Showing 87001 words to 90000 words out of 252707 words

Chapter 30 - HAJAR COMPLETE NOVELS By Nafisa Yusuf Nagoda.doc

corridor ta jigina da bango, Hajar tayi saurin juyar da kanta gefe tana goge cheeks dinta, Noor taso ta fahimci cewa kuka take amma kuma demon en gabanta shine ya kwashe mata tunani, har Waki ta raka Hajar kafin ta fito, direct kuma room dinta ta wuce tayi plugging Lap top dinta a charge. Hajar ta idar da sallah, kwanciya tayi kan carpet ta lulluSe da babban hijab din da tayi sallar, tara da rabi Mami ta shigo dubata, Mami ta dafa forehead dinta to feel her temperature, Hajar ta buWe idonta don ba bacci take ba, tunani ne iri iri ya cunkushe mata a brain, Mami tace "ki dena kwanciya kan carpet ga bed nan, ko headache en ne?", Hajar ta tashi zaune tana girgiza kai tace "A'a ya dena ciwo", Mami tace "toh alhmdllh, ya baki ci abincin da aka kawo miki ba, ko ba kya son sa?", Hajar tace "na ?oshi, naci da yamma", Mami tace "Okay, toh kisha drugs enki sai ki kwanta ko, if you need anything just let me know kinji", Hajar ta gyaWa kai a hankali, Mami na fita Hajar ta shiga bathroom, tayi wanka ta fito ta saka kayan baccin da Noor ta bata, like yesterday night wnn ma ba tayi bacci ba, saidai wnn daren lafiyar ta lou kawai dai ta kasa rintsawa.

&Hajiya ce zaune bisa 3 sitter a great room din Abba, tayi shirinta tsaf da shigar asun da asun na atamfa, ga Waurin kallabi irin na tsofaffin nan mai santi, ta zubawa Abba dattijon idanunta da suka sha farin kwalli tace "Muntari nidai ban fahimci zaman Usuman a gidan nan ba, ya Wauki matarsa su koma gidansu tinda ta warke sumul abinta, tinda dai waraka ta sauka to banga amfanin zama a nan ba, su koma gidan su kar aje a ?uma musu sata, don wnn uwar dukiyar da aka laftawa gidan Sarayi sai su shigar musu tinda banga alamar mai gadi ba, amma kuma dai naga wayar shokin zagaye da gidan, Sarayi ba zasu iya shiga ba gsky..", Abba yace "insha Allah this week zasu koma..", Hajiya ta katsesa da fadin "toh mai zai hana yau su tattara su tafi, nifa yau zan rugungunta na tafi, kamata yayi ma mu fita gidan nan tare dasu, nasan yanzu ma Umaru yana kan hanyar zuwa Waukata", da taushin murya Abba yace "Hajiya ku dan sake zama mana zuwa wani lokaci ko sati fa ba kiyi ba..", Hajiya ta girgiza kai tace "A'a A'a Muntari kasan dai ni adala ce, shekarata biyu a gidan nan banje gidan Salisusu ba ina nan, shima saina jingine masa shekaru biyu kafin na juyo nan idan Allah ya ara min lokacin". knocking door akay kafin aka buWe aka shigo, Mami ta shigo da sallama, ta sanar da Hajiya cewa breakfast dinta is ready, Hajiya tace a kawo mata abincin nan anan zata ci, Mami ta juya ta fita, babu jimawa ta dawo da tray a hannunta, tayi serving Hajiya creamy groundnut pap with yummy beans cake. Mami na gama serving dinta ta tashi zata fita, Hajiya ta ajiye cup en pap tace "Khadijah...", Mami ta juyo tace "Na'am Hajiya", Hajiya tace "naga jikin ?ar taki da sau?i toh shine nace me zai hana yau su tattara su koma gidansu..", Mami tace "Eh Alhmdllh ta samu sauqi sosai, amma dai bata gama shan drugs dinta ba, da sai nan da sati mai zuwa sai a mayar da ita Wakinta lokacin insha Allah ta gama shan drugs en, amma yadda kika ce ai haka za ai Hajiya", Hajiya ta rausayar da kai tana cin ?osai tace "ai shknn tinda kin kawo batun magani, shima mijin naki haka yace sai sati mai zuwa da yake bakinku Waya". kwanan Hajar hudu a gidansu Nurain, tin ranar da suka je wajen Hajiya bata sake fita daga part en Mami ba, everytime tana Wakin da aka ajiyeta, tana dai fita palourn Mami ta gaisheta sai kuma ta koma Waki, Sosai suka saba da Noor sbd tare suke kwana, da rana kuma ta zauna ita kadai idan Noor ta tafi schl, ?arfe biyar da minti huWu Noor ta shiga Wakin da Hajar take, dawowarta daga schl knn, wanka kawai tayi ta canza kaya, Noor tayi murmushi tace "masha Allah, waoh gsky kayan nan sun miki kyau", Hajar ta dubi kanta, straight skirt ne na english wears da shirt dinsa masu kyau, Noor din ce ta kawo mata su tinda daman kayanta take sawa, duk yawancin kayan da ta bata ?anana ne amma decent, don Noor ta fi son su sbd tafi zama comfortable dasu, Noor ta ringa yaba kyan Hajar da kayan, sun fi yiwa Hajar din ma kyau don ita data saka sau Waya basu mata kyan haka ba, Hajar tayi murmushi tace "an dawo schl lfy?", Noor tace "lfy alhmdllh, za kici Noodles?'', Hajar ta gyaWa kai tace "Eh zan ci", daman kaWan taci lunch da aka kawo mata, Noor tace "Ohk, let's prepare it together", Hajar tace "together?", Noor tace "yhap", ?in yarda Hajar tayi wai ita bazata fita ba, daga ?arshe ma tace ta ?oshi, da kyar Noor tayi convincing dinta ta yarda, zumbulelan Hijab din da take sallah ta kirma, Noor ta bita da kallo tace "keda zaki kitchen meye kuma na saka hijab", Hajar tace "in ba dashi ba na fasa zuwa", tare suka fito main palour suka shiga huge luxury kitchen din gidan mai shegen kyau, kitchen island ma wani irin makeke, ga cupboards da drawers suma manya wanda suka zagaye girman kitchen din, Noor ta Wakko pot kafin ta fara harhaWo ingredients, Hajar daga gefe ta tsaya tana kallonta, within 15mins Noor ta gama dafa wata shaWananniyar Noodles, ga fried egg with sausage, A babban plate ta juyo musu, Noor ta buWe fridge ta Wakko lemon kwali da ruwa ta bawa Hajar ta ri?e musu ita kuma ta Wakko plate en Noodles en, a Main palour suka zauna wanda Hajar ba taso hakan ba, Still Hajar tayi tana kallon Noor ganin abinda ta ajiye musu a maimakon fork, Hajar ta ringa kallon tsinkayen tace "meye kuma wnn?", Noor ta Wauki chopsticks din ta fara ci dashi, sosai ta iya amfani da Chopsticks, saida Noor taci loma uku amma Hajar ko attempting Waukar sticks en ma ba tay ba, Noor tace "ya naga ba kya ci?", Hajar ta Wauki Chopsticks en gabanta ta fara ?o?arin Webo Noodles din, daga ta Wiba sai ta zame, Noor ta ringa mata dariya kafin ta tashi ta shiga kitchen ta Wakko mata fork, Hajar tace "tayi daWi sosai", Noor tace "really, da fatan dai kin ri?e recipe din cause it's one of yaya Nurain's favorite", suna gama ci Hajar ta Wauki plate din ta shiga kitchen dashi, Noor ta juya tana kallon stairs jin footsteps, tini ta ajiye cup din lemon da take sha ta tashi da sauri ta ruga Wakinta, tsoron haWuwarsu take sbd wata red cancel ya turo mata akan project dinta da ta tura masa hakan yana nufin shirme tayi kenan, gashi yace sai yayi punishing dinta idan shirme tayi, shiyasa take avoiding dinsa kar ya kamata, Nurain ya ?arasa sakkowa downstairs yana kallon ?ofar part din Mami, kitchen ya nufa da cup din Coffee da ya gama sha, yana shirin murWa handle kawai yaji an murWa ta ciki kafin aka buWe ?ofar, kanta a ?asa tana tattare ?asan hijab dinta da yake sharar floor, ji tay tayi karo da abu, ta ja baya da sauri ta Wago kanta, girarsa a matu?ar haWe yake kallonta, Hajar ta zuba masa lulu eyes dinta zuciyarta na bugawa, ita tsorata ma tayi shiyasa take masa wnn kallon, da sauri ta janye idonta tabi ta gefensa zata wuce tinda akwai space sosai da yake ?ofar babba ce, ( mu bawa juna ha?uri daii ) shine abinda ya amsa a brain din Nurain within 1sec, this time around din ma junan zasu bawa ha?uri ko kuma ita zata basa, hannu yasa ya fixgota baya ya mayar da ita kitchen din, yace "kee are you mad?, dutse kika bige ne?..", Hajar ta yamutsa fuska tace "wa ya sani ko dutsen ne".......
'?
=؛? HAJAR =؛?
by Feenerh_feeche

{41..}
Nurain was more than shocked jin abinda ta faWa, wnn ?ar kucular yarinyar ce zata gaya masa haka, nawa take a wajensa, with hatred yake kallonta, itama Hajar da hatred din take kallonsa har wani zugii take ji a zuciyarta, da mugun sauri ta sake kewayesa zata wuce, hijab dinta ya taWeta saura ?iris ta baje a ?asa tayi saurin dafa handle, a fusace Nurain ya juyo da nufi koya mata hankali, a ransa ya ji dama faWuwar tayi ta dauje guiwa, Mami da ta fito daga part din Abba a daidai lokacin da Hajar ta taWe snn kuma lokacin da Nurain ya juyo a fusace sai taga kamar Nurain din ne ya hankaWota, Hajar da bata lura da presence din Mami a palour ba tayi sauri ta zagaya ta bayan kujeru ta shiga part din Mami, Mami ta bita da kallo kafin ta fara tafiya towards Nurain daya daskare a tsaye, tace "daman ka na gidan nan Nurain..?", don gaba Waya ya ?auracewa part dinta, kwana biyar knn bai shiga part en ba, saidai ya gaisheta a main palour ko kuma part en Abba idan sun haWu a can, Nurain yace "yeah, shirye shiryen kowama work nake so am busy in my room.." da haka ya shige kitchen, Mami ta bisa cikin kitchen din, ya ajiye cup din dake hannunsa a sink yana sauke ajiyar zuciya, Mami tace "i saw what you did Nurain", ya juyo ya zuba mata idanunsa da kana gani kasan ransa a Sace yake ba tare da yace komai ba don bai fahimci me take nufi ba, tace "why did you pushed her..?", Nurain was confused don brain dinsa ma ta kasa basa hadin kai yayi thinking, bai ma san me zai ce ba sbd bai gane me take cewa ba, da kyar ya samu kansa da cewa "Mami i don't get you", sosai ran Mami ya fara Saci kawai ta juya tabar kitchen din. Hajar na shiga Wakin da take ta kafa goshinta a bango tana jin suya a ?ahon zuciyarta, hawaye ne suka fara bin cheeks dinta kafin ta fashe da kuka gaba Waya, a haka Mami ta shigo Wakin ta tarar da ita, har harWewa ?afafuwan Mami suke ta iso wajenta ta ri?e both shoulders dinta tana tambayarta me ya faru, Hajar ta girgiza kai alamar ba komai tana ?o?arin danne kukan, Mami da hankalin ta ya tashi sosai tace "talk to me my dear what happened..?", kawai girgiza kai Hajar take ta?i tace komai, gashi kuma ta kasa haWiye kukan sbd zuciyarta a raunane take, da kyar Mami tayi consoling dinta duk da ta?i gaya mata damuwarta. Hajar ta shiga toilet ta wanke fuska ta fito, wani irin fige hijab Win jikinta tayi sbd ?amshin Nurain da ta fahimci akwai ajiki, kodai hancinta ne ke jin hakan, tayi wurgi da hijab Win a tsakar Wakin, ta juyar da kanta gefe tana kallon damtsenta inda ya rutsa ya fuzgota baya, cike da takaici tayi kwafa tace "Allah ya saka min da ka taSa ni..."

&Maama ta saki tsintsiya da abin kwasar sharar da ta sharo uban dattin dakinta wanda ke Wauke da mushen kuWin cizo da aka zubawa piya piya daren jiya tana kallon ?attin da suke shigowa da buhunhunan shinkafa, da catoon na spaghetti Macaroni da Indomie, ga kuma manya mayan jarkokin Mai biyu, Baba ne ya shigo yana nuna musu inda zasu ajiye kayan, har suka gama shigar da kayan Wakin Baba Maama bata dena kallonsu ba, Nabilah ma dake zaune gaban murhu tana jefa Wan wake sakin baki tay tana bin kayan abincin da ido, har kumfar Wan waken da ta zuba a tukunya ta fara zuba bata sani ba, Baba ya sallami yaran da suka shigo da kayan kafin ya ja ?ofar Wakin nasa ya saka mata kwaWo, Maama ta washe yalayen ha?oranta tace "sannu da ?o?ari mal, wnn irin uban kayan abinci haka, ai ma shekara muna ci wllh, Allah ya biya bu?atu ya bun?asa hanyar nema, shine nace dama ba Wakinka aka kai ba ga kitchen nan da ba a amfani dashi sai a ciro shirgin ciki a kai bola a zuba kayan abincin anan, kaga ba a ringa takura maka ba idan zamu Wiba, wllh tllh dama a kitchen aka ajiye...", Baba dai kawai jinta yake, ta sake cewa "idan ka yarda yanzu sai na ci Wammara na fara fiddo shirgin kitchen din, ina da ma piya piya saina feshe sa da shi gudun ?ananan ?wari..", direct Baba yace "Ai ba namu bane garar Hajara ce", Maama ta zaro mici micin idanunta tamkar an kwantali Wata tace "kam bala'i da masifa, me kake nufi mal, wai kanaso kace min wnn uban kayan Hajara za a kaiwa da sunan gara?", yace "Eh Rabii, kayan garar Hajara ne", Maama tayi wani murmushin takaici tace "wasa ma knn, nan da kake gani na ba karen hauka ne ya cijeni da zan zauna inaji ina gani a Webi kayan nan akaiwa Hajara ba, idan kai da matarka kun makance to ni garau nake, muna fama da yar Hausa Mai da yaji da tuwan dawa shine za a kwaso yar gwamnati da abincin kwali a kaiwa yar so ko, ni ban taSa ganin inda ake haka ba wllh, ai wnn ?arawa mai kuWi ?arfi ne, ce muku akay babu abinci a gidan nata ne, koda yake ashe baku je kunga gidan ?an yankan kan ba..", Baba yace "sai kuma kiyi, gara dai sai an kai mata, babu ruwana da cewar masu kuWi ne, mutuncin ?ata zan kare..", Maama ta fara fyace majina tana sharar kwalla don sosai maganar tayi mata ciwo tace "wllh Allah sai ya saka min nida ?a?ana yadda ake mana cin kashi a gidan nan...", Baba ya haWe rai yace "Da Hajara da su Maimuna duk Waya suke a wajena, idan kina ganin rashin adalci nake yi akan su to kwa kin yaudari kanki, dukka abinda na yiwa Hajara insha Allah irinsa zan maimaita idan Allah ya kawo lokacin auren su Maimuna" da haka ya barta a wajen ya matsa kusa da Wakin Umma ya kirata, Umma ta amsa ta fito tace "gani mal", duk tana jin abinda ya faru daga Waki, Baba yace "Jamilah ce zata amso kayan za?in ko?", Umma tace "Eh, in Allah ya yarda ranar juma'a za a kawo", yace "yawwa gobe knn, zuwa ranar asabar ko lahadi sai a kai mata garar ta", Umma tace "toh Allah ya nuna mana da rai da lfy, Allah ya saka da alkhairy", yace "Ameen" ya fita daga gidan, Nabilah da take jefa Wan wake ta Wago kai ta dubi Maama tace "dan Allah Maama ki ringa ragawa Babanmu, nifa yanzu na zama ?ar ba ruwana wllh, idan ma bai mana irin na Hajara ba ai Allah na gani..", Maama ta rausayar da kai tace "idan bai muku ba ni zan muku da yardar Allah, kuma sai Allah ya kawo muku mazaje wanda suka kere dan yankan kan da waccar shegiyar ta aura, ai tin yanzu ma na fara gani tinda Alhaj Win Maimuna a Habuja yake, kinga kuwa ai yanada kuWi". Umma na komawa Waki tayi dialing numbern Anty Jamilah, tana Wagawa bayan sun gaisa Umma tace "Jamilah ya maganar mai dubulan da alkakin nan ne..?, da ?arfe nawa zata bayar goben..?", Anty Jamilah tace "da safe tace wajen ?arfe goma", Umma tace "tom, ga su shinkafa da taliyar har an kawo, kin san mal da karfin hali tinda yaji cewa ba a jerawa Hajara kayan Waki ba ya dage akan sai an mata gara, yace bazai bari mutumcin ?arsa ya zube ba ace ba a kaita da ko tsinke ba, kuWin kayan Wakinta da aka siyar dasu yayi amfani wajen siyayyar garar snn kuma yace ragowar nata ne", Anty Jamilah tace "Alhmdllh, Allah ya saka da alkhairy, ai hakan shine dai dai wllh", Umma tace "wai ya ?ar taki kuwa? ni kam bana samun wayarta...", Anty Jamilah tace "nima haka Adda, ashe ma tana gidan su mijin, da naji bana samunta a waya shine na kira numbern wacca nake zaton kwanwar mother in law dinta ce wacca na amsa a wajenki ranar da muka dubota a hospital, shine fa take gayamin cewa ai Hajar na gidan surkanta", Umma tace "tofa ashe haka akay", daga haka sukay sallama.

&Da daddare da misalin tara da rabi, da Wan sauri Nurain yake sakkowa daga stairs ya zura right hand dinsa a pocket na dark brown sweat pant dake jikinsa, left hand din kuma yana shafa tsakiyar cikakkiyar sumar kansa, hanyar part din Abba ya nufa, ya murWa door handle na great room din kafin ya shiga da sallama, ya cire soft room slippers dinsa ya ?arasa ciki, har zai zauna kan carpet Abba ya nuna masa sofa don haka ya zauna a sofar, Mami ta gama zubawa Abba Moringa tea ta mi?a masa, ya amsa yana murmushi yace "thank you..", tace "ur welcome dear..", Mami ta Wago sukay ido huWu da Nurain, Wauke kanta tayi ta tashi ta shiga bedroom din Abba, Abba ya Wauki tean yayi sipping, sip uku yayi snn ya ajiye Mug din, ya rage volume din TV, Abba ya dubi Nurain da yake jiran kiran da ake masa yace "ya project din Mamana tace ta turo maka zaka duba mata...?", Nurain yace "Yeah she try", Abba ya gyaWa kai yace "good", after like 5secs Abba ya nisa yace "Uthmaan kasan me yasa na kiraka nan..?", Nurain dai kawai kallon Abba yake ya girgiza kai yace "A'a..", Abba yace "lokacin da Allah ya yiwa first wife dina rasuwa the mother of Sakeena, Sakeena was just 3months old lokacin da mamanta ta rasu, duk wanda yaga Sakeena sai yaji tausayinta sosai, dangin mahaifiyarta sun so su amsheta su ri?eta ni kuma nace bazan basu ba sbd tana Webemin kewar mahaifiyarta, a koda yaushe Sakeena na wajena sai idan zan fita aiki ne nake kaita wajen Hajiya idan na taso kuma na Wakkota mu koma gida,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login