuwan nasa matsala ne, wayarsa dake side dinsa ya Wauka ya ringa kallon screen dinta, after few seconds ya ajiye ba tare da yayi komai da ita ba, don yasan ma idan ya kira switched off zai ji, lumshe idonsa yayi gami da sauke ajiyar zuciya, Mami da ta fito daga bedroom ta ringa kallonsa without blinking, ?arasawa kujerar da yake kwance tayi ta kai hannu forehead dinsa tace "Are you sick Son..?", ya buWe lumsassun idanunsa sai kuma ya mi?e zaune yace "No", Mami tace "Ohk amma ya baka tafi gida ba ko baka san dare yayi ba..?", ya kalli clock yace "ban san dare yayi haka ba", Mami tace "Alright sai ka tashi ka tafi dare na kuma yi, ka bar ?aramar yarinya a gida", yace "Toh" da haka ya tashi yana jan rigarsa yace "Saida safe", tace "Allah ya tashemu lfy", ta bisa da kallo har ya fice, definitely tasan akwai abinda yake damunsa, ko ta tmbyesa ma ba gaya mata zaiyi ba sbd shi lamba Waya ne a fannin zurfin ciki da taurin kai, da kansa zaizo ya gaya mata idan abun ya ishesa dman haka yake.

&Yau kwanan Hajar uku a gida, sosai take jin daWin zamanta da Ummanta da little sister dinta, lokaci zuwa lokaci abinda ta ajiye ?asan zuciyarta ke tsikararta kuma nan da nan take yakice sa daga ranta, tinda tazo Baba bai mata mgana akan kwana ba sai yau, kuma shima cewa yayi ta tafi gidanta ko mijin nata bai dawo ba, da ta koma Waki tana kumbure kumbure ma Umma bata goyi bayanta ba tace ai tayi na Allah da ma'aiki kawai ta tafi, gashi bata gayawa Umma ainahin me ya faru ba, haka dai ta ?udurce a ranta yau da daddare zata sanar da mahaifiyarta gskyr lamari, Hajar na zauna kan darduma tin bayan da ta idar da sallar magrib, daga tsakar gida taji Umma na yiwa Sabrah mgana tana cewa "baza kije ki kai mata wayarta ba iye... kullum waya na hannunki sai game kike bbu kama ?afar yaro", Mu'azzam dake tsakar gidan shima yace "Ai wcca ta bata ce ba tada hnkali... bata san tsadar wayar bane shiyasa, Samsung ce fa ynxu ta faWi screen dinta ya fashe sai taja kuWi sama da dubu Wari wllh... a Samsung din ma fa tata babba ce..", Umma ta ri?e baki tace "wuce ki kai mata wayarta", Sabrah tace "Toh", sum sum sum ta tashi ta kaiwa Hajar wayar, Hajar ta amsa tace "Anjima kaWan saina baki ki cigaba da game din", Sabrah tace "Toh Addah" sai kuma ta juya ta fita, Hajar ta kalli wayarta ta a karo na farko tinda garin Allah ya waye, sam sam bata bi takanta don har Chargi ma Sabrah ce take sakata idan an kawo wuta, kuma tinda ta sakata a Airplane mode bata cire ba, a hankali ta kai hannu ta kunna wayar, tattare gira tayi bayan taga notification din messages, da sauri ta janyo labulen wayar ai kam taga ba a Airplane mode take ba, Sabrah ta cire garin danne danne, Hajar ta kwanta tana kallon messages din amma bata buWe ba, ta sauke numfashi a hankali ta kai hannu ta buWe guda Waya, saida zuciyarta ta buga kafin ta fara karanta message din, guda biyu kawai ta karanta taji idanunta sun ciko da ruwa, lokaci guda hawaye suka fara gangaro mata ta kife wayar don bazata iya cigaba da karantawa ba, ko minti goma ba ai ba wayar ta fara ringing, ita tsorata ma tayi don tayi nisa cikin tunanin da take, ta Wago wayar tana kallon screen dinta ba tare da tayi picking ba, a haka har kiran ya katse wani ya sake shigowa, ta kai hannu za tayi rejecting call din amma ta kasa, ba tasan lokacin da tayi picking ba sai kuma ta kasa kaiwa kunne, a hankali ta kara a kunnenta ba tace komai ba, ta jiyo muryarsa yace "Baby wife..", turo baki tayi ta masa banza, yace "Hajar..", tayi jimm kafin tace "Na'am", ajiyar zuciya taji ya sauke tayi sauri ta lumshe idonta tana jin tsigar jikinta na mimmi?ewa, yace "har ynxu baki huce ba Baby wife..?", ta masa banza tana wani turo baki, yace "please talk to me", nan ma shiru ta masa, Calmly yace "Am sorry Hajar, i shouldn't have said All that stuff, delete All that stuff from your head please, Am sorry Baby wife", Sosai jikinta yayi sanyi ta kasa ce masa uffan, hawaye ya cika idanunta, yace "Can i come for you now..?", ta girgiza kai kmar yana kallonta tace "No..", yace "Why..?", tace "Sbd kaxo ka tafi dani ka cigaba da min favor ko", ya sauke numfashi yace "Hajar.. wollah i take back all what I said", tace "Okay good night...", yace "Toh can i come and pick you tomorrow..?", katse kiran tayi without answering, nan ya ringa kiranta ta?i yin picking, message ta shiga ta tura masa Yess, daga hka ta danna wayar a Airplane mode. Washe gari sai yamma li?is Hajar ta cire wayarta a Airplane mode, dman tace da Umma ai yau ma zaizo su tafi ya dawo daga tafiyar. wajen ?arfe takwas na dare kiransa ya shigo wayarta, tana picking yace "how are you doing Baby wife..?", tace "Alhmdllh", yace "Good, Am here already", tace "Ohk" sai kuma ta katse kiran, Umma ta shigo ta ajiye warmer din abincin hannunta gefe guda snn ta kalli Hajar tace "baizo bane..?", Hajar ta girgiza kai tace "yaxo yana ?ofar gida", Umma tace "toh tashi ki tafi mna kin barsa yna jira", Hajar tace "Umma ba muyi sallama da Baba fa", Umma tace "Topa kin san dai ba ynxu zai dawo ba sai Anjima", Hajar tace "nidae zan jirasa", Umma ta buWe baki knn saiga sallamar Baba, yace "Ina Hajarar ne..?", Umma ta fita tsakar gida tace "gata nan mal", Hajar ta tashi ta tsaya gaban mirror zata Wauki handbag dinta, zuge handbag din tayi ta ciro duka kuWin da suke jakar ta ajiye kan mirrorn ta danne da robar mai, ta kalli Sabrah da ta bita da ido tace "Shhh karki gayawa Umma", da haka Hajar ta fita tsakar gida Sabrah tabi bayanta, Hajar ta du?a gaban parent dinta tana musu sallama, Baba ya dafa kanta yana saka mata albarka kamar yacca ya saba, tini hawaye suka cika idon Hajar don ji take kmar idan ta tafi bazata dawo ba, Maama da ke tsaye tsakar gidan itama tace "Au ai na sha kaWota akay da naga kwana biyu ta zaune a gida", daga Baba har Umma bbu wnda ya tanka mata, Sabrah kam fashewa tayi da kuka ita sai tabi Hajar, Hajar kam ta cake tace ta Wakko kayanta su tafi, Umma tace A'a makaranta fa, Baba kam daman bai yarda ba tin farko ya girgiza kai, Hajar tace "A cewa Yaya na tafi", Umma tace "zai ji". Walking slowly Hajar ta nufi soro zuciyarta na wani irin harbawa tamkar zata fito, tin daga bakin soron taji ?amshinsa da tayi mugun missing, ta saukar da kanta ta ?arasa fita, ko da wasa bata kalli position dinsa ba ta tsaya nesa dashi, ta Wanyi bowing tace "ina yini", kallonta yake without blinking sai kuma ya sauke ajiyar zuciya, one thing came to his mind cewa bata sanar da parent dinta ba. The ride was so silent bbu wnda yace uffan a cikinsu, ita kam Hajar window ta kalla ta ringa kallon titi, suna tsaye a wani traffic kafin a basu hannu Nurain ya juya Ninety degree yana kallonta, sosai taji kaifin idonsa a kanta amma ta?i ta juyo, slowly ya kamo hannunta ya ringa murzawa a tafin nasa, ta Wan juya ta kallesa, yayi pecking hannun nata yace "kinyi shiru", ta saukar da kanta ba tace komai ba, ya sake pecking hannun nata ai kam ta Wago ta kallesa, yace "ko saina buWe bakin", turo baki tayi zata fixge hannun ya?i ya sakar mata, da haka ya juya ya cigaba da driving don an basu hannu, da hannu Waya yake driving din Wayan hannun kuma yana ri?e da nata, suna shiga palour bayan sun isa gida Hajar ta nufi stairs, da sauri Nurain ya ajiye ledar roasted chicken da tsire daya siya a hanya ya ri?ota, kan kujera ya zaunar da ita yace "Are you still mad at me..?", ta girgiza kai, ya du?a gabanta yace "Hajar bana so ki haura upstairs baki huce ba..", Kneeling yayi yace "please forgive me Baby wife", tini ta zamo ?asa daga kan kujerar ganin abinda yayi tasa soft palm dinta ta toshe masa baki tace "wllh na ha?ura", lokaci guda ta faWa ?irjinsa ta sakar masa kuka tace "Wllh na ha?ura.. nima kayi ha?uri", tini yayi wrapping dinta sosai tamkar zai Sallata, ta lumshe idonta tana sauraron bugun zuciyarsa tana kuka a hankali wnda ta rasa dalilinsa, in a whisper tone yace "I missed you Baby wife"......
'?
=؛? HAJAR =؛?

{81..}
Saida Hajar taji fitarsa masallaci da asuba snn ta buWe idonta, a hankali ta muskuta ta sauko daga gadon tana ?arewa kanta kallo, rigarsa ce a jikinta wcca ta tsaya mata a rabin laps, bata san lokacin da wani murmushi ya kufce mata ba, sai kuma ta saukar da kanta tana jin wata azabar kunya, ilahirin jikinta ya kwaso ainahin ?amshin mijinta mai sanya nutsuwa, sleeping gown dinta dake yashe kan tiles da ribbon dinta ta dauka ta nufi door da sauri, bata so ya dawo ya tarar da ita a room dinsa cause bazata iya haWa ido dashi ba, room dinta ta wuce direct ta shiga bathroom ta dauro alwala, tana idar da sallah ta koma gefen gado ta zauna don har ynxu tana jin slight pain, gaba Waya memory din last night ne yake mata yawo a brain, komai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login