Showing 156001 words to 159000 words out of 298130 words

Chapter 53 - KURKUKUN KADDARA (TAKUN KARSHE) BY BOSS BATURE.doc

gurasa ba sai Yau, kai harta dambun shinkafar yaune karo na farko daya fara cinshi, yaji dadin abincin har ?warar cikinsa yayi, Angel dake kallonsa sai faman sakin murmushi takeyi ba tare da ya lura da ita ba, bayan sun kammala cin abincin kowa yayi kulu wash rabu hani'an danejo ta kwashe kayan abincin ta nufi kitchen da su
"Daughter, dare yayi muje na raka ku gida, Kada chief Ya tuhume ni, kinsan yanzu bani da hurumin daukarki tun da a karkashin kulawarshi ku ke har zuwa time da zamu kammala bincike"

"Bakomai daddy, na fahince ka," shafa gefen fuskarta yai, danish dake kallon su tuni ya hade ransa, shi fa har yanzu bai daina kishi da taj ba, saboda baisan ala?ar dake a tsakanin iyaye da dansu ba.

Fitowa danejo tayi daga kitchen, ganin su tsaye yasa tace"ya akai nagan ku a tsaye ku zauna mana muyi firar yaushe rabo"

Taj ya ce"Zasu tafi ne" Waure fuska tay"bangane me kake nufi ba, nayi zaton ta dawo gida kenan," girgiza kai yai"ay tana a gidan amma a part din chief suke da zama, zata dinga zuwa kuna gaisawa da juna...." dakyar ya samu ya fahimtar da ita, atare suka raka su unaisah har gida kafin sukayi masu sallama.

Lokacin da suka shiga falon babu kowa har sun koma bedrooms dinsu alamar time din bacci yayi, kamar kar su rabu da danish har saida ta raka shi bedroom dinsa kafin ta dawo ta nufi nasu dakin, tana shiga ta samu deeja kwance kan gadon su sai jan minshari takeyi, murmushi tasaki tana kallon ta, har yanzu kwalliyar dazu ce akan fuskarta duk ta ca6e kamar ?ar mahaukaciya, ta jima tana kallon ta, kafin ta fara cire kayan jikin ta, ta musanya dana bacci, fuskarta dauke da annurin farin ciki, ta hayekan gadon, bata damu da rashin ganin batool ba, tasan bazata wuce dakin aunty ummin su ba, huggin pillow tai, Allah ne kadai yasan dadin da take ji sam ta manta da zancen kiran aunty pretty gaba daya tunaninta akan abun farin cikin daya faru yau ne

______________________________________
'?


Zaune ya ke kan sofa ya Waura ?afarsa Waya bisa Waya, yayin da idanunsa ke akan laptop din gabansa da yake operating lokaci Waya ya Wan dakata Ya jingina bayansa jikin Sofa haWi da lumshe idanunsa zuciyarsa a cike take fal da tunanin prettynsa har yau jiran hajiya laurat yake yi don jin amsarta, tun jiya bayan kammaluwar dinner din hateem ziyad ya nemi alfarmar yin magana da ita bayan sun ke6e cikin girmamawa ya gaishe ta, ta amsa masa daga bisani ya fara kora mata jawabi game da bukatarsu, lokaci Waya yanayin fuskarta ya canza zuwa 6acin rai kamar bata son zancen Benazir da yake yi mata, acikin ranta tayi mamakin jin cewa a hannun Zaki ta faWa ita sam ta manta da rayuwar benazir tamkar ma ba'a halicce ta adoron duniya ba, saboda tun fil azal hajiya laura basa ga maciji da hajiya layla wata irin gaba ce atsakaninsu shiyasa bata shiga shirgin abun da ya shafi layla, a lokaci shi kanshi ziyad ya lura da 6acin ran da take a ciki amma sai ta waske ta ?a?aro murmushi tana fadin Allah sarki benazir ashe dama zaki ne ya taimake ta? Alhamdulillah wlh nayi murna ziyad, sai dai abun da ya daure min kaina babu wanda Ya kirani daga gidan Ya fadamin cewa anganta amma in sha Allah zan fidda lokaci inje can gidan da kaina don in tabbatar ta dawo in yaso daga bisani zan tuntu6i shi zaki din...." akan haka suka ?are magana ziyad yai mata godiya kafin suka rabu.

A hankali Zaki ya buWe idanunsa Yana kallon ceilling din falon, duk don saboda son haWuwa da ita, ya Waga tafiyarsa canada.

Yayi zurfi a zancen zucin nasa muryar turai ta ratsa kunnansa

"First born barka da hutawa" ta faWa tare da daura masa mug din coffee kan table, murmushi ya sakar mata, yana Waya daga cikin abun da yake burge shi da mommyn nasu in har zata ganshi zaune yana aiki akan laptop sai ta kawo mashi coffee .

"Mom har yanzu baki yi bacci ba"? ya faWa yana kallon ta.

"Tayaya zan iya runtsawa Jazz bai dawo ba, daddynku bai dawo ba shima, su nake jira su dawo sai in kwanta" tayi maganar tare da Waura gwiwowin hannunta bisa ga hand sofa din da zaki yake zaune idanunta akan fuskarsa

"Ko akwai wani abu dake damun ka ne"? Ta fada cikin kulawa

"Babu komai" ya bata amsa atakaice tare da kai hannu ya dauki mug din Ya soma kurbar coffee

"My son, tayaya zaka 6oye min damuwarka, bayan ni mahaifiyarka ce, ta ido kadai ina gane damuwarka, tun lokacin da ka shigo ?asar nan na lura da damuwa aranka"

Sauke mug din yai kan table kafin ya dubi hajiya turai"nagode da kulawarki agare ni, amma ki kwantar da hankalin ki ba abun da ke damuna"

GyaWa kai tay"haka nakeson ji" ta faWa ne ba dan ta yadda da maganarsa ba tasan baya son taji ne

"Bari na shiga ciki, ka kula min da kanka" amsa mata yai da toh

Bayan tafiyarta ajiyar zuciya ya sauke, bawai baya son fada mata bane yafi son ya fara jin halin da take a ciki in har ta isa gida lafiya, kuma iyayen ta sun kar6eta ba abun da zai hana shi sanar da nashi iyayen labarin ta.

?arfe goma da rabi, jazz da sir mubarak suka dawo gidan lokacin da suka shigo falon tuni Zaki Ya koma room dinsa ba su taras da shi ba,

Hajiya turai na kwance kan gado tajiyo sautin sallamar sa, jikinta har rawa yakeyin wurin saukowa daga kan gadon da sauri ta nufe shi yana atsaye cikin shiga ta kakinsa

"Sannu da dawowa, tun dazu nake ta jiranka nayi kewarka yau kayi dare " cikin nuna kulawa tayi maganar tare da ruko hannunsa suka shiga dakin

"I'm sorry bansanar da ke zan kai dare ba, wani aiki ne mai muhimman ci Ya ru?e ni" ya faWa Yana kallon cikin idonta,
"Ba nace ki daina jirana ba? daga kinga nayi dare to ki kwanta kiyi bacci"
Ma?e masa kafaWa tayi"kai ma kasan bazan iya jurewa ba...." murmushi ya Wan saki"kinsan me na tuna"? Girgiza mashi kai tay alamar a'a"

"WaWannan twins din na wurin Owais, ko da yake yace min ba twins bane, Waya ta girmi Waya" da mamaki hajiya turai tace"ikon Allah, amma nayi mamakin jin hakan komai nasu fa iri Waya kamanninsu sun 6ace"

"Zai iya yiwuwa yan gida Wayane" jinjina kai tay alamar eh

"Yaran sun kwanta min araina, kinsan ni da son ?a'?a mata, duk family dinmu ni kadai ne nake da ya'ya maza ina alfahari da hakan amma inason ya'ya mata, ga hateem nan shi mazan yake so Allah bai bashi ba"


shiru mom turai tayi kamar ta dan shiga damuwa, sam bai lura da halin da ta shiga ba, ya nufi toilet Ya shige jin ?arar rufe kofar shi Yasa jiki asanyaye ta koma gefen gadonsu ta zauna idanunta sun ciko tab da kwalla..

Ceilling ta ?urawa ido tana tunano wani abu da ya ta6a faruwa acan lokacin baya shakeru da suka gabata, ta ta6a haihuwa ya'yan suna mutuwa wanda silar hakan Yaja har sir mubarak Ya hanata haihuwar gaba Waya gudun kada itama tarasa ranta kamar yadda ya'yan da take haihuwa suke rasa ransu da zarar sun dira a duniya, Allah kadai yasan halin da ta shiga awannan lokacin saboda ta kwallafa rai akan son taga ta haihu da sir mubarak sai dai Allah bai bata ba shiyasa har su hajiya saratu suke yimata gorin sai dai taci ta kasayar

Yunkurawa tayi jiki ba kwari ta mike ta futo daga Wakin nasu ta nufi bedroom din jazz sai da ta matse kwallar da ta taru a idanunta kafin tayi mashi sallama shiru ba'a amsa mata ba, har ta fara tunanin ko yayi bacci ne, shigarta ke da wuya kwatsam taci karo da wayarsa dake yashe kan floor ga dukkan alamu wurgo da ita yayi, hatta lap coat dinsa anan ya jefar da ita, hankalin ta ba karamin tashi yayi ba, a razane ta kalli gadonsa a zaune ta same shi tsakiyar mattress, Ya kifa kansa bisa gwiwowin sa, lokaci Waya ta rasa sukuninta da sauri ta nufi kayan nashi ta kwashe su ta je ta ajiye masa kafin ta dauko wayar ta nufin gadon nashi ta hau sama ta zauna tana fuskantar shi

"Jazz meke faruwa dakai ne"? ta fada fuskanta dauke da matsananciyar damuwa

Shiru babu alamun zai tanka mata

"Nasan kana ji na jazz, ka Wago ka kalle ni sannan ka fadamin meke damunka" A hankali Ya Wago da fuskarsa wadda ta ji?e sharkaf da hawaye idanunsa sun kaWa jawur, wani irin bugu taji zuciyarta tai muryarta na rawa ta furta"jazz kuka kake? Meke damunka ne? Ko bakada lafiya ne? AruWe ta fada tana shafa fuskarsa

"Jazz dan Allah ka fadamin ko hankalina Ya kwanta" da?yar Ya iya motsa la66ansa Ya furta sunan faryat, lokacin Waya annurin fuskar hajiya turai Ya Wauke Wuff, saboda ta fahimci silar shigarshi halin da yake aciki, batasan ya zatai da jazz ba, tayi fama da shi akan ya rabu da faryat amma ya?iya saboda tasan bazata ta6a auran shi ba, hasalima ma yarinyar bata kwanta mata aranta ba, saboda fitsararta da rashin kunyarta..

"Jazz yaushe ne zaka daina yaudarar kanka akan yarinyar nan? sau nawa ina maka gargadi akan ka fita sabgarta? Na fada maka ba sonka takeyi ba yakamata ka hakura ka nemi wata ay ba ita kadai bace mace a duniya....." kafin ta ?are maganar ya tarin numfashin ta da cewa"bazan iyaba mommy, Allah ne ya jarabce ni da sonta, wallahi nayi kokarin cireta araina amma na kasa ki tayani da addu'a Allah ya yaye min sonta in ba haka ba zatai silar da zan rasa raina..."

har saida gaban turai Ya fadi jin abun da yace, ta fahimci mahaukacin son da yakema faryat ba lallai Ya fahimce ta ba

"Me tayi maka ne"? labari Ya fara bata na abun da Ya faru tsakaninsu lokacin da ya je wurinta bai 6oye mata komai ba, har nemansa da tayi don ya bata hadin kai,

"Mom kullum na kirata sai ta ci mutuncina, tace wai ni ba namiji bane tunda bazan iya biya mata bukatarta ba, sannan bazata ta6a auran mara asali dan tsohuwar mai aikin gidan su ba...." ya faWa idanunsa cike tab da kwalla

Ita kanta hajiya turai hawayen ne ke sintiri kan kuncinta, ta tsani taji ana yi mashi gorin asali kamar kanshi farau, ta rasa gane meke damun wasu mutanan sun manta cewa bawa bashi ke daurawa kansa ba? Allah ne Yake kaddara masa rayuwarsa?

"Jazz ta yi kuskure A kalamanta, wallahi sai tayi danasani, saboda ka fi karfinta nesa ba kusa ba, kuma kaine cikakken mai asali tunda kana jin tsoron Allah kuma ka tsare mutuncinka, ni in banda kaddarar so ina kai ina Faryat"? ta faWa ranta amatu?ar 6ace

"Tafi ni komai tun da tana da asali"

"Kaima kana da asali jazz" da sauri Ya kalle ta

"Mom bangane me kike nufi ba, ke da kanki kika fada min baki da kowa a danginki mahaifina Ya rasu" girgiza kai tayi"na fada maka hakanne saboda ka fidda rai da kowa nawa, bana son maganar jazz ka cigaba da hakuri in sha Allah komai ya kusa zuwa karshe" tun da tafara magana jazz Yake kallonta har yau ya rasa gane dalilin dayasa bata son tayi maganar abun da Ya shafi danginsa, shi dama yasan dole tana da family dinta akwai dai wani abin da take 6oye masa, duk da yana neman ?arin bayani daga gareta sai dai ya hakura yabarwa zuciyarsa zai cigaba da hakuri kamar yadda ta ce har zuwa lokacin da zata sanar da shi komai....

Shiru sukayi na wani lokaci babu mai magana a cikin su,

"Ina ibad"? ya tambaya yana kallon ta

"Tun bayan sallar Isha' Yai bacci, ya yi jiran dawowarka har fadamin yai ya kira layinka bakai picking ba"

murmushi yayi"Allah sarki Wan uwana, dama nasan dole ya neme ni, na sanya wayar a silent ne saboda aiki da nakeyi"


"Bari na kawo maka dinner dinka nasan kana jin yunwa, but pls ka shiga toilet ka wanke fuskarka bana son ganin hawayen nan" ta fada tana nuna face dinsa da yatsa amsa mata yai da toh da sauri ya sauko daga kan gadon Ya nufi toilet.

Tana ta bin bayansa da kallo har ya shige kafin Ta mike ta fito daga dakin

Kitchen ta shiga ta shirya masu abinci ta fara kaima jazz a room dinsa kafin ta dauki na sir mubarak ta nufi dakin su

Lokacin da ta shiga a tsaye ta same shi hannun shi ru?e da wayarshi Yana daddanata har ya sanya kayan baccinsa

"Ina kika je ne" ya fada ba tare daya kalle ta ba

"Na shiga kitchen shirya maku abinci ne," ta fada tare da ajiye masa tray din bisa table, murmushin gefen fuska ya dan saki batare data ankara ba, abun da bata sani ba tun time da ta shiga dakin jazz Ya fito Yabi bayanta gaba daya ya ji maganganun da su ka tattauna har recording voices dinsu yayi a wayarsa, yayi mamaki abun da yaji suna tattaunawa, maganganun sun tsaya masa aransa, wani lokaci turai tana da zurfin ciki, in har ba la6e yayi mata ba ita da jazz bayajin damuwarsu sai in tura takai bango tukunna take sanar da shi.

_______________________________
'?

Aneelerh har tayi shirin kwanciya bacci, sautin ringing din wayarta ya dakatar da ita, A hankali ta kai hannu ta dauki wayar ganin sunan surukar arzi?i yasa tayi saurin picking call din idanunta na akan baby junaid dake kwance kan mattress Yana sharar baccin sa

Cikin girmama suka gaisa da junansu

"Aneelerh kwana biyu? Ya ki ke Ya su mamin"?

"Alhamdulillah, muna nan lafiya lou"

"Ina jikan nawa ko har anyi bacci"

"Yayi bacci tun Wazu"

"Allah sarki nayi missing nashi, Ya maganar zuwan naku?

"In sha Allah, cikin week din nan zamu zo"

"Allah yakaimu lafiya" ta amsa mata da ameen daga bisani sukayi sallama taso ta fada ma hajiya adama zancen dawowar benazir amma ta bari sai benazir Win tazo gidansu sai ta kira ta awaya suyi magana don ta bata mamaki, murmushi tayi tare da ajiye wayar kan nightstand, ta janyo junaid on her chest ta rungume abun ta.

_________________________________
'?


_Dare Mahutar bawa, sai dai bakowa ne ke samun kwanciyar hankalin runtsawa a cikin sa ba, saboda akwai wanda ya manta yaushe rabon da idanunsa su runtsa saboda rashin kwanciyar hankali_

*=?y?GIDAN KURKUKUN ?ADDARA=?y?*


Daki ne madaidaici mai fadi da tsayin gaske, irin ginin dutsen nan ne dayai shekara aru aru, daga saman dakin fitilun kwai ne guda uku masu haske idan ka kalli bangon dakin ta ko'ina jirwayen jinine da ya daskare, kai harta iskar dakin ta gauraya da karnin jini da warin jikin mutanan dake rayuwa a cikin sa.

Matasan ?an matane zazzaune kan gadajen ?arfe, kowaccen su tana asanye da guntuwar riga launin ja wadda bata rufe gwiwar ?afarsu ba sun rame sun ?anjame fatar jikinsu duk sahun yakushi da kurajen fata kai gaba dayansu sun koWe baka gane fari acikin su saboda duhun da fatarsu tayi wanda bakomai ne yajawo hakan ba face u?ubar da suke fuskanta, wadannan bayin Allahn babu irin tashin hankalin da ba su gani ba sunga bala'e da masifa tsirararsa, gaba daya an salwantar da rayuwarsu, tun lokacin da aka kaddara masu rayuwa agidan kurkukun ?add?????
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
ara amfani ake da su kamar injina, babu wani sassauci.

gaba Wayansu babu wacce ta haura shekara sha bakwai dukansu matasan ?an matane gwanin ban tausayi, dukkan gabban jikinsu sun raunata, ko tafiya ba su iyayi sai dai adauke su akai su inda za'a yi amfani da su in angama a dawo da su=?-? zuciyarsu da fargaba take bugawa, numfashin su da tashin hankali suke buso shi, idanunsu sun kumbura suntum sun ?afe saboda tsabar kukan da suke sha wanda tun sunayi hawaye na zuba har takaiga ruwan hawayen sun daina fitowa sai dai kukan zuciya mai Wacin gaske, basu da wani burin dayawuce Allah Ya dauki ransu su huta.


Biyo bayan da Garkuwa Ya gudu tare da wasu daga cikin prison ha?i?a ran Elders yayi mugun 6aci matu?a sun harzu?a evil heart dinsu ta hasala, wanda silar hakan Yaja suka fara azabtar da sauran prisoners dake agidan kurkukun ?addara, babu imani ko miskala zarratin yanzu ko abinci mai dadi babu a gidan kurkukun ?addara babu wani jin dadi ko na da?i?a sai ba?ar izayar rayuwa, Allah ne kadai Yasan adadin jinin da suka zubda na yaran da suke raino, da kuma Yaran da suka gur6ata ma rayuwa, wani shiri suka fara yiwa kansu saboda suna hasashen akowani lokaci za'a iya kawo masu farmakin bazata, kuma suna da tabbacin asirin su yana dab da tonuwa, basu ta6a fuskantar barazana da tashin hankali irin na wannan lokacin ba!!

_Zaman tattaunawa sukayi a karo na biyu a dakin sirrinsu wanda a lokacin suka yanke shawarar za su ba Waya daga cikin Evil giant Win da suke da su horon zama prison shield saboda asamu wanda zai maye masu gurbin Garkuwar su da suka rasa saboda sun fahimci yayi masu nisan kiwon da ba zasu iya tan?wara shi ba, da bu?atar su samu wanda zai zamanto abokin karawar Garkuwa, saboda a halin Yanzu Idan aka kawo masu farmaki tare da shi to kuwa tabbas za'a ci galaba a kansu tun da babu wani giant da zai Iya karawa da shi idan ba su elders din ba, amma Idan suka gurfanar da sabon Giant din su mai ru?e da mukamin prison shield zai yi wuya a iya rusa su in ba wani iko na Allah ba, sannan shi wannan giant din zai iya aikata duk wani rashin imani da suke so, ba a halicci zuciyarsa da imani acikin ta ba, ba?in mugune kuma azzalumin mutun ne shu'umi mai hadarin gaske, baisan menene tausayi ba, kurma ne sannan makahone bayaji baya gani in ba umarnin ubayen gidansa ba wato Elders, Shi fa wannan giant din baida mararraba da bakin shaidanin Aljani saboda sune suka rinjayi halittarsa ta Wan adam_



*Daga Al?alamin Boss Bature=؋?
'
'?*


*Littafin kurkukun ?addara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura*

3196407426

First bank

Bature Hafsat Muhammad,

*bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login