Showing 279001 words to 282000 words out of 298130 words

Chapter 94 - KURKUKUN KADDARA (TAKUN KARSHE) BY BOSS BATURE.doc

ba, ko dan na damu da kaine"? nutsuwa yayi yana kallon kyawawan idanunta kwata kwata ta?i yarda su haWa ido saboda sunyi kusa da juna kuma bata son ta jefa kanta cikin irin halin da suke tsintar kan su duk in su ka haWu da juna.


Ba zato ba tsammani taji ya shigar da yatsunsa a cikin nata ya yi tighting din su wani irin shock taji har tay kokarin zame hannunta daga nashi amma ya ?ara ?an?ame su ta yadda bazata iya kwatsar kanta ba.

Arude ta furta"pls ka sakar min hannuna! Kada wani gan mu," can ?asan makoshi ya furta"Ke kika fara ru?e min hannu, don haka bazan saki ba" ya faWa yana kallon idanun ta so yake ta juyo su fuskanci juna ko ya samu nutsuwar da yake samu agurinta amma taki bashi haWin kai.

Babu wanda ya lura da halin da suke a ciki, Hankalin yan uwan su na kan su Taj da mutanan su.

Bayan wasu ?an mintuna, taj Ya nufo su gurin su suna ganin shi suka fara sauke ajiyar zuciya dama duk sun takura da zama su kadai

"Batool, Unaisah da ku zamu fara, Bismillah ku taso ku shiga daga ciki" ya fada tare da nuna masu ?ofar Questioning Room din.

Batool harta fara jin faduwar gaba amma da taji tare da Unaisah ne sai taji hankalinta ya kwanta.

?o?ari take ta mi?e Danish Ya?i sakin hannunta, fargabanta kada daddynta ya gani dakyar ta samu ta ?wace hannunta daga nashi ta ta ruko hannun Batool suka bi bayan daddyn ta.

bayan sun shiga Wakin suka tsaya suna ?are mashi kallo, wasu hadaddun kujeru ne biyu suna fuskantar Waya daga tsakiyar su madaidaicin table ne.

ga wani two-way mirror a jikin bangon dakin, wanda anyi shine saboda masu duba wanda ake tambaya su samu damar kallon shi daga Observation ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?Room, tsabar tsaron Wakin hada Surveillance Cameras (Kyamarorin sa ido) Nau'o'in Soyayyun kyamarori masu daukar video recording, ta kowace kusurwar dakin har ta cikin fitilun kwai da jikin kofa duk sune a makale ba zaka ta6a ganin su ba in ba an fada maka akwai ba,

gaba daya sun shagala da kallon Wakin har saida taj yayi masu gyaran murya kafin suka yi saurin kallon shi

Murmushi yayi masu"ku zauna mana" muryar Unaisah da yar shagwa6a tace"daddy zamu iya cire mayafin daga kan fuskar mu? Wlh ya takura mana"

da kan shi ya cire mata mayafin, Ya yi mata rolling akanta, Ya matsa gaban Batool ya warware mata na kan fuskarta itama ya naWa mata akan ta, sai dadi takeji ganin yayi mata yadda yayi ma Unaisah.

Bayan sun zauna ya Wan dafe table din gabansu da tafukansa Ya dubesu da kyau

"Pls kada ku bamu kunya, ku natsu ku kwantar da hankulan ku gurin amsa mashi tambayoyin da zai yi maku, Mutun Waya ne zaiyi maku tambayoyin dan haka ku kwantar da hankalinku" kallon juna su ka yi atare kafin suka dube shi.


Murmushi ya sakar masu "ina fatan zakuyi min haka" atare suka haWa baki gurin first"Eh" yar dariya yayi"lokaci yayi zan tafi, ku kula mun dakan ku"

amsa mashi su kayi da "toh"

Bayan fitar shi daga dakin kusan atare suka sauke ajiyar zuciya, kowa da abun da yake sakawa aran shi, damuwar Unaisah akan Danish tana ji aranta zaiyi wuya ya basu hadin kai.


"Sis Wai wanene Zai yi mana tambayoyin"? Batool ce tayi mata tambayar kafin ta bata amsa suka ji motsin shigowar mutun atare suka kalli kofar Wakin.

har sai da gaban su ya fadi saboda ba su tsammaci ganin chief owais ba, ta wani bangaren sunji dadi saboda sun san wanene shi sun kuma yarda da shi Wari bisa Wari.

Walking Slowly yabi ta bayan kujerun su Ya nufi frigde ya buWe ya dauko juice mai sanyi ya haWo da cups biyu ya daura akan table din gaban su, duk wani motsin shi akan idanun su yanayin yadda yake tsiyaya masu ruwan lemun a cup ba ?aramin tafiya ya yi da imanin su ba, komai nashi cikin aji, ?asaita da nutsuwa yake yin shi"

kwata kwata bai Wago Ya dube su ba, har sai da ya gama zuba masu juice din mai sanyi a cups Ya tura ma su agabansu kafin a hankali Ya zauna tare da Waura kafarshi Waya kan Waya, ganin sun?i daukar cups din yasa shi tunanin ko basu san su ya zubawa ma ba, kamar ya sani kuwa ai gani suke basu kai matsayin da chief zai zuba masu lemu a cup ba.

Da index finger din shi ya nuna masu Cups din, Hakan yasa suka fahimci nasu ne, a tsanake suka Wauka suka fara sha a hankali don kada yaga sun yi ?auyanci musamman Unaisah da aji take shan juice din yayi mata dadi ga sanyi.

A gayun ce ta rage kaWan a cup din ta ajiye kan table, Batool kuwa duka ta shanye shi har tana sha?e wa cikin raWa unaisah ta yi mata magana don kada ya ji su

"shashasha, Ki yi irin na yan gayu ki rage kaWan, kada yaga hadamarki"

baiwar Allah idanunta amarairaice ta kalli cup din ta shanye kaf tsoronta kada Unaisah tayi mata faWa sunnar dakai ?asa Unaisah ta yi ganin chief na kallonta wata irin kunyarshi da nauyinshi ne suka kamata.

mayar da idanun shi yayi kan Batool in a cool voice ya furta"kin koshi ko in ?ara maki"? Maimakon ta bashi amsa sai ta kama kallon unaisah, nan take ya fahimci tana jin tsoron tayi mata fada.

bai jira amsarta ba, ya ?ara mata juice Win a cup"ki dauka" jikinta asanyaye ta kar6i cup din takai baki saida ta shanye kafin ta ce"thank you"


"Neva mind," ya faWa tare da gyara zaman shi

"Can we start?" ya fada yana kallon su


Atare suka amsa mashi da Eh, tun kafin su zo head quarter din an sanar da su da harshen turanci za su yi magana saboda duniya ce zata saurari tattaunawar su.

Shiru ya yi yana duban su da alama nazarin wani abu yake yi tsawon mintuna kafin kasaitacciyar muryarshi ta katse shirun na su


"Da farko Inaso ku gabatar da min da kan ku" Unaisah ce ta fara gabatar da kanta kafin batool ta yi nata introduction din.

"Tayaya akai kuka tsinci kan ku agidan kurkukun ?addara"? Kallon juna su ka yi, kafin Unaisah ta fara bashi labarin lokacin da ta gudu daga rigar fulani da yadda Bakar mota tayi parking agabanta aka zuro hannu daga ciki suka dauketa.

"Daga nan ban kara sanin inda kaina yake ba.." tiryan tiryan ta labarta mashi, bayan ta kammala nata cikin kuka saboda duk lokacin da ta tuna rayuwar da sukayi a kurkukun kaddara sai taji zuciyarta ta kare musamman mutuwar unaizah da majnoon dinsu, Ya mai da duban shi ga Batool jikinta sai kerma yake duk ta rasa nutsuwarta gaba daya sun fahimci halin da take a ciki.

Jin tayi shiru yasa Unaisah ingiza kafadarta, Muryarta na rawa ta fara magana.

"Ni bansan lokacin dana tsinci kaina agidan kurkukun kaddara ba, tsohuwar da ta raine mu wadda muke kira tsohuwa Tamira ta ta6a faWa mana tun muna jarirai aka kawo mu gidan kurkukun, itace ma ta shayar da mu ta kuma raine mu har muka mallaki hankalin mu"

dakyar ta ?are maganar duk tabi ta ruWe saboda kwarjinin da chief ke yi mata duk in ya Wago da ido ya kalleta tun bai fahimta ba har ya fara Wago ta, shi dinne akwai jan hankali dole mace ta ruWe agaban shi kamshin turaren shi kadai ya isa ya susutar da su balle kuma shi din gaba Wayansa.

Kamar Wan jarida haka ya tsare su da tambayoyi tun suna amsa mashi cikin dadin rai har suka fara galabaita tuni Gumi ya fara wanke goshin su duk da sanyin A.c din dake dakar fatar su, numfashin su har sauri sauri yake gurin fita musamman Batool kirjinta sai sama da kasa ya ke yi ta fara rikicewa, wata tambayar ma da kunya suke amsa mata saboda nauyin amsa mashi da suke ji.

"Bayan sun Wauke ki na tsawon watanni me su ka yi maki" ya fada tare da nuna batool da girarsa, sunnar da kanta ?asa ta yi gaban ta na faWuwa.


"Ina sauraron ki" ya fada cikin aji yana duban Batool

"Can I help her"? Unaisah ce tay maganar, tana faman jujjuya eye balls dinta

"Rasa kunya 6eran tanka, nasan zata aika" big guy ne ya faWa da zolaya yana kallon Taj, ashe suna atsaye gaban Mirror suna kallon su tare da su COO, CI, and Senior agents daga observation Room.

harara Taj Ya jefa mashi"bana son Iya shege wlh"


Big guy yace"gaskiya ke bakaso jarin ka bata da kunya, ita sister dinta tana jin kunya shine ita rasa kunya take fadin zata taimaka mata..." murmushi Taj yai batare daya ?ara tanka mashi ba.

Girgiza kai chief yayi "No, I prefer her to tell me herself, kinsan ance wa?a bakin mai ita tafi dadin sauraro ko ba haka fa"? Ya faWa tare da daga mata gira, cike da jin kunyar shi ta sunnar da kanta kasa tana dan sakin murmushi.

Kayataccen murmushin gefen fuska ya dan saki tare da kallon Batool da ta tsare shi da idanunta.

Yawu ta haWiya kutt sautin Ya fita, cikin rawar murya ta fara en ena hakan yasa shi dakatar da ita"ki fara daidaita nutsuwarki" tuni tasha jinin jikinta muryarta na rawa ta amsa mashi da toh, shiru su ka yi na tsawon mintuna kalilan kafin yace da ita kin shirya amsa min"? Yanayin yadda yayi mata magana yasa taji wani bakon abu ya ziyarceta wanda batasan menene shi ba.

Jinjina mashi kai tay alamar eh kafin atsanake ta fara bashi labarin abin da ya faru da ita bayan giants sun dauketa na tsawon watanni.

runtse idanun shi yayi tare da dafe forehead din shi da hannu Waya, wani irin tsantsar bacin rai ne ya ziyarci zuciyar shi, hatta su taj dake kallon su jikin su yayi mugun yin sanyi, sauran jami'an dake kallon su babu wanda ran shi bai 6aci ba, jikin su har tsuma yake yi tsabar fusata.

Lokacin da ta karasa bashi labarin, dakyar ya iya buWe idanun shi ya dube fuskarta suka hada ido cikin na juna

"Iya abunda su ka yi maki kenan? cikin sanyin murya da yar sheshshekar kuka tace Eh

Ajiyar zuciya ya Wan sauke kafin ya furta"idan kunayin jinin al'ada ne kadai suke daukar ku"? Tace eh

Mayar da duban shi yayi kan Unaisah"ke fa"? da gira yai nuna da ita.

Cikin sanyin murya ta fara bashi labarin abun da ya faru lokacin da ta saci hanya ta fita daga dakin su na gidan kurkukun ?addara ta tafi neman Neman Danish har tsautsayi ya rutsa da ita ta haWu da tsohuwa zafreeen.

Bata boye mashi komai ba, sai da ta sanar dashi, abun da yafi kona mashi rai wankan jinin da matsafan su ka yi mata bayan sun tu6e mata kayanta, ga kuma azabtarwar da suka yi mata cikin shesshekar kuka tace"ta karfi ta tsiya suka sa ni na farke mace mai tsohon ciki da wuka har jaririnta saida wukar ta yanka, bayan haka suka tursasa min saida suka bani naman mutun tafasasshe suka sa karfi gurin banbare bakina kafin suka tura min naman, har ciwo saida naji gurin ya dinga bleeding...."

wani irin tsantsar tausayin su ne ya kama shi da sauran jami'an da ke kallon su, chief baisan sa'adda Ya ruko yatsun hannunta a cikin nashi ba, saboda ta bashi tausayi sai yaji kamar ya yi huggin din ta da alama ya manta da jami'an dake kallon su.



*DAGA AL?AMIN BOSS BATURE=?%?
'?*

*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08169856268 ko 08103884440*_______________________________________
'?=؋?
'





Calmly yace"share hawayen bana son ganin su" jinjina mashi kai tay alamar toh

Ya zuba mata juice A cup Ya mi?a mata, Yatsun hannunta na kerma ta dauka takai baki ta yi kur6a Waya ta aje, ta nutsu tana jiran tambaya ta gaba

"Sun ta6a yin raping Win ki"? Dakyar yai mata tambayar saboda fargaban amsar da zata ba shi.

Shiru tayi jimm tana tunanin meye ma raping din? Ko yana nufin irin abun da matsafan su ka yi ma su Deeja kamar yadda ta bata labari.


Shirun da ta yi ba karamin kayar mashi da gaba tayi ba, hankalin shi ya tashi matu?a.

"Ko baki gane me nake nufi ba" da sauri tace"na gane, ni ba su ta6a yi min ba, saboda sai wanda ya fara jinin al'ada suke yi mawa"

Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke tare da lumshe idanunshi wani irin sanyine ya ratsa zuciyar shi ita kanta ta lura da yanayin shi tayi mamakin hakan.

Sun Wauki tsawon lokaci Yana jera masu tambayoyi Cikin ikon Allah suka amsa mashi duk wata tambaya da yayi masu babu abun da suka boye mashi saida suka faWa mashi komai da suka sani dangane da rayuwarsu agidan kurkukun kaddara daga farko har zuwa lokacin da suka tsira daga kurkukun.

gaba Waya jami'an dake kallonsu saida zuciyarsu ta karaya da tausayin rayuwar yaran musamman wadanda basu san labarinsu ba, abun ya girgiza su ya yi matukar Waure masu kai da al'ajabi, suna sauraran abun kamar amafarki saboda al'ajabin da ya rufe su, abin da yafi karya masu zuciya labarin Unaizah, wlh hankalinsu yayi mugun tashi sun girgiza da jin rashin imanin da matsafan suka yi mata, duk irin dauriyar jami'an isod sai da idanunsu suka kaWa jawur tsabar fusata sunji zafin mutuwar yarinyar da yadda uban ta ya yaudareta ya salwantar da rayuwar ta tsabar mugunta da zalunci.

"Menene Sunan mahaifinta"? Ya jefa ma Unaisah tambayar.

Wani ikona Na Allah gaba daya ta manta da sunan kamar an shafe mata shi a kwakwalwarta.

Girgiza kai tay"na manta sunan shi, amma idan na tuna zan sanar dakai, ta dai ta6a fadamin babban mutun ne a Nigeria" jinjina kai chief yayi"A cikin backpack din dinta da sojojin america suka ba mu, munga textbooks, jotter da diary kun ta6a buWe su"? Shiru ta yi jimm kafin ta girgiza kai"bazan iya tunawa ba, amma yan zu backpack din tana adakin mu tun lokacin da na kar6a agurin daddyna"

"Okey, Idan muka koma gida zan kar6a" amsa mashi tayi da toh

Sara ma su yayi da hannun shi kafin ya jinjina masu da babban yatsan shi, gaba Waya suka saki murmushi

"Thank you for your cooperation, Unaisah and Batool, The information you provided will help us find the oppressors and put an end to them In sha Allah" ya fada yana kallon su, at same time suka sauke ajiyar zuciya, dama a?agare suke da ya kammala yi masu tambayoyin don ba karamar gajiya su ka yi ba.

Mi?ewa ya yi ya nufi room door suka bi bayan shi, suna fitowa daga dakin da sauri Yan uwan su suka nufo su suna tambayar su me aka tambaye su.

"Ku bari idan ku ka shiga zaku ji abunda muka ji amma fa akwai juice me sanyi zaku sha dadi" unaisah ce tayi maganar.

Tun fitowarsu Chief Ya Bar wajen Ya nufi Observation room saboda ba shi ne zaiyi ma sauran tambayoyi ba.

Tayi mamakin ganin Danish yana bacci ya langwa6e kan shi saman kujera da alama yaji dadin sanyin a.c din dake ra6ar shi, hakan ba karamin tada mata hankali yayi ba, gani take kamar baccin nashi bana lafiya bane da sauri ta nufi Sofa din ta zauna daga gefensa ta ?ura ma shi ido tana fuskar shi.

Taj ne ya fito daga dakin da suke Ya nufo gurin su, Mutum uku Ya kira Parveen, Jemimah da Azeeza su uku aka shiga da su dakin tambayar, ahaka aka dinga dibar su Waya dayan duk wanda ya fito daga Wakin jikin shi ba kuzari ga zufa saboda galabaita da tambayoyin da akeyi masu saukin su akwai Juice da ruwa me sanyi ita jemimah uwar son banza daga anyi mata tambaya daya sai tace ta gaji abata lemu ta ji?a makoshin ta, ahaka aka samu ta amsa tambayoyin, haka itama parvin Jami'en da yayi mata tambayoyi yasha bakar wahala saboda shiririta da ta saka ga rashin nutsuwa kafin agama yi mata tambayoyin saida tasha juice yayi cup goma, Deeja kuwa dama basu sanya ran zasu samu wani abu daga gareta ba saboda ta6in hankalin ta, kamar ma bata jin dadin jikinta ko irin haukan da takeyi masu agida batayi a headquarter din ba tana zaune kan sofa ta yi shiru tana kallon duk wani mai giftawa.

?aya bayan daya saida suka amsa tambayoyin da akayi masu, mutun huWu da jami'an suka ji dadin tattaunawar su da yaba kokarin su Unaisah da Batool sai mazan cikin su duk da bakomai suka iya tunawa ba kamar abun da ya faru da su lokacin da aka Wauke su na tsawon watanni sun kasa tuna abun da akayi masu sun dai san sunci ba?ar azaba kuma duk wanda yaji alamomin da suka dawo hayyacin su da su a jikinsu zai fahimci hada homo su ke yi da su.

Jami'an Sun firgita da jin irin rashin Imanin da matsafan suke yi ma su, sunji abun da Ya gigita tunanin su ba dan juriya irin tasu ba da kuwa sun fashe da kuka saboda bakin ciki da takaicin abunda akayiwa yaran da ba su ji ba basu gani ba, suna ji aransu idan ya'yansu ne hakan ta faru da su ya zasuyi? Wlh har zuciya zasu iya hadiya su mutu.

Bayin Allah gaba Waya sun dawo kan kujerun sun zauna, fuskokin su sharkaf da ruwan hawaye saboda an fama masu raunin dake a cikin zuciyar su, idanunsu sun kaWa jawur kamar jan gauta, sun yi shiru suna tuna rayuwarsu ta prison babu mai magana a cikin su, yanzu saura mutun Waya ya rage a shiga dashi dakin tambayar, sun ma rasa taya zasu farkar da shi daga bacci, ya hakimce kan sofa Hankalin shi kwance yake fitar da numfashi shi baisan meke wakana ba.

Agaban kujerar da ya ke zaune jami'an suka tsaya suna kallon shi daga cikin su hada chief da taj da big guy.

"Sir, Mu tada shi daga baccin"? taj ne ya faWa tare da kallon chief

"Bana so mu takura mashi, Mu jira zuwa lokacin da zai farka inaga zaifi" girgiza kai big guy yai"Sir ni anawa shawarar mu tada shi, saboda yaron yana da nauyin bacci, bamu san lokacin da zai farka ba ga ba?in mu na america


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login