Showing 1 words to 3000 words out of 252707 words

Chapter 1 - HAJAR COMPLETE NOVELS By Nafisa Yusuf Nagoda.doc

??ࡱ?>?? +????????????? ?
?
? ?
?
???????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????

 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?Root Entry???????? ?F
WordDocument?????)0Table????????
Data
???????????????????? P?BO)KSKS??)?????????ppmmmm=Q??)m??????????$U?*pmm??mmmm?1?Q1?Q?1Q??mQ 
=؛? HAJAR =؛?
by Nafeesah Yusuf Nagoda....
'?
A.K.A
~~(Feenerh_feeche)~~

BISMILLAH..

Dukkan godiya ga Allah ma Waukakin sarki da ya bani ikon fara rubuta wannan littafi, kuma ina ro?onsa ya bani ikon hattamashi lafiya, Wumbin gaisuwa zuwa ga mahaifiyata Haj Anty, My sisto Hajiya kema ina mi?o gaisuwa, my little sister Mancy and my little brother Aliyu kuma na gaisheku da gudummuwar ku wajen disturbing Wina idan ina update, my fans kuma bazan manta daku ba a duk inda kuke Feenerh_feeche na gaisheku.

Let's connect....
_Facebook account @ Feenerh feeche
_Facebook page @ Feenerh feeche Novels
_Facebook group @ Feenerh feeche Novels
_Arewabooks @Feenerhfeeche02

~~~~~~

{1..}
wane mahalukin ne da yake lungun ?unshi a unguwar Dala bai san gidan gini ba, aiko unguwar ka shigo sai ka san gidan gini ballanta ?an unguwa, gida ne wanda yayi fice yayi shura a fannin hargitsi da rashin zaman lafiya, hakan ya samo asaline daga iyalan gidan da suka kasance ?an bala'i da jaraba, Magidancin gidan da ya kasance wani soloSiyo matansa biyu suke juyasa tamkar waina a tanda yadda sukaga dama, Allah ya azurtasa da ?a?a mata har guda biyar da maza uku, matarsa ta farko ?a?anta biyar ta biyun kuma guda uku, kullum a gidan gini sai anyi hatsaniya tsakanin matan gidan domin tamkar suna ganin hajin junansu, kwata-kwata basa jituwa kullum cikin tashin hankali suke, ?a?ansu mata ko wacce ta shigewa uwarta, wataran idan faWa ya kacame har saita kai ga ma?ota suna shigowa rabasu saboda wataran har dambe suke idan cacar baki tayi zafii, tin ma?ota na shigowa rabasu har ta kai ga an watsar dasu ana barinsu suyi faWansu iya iyawarsu su rabu dan kansu, kai wataran idan abu yayi tsamari har sai an raunata wasu, idan akai wannan gagarumin dambe haka gidan yake yin kaca kaca, filin tsakar gidan da ko daSe babu sai burjin ?asa ya koma tamkar gidan mahaukata da shirgin da akai jefe-jefe da doke-doke wajen dambe, haka Magidancin nan zai shiga tsakaninsu yana ?o?arin rabasu amma faWa ya?i ?arewa daga matan har ?a?an nasa basa saduda sai ya yanke jiki ya faWi wanda a sanadin haka ya haWu da hawan jini, Malam Adamu mai gini shine magidancin wannan Wan bala'in gida. da matansa biyu ta farko Rabi'atu wacca ake kira Maama saita biyu Fatima wacca ake kira Umma.

&Wani irin gyatsine take tana hura Wan siririn hancinta ta fito tsakar gidan da yake duk cakwalkwali saboda ruwan da aka she?a daren jiya, hannuta ri?e da brush dinta da ta matso tooth paste akai, can wajen da suke tara ruwa cikin manyan tukanen ?arfe irin wanda ake abincin gidan biki ta dosa, ta ajiye brush din hannunta akan wata murguWaWWiyar kujera, ta Wauki buta ta buWe tukunya Waya ta kantami ruwa ta wuce hanyar banWaki dake cikin wani lungu da wata siririyar kwata wacca ta Sulla har cikin banWakin tayi waje, ?ofar banWakin ta langa-langa ta bubbuga, daga banWakin aka yi mata gyaran murya, a hasale tace "koma waye aciki yayi sauri ya fito a matse nake!!!", wajen minti biyar tana jira amma ba a buWe ?ofar banWakin ba, ta sake bugawa da ?arfi tace "wai wace shegiyar ce aciki ne??, dalla malama ki fito", daga cikin banWakin aka ja wani dogon tsaki, a hasale ta banka ?ofar daman bata da sakata bare mukulli, turo ?ofar kawai ake sai a tokareta da wani mulmulen dutse da yake cikin banWakin, Maimuna da take cikin banWakin ri?e da buta a hannu ta kalli Hajar sama da ?asa ta daka tsaki ta fito daga ciki, daman ta gama amfani da bayin amma da ta ji Hajar tana jiranta shine ta?i fitowa, Hajar ta karkaWa kai ta dubeta tace "zaki sani ne??" ta shiga bayin tayi uzirinta ta fito, ta tsugunna gaban rariya tayi brush ta wanke fuskarta, ta mi?e ta shiga Wakin umma wacca itace mahaifiyarta, umma da take zaune kan darduna tana irga cinikin kulelen da tayi jiya da yamma tace "makaranta zaki tafi Hajara?, toh wane zai auno min wake ya siyo min manja?", Hajar ta buWe wardrobe Win da ta gama fatattakewa gata wata old modern gaba Waya ?ofofinta sun cire saidai a jingine su, ta zaro ironed uniform Winta tace "toh bari na shirya saina je na auno miki waken", umma tace "dama ha?ura kikai da zuwa makarantar nan gashi kin makara kuma anyi ruwan sama nasan ajinku ma ya cika da ruwa", Hajar tace "A'a nidaii umma zani kinsan shirye-shiryen jarabawa muke, yau za ai mana thumb print wanda za muyi amfani dashi wajen rubuta NECO", Umma ta lalo kuWi ta mi?a mata tace "wake kwano Waya sai manja rabin kwalba", Hajar ta karSi kuWin ta ajiye kan shirgin ?ullin kaya tace "ita Sabra ba zata makarantar ba??", Umma tace "Eh babu inda zata gaskiya, makarantarsu tafi taku lalacewa ko taje ma nasan dawowa zatai aii duk ranar da akai ruwa ba ayi", Hajar tace "tom", umma ta ?ulle ragowar kuWinta a haSar zani ta fita, Hajar ta janyo uniform Winta ta saka wanda sukay mata kyau duk da cewa ba wasu kayan ado bane, ta Wauki kuWin ta Wakko slipers dinta a bayan ?ofa ta saka ta fita tsakar gida, umma ta gani tana wanke gwangwanayen kulele can bakin rariya, suka haWa ido da Maimuna da take faman haska madubi a fuskarta tana mulka wani sabulu, Hajar tace "Banza mai bleeching", umma ta juya ta daka mata harara ta nuna mata ?ofa tace "akul zoki fita aiken da nayi miki", Maimuna ta Waga murya tace "uwar kice mai bleeching shiyasa ta haifeki fara", Maimuna ta cigaba da shafe fuskarta da take tamkar ta larabawa amma ?afar nan da hannu ba?i ?irin sai kace tayi dilke da gawayi, Sa'adatu ce ta fito daga Wakin Maama itama dai fuskar nan taci bleeching daidai gwargwado tace "wai me naji mara kunyar yarinyar nan take faWa miki ne??", Maimuna tace "aina gwaSa mata maganar da ta dace da ita shegiya nunar rana", Nabila ma ta fito daga Waki tace "aii ni haushi kike bani Maimuna, ki zauna kina takun sa?a da waccan ?ar tatsitsiyar yarinyar har tana gwaSa miki magana", Sa'adatu ta dungurewa Maimuna kai tace "shashasha kawai" ta koma Waki, umma duk tana jinsu bata ce musu komai ba kawai wankin gwangwanayenta take, Nabila ta Wauki buta ta shiga bayi, Maimuna ta cigaba da Washe fuska da sabulu. Hajar tana fita daga gida ta kama hanyar shagon iliya mai awo, duk arean shine mai awon da yake fitowa da wuri, wani Wan madaidaicin shago ne da ake siyar da kayan awo na masarufi da dai sauran ?an tarkace, wasu maza ne a bakin shagon Waya yana kan benci ya kara rediyo a kunnensa Wayan kuma yana Wura manja a kwalba a kan wani tebur da yayi da?al-Wa?al da mai da ?ura, Hajar ta tsaya a bakin shagon tace "salamu alaikum", mai Wura manjan wanda shine mai shagon wato iliya yace "wa'alaikumus salam", Hajar tace "mal iliya a bani wake kwano Waya manja rabin kwalba", iliya ya shiga shago ya auno wake ya fito waje ya zuba manja a farar leda ya haWesu a babbar leWa ya mi?a mata, ta ciro kuWinsa ta basa tace "Allah yasa dai manjan mai kyaune, ba irin na jiya mai warin mushe ba", iliya yace "idan an samu wata matsalar a dawomin da kayana saina baku kuWinku", ?asa ?asa Hajar tace "uhmm sai kace gaske.." ta kama hanya zata bar bakin shagon mutumin da yake kan benci ya cire rediyon kunnensa yace "ke hajara akwai kulele??", ta juya tace "ka cire ke Win mana ka bar hajara, babu kulele sai anjima", ya kaWa kai irin ai halinki ne yace "toh idan an gama ki kawomin ta Wari biyu nan sai na baki kuWin", ta yamutsa fuska tace "saidai ka tura yaro ya siyo maka" tayi gaba abunta, iliya ya koma kan benci ya zauna yace "ita da sau?i fa", munkaila yace "inafa sau?i, kasan ma?otanmu ne mun haWa katanga dasu ta fuskar baya, wallahi shekaran jiya suna hatsaniyar nan tasu da suka saba iyalina ta shiga yi musu sulhu, wannan ja'irar yarinyar ce ta kwaWa mata bokitin ?arfe a hannu tazo kwaWawa ?ar uwarta. harfa saida ta fitar mata da jini", iliya yace "aii mal Adamu bashi da iko da gidansa ace bazaka iya tsawatarwa matanka ba, abinda sukaga dama za suyi, ni ban taSa ganin lusarin namiji kamarsa ba, sai kace wanda suka shanyesa", munkaila yace "ai a shanye yake, kai kana ganin wannan mutumin kasan shanyayye ne ainun, yanzu fa ?a?an nan nasa shafe-shafen nan na zamani suke, ni jiya da naga wata ma acikinsu ban ganeta ba saida naga tukubar hancin", iliya ya kyalkyale da dariya yace "ai jiya wata tazo nan siyan shinkafa wallahi data mi?omin kuWi na Wauka wani ne ya zuro hannu ta bayanta ya mi?omin kudin ba ita ba", munkaila yace "Allah dai ya kyauta ya shirya mana zuri'a". iliya ya tashi zai bawa wani yaro da yazo aunar masara, munkaila ya kara rediyonsa a kunne ya lumshe ido yana karkaWa kai. Hajar na komawa gida ta tarar da umma tana tashin wuta a kurfotu, ta wuce Waki ta ajiye aiken ta fito ta kalli umma tace "ni zan tafi bazan daWe ba inayin thumb print zan dawo", umma tace "bazaki jira na dama kunu ba??, haka zaki tafi makarantar ciki kwalam", Hajar ta kalli gawayin da umma take ?o?arin cinna masa wuta taga akwai lema ajikinsa tace "idan na dawo nasha, bari na gaida Baba". ta shiga Wakin Baba da ?ar sallama, yana zaune gefen katifa yana jan wata doguwar cazbaha, ta tsugunna tace "barka da safiya Baba, an tashi lafiya??", Baba ya dubeta da wani irin yanayi, duk cikin ?a?ansa mata yafi jinta a zuciyarsa, yace "lafiya lau Hajara, makaranta za a tafi?", tace "eh Baba, zanje ayi mana thumb print na jarabawar NECO da zamu zana", yace "Toh Allah ya bada sa'a" ya ciro Wari biyu a aljihun wandonsa ya mi?a mata, ta sa hannu biyu ta ?arba tace "nagode Allah ya saka da alkhairy". ta mi?e ta fita, a bakin ?ofa suka kusan yin karo da Mu'azzam wanda shine babban yayanta da suka haWa uwa da uba Waya, Mu'azzam ya Salla mata harara ya haWe rai yace "bani hanya..", da sauri ta matsa masa hanya ya shiga ita kuma ta kama hanyar soro.

&A hankali yake murza steering Win Wumemiyar motar da yake driving, wayarsa da take gefensa ta hau tsuwwa, looking at the road ya kai hannu yayi picking ya kara a kunne yace "Salam Mami, har yanzu dai ban gane street Win ba, i thought Dala kika ce koh??", ya Wanyi shiru sai kuma yace "ohk nagane, inajin nabi wrong way ne", wayar ya katse ya fara juya motar a Wan tsukun layin da kwaltarsa ta gama ragargajewa, da yake expert ne wajen lailaya mota ya juyata cikin sau?i ya koma Wayan side Win kwarSaSSen titin, yana fara tafiya wani mai mashin ya yanko gabansa tamkar an wurgosa, da sauri ya Wauke kan motar yayi gefe da ita, motar ta faWa cikin wani ruwan kwatami na ruwan sama da kwatocin gidajen mutane da suka Sulla cikinsa, ruwan kwatar da jar ?asa ya feshe Hajar da take tsaye a bakin wajen tana jiran napep, gaba Waya uniform Winta suka Saci da jar ?asa, ga wani wari da ruwan yake na kwata, Hajar tabi jikinta da kallo ta hangame baki, a matu?ar zafafe ta dubi motar da tayi mata wannan aika aikar lokacin da mutumin ciki ya buWe ?ofar driver......
'?

=؛? HAJAR=؛?
by Feenerh_feeche

{2...}
Fitowa yayi daga motar yana hangen mai mashin Win da ya shigo masa har ya bulale tsukun layin da haya?i ya fece, cikakken gashin kansa ya shafa yana ?an?ance ido sai kuma ya kalli motar tasa da take cikin kwatami tsamo-tsamo, gefenta ya karkace wajen driver ne kawai bai shiga kwatamin ba, tsirarun mutanen da akai abun a kan idansu suka taso, Hajar da zuciyarta take tafasa tana kallon uniform Winta da bazasu taSa tafiyuwa a wajenta a haka ba, wani ?ululu ne ya tsaya mata, what the heck isn't he going to apologise, a hankali ta taka tana tsantsamin kanta ta isa gabansa inda yake ?o?arin buWe motar zai shiga, ya kai hannu kenan zai buWe ?ofar motar ta ri?e handle Win tace "malam ba kaga abinda kayi bane??", da wani irin salo ta juya fararen idonta ta nuna masa uniform Win jikinta dasu, kallo Waya tak yayi mata yace "ohk sorry it was not my fault", up and down ta kallesa ta tsugunna ta kwarfo ruwan dattin a duka hannayenta ta shaSune masa a farar Tshirt Win jikinsa, ta kama hanya fagam-fagam zata bar wajen, wani mutum ne ya kalleta yace "amma wallahi ke dai baki da kirki..", ta juya ta kallesa sai taga da Wan girmansa zai iya kaiwa sa'an babanta hakan yasa ta mayar da asalin abin tayi niyyar fada tace "oh shi bakuga rashin kirkinsa da ya feshe ni da kwatami ba", mutumin yace "amma ai ba sa'an ki bane kuma ya baki hakuri yarinya", cike da tsiwa Hajar tace "banga zan iya hakura ba gaskiya" tayi gaba abunta, wani ne ya taso yace "au baka ganeta ba aii ?ar gidan gini ce zata iya aikata abinda yafi haka ma". kawai gaban Tshirt Win jikinsa yabi da kallo lokacin da kunnensa yaji (au baka ganeta ba, ai ?ar gidan gini ce zata aikata abinda yafi haka ma). Hajar na shiga gida tin daga soro ta rushe da kuka, ita duk wannan tsiwar ta ta kuka baya mata wuya, daga zarar zuciyarta ta Saci tom sai tayi kuka take jin daWi, da Sa'adatu ta fara cin karo hannunta ri?e da bokitin ruwa da kwandon soso da sabulu zata shiga bayi, Sa'adatu ta daka wani uban tsaki tace "da murya sai kace ta gardawa an cikawa mutane gidan uba", Hajar ta sharce hawayen idonta tace "saiki nuna wanda ya diro daga sama jahila" ta ?arasa shiga ciki, Sa'adatu ta mulmulo wata ashariya tace "ni yarinyar nan zata kira jahila" ta dire bokitin da kwandon ta biyota da gudu, kafin ma ta cimmata harta shige Wakin umma, Mu'azzam da yake bakin ?ofa ya kalleta sama da ?asa yace "ina makarantar??", Hajar tace "ba ina tsaye a bakin titi ina jiran napep ba wani mai mota ya fesa min cakwalkwali", ta cigaba da kukanta, Mu'azzam yace "A'a kinga malama ki rufewa mutane baki, ki canza wasu kayan ki tafi makaranta", Hajar na shesshe?ar Kuka tace "toh aii banida wasu uniform Win kuma ance kowa da kayan makaranta za ai masa online registration", umma tace "Mu'azzam dan Allah daure ka rakata makarantar nan tinda kace yau bazaka aiki ba, ke kuma maza kije ki Wauraye jikinki kizo ki canza kaya", Mu'azzam yace "karki Satamin lokaci ina ?ofar gida", ya fita daga Wakin, Hajar ta wuce bakin rariya ta cire hijab Win jikinta ta Webi ruwa a buta ta fara Wauraye inda cakwalkwali ya Sata ta, cikin sanWa Sa'adatu ta taho ta cakumo wuyanta tace "yanzu sai ki gayamin wace ce jahilar??", Hajar tace "dalla malama sake ni..", Sa'adatu tace "an?i a sake kin, me zaki iya??", Maama ta yaye labule ta le?o tace "naWi ?ar iska, ki canza mata kamanni", Sa'adatu ta sake ma?ure wuyan Hajar har saida idonta suka firfito amma baki nan bai mutu ba cewa take "Allah ya isa, muguwa azzaluma mai bleeching", mai bleeching Win nan shi yafi ?onawa Sa'adatu rai don haka ta kamata da kokawa, Hajar da take ganin bazata Sata lokacinta a nan wajen ba ta daddage ta danna mata wani mugun cizo a damtse, Sa'adatu da zafin cizo ya ratsa mata kwakwalwa da sauri ta saketa ta lailayo ashar tana kallon damtsenta da ha?oran Hajar suka fito ainun, cizon ya shigeta sosai domin ?iris ya rage wajen bai fashe ba domin kuwa jeka huda yayi, Hajar ta manna aguje ta shige Wakin umma tana waiwayen Sa'adatu.

&Sanye take cikin fararen kaya riga da wando sai wani Wan ?aramin hijab V-shape, ta Wora kimono a saman kayan, hannunta ri?e da mug mai Wauke da coffee, a hankali take tafiya har tazo ?ofar office Win tayi knocking a hankali, daga ciki akace "come in..", ta murWa handle ta shiga ciki da ?ar sallama, secretary ta amsa tace "welcome Nurse Ruqayyah..", tace "yawwa Halima Doctor bai ?araso ba ne??", Halima tace "yes i think he is on his way", Ruqayyah tace "Ohk, bari na jirasa aciki", Halima tace "ohk then", Ruqayyah ta shiga babban office Win da ya gama ?awatuwa, ga wani ?amshi da sanyin Ac da yake tashi a cikinsa, Mug Win hannunta ta ajiye kan table ta Wauki hoton da yake dirke a gefen table Win wanda ya haska fuskar wani mutum wanda yake sanye da lab coat ya rataya stethoscope a wuyansa, hannayensa zube a pocket ga kuma wani murmushi da yake shimfiWe a fuskarsa, Ruqayyah ta zauna kan chair still looking at the picture, 20mins passed amma bata gaji da kallon picturen ba, ?ofa aka murWa mutumin da yake cikin picturen ne ya shigo, hannunsa ri?e da briefcase, a hankali ya mayar da ?ofar ya ?araso ciki yana kallon Ruqayyah da take ri?e da hotonsa, briefcase Win ya ajiye akan table sannan ya cire lab coat din jikinsa ya ratayeta ajikin kujerar zamansa kana ya zauna, ajiyar zuciya ya sauke yana kallonta yace "good morning babe.. tinda yau ba za a gaishen ba", ta kallesa a fakaice ta zumSuro baki tace "Dr yau mesa ka makara?, kuma nasan kanada surgery scheduled yau at 12pm", with a soft smile on his face yace "really akan surgery nan kika damu ko kuma mai yin surgeryn?", wani irin cuno baki tayi tace "of course not i care for the surgery not the surgeon", murmushin da ya bayyana fararen ha?oransa yayi yace "My coffee ko yau rowa za ai min?", ta mayar da hoton mazauninsa ta Wauki Mug Win da ta ajiye ta mi?a masa tace "Here", ya amsa yace "thanks", one sip yayi ya ajiye yace "ya huce aii", tace "tinda ka makara yau mai sanyi zaka sha, now tell me, mene ya makarar da kai?", yace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login