Showing 21001 words to 24000 words out of 298130 words

Chapter 8 - KURKUKUN KADDARA (TAKUN KARSHE) BY BOSS BATURE.doc

faWo"? Da?yar Ya ?are maganar, ganin wani mugun kallo da chief owais Ya watsa mashi, nan take Ya haWiye yawu ya soma ?an kame kame
Rai amatu?ar 6ace yace"malam, fuce kabar Wakin nan, meye ala?arka damu da har zaka katse Prime minister Yana magana, wannan abune daya shafi dangin mu bana ka ba" Tsabar mamakin kalaman Owais Yasa kowan nan su Ya dube shi, musamman Hajiya saratu ta muzanta da jin cin mutuncin da Owais Yayima mijinta.

Babu kunya Pravin Yace"Owais kai har yanzu yarone, duk abunda zaka fada min ba zan ji haushi ba, Ina yi maka uziri, kuma magana da kaga Inayi don in kare dangin ku ne saboda halaccin da kuka Yi min....." Azafafe Owais Ya yun?ura Ya mi?e tsaye, Yana naWe hannun rigarshi tamkar Mayun wacin zaki haka Ya tunkari Pravin, An rasa wa zai dakatar dashi, kafin Owais ya ?araso Pravin yayi saurin nufar ?ofa ya buWe ya fuce yana huci Ya maida ?ofa Ya datse.

Juyawa owais yayi ya koma inda ya tashi ya zauna.

Da buWar bakin Prime minister sai cewa yayi"My son ka yi abunda Ya dace" wannan maganar Ta hateem ta ta6a zuciyar Hajiya saratu
Ranta a6ace tace"yaya hateem, kana goya mashi baya saboda Yaci mutuncin mijina"?

Prime minister bai tanka mata ba, bai kuma Wago da ido Ya kalle ta ba. Hakan Ya ?ara 6ata mata rai, harara tadinga jefawa Owais Ko kallo bata ishe shi ba, baima san tana yi ba.

Shi dai baba Obie, Ya zubawa sarautar Allah ido, don wannan fadan Yafi ?arfin shi.
His excellency abdul Razak ne Yace"Owais, Kai muke sauraro muna son jin ?arin bayani dangane da Yaron daya rikiWa da kuma Yarinyar dake atare da shi"

Kusan mintuna da Yin maganar abdul Razak Kafin Ya furta"Marayune su goma sha Waya nake ru?o a hannuna, dukansu agidana suke da zama, a ?ar?ashin kulawata," Iya abunda Ya furta mashi kenan
"A ina ka tsince su"? Shiru yayi bai bashi amsa ba Har saida His excellency abdul Razak Ya maimaita mashi maganar a tunaninshi kobai ji mai yace bane
"Sojojin america ne suka tsince su A daji, shine suka dam?a case dinsu a hukumarmu, saboda Yaran sun faWi cewa Su ?an Nigeria ne, Waya daga cikin Yaran ma akwai mahaifinta mun same shi, muna zargin masuyin garkuwa ne suka sace su daga Ahlin su, shi kuma yaron aljanune suka shige shi a dajin sune suke canza mashi halitta, wannan shine Iya abunda nasani dangane da su" atakaice Ya ?are bayanin.
Gyaran murya senate Lafeef Yayi kafin Ya soma magana
"Mun riga da mun Yanke hukunci, Bamu bu?atar Yaran su ci gaba da zama a estate dinmu! Saboda Lafiyar mahaifinmu, sannan mun yanke ala?arka da su, shi kuma prime minister zai koma canada adai dai date din da aka bashi umarnin komawa, don ba zamu lamunci gangancinku na son taimako Ya jefa rayuwar Ahlinmu cikin matsala ba, don ni har Yanzu ban yarda da Yaran ba, tunkafin ma in gansu Hankalina bai kwanta da su ba, tayaya za'a tsinci Yara adaji sannan akawo su estate dinmu? Meyasa su sojojin american basu ru?e su ba a hannunsu ba? Saboda sunsan ba alkhairi bane shiyasa suka manna maku su" fuskar shi babu annuri yayi maganar.
Hankalin prime Minister Ba ?aramin tashi yayi ba Jin abunda suka ce, kasancewar shi mutunne mai biyayya ga yayyan sa ko kara suka ajiye mashi bai iya ?etare wa, mutun Waya ne zai Iya dakatar dasu wato mahaifinsu sai dai ga dukkan alamu shima Yana goyan bayan hukuncin da suka Yanke,
Muryarshi asanyaye ya furta"kada kuyi min haka, saboda ku nazo ?asar nan a ?alla nakusa shekara ban samu damar zuwa gida ba, Yanzu Idan na koma bansan ranar dawowa ba, Baba ka sanya baki a maganar nan"

His excellency Deen dake zaune Yace"Idan saboda mu kazo ?asar nan, kada ka damu, ka tafi kawai mu zamu zo inda kake, idan ma takama duk sati zamu Iya shigowa Canada kasan bamu da matsalar abun hawa" ya faWa yana ?ara jaddada mashi"zamu Iya barin aikinmu mu Wauki hutu saboda kai, munyi maka al?awarin hakan, zamanka a ?asartamu ne bamu yarda da shi ba, don ba zamu yi gangancin da zaka cutu ba har wani abun Ya same ka, Idan ka manta wanene kai bari in tuna maka, prime minister na ?asar canada" du?ar da kanshi ?asa yai hawaye tuni sun cika idanuwanshi, bakomai yake jimawa ba face Yaron daya ?wallafa ran shi, yasan idan harya haura ?afa yabar ?asar nan da wuya su sake haWuwa, watakil ma daya daga cikinsu yabar duniyar batare da sun yi tozali da juna ba.

Jikin Chief owais yayi sanyi la?was, hankalinshi na akan prime minister, shi kadai Yasan damuwarshi

His excellency abdul Razak ya numfasa kafin ya Waura da cewa"kai kuma Owais, ba zamu hana Ka Yin aikin ka ba, sai dai babu zancen Yara su cigaba da zama agidan nan, ka kaisu gidan marayu ka haWa su da wadanda zasu cigaba da rainonsu"

Takaici Ya hana Chief Owais furta masu komai, gaba Wayansu hankalinsu ba akwance Yake ba.

A hankali Baba Obie Yake kallon fuskar Prime minister data Chief owais, ga dukkan alamu Ya fahince su sai dai Yana jin tsoron wani abu Ya same su ta silar taimakon da suke Yi, shiyasa bai dakatar dasu senate lateef ba.

"Baba, dan Allah kace wani abu, nasan zaka fahimce ni, wallahi Ina ?aunar Yaron, baka ganshi ba Yana kama dani da Nazli, komai namu iri Waya kamar ni na haife shi" muryarshi tamkar zai fashe da kuka yayi maganar, basu ta6a ganin raunin prime minister ba sai Yau da Allah Ya jarabce shi da ?aunar wani bare

"Hateem! Wannan bai shafe mu ba, kowani Wan adam yana da masu kama dashi a duniyarnan, shi kuma mugun mutun ba'a gane shi a suffar shi yakan shiga cikin mutanan da yake hari yayi rayuwa dasu na tsawon lokaci Yana kyautata masu rana Waya yake tarwatsa su da makircin shi, na fadi wannan maganar ne don ni har yanzu ban yarda da yaron ba, dashi da sauran ?an uwanshi, mutanan da aka tsinta a daji, wama yasani ko ?a'?an aljanu ne kuka dauko mana" senate Lateef ne ya faWa Yana watsa hannayen shi.

A hankali prime minister Ya zura hannu cikin aljihu ya Wauko wayarshi, wadda tun safe rabon shi da ita, a gida yabarta gudun kada atakura mashi da kiraye kirayen waya, sai Wazu da suka shiga gidan Ya kar6eta daga hannun gimbiya mujeedat.
Layin Sharufudeen Ya dannawa Kira, bugu uku Yai picking,
"Ina agida, dan Allah kazo, idan ba haka ba komai zai Iya faruwa"
On the other hand muryar sharafuddeen Ta amsa mashi da toh, gani nan zuwa, ka kula min da kanka" amsa mashi yai da toh kafin yai rejecting kiran
"Meye amfanin Kiran Sharafudden da kayi? Dakai dashi duka a ?ar?ashin ikon mu kuke, mune agaba daku" cikin nuna isa senate lateef Ya furta maganar
Cikin sanyin murya Hateem Yace"nasan da hakan Yaya, amma shi zai Iya fahimtar zuciyata fiye da kowa, kuma zai kwantar min da hankalina"

"Kana nufin mu bamu Iya kwantar maka da hankalinka? Kodan saboda shine sha?i?inka"? A harzu?e senate Lateef Ya furta maganar
Da sauri Baba Obie Yai masu gyaran murya gudun kada su fara Yi mashi ?an ubanci abun da Ya tsana arayuwarshi.

Gaba Waya Hankalinsu ya dawo kanshi"Ya Isa Haka! ya Isa, bana son nasake Jin wani Ya furta magana acikin ku" Shiru sukayi batare da wani ya kuma cewa Uffan ba
"Baba abincin fa Yana hucewa, Yakamata Kaci" hajiya saratu ce tayi maganar cikin nuna damuwarta
Kallon Owais yayi nan take Ya fahimci me Yake nufi
Hannu owais Ya sanya cikin plate din da hajiya saratu ta zuba mashi abinci

Ya soma Webowa Yana bashi abaki Yana ci,
Hakan Ya ?ara 6ata mata rai, wato ita ta bashi abinci da hannunta Ya?i Ci sai Owais daya fi ?auna, shi ya za6a ya bashi abinci
Bazata juri kallon su ba, mi?ewa tayi tana fadin"Baba Allah Ya ?ara Lafiya, Ni zan wuce Waki" bata jira amsar da zai bata ba tayi saurin fucewa daga Wakin.
Senate latef ma ranshi ya sosu, duk irin rashin Wa'ar da Owais Yayi ma Pravin baba obie bai dakatar da shi ba, after that Ya sanya shi bashi abinci abaki, bayan Hajiya saratu itace tafara Yun?urin bashi amma Ya?i kar6a, ba tun yau ba ya saba nuna banbanci akan Sauran Jikokinshi da Owais, Hatta Ya'yan Hateem Yafi Ji da su akan nasu me hakan ke nufi"? Aranshi ya sa?a maganar

(Nidai nace na shiga uku, Kada afara ?an uba A family Obinna, Rikicin zai haWe mana)

Yayin da chief Owais Yake ba baba Obie abinci abaki, Ya tsare shi da ido Yana bin shi da kallon so da ?auna kamar zai haWiye shi, Lemu mai sanyi ya zuba mashi a cup Ya mi?a mashi, Ya sanya hannu Ya kar6a Yana sha, har cikin ranshi Yaji dadin hakan aduk lokacin da ranshi ya 6aci indai Owais Yana atare dashi wani irin sanyi ne yake ratsa zuciyarshi tuni yake neman damuwar Ya rasata.

In a respectful voice Chief Ya soma yi mashi magana, ta yadda babu mai iya jin su.

"Kai kadai ne zaka Iya fahimtata, saboda kai ka raine ni tun ina ?aramina, aduk lokacin da na sanya buri akan abunda nakeson cimmawa kaine kake ?arfafa min gwiwa don ganin nakai ga matakin nasara, babana kada ka bari wannan karan in faWi ?asa, yakamata ka sanya baki awannan maganar, kasan bazan ta6a kawo wani abu da zai cutar dakai ba, Ha??ina ne in kareka daga dukkan wani abun farmaki, yaran nan mutanene kamar kowa, basu da niyar cutar da kowa, saida na zurfafa bincike akansu na tabbatar da hakan tukunna na kawosu cikin gidana, bazan Iya yin nesa da su ba, Kuma bazan Iya dakatar da hukuncin da iyayena suka zartarba, amma kai zaka Iya dakatar da su,' cikin tausasa harshe Ya ?are maganar tare da ru?o hannayen baba obie acikin nashi, Ya ru?e su sosai.

"Baba, Yaran nan basu da kowa, suna bu?atar wadanda zasu tallafi rayuwar su, nasani ba dole saini zan taimake su ba amma na riga dana daukarwa kaina al?awarin bazan ta6a rabuwa dasu ba, A yau ina so ka nuna min ?aunar da kake Yi min, da goyan bayan da kake bani, baba kada ka bari arabani da yaran nan ko a tursasamin akan in fitar da su daga gidana......." yanayin yadda owais yake yi mashi maganar yayi matu?ar karya mashi zuciya, tuni jikinshi yayi sanyi la?was, launin idanuwanshi har sun Wan canza kala.

Shi kadai Yake jin me owais Yake Fadi mashi, sauran saidai su bi da ido, prime minister dai tunda ya dukar da kanshi kasa bai ?ara dagowa ba, shi kadai Yasan abunda ke damun shi, zuciyarshi tafarfasa take yi tamkar ana rurata da garwashin wuta, Aranshi ya ayyana koda zai bar ?asar bazai daina bin diddigin rayuwar yaron ba, bazai ta6a bari Ya wulakanta ba.

Lumshe ido Obie Yai a hankali ya ware su kan fuskar Owais
"Zanyi tunani akai" atakaice Ya furta mashi maganar, ajiyar zuciya chief owais ya sauke, ya riga dayasan ?aunar da yake mashi bazai Iya jurar 6acin ranshi ba
"Allah ya ?ara maka lafiya kakana, da anjima kafin ka kwanta bacci zanyi maka tausarnan dana saba yi maka duk idan nazo nigeria, nasan zaka ji daWi"
Dariya baba Obie Yai har hakoransa suka bayyana fafare ?yal da su
"Owais ka iya fadanci, kasan duk wata hanya da zaka faranta min, Allah yabarmin kai jikana" amsa mashi yai da Ameen.

daga haka basu ?ara Yin magana ba, sai dai kallon juna da sukeyi jefi jefi, su sanate lateef sun zama ?an kallo, kamar hotuna haka suka zauna zugudun suna kallon su.

Bayan wani lokaci Jiniyar Motoci ta karaWe Estate din, nan take ransu Ya basu cewar Mai girma sharafudeen ne Ya ?araso gidan, tun abakin entry hall din shiga falo, Security details dinshi suka dakata da take mashi baya kamar yadda ya basu umarni, shi kadai Ya shiga Gidan Cikin shiga ta alfarma tsadaddiyar shaddace a jikinshi launin kore, duk Inda Ya gifta masu aikin gidan a gaggauce suke russinawa su gaishe dashi kamar zasuyi mashi sujjada, A main falo din gidan Yaci karo da sheikh Imam tare da Taj zaune saman Royal sofa, Hankalinsu kwance suke tattauna fira atsakaninsu, sunyi jiran ganin mutanan gidan shiru basu fito ba har sun fara tunanin kodai babu lafiyane? Musamman lokacin da pravin ya fito daga dakin baba obie ko kallo basu ishe shi ba, har kallonsu yayi amma ya?i tanka masu, hakan ya sosa zucuyarsu, haka itama hajiya saratu tazo ta wuce ta falon bata bi takansu ba, har ?wara su twins sun gaishe da sheikh Imam, suka kuma gaida Taj kafin suka wuce.

Zuwan sharafudeen Obinna, Ya faranta masu rai, tunkafin Ya ?araso garesu Yake Fadin"wa nake gani kamar babana Imam malik," mi?ewa Imam yayi ya nufe shi suka rungume juna kafin suka raba jikinsu
"Ashe rai kanga Rai? Baba Imam s???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ai yau zansa ka a idona? Gaskiya nayi fushi" Ya faWa Yana haWe fuskarshi
Dafe kafaWarshi sheikh Imam Yayi"Masha Allah, Sharafuddeen Bana ?asar, shiyasa baka ganina akai kai, amma yanzu tunda nazo in sha Allah zan dinga shigowa Villa muna gaisawa'
Sharafudeen na murmushi Yace"Idan ma bakazo ba, Ni zanzo har inda kake, wallahi nayi farin cikin ganinka, tun yaushe kazo ?asar"
Shiekh Imam Yace"Yau da sassafe Nayi sammakon shigowa ?asar, saboda kiran da Wan uwanka yayi min"

"Masha Allah, Ina fata komai lafiya"
Sheikh Imam Yace"lafiyalou, Ga abokin Aikin Owais Ku gaisa da shi" Ya faWa Yana nuna mashi tajudeen dake azaune, kamar ya sanshi haka Ya nufe shi da fara'a, da sauri Taj Ya mi?e suka rungume juna, ha?i?a yasha ruwan mamaki, bai ta6a ganin mutane masu ru?e da babban mu?ami da suke da sau?in kai irin Hateem da Wan uwansa sharafuddeen, yajima yana mamaki da al'ajabinsu, kowa nasu ne basu Wauki duniya da zafi ba.

Raba jikinsu yayi daga na juna"yalla6ai sannu da zuwa, Ina wuni, Ya hidima da jama'a, ubangiji Allah ya taimaka"
"ameen mutumina, Ina fata na same ka Lafiya"da mamaki Taj yake kallonshi jin ya kira shi da sunan mutumina kamar yadda yaji Wazu Hateem Ya kira shi da sunan
Ganin alamun ruWu akan fuskarshi yasa mai girman sharafudeen cewa"Owais Ya fada min komai dangane dakai, ganinka ne kawai ban ta6a yi ba, nasan zakayi mamaki dana gane ka ba tare dana tambaya ba" ya faWa yana sakar mashi murmushi, shima taj din murmushin yayi har cikin ranshi ya ?ara ?aunar Chief owais.
"Babu isasshen lokaci, In sha Allah zan samu time din da zamu tattauna dakai" ya fada Yana bubbuga kafaWar taj da hannunshi.
"Toh Yalla6ai, nagode sosai" kallon shiekh Imam yai"baba mu shiga daga Ciki" yai maganar tare da ru?o hannunshi suka nufi part din baba obie,

Zama taj yayi akan sofa, fuskarshi Wauke da murmushi, Ji yake tamkar ya zuba ruwa a kasa yasha, acikin ranshi ya furta"Allah nagode maka da haWani da mutanan kirki acikin rayuwata"
Wayarshi Ya zaro daga aljihu ya soma tunanin Kiran Big guy don Yaji awani hali su Unaisah suke aciki sun ci abinci ko kuwa.
Kiran na shiga big guy yayi picking
"Ya mutumina kana Ina ne? Na dawo gidan na taras baku nan"
"Mun shigo gidan baba Obie ne mu dukanmu muna anan"
"Okey, Ina fata komai na tafiya yadda yakamata"
"Taya zan sani, nifa ka ganni nan a falo, Ina zaman jiran fitowarsu, Allah yasa dai mu ji alkhairi, don kuwa naga wannan ba'indiyan da kake bani labari sai mazurai yake yi, ko gaishe mu bai yi ba"
Sautin dariyar big guy ne Ya karaWe kunnuwanshi
"Itama wannan matar, mai kama da su chief owais ta fito tagan mu bata gaishe damu ba"
"Dama ya za'ae ta gaishe dakai, taga ba?uwar fuska, matar da bata sakar ma bare fuska, sai dai shi sheikh Imam din ne dai bata kyautaba tun da aminin baban su ne, wata'?ilma bata ganku bane shiyasa bata gaishe da shi ba"
Boss yace"nima nayi tunanin hakan"
"Shi kuma wannan gabjejen ?aton dangin su kirishna, kabarshi kawai, mutumin banza, baida mutunci, shi da yazo cin arzi?i yayi kane kane a dangi" da zolaya big guy yayi maganar, taj yayi dariya cike da nishaWi yake sauraron shi.

"Very soon zamu yi mashi korar kare daga family din, tun da ba gidan ubansa bane" acewar big guy gaba Wayansu suka tuntsire da dariya
Bayan sun tsagaita Boss man Yace"dama na kirane don inji lafiyar ?a'?ana"
"Kai dai fadi gaskiya, Ko dai ka Kira Kaji Lafiyar Jarin ka, Ifrituwar Yarinya wlh Wazu data la6e a bayan labule, naso ace ka bari chief Ya sha?i wuyanta, Yasin sai tayi jinya a gadon asibiti, Yarinya sai ?iriniya kamar ansanya mata battery" fashewa taj yayi da dariya
"Cin mutuncin Ya isa haka, Na lura ba?in ciki kake Yi da ita shiyasa ka sanya mata ido, Ni dai yanzu fada min suna ina.

Sai da Ya Mula Yasha Iska tukunna Yace"Sun ci sun ?oshi, kowannansu Ya koma dakinsa, harma sunyi wanka sun canza sutura, Na rakasu dakin Danish sun ganshi, Yanzu haka kowan nan su Ya koma dakin shi,"

Ajiyar zuciya Boss man ya sauke"Alhamdulillah, Naji dadin jin hakan, inataso in tambaye ka ka tuntu6i 6angarensu Salsabeel"?

"Bakasan meya faru ba" nan fa big guy ya kwashe duk abunda Ya faru Ya sanar dashi, hankalinshi Ya dan tashi
"Bawan Allah jazz, abu baiyi dadi ba, Allah ya bashi Lafiya, In sha Allah zamu fidda lokaci muje duba shi, Har Yanzu suna a asibitin ne"?

" Na kira Major Waya Ya fada min cewa An sallame su, Jikinshi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login