Showing 147001 words to 150000 words out of 252707 words

Chapter 50 - HAJAR COMPLETE NOVELS By Nafisa Yusuf Nagoda.doc

biyu. Nurain dake zaune a wani makeken conference hall tare da collegue dinsa da suka zo workshop din suma, ya dena kallon abinda aka haska musu a projector ya dubi wayarsa dake kusa da Laptop dinsa da take vibrate a karo na biyu, saida wayar ta katse snn ya tashi daga kan chair dinsa yayi excusing kansa ya Wauki wayarsa ya nufi ?ofar fita daga conference hall din, a bakin ?ofar hall din ya tsaya ya shiga kiran numbern, Hajar ta kalli wayar hannunta jin tana ringing, har ta ha?ura da taji ba a Waga ba, a hankali ta kai slim finger dinta tayi picking ta kara a kunne ba tace komai ba, silence Win seconds ne ya biyo baya kafin yace "what..?", shiru tayi masa ta?i mgana, ya ciro wayar daga kunnensa ya kalli screen dinta sai kuma ya mayar kunne yace "mene ne...?", tace "ni cikina ne yake min ciwo", jim yayi kafin yace "ohk.. na siya miki drug jiya sai ki sha..", juya lulu eyes dinta tayi tace "ni ban gansa ba..", yace "ohh ba kinyi amfani da abinda na kawo miki jiya at night ba.. so ki duba cikin ledar", Hajar tayi shiru tana tunani mene abinda ya kawo mata tayi amfani dashi, lokaci guda ta tuna ai kam ?it ta kashe wayar tana turo baki, walking slowly ta isa gaban box din kayanta ta dur?usa ta buWe, ledar da ta saka ciki ta buWe ta fara ciro pack din sanitary pad din, a can ?asa ta hango wata ledar tana buWewa taga kwalin drug, ta Salli 2tablets ta sha da bottle water, ko 3mins ba tayi da sha ba ciwon ya sauka gaba Waya babu shi, ta koma ta zauna ta cigaba da watching movie din da take.

&Maama ta fito daga Wakinta da wata fatattakakkiyar tabarma a hannunta wacca ta gama zarewa tass, inuwar dake gaban Wakinta ta samu ta shimfiWa tabarmar ta zauna, Nabilah dake zaune tsakar gida tana tankaWe tace "Maama wace miyar za a kaWa kuka ko kuSewa..?", Maama ta juya hannu tace "duk wacca kika kaWa..", Nabilah tace "bari na kaWa kuSewa kawai don Baba yafi sonta...", Maama dake susar kai ba ji ba gani ta dena susar tace "kuka zaki kaWamin bana son wata kuSewar banza kayan zawayi..", Nabilah tace "amma Baba yafi son kuSewa kuma kinga baya jin daWi...", Maama ta ?unduma mata wani ashar harda da?uwa tace "uban da ya haifeki ya hau fel waya ya diro, ni zaki yiwa tsarin banza, ince baya gidan tin safe ya fita da wani kike cewa baya jin dadi, wnda baya jin dadi ne zai fice tin safe..", Nabilah ba ta sake cewa komai ba ta cigaba da tankaWenta, Sa'adatu ce ta fito daga Waki sai sharSa uban gumi take, ta zauna kusa da Maama tana sharce zufa tace "kai Wakin nan akwai zafin bala'i da masifa sai kace gidan burodi wllh..", Maama tace "uhmm tsakar gidan ma ba dama, idan iska ta kaWo sai ta gama baWaWo zafin rana take zuwa sai kiji kamar daga jahannama ta huro", Sa'adatu tayi tsaki tace "shiyasa na tsani zaman gidan nan, zafi da kuWin cizo ma kawai sun ishi bawa..", Nabilah ta ajiye rariyar hannunta ta juyo tana kallon Sa'adatu sai kuma ta taSe baki tace "ya za kiyi tinda a nan Allah ya ajiye ki..", Sa'adatu ta hura hanci tace "Maama ki mata mgana kinga dai ban saka da ita ba ko", Maama tace "bari Nabilah..", Nabilah ta gallawa Sa'adatu harara ta juya ta cigaba da aikinta, Maimuna ce ta fito daga Waki fuskarta duk kumburin bacci da kwandon soso da sabulu a hannunta, ta wage baki tana zabga hamma babu a'uzubillahi bare ta rufe baki, bokiti ta Wauka ta Webi ruwa ta shiga toilet. tin daga soro Balaraba ta shiga zabga sallama, ayam ta shigo gidan tana kiran sunan Maama, Maama ta turSune fuska ta juyar da kai, Balaraba ta ?arasa shigowa tana kallon Maama tace "haba ?awalli romon jaSa babu faWa me ya kawo gaba Rabi", Maama ta haWe rai tace "lfy zaki shigo gidan matan aure da hayagaga..", Balaraba ta wage baki tace "nidae zuwa nayi biko naga kwana biyu kin Wauke ?afa sam bana jin Wuriyarki..", Nabilah ce kawai ta gaida Balaraba Sa'adatu kam ko kallon arzi?i ba ta mata ba tana danna wayarta, wayar nan da za a buWe maka gallery ka shiga video to tsaf mutum zai iya makancewa don babu komai a ciki sai videos din batsa da shashanci, Balaraba ta zauna kan tabarma tace "kai wnn ma duk ta ruSe cin jiki za tay..", Maama tace "da sai ki taho da wacca zaki zauna ai..", Balaraba tace "kyaji dashi dai.. idan da kinsan da mai nazo miki da tini kin fara nan nan dani wllh tllh..", Maama ta taSe baki tace "haba Balaraba ke har akwai wani abin arziki da za ki zo min dashi har nayi rawar ?afa nayi nan nan dake.. hmm wane dare ne jemage bai gani ba ai sai na mutuwarsa..", Balaraba tace "da dai kin taso mun shiga daga ciki..", Maama tace "mu shiga daga ciki a ina... dawa za a shiga daga cikin..?", Balaraba ta fakaici kallon Nabilah da Sa'adatu sai kuma ta marairaice fuska tace "haba Rabi ai kya bari kiji abinda nazo miki dashi tukunna", Maama ta tashi tana gyara haSar zaninta ta shiga Waki Balaraba tabi bayanta. Maimuna ta fito daga wanka ta tsugunna gaban rariya tana goge kaushi, Nabilah da ta gama ruWe tace "Maimuna ki Wan temaka kiyi wanke wanke babu ko kwanunkan da za a ci abinci da daddare", Maimuna ta girgiza kai tace "chabWi tin da baki gayamin ba saida nayi wanka..", Nabilah tace "knn dai baza kiyi ba..?", Maimuna tace "kwarai..", Nabilah tayi kwafa ta saka hijab ta fita zata siyo daddawa, Maimuna ta ?arasa goge ?afarta ta tashi zata shiga Waki, juyawa tayi tana kallon Sabrah da ta shigo gidan yanxu ta dawo daga islamiyya, Maimuna tace "ke zo nan..", a hankali Sabrah ta isa kusa da Maimuna tace "gani", Maimuna tace "ga can kayan wanke wanke wuce ki zauna kiyi", Sabrah ta kalli kayan wanke wanken tace "toh bari na cire kayan makaranta Umma tace ina dawowa na ringa cirewa..", Maimuna ta buWe baki ta lailayo wata ashariya ta lafta mata tace "zaki wuce ko saina sumar dake shegiya..", Sabrah taja da baya tana ?un?uni tace "Umma tace na dena zama da uniform fa..", Sa'adatu dake kallonsu tace "kika tsaya wnn figigiyar yarinyar tana mayar miki da martani, shegiyar yayarta ma haka ta barmu bare wnn ?ar tsituwar, ci uwarta kawai..", babu tausayi Maimuna ta ma?ure yarinya ta shiga gaura mata mari, Sabrah ta fasa wata gigitacciyar ?ara sbd har taurari take gani, cikin bacci Umma taji ihun ?ar autarta, ita bata ma san lokacin da baccin ya Webeta ba, da sauri ta fito tsakar gida, har lokacin Maimuna ba ta dena wankawa Sabrah mari ba, Maimuna na Wago kai sukay ido huWu da Naseer dake tsaye ya harWe hannu yana kallonta, da sauri ta saki Sabrah ta kwasa a guje zata shiga Wakin Maama, da sauri Umma da zuciyarta ke tafasa hundred degree Celsius tasa mata ?afa. Maimuna saida tayi nadamar marin Sabrah da tayi, dan da Naseer ya ringa haskata da maruka saida ya fasa mata baki, kunnenta kam gaba Waya signal dinsa ta Wauke, da kyar Maama ta kwaci Maimuna daga hannunsa, daman yanada cikinta, Umma dai tinda ta janye ?ar autarta ta wuce Waki da ita.

&Tini Hajar ta fara sabawa da zaman hotel room din, yau kwanansu huWu kenan, tin ranar da ya bata waya kullum saita kira Ummanta sun gaisa, da daddare da misalin ?arfe tara na dare, Hajar na zaune kan carpet tana kallon wani film na comedy mai suna home alone, Nurain na zaune kan couch da pajamas a jikinsa yana operating laptop, wayarsa ya Wauka ya shiga lalubo numbern wani friend dinsa da sukay karatu tare a India, cikin numbers da yayi saving akan email ya samo numbern abokin nasa da yayi saving da Dr Hammad, dialing numbern yayi ai kam tana fara ringing akay picking, Nurain na sallama Hammad ya ganesa with his voice, bayan sun gaisa Hammad yace "how are you doing yasu Mami...?", Nurain yace "fyn alhmdllh..?", Hammad yace "to masha Allah sai yau aka tina dani kenan", Nurain ya shafa sumar kansa yace "Ai gani ma a garin ku", Hammad yace "really are you in town..?", Nurain yace "yeah, since Sunday ma ina..." shiru yayi jin wata dariya da Hajar ta she?e da ita, ya ringa kallonta tana dariyarta her eyes fixed on tv, ta Wan juyo ta kallesa har lokacin annurin fuskarta beyi fading ba, ganin sunyi ido huWu tayi saurin tsuke fuska ta juya ta cigaba da kallonta, jin shiru Hammad yace "hello are you there..?", Nurain yace "yeah" suka cigaba da magana, wani abin dariyar aka sake yi a film din, Hajar couldn't help it but to laugh hard, ta toshe bakinta da palm dinta tana ?o?arin tsaida dariyar, ta gefen ido ta fakaici kallonsa ai kam taga ashe kallonta kawai yake, ta turo baki tayi twinkling lulu eyes dinta, tashi yayi ya Wauki remote din TV ya danna off ya koma ya zauna ya ajiye remote din a side dinsa, Hajar ta wani haWe gira ganin ya kashe mata kallo, juyowa tayi tana kallonsa taga wayarsa ma yake ko a jikinsa, haka kurum don ba?in hali shine zai kashe mata jin dadinta shi kuma ya koma gefe yana wayarsa, wani irin turo baki tayi ganin yayi murmushi kawai zuciyarta ta bata ai da girlfriend dinsa yake waya, mi?ewa tayi tana kallon remote din da ya ajiye gefensa, tafiya ta fara yi kamar zata wuce still tana kallon remote din, da sauri ta kai hannu zata wafci remote din, kafin ta kai ga Wauka shi ya rigata Waukewa ya Waga sama, ai kam taci tuntuSe da ?afarsa gaba dayanta ta faWa kansa, a gigice ta fara ?o?arin Wagasa ta wani zaro ido, bai bata damar hakan ba yayi saurin dafe bayanta ta sake faWawa ?irjinsa, a hankali yace "i will call you back" da haka ya cire wayar a kunnensa ya ajiye gefe, mutsu mutsu kawai Hajar take alan a dole tana so ta sauka a jikinsa, daman da hannu Waya kawai ya ri?eta, jin yadda take motsi kawai ya zagayeta da Wayan hannun, wani irin bugu zuciyarta ta shiga yi hancinta ya cika da ?amshinsa gashi har saukar numfashinsa tana ji.....
'?
=؛? HAJAR =؛?

{64..}
Sosai yayi wrapping dinta a ?irjinsa har saida ta dena mutsu mutsun da take, tayi lamo zuciyarta na tsananta bugu, gaba Waya ta gigice ta rasa sukuni, after a while taji ya sassauta ri?on da ya mata, ai kam tayi wuff ta fincike kanta ta Wagasa, ta koma da baya tana jan fingers dinta murya ?asa ?asa tace "wllh bbu kyau haram ne..", tsuke piercing eyes dinsa yayi yana kallonta yace "mene babu kyau..?", ba tasan lokacin da ta galla masa wata shegiyar harara ba tace "me yasa zaka taSani ai kasan haram ne..", ya haWe thick eyebrows dinsa yace "Nah.. ohh naga ke kika faWo kaina young lady or is it a coincidence", ta zuba masa lulu eyes dinta sai kuma ta haWe rai, yayi slight smirk ya nuna remote din dake gefensa yace "you can take it..", kallon remote din tayi ta wuce ta bar wajen, juyawa yayi yana kallonta ganin ta nufi gado yace "hey ga remote din fa ko kin fasa kallon ne..", banza tayi dashi ta hau gado abinta ta rufa da duvet tana turo baki, taSe baki yayi ya juya murya ?asan ma?oshi yace "Silly girl..." ya Wauki wayarsa ya kira Hammad, tinda Hajar ta kwanta take sha?ar ?amshinsa da take jinsa a kayanta, ta ringa juye juye tana yamutsa fuska, lokaci guda ta mi?e zaune ta ja siririn hancinta, ko dai ta cire kayan ne ta huta, komawa tayi ta kwanta kawai bata dade ba bacci me nauyi ya Wauketa wnda hakan yanada nasaba da ni'imtaccen ?amshin da ta ringa sha?a ita bata sani ba. da asuba ta farka, a hankali ta fara buWe idonta jin wata qira'a mai daWi tana shiga kunnenta, ta fara surveying Wakin da ido, zaune ta gansa kan prayer mat sautin qira'ar yana tasowa daga wajensa alamar dai shi yake karatun, tarwal Hajar ta buWe idonta tana kallonsa, a zuciyarta kam mamaki take ai tasha boko kawai ya saka a gaba, ita tinda take ma ta taSa jin qira'a mai daWin wnn, gashi kuma ba taga Alqur'ani a gabansa ba alamar da ka yake yi, ta yamutsa fuska a ranta tace ba wani nan ya sayyadi ya fisa, ta lumshe idonta tana tunanin ya sayyadinta wnda WaiWaikun ranaku ne bata tinawa dashi. tashi Nurain yayi bayan ya hattama iya izifin da zaiyi, ya kunna hasken Wakin sosai, ya Wan fakaice kallon gado, da sauri ya Wauke kansa ya wuce ya buWe closet ya Wauki kayan da zai saka ya shiga wanka, after 15 minutes ya fito already ya saka kaya a bathroom yana goge cikakkiyar sumarsa da small towel, Hajar da ta buWe idonta tin bayan shigarsa bathroom tayi sauri ta rufe ganin ya fito, saida yasha white coffee snn ya Wau jakar Laptop dinsa ya fita wajen bakwai da rabi, yana fita Hajar ta diro daga kan gado, da sauri ta shige toilet tayi wanka, tana fitowa ta kimtsa kanta tsaf don har combing hair dinta tayi, ?arfe takwas da rabi aka kawo mata breakfast, kaWan taci abincin don bata jin yunwa sbd tasha coffee, wayar da ya bata ta Wauko tayi dialing numbern Umma, tana fara ringing Umma ta Waga, bayan sun gaisa Hajar tace "Umma yasu Baba da Sabra da Yaya...?", Umma tace "kowa lfy lou alhmdllh, kema ai lfyr kike ko..?", Hajar ta gyaWa kai tace "uhmm", Umma tace "toh Alhmdllh... Allah yayi albarka sai anjima..", Hajar tace "toh sai anjima..", Umma ta katse kiran. har ?arfe sha biyu Hajar na zaune kan couch tana kallon tv, daga wnn channel din zuwa wata channel din, ita zaman waje Wayan nan ya fara isarta fa, ba chass ba Ass saidai kawai taci abinci tayi wanka sai kwanciya, ta dubi agogo taga ?arfe biyu saura, ita lokacin ma baya mata sauri yanzu, kallon ?ofa tayi jin an murWa handle, a hankali ya turo ?ofar ya shigo, ido huWu sukay, da sauri Hajar ta Wauke kanta, yayi sallama ciki ciki itama ta amsa masa ciki ciki, tini room din ya kaure da pure men scent dinsa, da yake yaune last day na symposium din shiyasa suka tashi da wuri, daman na kwana biyar ne so a yau da take Friday suka gama, tana ganin ya shiga bathroom ta tashi daga kan couch ta Wauki ledar lunch da aka kawo mata ta koma bakin gado ta zauna ta fara ci, Nurain ya fito daga bathroom bayan yayi refreshing kansa, a fakaice Hajar ta dubesa, lokaci guda ta tsura masa ido tana kallon farar Shirt ?al dake jikinsa, brain Winta ce ta amsa ta fara sinking, kallonsa take babu ?iftawa tana so ta tina wani abu da yake mata yawo a brain, kamar fa ba lokacin da ya kusan bige yaron nan ta fara ganinsa ba, tabbas da ta ga wnn farar Shirt din tana ?o?arin tina wani abu, don ita gaba Waya ta manta encounter dinsu ta farko ta biyu da ta uku saita huWu kawai take tinawa, ya juya ya Wan kalleta, ganin kallon da take masa ya tsuke ido, wayarsa da tayi vibrate ya Wauka yaga Hammad ne ke kiransa, bai Waga kiran ba ya sake kallon Hajar da har lokacin bata Wauke idonta daga kansa ba, ya kalli Shirt dinsa wacca ya lura ita take kallo, jan Shirt din yayi kafin ya haWe gira yace "hey what are you starting at..?", ganin bata amsa ba kuma bata dena kallon nasa ba kawai ya fara tafiya towards her, twisting fingers dinsa yayi a daidai fuskarta wnda ya bada sautin Was Was, ai firgigit ta dawo daga duniyar da ta lula, haWe gira tayi ganinsa daf ta ita, ta ajiye spoon din hannunta kan takeaway din abincin da take ci, Calmly yace "what are you starting at..?", ta juya idonta tace "is there anything to stare at..", ya ringa kallon pink lips dinta da take mgana ta wani cokalosu, ya buWe baki zai mgna knn wayar hannunsa tayi vibrate, ya Wauke idonsa daga kallon lips dinta ya koma da baya, picking kiran yayi ya kara a kunne yace "ohh Hammad..", from the other side Hammad yace "are you coming..?", Nurain yace "wait ai nace ka turomin inda zamu hadu ko", Hammad yace "Oh c'mon gidana fa zaka zo Dr", Nurain ya sauke ajiyar zuciya yana shafa kansa yace "kawai mu hadu a wani Eatery or Coffee shop haka mna..", Hammad yace "No.. saidai ba ziyarar zaka kawomin ba..", Nurain yace "Alright you know i don't have the Address right...", Hammad yace "ohh i will send it to you right away", Nurain yace "better" da haka ya katse kiran yana sauke ajiyar zuciya, bbu jimawa message din Hammad da ya turo masa da address ya shigo, ya zauna kan couch bayan few seconds ya kwanta ya mi?ar da legs dinsa, da hannunsa yayi pillow lokaci guda bacci ya Webesa, Hajar na gama cin abincin ta rufe ragowar, itama baccin ne ya tafi da ita daga Wan mi?ewa. Nurain ya farka wajen ?arfe huWu, stretching jikinsa yayi bayan ya mi?e zaune, da sauri ya wuce toilet ya dauro alwala gudun lokaci ya ?ure masa, yana idar da sallah ya juya yana kallon Hajar da ke bacci har lokacin bata farka ba, ya sauya kayan jikinsa daga ?anana zuwa manya, text din da Hammad ya turo masa ya buWe yana karantawa, shi kam dai yaso su haWu a wani wajen ba gida ba, dama dai gidansu ne bazai damu ba, wayarsa ya saka a front pocket yace "damn it", ya sake kallon position din Hajar, du?awa yayi gabanta yayi tapping dinta a hankali, ta buWe sleepy eyes dinta, da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login