Showing 249001 words to 252000 words out of 298130 words

Chapter 84 - KURKUKUN KADDARA (TAKUN KARSHE) BY BOSS BATURE.doc

zauna tana fuskantar su..
"Lafiyalou auta,"

"Barka da safiya auntyna, kin tashi lafiya? murmushi tasakar ma chief da fara'a tace"lafiyalou my son, ina fata kaima haka ya aiki"?
Yace"Alhamdulillah"

"I'm sorry na shiga busy, kwanaki nace zan shiga asibiti in duba patient din nan banje ba, Ya jikin nata? Ya kuma babynta Unaisah ina fata suna lafiya"? cikin kulawa tayi maganar tana duban shi.

"She's feeling better, almost 3 days da sallamarta, unaisah tana lafiya"

"Masha Allah, naji dadin jin hakan"

tun da suka fara magana baba obie ke kallonsu cike da mamakin taya akai suka sasanta tsakaninsu, shi dai yasan tsakanin jikallan nasa da autarsa ba sa jituwa.

gaba Waya sun fahimci kallon da yakeyi masu, murmushin gefen fuska ya saki har cikin ranshi yaji dadin shiryawarsu"tun yaushe kuka sulhunta tsakaninku bansani ba"? Ya faWa yana kallon su
Murmushin dattako hajiya saratu tayi batare data furta kalma ba, chief ne ya bashi amsa da cewa"me ka gani baba?
Nuna su yayi da yatsan shi"ga abunan azahiri, ku fadamin wani Wan arzikin ne ya hadamin kanku? Ni dai nasan baku jituwa"

tattausan murmushi sukayi
Hajiya saratu tace"Allah ne ya hada kanmu, dama can shaidan ne ya shiga tsakaninmu amma muna kaunar juna, ko ba haka ba my son" ta faWa tana kallon shi

"Hakane baba, kuma in sha Allah ba za'a kara jin kanmu ba" har cikin ranshi yaji dadin maganarsu, dama baya son sabanin da suke samu atsakaninsu.

"Alhamdulillah, naji dadi ubangiji Allah ya cigaba da hada mun kanku, Allah ya kara dankon zumunci atsakaninku, shi kuma shaidanin daya shiga tsakaninku Allah Ya kare mu daga sharrinsa"

A tare suka amsa mashi da ameen, kwata kwata baiyi masu maganar mara lafiyan dayaji sun ambata ba, hankalin shi ya karkata akan jituwar da suka samu.

Mi?ewa chief yayi da sauri baba obie yace"Grandson ina zuwa bamu gama yin breakfast ba"?


"I'm sorry, Grandpa. I'll come back later"

ya faWa tare da russinawa ya sumbaci forehead dinshi hajiya saratu dake kallonsu ba karamin burgeta sukayi ba, sabanin da da take jin haushi intaga baba obie da owais suna bama junansu kulawa kamar uba da da, abun yana 6ata mata rai saboda ita aganinta baya son twins saboda ubansu ba jinsinsu bane shiyasa yake nuna wariya tsakaninsu, abun da ta fahimta ayanzu owais yana matukar girmama baba obie biyayya yakeyi mashi sau da kafa dama ita zuciya tana son mai kyautata mata.


Tayi zurfi a tunaninta, muryar baba obie ta katseta, firgigit tayi tare da kallon shi, har chief ya fita daga dakin bata lura ba.

"Fada min meke damunki? Tun shigowarki na lura da yanayinki kamar bakya jindadi ko"? Gyara zama tayi, kafin ta fara kora mashi jawabi.

"Baba akan marwa ne! Naga ciwon nata yayi tsauri shine nace me zai hana amaida ita garinsu gaban iyayenta? Ita kanta zataso ta kasance a karkashin kulawarsu hankalinta sai yafi kwanciya, ba kamar nan ba, ba dangi iya bana baba, kuma kaga ciwon nan nata bana lafiya bane, zata iya goga ma wani...." fuskarta ayamutse tayi maganar, kamar irin ta damu da ita din nan.

Shiru baba obie yayi jim kafin yace"Auta, kin taba zuwa duba lafiyarta ne"? Waure fuska tayi
Murmushi yai"nayi mamakin jin maganarki, inace tin ranar farkon da ta fara lalurar baki kara le?awa ba, aranar ma guduwa kikayi daga dakin ko"? Ya faWa da zolaya, sunnar da kanta kasa tayi batare da tace komai ba.

"Meyasa zaki ce amaida marwa garinsu? Ko dan saboda lalurarta? Da can da take mana hidima bamu guje ta ba sai yanzu da Allah ya jarabce ta? Munyi mata adalci kuwa? Yamutsa fuska tayi"baba ka fahimce ni, nasani ba ita ta daura ma kanta ba, babu wanda yafi karfin Allah ya jarabce shi, amma ni dai aduba mana, saboda lalurarta su twins suka daina kwana gida, kasan su da kyankyami kuma abune da basu saba gani ba, shiyasa duk suka firgice, ni kaina hankalina ba akwance yake ba, wlh dakyar nake iya bacci agidan nan gani nake kamar nima abun zai shafe ni..." da mamaki baba obie ke kallonta, ta haWe rai ba annuri akan fuskarta, duk zaman nan da ake baisan cewa su twins sun bar gidan ba sai yanzu da yaji a bakinta ay da tuni yasa an dawo da su.


"Indai akansu twins ne zansa su dawo gida, amma marwa bazata koma gurin iyayenta ba, har sai ta samu lafiya, saboda anan ta samu lalurar, kuma anan zata samu warakarta in sha Allah, Ni ba zan bari mutuncina ya zube a idon jama'a ba, yarinya da lafiyarta ta fara aiki agidan nan sai kuma in maida ma iyayenta don amfaninta ya kare uhyum? Kiyi tunani mana, su kansu iyayenta ba za su ji dadi ba, su ga mun maida masu yarinyar su da nakasa a jikin ta.. "


Ran hajiya saratu ya 6aci muryarta tamkar zata fashe da kuka tace"baba ban taba neman abu agurinka kaki yi min ba, sai yau saboda kawai na nuna bana son zaman marwa agidan nan! Yakamta ka duba lamarin nan baba fisabilillahi saboda ita su twins sun kasa zama gidan nan, nima na rasa kwanciyar hankali, baba kafison farin cikin marwa akan namu kenan..." yunkurawa tayi zata mi?e da sauri ya dakatar ta ita"saratu koma ki zauna" zama tayi fuskarta ba fara'a...
Bottle water ya dauka me sanyi ya tsiyaya mata ruwa a cup ya mika mata, tana faman haWe rai ta kar6a ta kurbi ruwan sau uku kafin ta ajiye tana kallon shi.


Yayi shiru yana nazarin maganar ta, arayuwarshi baya son bacin ran ya'yan shi, sannan baya son duk wani abu da zai haifar da rashin kwanciyar hankali atsakaninsu, sai dai bayajin zai iya mayar da marwa garinsu ahaka batare da taji sauki ba, yanajin tausayin ta, bayan haka bazaiso mutuncin shi ya zube agurin iyayenta ba.

"Baba nasan me kake tunani, indai akan iyayenta ne, wlh daga mun basu kudi zasu ja baki suyi shiru, kaga sai suci gaba da yin jinyarta, ni nayi alkwarin zan dauki nauyin duk wani abu da za'a kashe gurin nema mata lafiya, ni kawai gidan ke banaso ta zauna" gauran numfashi yaja kafin ya dubeta"auta" tace"naam baba"
"Kada ki makara, ki tashi ki tafi aiki, zanyi tunani, in sha Allah idan na yanke shawara zan sanar dake" amsa mashi tayi da toh, kafin ta mike tayi mashi sallama ta fuce daga dakin.

__________________________________
'?

Lokaci Waya Zuciyarta ta fara bugawa da matsanancin ?arfi tamkar ana buga ganga, numfashinta ya fara fita cikin sauri, yayin da kirjinta ke harbawa yana sama da ?asa da kokarin jawo iska a cikin hunhunta, wani irin gumine ya fara tsasstsafowa ta cikin hudojin gashin jikin ta, zufa ta soma gangarowa ta cikin nannaWaWdiyar sumar kanta tamkar yayyafin ruwan sama jikinta ne ya fara kakkarwa, Yatsun kafafunta dana hannunta suka kama kerma, idanunta suna arufe gam ta matsesu, fatar kwarin idanunta sai kerma take sakamakon kwayar idanunta dake jujjuyawa, kokari take ta buWe idanunta takasa saboda raunin da sukayi, jikinta tamkar babu jini saboda rashin kuzari, ga wata matsiyaciyar kasala data daskarar da ita daga yunkurin da take yi na son farkawa, Allah kadai Yasan tsawon makonnin da ta dauka bata acikin hayyacin ta sakamakon duguwar sumar da tayi.

A kalla ta shafe awa cikin mayuwacin hali tana kokarin ?arfafa kanta donta samu damar buWe idanunta, ta ko'ina ba sau?i, jikinta tamkar an daddaure shi da igiyar kaca, sai faman?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? jijjiga jikin takeyi donta samu kwarin gwiwar tada kanta.

La66anta dake a bushe ?amas fatarsu ta faffashe hada busasshan Wigon jini, da ?yar ta iya moving dinsu ta furta"GABRIEL" kwata kwata sautin muryarta baya fita, cigaba da ambaton sunan tayi duk da radadin da makoshinta keyi mata mai azabar zafi, meyasa ta ambaci sunanshi? A karo na farko data dawo hayyacinta? Saboda shi ne aranta.


Lokaci Waya ba zato ba tsammani kwatsam tayi wani yunkuri da iya karfin ta na karshe ta daddage ta banbare kanta daga jikin abunda take a kwance tayi wata irin zabura ta mi?e zaune tana faman jan numfashi, sannu A hankali ta buWe idanunta wani irin duhune bakikkirin ya mamaye ganinta, bata ganin komai tamkar ta makance, batasan a ina take ba? Meya faruwa da ita? ta manta komai, kamar tayi loosing memory din ta, tayi matu?ar rudewa ta rikirkice tunaninta ya gushe, daddafe kanta tayi da tafukan hannayenta cikin rawar murya ta furta"A ina nake? wa ya kawo ni nan? Meya faru dani? Babu mai jina ne? Kuyi min magana bana ganin komai, ko dai na makance ne...." sautin muryarta baya fita dakyau.
Kamar ta fasa ihu haka take ji, saboda takasa gane meke faru da ita? A ina take.


A lokacin da batay tsammani ba, kwatsam ba zato ba tsammani, wani siririn haske ya kurdado ta saman gurin da take, Waro idanu waje tayi cikin tashin hankali da tsantsar rudani take kallon hasken, A hankali hasken ya fara mamaye Wakin har saida ya karaWe cikin sa tamkar da rana.

Idanunta suka washe, amatu?ar ruWe take kallon inda hasken ya fito ashe fitilune na saman ceilling din dakin, da sauri ta dubi inda take a zaune, Metal bed ne (gadon ?arfe) irin kirar zamanin da na kaka da kakanni, Gadon Yana da girma da tsayi, ga wata lumbutsetsiyar katifa tattausar gaske mai dadin zama hada matassan kai guda biyu, daga saman gadon Yana da rumfa hada labulaye a kewaye da shi, kamar irin gadon sarakuna

Gaba Waya ta ruWe ta rasa gane waya kawo ta dakin? Da sauri ta kalli kayan jikinta, farar riga ce shara shara kamar matacin kwakko, komai na jikinta ana gani, rigar tana da dogon hannu, tsayin ta bai wuci Iya gwiwar ta ba.

Sumar kanta kamar an kifa mata yayi, ta bushe ba gyara duk gashin ya yamutse, ?o?arin saukowa tayi daga kan gadon sai dai ta kasa saboda tsayinsa bata san ya zatay ba, matsawa tayi daga bakin gadon ta le?a ?asa cikin sa'a ta ga matakala irin ta bene mai hawa shida, numfashi ta Wan ja tare da sauke ajiyar zuciya, a hankali ta Waura ramammun kafafuwanta kan matalar farko ta yunwa zata mi?e aikuwa wani irin jiri ya kwashe ta saboda rashin kwarin jikinta gaba Waya ta kundumo ?asa timmm! ba karamin dakuwa tayi ba, amma saboda karfin hali da kwarin gwiwa irin nata ta daddage ta mi?e tana faman fitar da numfashi mai haki kamar wadda tasha uban gudu

mi?ewa tay tsaye tana kallon katafaren Wakin mai girman gaske, gado Waya ne aciki sai book shelve ma'ajiyar littattafai, da tsoffin akwatinan karfe daga gani tsohuwar ajiya ce, ga wardrobe mai girma ta jikin bango, wurga idanu tayi kan tukwanan kasa da ta gani girke a kasa, Waya saman Waya an jera su daurin Waurin sunyi sauro a jikin bangon da suke, hada kwaryaye rufe da faifan su, hada tukwanan furanni masu ban sha'awa daga gani koma wanene mamallakin Wakin ma'abocin son kayan laka ne ko kuma makerin su ne.

A hankali ta Wauke idanunta daga kan tukwanan ta bi bangon dakin da kallo, zanunnuka ta gani masu ban sha'awa, a hankali take tafiya tana nufar tsakar dakin tana cigaba da kallon abun mamaki da al'ajabi gami da rudani ita dai batasan waya kawota cikin shi ba! Ta manta komai.


tana cikin jujjuya idanu karaf ta hango Madubi zagayayye yana da mari?i dake ajiye kasa...takawa tayi cike da fargaba ta nufi madubin yayin da zuciyarta ke cigaba da harbawa da karfi da karfi..tsayawa tayi agaban madubin tana kallon fuskarta, ta tsorata da ganin ramar da tayi, kashin wuyanta ya kwambare kamar zai fasa fatarta, ziraran yatsun hannunta ta daura akan wuyan tana shafa kashin kafin ta motsa yatsun a hankali ta shafa fuskarta, manyan idanunta dara dara launin brown ta zare su tana bin kanta da kallo, tana iya hangen dukiyar fulaninta sun rame sun kanjame bayan ada ba haka take ba, tana da kira irin ta karfafan mata masu jini ajika amma yanzu ta rame ta bushe ta faWa kamar ba ita ba.

da zata iya tuna mummunan abunda ya faru da ita har zuciya zata iya hadiya ta mutu saboda tana da fusatacciyar zuciya, idan ta rikice babu mai iya sarrafa ta.

ta jima tana kallon kanta a cikin madubin, jiri jiri ta fara gani a idanunta da sauri ta dafe cikinta dake yi mata kukan yunwa ga wani kishin ruwa na fitar shari'a, makoshinta ya bushe ?amas ko yawun da zata hadiya ta samu relief din kishin babu shi abakinta.

juwa ce ta kwashe ta gaba Waya jikinta ya rinjayeta ta yanke jiki ta faWi ?asa a sume..


Cikin abunda baifi minti ashirin ba kacal, taji safkar ruwa mai sanyi kan fuskarta, dogon numfashi taja haWi da sauke ajiyar zuciya sam takasa ta6uka komai, ko yatsan hannunta bata iya motsawa saboda rashin kwarin jiki.

cikin mawuyacin hali ta Wan yi karfin halin buWe idanunta biji biji take kallon mutumin dake tsaye akanta batasan wanene ba.

Cikin disasshiyar murya ta furta"ruwa!ruwa!ruwan, zan sha! Kishi nake ji..." dakyar sautin muryarta ke fita tana tsaka da sambatu taji an kanga mata wani abu kamar bakin gorar ruwa saitin bakin ta, wani irin sanyine ya ratsa zuciyarta, lokacin da ruwan ya ji?e makoshinta nan da nan ta fara kwankwaWarshi makoshinta har wani sauti yake badawa kwat kwat...!!

"Ki sha A hankali kada ki sha?e" cikin kunnanta ta tsinkayi muryar dattijuwar dake mata magana.

Sai dai kwata kwata bata fahimtarta, tafi bu?atar ruwan fiye da komai ayanzu kamar rayuwarta ta dogara akan shi.

saida tasha mai isarta kafin ta fara numfarfasawa tana haki, wata irin nutsuwace ta shige ta, hatta bugun zuciyarta da fitar numfashinta sun daidaita, ganinta dawo daidai sannu a hankali take kallon fuskar tsohuwar da ta tallabe kanta akan kirjinta, hannunta yana ru?e da gorar ruwa, tana asanye da alkyabba fara sol mai hula, tsohuwace tukuf fuskarta duk tamoji tamoji, gashin kanta fari fat hurhura ta mamaye ko'ina na gashin, hatta gashin jagirarta fari ne fat, daga ganin tsohuwar tayi gwagwarmaya a duniya, tsufanta bai boye kyawunta ba, bakowa bace wannan face Tsohuwa

*KHALA* dattijuwar arzi?i, fara mai farar aniya, tsohuwa mai zuciyar imani, macace mai tausayi da jinkan mutane, abun da zai baka mamaki tana Waya daga cikin Elders na kurkukun ?addara sune masu fada aji, tana da ?arfin iko, amma meyasa ta fita daban acikin suI ?

Gabriella ta tsareta da idanu tana binta da kallon kurulla, fuskarta da alamun ruWani

kamar yadda take kallonta haka itama tsohuwa khala take kallon ta.

la66anta na kerma ta furta"wacece ke? Wa ya kawo ni nan? Meya faru da ni? Ki fadamin ina son sani" shiru tsohuwar tayi nata ce mata komai ba.


"Kinyi shiru baki ce mun komai ba, meyasa kike kallona? Wacece ke?....." ta faWa arude tana tararraba idanu.

Tattausan murmushi ne ya bayyana akan fuskar dattijuwar, cikin sanyin murya ta furta"Sunana Khala, nasan baki sanni ba, kuma baki ta6a jin labari na ba, yau ne karo na farko da kika fara ganin fuska ta..." cike da dattako tayi maganar.

Ta Wan dakata tana kallon gabriella.

"Yau tsawon makonni Ina jinyarki, Due to the traumatic brain injury that put you in a coma, I know you can't remember what happened to you because you've lost your memory..." tun da ta fara magana Gabriella ta nutsu tana kallonta.

"naji dadin samun lafiyarki, inatayaki murna"

ta fad'a fuskarta Wauke da annurin farin ciki, ita dai gabriella takasa gane komai, gaba daya arude take da tsohuwar, bata fahimtarta


"Naji kin ambaci nayi jinya tsawon makonni bana acikin hayyacina, meya faru dani"? Girgiza kai khala tayi"I won't tell you because I don't want you to remember what happened to you, ko dan saboda lafiyarki, a yanzu nafi bukatar kwanciyar hankalinki, saboda ina da buri akanki"! AruWe Gabriel take kallonta, harta buWe baki zata tambayeta wata irin yunwa ta murWa cikin ta, da sauri ta dafe cikin da hannu tana faman yamitsa fuska ta kalli khala"ki taimaka min da abinci, yunwa nake ji..."


Ajiye gorar ruwan hannunta tayi, tare da taimaka mata ta zauna dakyar, Sandar ta dake ajiye kasa ta Wauka, ta mike tare da juyawa ta nufi wani teburi dake a dakin hada kujeru biyu a kewaye da shi, daga saman teburin kwanukan abinci ne.


Ta Wauko bowl Waya ta juyo tare da kallon Gabriella


"Bansani ba ko kin iya cin zogale da kuli..." tunkan ta ?are maganar gabriella tace"Ina ci, koma menene zanci.." murmushi khala tasaki ta nufo gurinta ta mi?a mata kwanon, Hannunta na kerma ta cire murfin ta fara dibar zogalen tana ci, duk da babu WanWano abakinta, kunnuwanta har motsi sukeyi tsabar dadi, hannu baka hannu kwarya take duma loma tana turawa a karamun bakin ta kamar zata shake, kamar kyaftawar ido ta lamushe shi tass hada sanya harshe tana lasar kwanan..dariya khala tayi"kin koshi ko kina bukatar kari" da sauri ta Waga mata kai, juyawa khala tayi cikin takun dattako ta koma gaban table din ta buWe wani kwano mai Wauke da tsokokin nama taje ta mika mata kwanon"kalacina ne na safe, da naci na rage, bansan yau zaki farfadowa ba, shiyasa ban tanadar maki abinci ba, amma kiyi hakuri da wannan, idan aka kawo min lunch dina zan baki kici ki koshi" kar6e kwanon gabriel tayi hannunta na kerma ta fara daukar tsokar tana ci, sai da tacinye tass khala ta Wauki gorar ruwan ta mi?a mata, ta kar6a ta sha.

Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke wani irin relief taji a jikin ta, duk da bata koshi ba, taji Wan dama dama a cikinta.

Kokarin mikewa tayi da sauri khala ta taimaka mata ta mike tsaye kan kafafunta, cikin sanyi murya tace"har yanzu baki bani amsar tambayoyin da nayi maki ba, na ruWe na kasa tuna komai, wanene ya kawo ni nan? Ko kece? Sannan meya faru dani? A ina nake?

"Ki manta da komai, sai ki zauna lafiya, tunawar baida amfani, idan kika bani hadin kai, kuma kika bi sharuddan da zan fada maki zaki tsira da rayuwarki, idan kuma kikayi min gaddama zaki dawwama awahala..." kalamanta sun rikita gabriela cikin rawar murya tace"meyasa zaki hanani tambayarki? Ina son nasan wacece ni! Meya faru dani, ina ji araina kamar na manta wani abu arayuwata, dan Allah ki tuna min..." dafa kafadarta tsohuwa khala tayi"nayi maki al?awarin zan baki amsar tambayoyinki amma ba yanzu ba, har sai zuwa lokacin da tunaninki ya dawo dai dai..." shiru gabriella tayi gaba daya jin kanta take kamar ba ita ba, kamar ma


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login