Showing 129001 words to 132000 words out of 298130 words

Chapter 44 - KURKUKUN KADDARA (TAKUN KARSHE) BY BOSS BATURE.doc

ne? Waye ya ta6a min ke yanzun nan in Waura Wamarar yin ya?i da shi"! ta faWa babu wasa akan fuskarta, Cikin shesshekar kuka zahra tace"a.. Aunty Aneeleerh zayn! Na shiga uku! Hajiya saratu ta haWa ni da masifa, ashe lokacin da ta turamin sakon nan tace min in zabi daya daga cikinsu nayi kuskuran rubuta sunan zayn a maimakon zaid shine fa ta haWa ni dashi, aunty aneelerh baki ji kalaman daya furta min ba.........' a tsanake tafara bata labarin abun da ya faru jiya bayan da hajiya saratu ta kira ta.

Fitowa tai daga hall din tana ta faman yan kalle kalle can ta hango hajiya saratu tsaye abakin motarta, Cikin girmamawa ta ?arasa daga gefen ta, bayan sun ?ara gaisawa zahra tace "mommy gani" murmushi hajiya saratu tasakar mata tare da ruko hannunta acikin nata"mu shiga ciki, inaga zaifi muyi magana a tsanake" ta fada tare da buWe murfin backseat, bayan sun shiga taja kofa ta rufe, Zahra sai faman bin cikin motar take da kallo, saboda haduwarta ga sanyi a.c dake ratsa fatar mutun

Shiru sukayi babu mai magana, Hankalin hajiya saratu na akan wayar hannunta da take Wan daddanawa,

"Zahra," ta ambaci sunanta, da sauri ta amsa da na'am
"Ina fata kin nishadantu da dinner din nan," tana dan murmushi ta jinjina kanta tare da cewa"Eh mommy, Alhamdulillah, naji dadin gayyatana da kikayi, I can't thank you enough"

Murmushin dattako hajiya saratu tayi"kada ki damu, kin cancanta ne, ni kaina najima ina mamakin yadda kika kwanta min araina, saboda ba kowa nake mu'amala da shi ba, ina da wuyar sha'ani zahra " ta faWa ba tare da ta Wago da idonta dake akan screen in wayarta ba.

Zahra sai faman sakin murmushi takeyi taji dadin maganar da hajiya saratu ta furta mata.

"Kinsan meyasa na kira ki"!

"A'a"

"Idan ba zaki manta ba, Kwanakin baya na tura maki hoton twins dina, har nace idan na baki za6i wanne kike so acikin su, ashe kin bani amsa ban samu damar duba sakon ba sai daga baya na gani"

Dakatawa tayi da yin maganar, zahra nata kallon gefen fuskarta burinta ta karasa maganar nata, sai dai ta fahinci bata cika son magana ba.
ba ta zaci zata dago ba, aikuwa karaf suka hada ido cikin na juna, wani irin kwar jini tayi ma zahra da sauri ta dukar dakanta kasa tana wasa da yatsun hannunta

Daura wayar tayi akan laps dinta, ta ruko hannun zahra acikin nata, kafin ta soma magana
"Zahra na yarda dake, Kamar yadda na fada maki kin kwanta min araina, kuma na yaba da hankalin ki, kyawawan Wabi'unki da halayen ki sune suka sa har nafara kwadayin ki zama wani bangare na rayuwana, Ina nufin ina so ki zama surukata zahra" cikin kwantar da murya hajiya saratu take yi mata magana tamkar ba aunty masifatu ba
Zahra jikinta yayi wani irin sanyi, ga wani annurin farin ciki daya lullu6eta duk da tana jin fargaban wanda za'a haWa ta da shi Yaki amincewa...

"Naji kinyi shiru bakice komai ba, Ni bazan maki dole ba, kada kiji nauyn fada min abunda ke aranki, saboda nima bazan bari ki auri wanda zuciyarki bata so ba"

Numfasawa zahra tayi fuskarta da Wan murmushi ????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? tace"mommy wa zai ki jinin ki? Ni ay abun farin cikine agare ni, saboda nima kin kwanta min araina, bazan 6oye maki ba, nayi mamakin tayin da kikayi min, saboda ni aganina ban kaiba mommy, ya'yanki sunfi karfi na, sannan inajin fargaban wanda zaki haWani dashi yakini, tun da bamusan juna ba....." ta ?arasa maganar idanunta cike tab da kwallar murna.

Jinjina kai hajiya saratu tayi kafin ta furta"kada wannan ya dameki zahra, bana so na sake jin kin furta matsayin ki bai kai ba, ni na za6e ki don haka kada kiji komai, ?a'?ana kuma ni nake iko da su, abunda nakeso shi zasuyi don haka ki kwantar da hankalin ki, wadannan hawayen da nake gani ki share su" ta fada tare da zaro mata hanky ta mika mata, yatsun hannun zahra na kerma ta kar6a tafara shaye hawayen ta.
Wayarta ta dauka tare da dannama zayn kira, bayan yai picking cike da bada umarni tace"ka sameni abakin hall yanzun nan Ina jiranka"! Bata jira amsar shi ba tai rejecting call din, tare da mayar da dubanta ga zahra
"Nayi mashi magana yanzu zaizo sai ku fahimci juna" cikin sanyin murya ta amsa mata da toh, sam bata kawo ma ranta zata ga akasin zaben da tayi ba.

Kusan mintuna Kafin akayi knocking, murmushi hajiya saratu ta saki, tare da kallon zahra"ki gyara nutsuwarki, Yanzu zai shigo ku gana da juna" amsa mata tayi da toh, bayan fitar hajiya saratu, da sauri zahra ta bude purse dinta ta curo hanky ta goge fuskarta, ta zaro yar hodarta ta barbaWa, hada jan baki ta murza ma la66anta, Jin motsin buWe motar yasa tayi saurin maida kayan kwalliyar cikin purse din.


tun daga kan kamshin turarensa daya daki hancinta tafara jin wani irin fargaba, a wani slow ya zauna kyakkyawar fuskar nan tashi a haWe Yaci mur, ko kallon inda take baiyi ba balle ma ya nuna alamar yaga mutun a motar, da farko bata gane wanene ba acikin su,

Dakyar ta furta"ina wuni"

Banza yayi da ita, saima ya zaro wayarsa yaci gaba da dannata, nan take ranta ya bata cewar ZAYN ne, Hankalinta a matukar tashe take duban gefen fuskarshi, mutun har mutun ga kyau sai dai babu mutunci ko miskala zarratin, gaba Waya tarasa sukuninta tun kan aje ko'ina harta fara danasani, mamakinta tayaya akai zayn ya kasance wanda za'a hada ta dashi bayan zaid ne ta canka ba shi ba? Ko dai hajiya saratu tayi kuskure ne..."

Tayi zurfi a tunaninta muryarshi ta ratsa kunnanta"wani tsautsayine yakai ki amincewa da zancen haWani dake? Kinsan wanene ni"? Adabarbace tace a'a amma in ranka ya 6aci kayi hakuri ni ma bada son raina ba.."
"Meyasa tun farko bakice mata baki sona ba"! A kausashe ya furta maganar,

Muryarta na rawa tace"saboda bazan iyaba"

"Wallahi idan kina son zaman lafiya ki janye zancen hadani dake da gaggawa idan ba haka ba ciwon zuciyane zaiyi silar mutuwarki, saboda ni nan da kike gani na ba mutumin kirki bane Wan iska ne ni, sannan bani da mutunci .." Ras taji gabanta ya fadi, tunda yafara magana bai kalle ba, baima san wacece

wani irin wahalallan yawu ta haWiya, amatukar rude take kallon shi jikinta na kerma

"Nasan bazaki so ya'yanki su yi rashin dacen uba ba, shiyasa nake gargadinki, tun kafin kiyi danasani mara amfani, ke in banda ma haWama da rashin sanin ciwon kai ina ke ina Zayn pravin obinna? Nayi maki kama da sa'ar auranki? Wai ke yar wacece ma"?

Hawayen dake taruwa a cikin idanunta tuni sun fara wanke fuskarta
Hankalin shi kwance yaci gaba da cewa"Ni nasan ba hakanan kika kyale mommy ba, Allah kadai Yasan me kika kulla da har ta amince zata hada ni da ke, idan ma kwaWayin abun duniyane ya rufe maki ido to ki fadamin nawa kikeso tun daga miliyan biyar har abun da yai sama zan baki kije kija jari ki rufawa kanki asiri...." sautin shesshekar kukanta ne ya cika masa kunnansa, a zafafe ya juya da niyar ya dauke ta da mari kamar an ruke hannunsa ya dakata cak Yana huci idanunsa akan fuskar zahra da hawaye ya gama wanke ta, bakomai ne yaja hankalin shi ba face kyawun fuskarta ba laifi tana da sura dai dai wadaidai saidai baya jin zai iya kula macen da bata kai matsayinsa ba
Sassauta muryarshi yayi"ke, yi min shiru in ba haka ba zan 6ata maki rai"

yatsun hannunta na kerma ta toshe bakinta, sam takasa kallon cikin idanunshi gashi ya matso kusa da ita kamshin turarensa duk Ya gama kashe mata jikinta
"Idan kinason zaman lafiyar, Kije ki fada mata, baki sona banyi maki ba"muryarya da shesshekar kuka tace"kayi hakuri amma ni bazan iyaba, saboda ina ganin girmanta, sai dai kai ka je ka faWa mata" dakyar ta kare maganar tana faman jan numfashi

"Tausayinki nake ji bana so kiyi danasani, wallahi bani da mutunci, ni banma shirya yin aure ba, saboda baya agabana, Ni nafi sha'awar inyi sharholiya ta son raina" ya fada yana shafa sajen fuskarsa" yanzu ke kin yarda ki auri dan iska mai mu'amala da matan banza"? Ya fada yana cizon lips dinsa da masifa
Jinjina mashi kai tayi alamar eh, ita kanta batasan tayi hakan ba, batasan ya akai zuciyarta take jin kaunarsa ba, a maimakon taji haushin kalamansa.

Dafe kanshi yai da hannu Waya kafin ya furta"look, Idan burgeki nakeyi naji zan baki kaina, amma ki janye batun nan, saboda ni ban shirya ma aure ba, ko auran zanyi bazan auri wadda batakai aji na ba, bana so ki jefa rayuwarki cikin hatsari, kada kiga kamar ina lallashinki mommyn mu kaifi Wayace idan ta furta magana babu wanda ya isa ya dakatar da ita, shiyasa nake lalla6aki saboda ke kadaice zaki canza ra'ayinta" zahra dake ta faman yin shesshekar kuka muryarta na rawa tace"har abada bazan iya tunkararta da maganar nan ba sai dai kai kaje ka fada mata..." bata ?are maganar ba ya daka mata tsawar data firgitar da ita
Nuna ta yayi da yatsan hannun shi"Share hawayen kan fuskarki, ki tashi muje ki fada mata baki sona banyi maki ba" muryarta kasa kasa tace"ay na fada maka bazan iyaba..." bata kare maganar ba, taji ya haWe bakinsa acikin nata, wani irin bugu zuciyarta tayi mata, gaba Waya takasa tabuka komai, har sai da Ya gama abunda zaiyi kafin ya zame harshensa, Yai saurin zuge glass din motar Ya tofar da yawun bakinsa.

tsabar wulakanci Ya zari hanky yana kara goge bakinsa kamar wanda ya ta6a najasa, rushewa tayi da matsanancin kuka ganin irin wulakancin da yai mata, abunda yafi ?ona mata rai sanya mata harshe da yai abakinta, arayuwarta ta tsani namijin da ba muharraminta ba ya ta6a ta,
Tsawa yakuma daka mata tuni ta shiga taitayinta.

"KaWan kika gani, wannan so mun ta6ine idan har baki janye kudirinki akaina ba, zan cigaba da amfani dake ne" ya faWa yana mai kara jaddada mata
"Ki share hawayen nan, Ki tashi muje ki faWa mata kinjanye" muryarta na kerma ta amsa mashi da toh, shu'umin murmushin gefen fuska yasaki, dama yasan zata amince ko dan saboda abinda yai mata don ya fahinci ba yar hannu bace tana da kamun kai shiyasa ya tsorata ta.

Hanky ta zaro ta share hawayen fuskarta, sannan ta daidaita nutsuwarta, kafin ta buWe motar, ta fito shima ya fito ta Wayan bangaren suka nufi hajiya saratu dake atsaye can nesa da su.

Tunkafin su karaso ta nufosu, fuskarta da fara'a tace"Son, Ina fata kun sasanta kanku"!
Nunata zayn yai"ki fada mata abun da kika gaya min acikin mota" amsa mashi tayi da toh kafin ta kalli hajiya saratu zuciyarta cike fal da tsoronsa ta ce"Mun gama magana dashi, Kuma mun fahimci juna" a gigice zayn yake kallon zahra jin abunda tace, zuciyarsa ba karamar hasala tayi ba, bai ta6a tsammanin yarinyar zatay taurin kai ba.

"Zahra kin tabbata yayi maki? Amma meyasa naga idanunki sunyi ja"? Da sauri zahra tace"kaina ne keyi min ciwo, har fada masa nayi, shine yace yakamata na tafi gida na huta, zamuyi magana awaya..." da tsantsar mamaki zayn yake kallonta, gashi ba halin Ya karyatata, don ya fahimci ta kama zuciyar mommynsu.

"Naji dadi my son, dama nasan bazaka ?i tayin da nayi maka ba, da ace zaid ne ba lallai ya amince ba saboda shi na daddynsa ne kai kuma nawa ne, hakika yau ka faranta raina my son, Allah yayi maka albarka, zahra kema nagode maki sosai da kika aminta da tayina in sha Allah ba zakuyi danasani ba, Ina da tabbacin hakan, Ta fada tare da janyo zayn da zahra tayi huggin dinsu tana Wan bubbuga bayansu, sai faman farin ciki takeyi yayin da su kuma zuciyoyin su suke a kuntacce da bakin ciki.

"Zayn ko zaka kaita, Gida"? Ta fada bayan ta raba su daga jikinta, da sauri zahra tace"mommy kin manta nazo da mota dina"
"Oh eh hakane, na shafa'a, Muje son mu rakata ta tafi gida" atare da zayn suka raka zahra bakin mota bayan ta shiga ta zauna, hajiya saratu tace"surukata, Anya zaki iya driving dinnan kuwa? Ko dai zayn yakai ki" wani irin mugun kallo zayn ya watsama zahra da sauri tace"a'a mommy, wallahi zan iya, ay ba sosai nake jin ciwon kan ba"

"Toh zahra Ki kula min da kanki sannan ki gaishe min da mutanan gidan"

"In sha Allah ngde ssae"

Harara hajiya saratu ta watsa ma zayn"kai bazakai mata bankwanan ba, ahaka zakuyi auren" yana faman yamutsa fuska yace"bye, sai mun yi waya" aran shi ya furta "zakiyi danasani,"

Bayan ta baro estate din har ta hau kan titi tana driving, zuciyarta bata daina tariyo mata kalaman zayn ba.

Uban tagumi aneelerh ta zabga da hannu Waya, tana kallon zahara data kammala bata labari

"Zahra kinyi kuskure wlh, meyasa baki Wauki shawararshi ba kin fada mata baki son shi? Zahra ina guje maki auran mutun mara kunya irin shi! Kowace uwa burinta ta sama ma ya'yanta uba nagari wanda zasu koyi da shi su kuma yi alfahari da shi ba irin zayn ba, sam bai dace dake ba" zuciyarta ajagule tafada, kwata kwata zayn bai kwanta mata aranta ba, tun kafin ma ta ganshi.


Zahra Tana shesshekar kuka ta ruko hannunta"ki tayani da addu'a, ita nafi bukata, Aunty aneeleeh bawai nakasa fada mata bane, Ina son shi ne"
Jinjina kai aneeleeh tayi"inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un! Shikenan, zan tayaki da addu'a Idan alkhairi ne shi agare ki Allah Ya tabbatar mana dashi, idan kuma akasin hakan zan roki Allah Ya shiga tsakaninku, bayan haka dole su mami suji maganar nan"

kwantar mata da hankali aneelerh tacigaba dayi saida komai ya lafa tukunna aneelerh tace"Ina alkwarina? Kince zaki Waukar min hotunan dinner in gani, Jiya da su na kwana araina, ganin kin kwaso gajiyane yasa ban takura maki ba"

Murmushi zahra tasaki tunawa da Unaisah, yarinyar data kwanta mata aran ta.

"Aunty aneeelerh, akwai labari, zaki sha kanun labarai, " ta fada tare da janye baby juanid dake langwa6e ajikinta, kamar maijin bacci Yai shiru Yanata sauraronsu.

Gado Ta nufa ta dauko purse dinta ta curo wayarta donta nuna ma aneeleeh hotunan da ta dauka tare da unaisah

Kwatsam wayar ta fara ringing, da sauri tayi picking ganin sunan abie
Barka da safiya abie ina kwana"?
"Lafiyou, zahra, Ina aneeleeh ne"? Da sauri tace gatanan adakina

"Okey ki fada mata, ?awarta ta turo min da sako ta layina, ta zo ta same ni a daki ina jiranta!" amsa mashi tayi da toh bayan ya kashe kiran ta dubu Aneelerh dake kallon ta, cike da son jin me abie Ya faWa mata.


"Abie ne ya kira, yace in faWa maki Kawarki ta tura mashi da sako ta layin shi kije ki same shi adaki"

Da alamun mamaki Aneeleerh ta furta"?awata kuma? Anya kuwa abie ya karanta sakon dai dai? In bahaka ba ni wata ?awace gare ni da zan bata layin abie"

"Aunty Aneelerh kije kawai ki gani, bamusan menene aka turo ba" amsawa tayi da toh a hanzarce ta mike ta bar junaid adakin.

Ruko hannun shi zahra tayi"zonan In nuna maka hotunan dinner,"
Gefen gado ta zauna tare da daura shi kan laps dinta, ta buWe gallery tana nuna mashi hotunansu, lokacin data buWe hoton Unaisah, wuff Junaid Ya fusge wayar daga hannunta Yana fadin"Angel! angel! angel"! Har saida gaban zahra Ya fadi, a matukar rude take kallon shi ba tare data fahimci me yake nufi ba.


*SALSABEEL=ث?*

Zaune Yake kan sofa hannun shi ruke da wayar shi, Har ya kammala shiryawa, sai faman duba agogo Yake yi, Har ya fara gajiya da jiran su, Wagowa yai tare da kallon su, suna a zaune tsakar falon suna cin abinci, mutun Waya ce ke babu acikin su, Khadeeja dake acan cikin toilet tana wanka, a kalla ta shafe kusan awa Waya da rabi har yanzu bata fito ba, gashi har yan uwan ta sun kammala shiyawa.

"Dan Allah ku yi sauri ku ?arasa, kun ga har karfe sha biyu ta buga" amsa mashi sukayi da toh
"Yaya salsabeel, Khadeeja fa? Har yanzu bata fito ba, ko ban da ita zamu tafi" rubeena ce tayi maganar.


"Bansan ya zanyi da ita ba, so take ta 6ata mana lokaci, bari naje na dubo ta" ya fada tare da mi?ewa Ya nufi upstairs.

"Wallahi Dama mu tafi mubar ta a gida, kada ta mana hauka, tun da ya salsabeel Yace wurin gasar kyau zamu je kuma in muka ci za'a bamu kyautar wani abu" acewar hibba.

rubeena na murmushi tace"ni zan cinye ma gasar saboda nafi ku kyau" harara hawwa ta galla mata"a haka din? Dubi kumatunki, kuma ay cewa yai sun fi son mace doguwa mai gashi, mara jiki, me dogon hanci" daure fuska rubina tayi rai a6ace tace"wlh indai bani zanci ba sai dai kowa ya rasa" ta fada tare dakai hannu ta dauki robar zuma ta dinga watsa masu akan rigunansu, azabure suka mike suna faman zare idanunsu ganin ta 6ata wankan su.

"Wallahi baki isa ba, Saina rama mana" sarah ce ta fada da sauri ta fisge zumar ta matsa mata a jikin rigarta, fashewa tayi da kuka tana fadin wayyo Allah ya salsabeel sun 6ata min kayana, shikenan ni bazanci gasar kyau ba, zu?unnawa tayi gaban kayan abincin tana haki ta dauki coke da niygar ta watsa masu, dam?o hannunta Hawwa tayi nan fa faWa ya kacame a tsakaninsu, daga wadda za'aja ja ma gashin kai sai wadda aka ca6e ma kwalliyar fuskarta, Mubeen dake a zaune yana kallon su sai faman tikar dariya yakeyi

Duk wannan budurin da sukeyi salsabeel bai sani ba, Yana atsaye bakin kofar toilet din dakin su khadeeja, ba irin bugun kofar da baiyi mata ba akan ta fito, amma ta?i ko tanka mashi.

Rai a6ace yace"wallahi idan kika bari nasa kafa nabar dakin nan sai dai ki zauna agida, Babu inda zaki je" muryarta da shesshekar kuka tace"wayyo Allah ya salsabeel ba kaine kace zamuje gasar kyau ba, shine fa nakeso in koma fara" waro ido waje yai jin soki burutsin ta, cike da takaici ya furta"Baki da hankali ne? Tayaya za'ai ki koma fara? Waya fada maki sai farare suke cin gasar kyau? to bari ki ji in fada maki bakake sune suka fi lashe


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login