Showing 114001 words to 117000 words out of 298130 words

Chapter 39 - KURKUKUN KADDARA (TAKUN KARSHE) BY BOSS BATURE.doc

yana kuka babu mai lallashin wani a cikin su, ummi da batasan kan zancen nasu ba tuni itama ta fara matsar ?walla cikin rauni na murya tace dan Allah ku fahimtar dani ku yi min bayani tun kafin zuciyata ta buga, saboda hankalina ya tashi na kwaWaitu da son jin tarihin rayuwarku......."

Lumshe ido chief owais yayi, zuciyarshi ta karaya, wankan suit ne ajikin shi, bai jima da dawowa daga Airport ba wurin rakiyar prime minister.

A hankali Ya dubi Big guy dake a tsaye gefen sa, hawaye ya gani sun cika mashi idanunshi,

Shi kanshi dauriya ce kawai, amma kalaman su sun ta6a ta6a zuciyarsa.

Cikin sanyin murya ya furta"ka kira salsabeel a waya ka faWa masa inji ni ya shirya sauran yaran, su zo nan gida su sameni, inaso suga yan uwansu"

cikin girmamawa big guy yace"okey, sir." ya faWa tare da zaro wayarshi ya danna ma salsabeel kira wayar na fara ringing, yayi picking,

"barka da safiya yalla6ai"

"Yawwa barka, Ina fata dai ban katse maka baccinka ba" muryarshi da yar dariya yace"ay bana yin baccin safe saboda khadeeja kasan halinta kamar mai fama da cutar yunwa, tun da safe take tashina, don in shiga kitchen in dafa mata indomie"

"Allah sarki, ka cigaba da ha?uri da ita, Yanzu dai gani tare da chief, yace yana son ganin ka da sauran yaran yanzun nan ku same mu agidansa"

Muryar salsaleen da dan rudani yace"yallabai badai wani abune ya faru ba? Naji kace nazo da yara da sassafen nan"
"Ba wani abu kazo kawai, " amsa mashi yayi da toh, kafin su ka yi sallama Ya maida wayar cikin aljihu...

Angel dake atsugunne bakin kofar toilet din, jikinta ya gama yin sanyi tamkar wadda aka zarewa laka, duk abunda su batool ke fadi akan kunnanta tuni tayi shiru ta dakata da yin kukan, ita kanta bata ta6a tsammanin sun ru?e kyautatawar da take yi masu ba acikin zuciyoyin su, shiyasa ake son bawa ya kasance yana aikata abun alkhairi arayuwarsa saboda duniya tayi alfahari dashi, al'umma su yi koyi dashi ko bayan ba ranshi, unaisah dai ta bada gudummuwa ta bangarori da dama harta ta bangaren addinin musulunci ta musuluntar kuma ta fadakar Allah ne kaWai zai iya biyan ta.

Cikin shessher kuka suka soma yi mata magana, muryoyinsu duk sun disashe

"Yar uwarmu rabin ranmu, amadadin abban mu, muna baki hakuri dan Allah ki taimaki daddynmu, Kiyi hakuri ki fito yana son ganinki, daddy ya gane kuskurenshi kuma ashirye yake daya baki hakurin laifin da yayi maki.... " magiya suka dinya yi mata duk don su samu ta buWe masu kofa

"Unaisah kin manta irin kyautatawar da daddynmu yayi maki tun kina karamarki, lokacin da mommynki ta gudu tabar ki a cikin kwamin wanka, ya daukeki yaci gaba da baki kulawa duk da kasancewar bakyajin magana ahaka yaci gaba da rainonki saboda irin son da ya ke yi maki shi bai tafi yabar ki ba, unaisah da bakin ki ki bamu labarin nan ko kin manta ne......" gaba Waya kowan nan su ya ?osa ta fito saboda ta rungumi daddynta.

Ba zato ba tsammani, suka ga taj Ya dafe saitin zuciyarshi yana ambaton inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un Muryarshi da wani irin sauti na tashin hankali, gaba Waya suka zabura da sauri suka rufe shi suna ambaton daddy meke damunka? Baka da lafiya ne...."

Jin wannan maganar yasa unaisah yin saurin mi?ewa, yatsun hannunta na kerma ta soma kiciniyar buWe kofar, a fujajen ta fado dakin, ganinta yasa suka bata hanya, ta faWa jikin tajuddeen ta ?an?ame shi tana kuka take fadin daddy dan Allah kayi hakuri nasan nice na bata maka rai, ka tashi ka ji daddyna abun alfahari na, la66anta na kerma takeyin maganar, hawayen fuskarta tuni sun wanke fuskarshi, sumbatar goshin shi tayi, tare da manna masa wani kiss din kan kuncinsa ...." sai da taj ya bari ta gama firgita, tukunna ya buWe idanunsa fuskarshi dauke da murmushi, fashe mashi tayi da kuka da sauri ya janyota jikinsa suka rungume juna tamkar zasu koma mutun Waya tsabar yadda suka matse junan su lallashinta yaci gaba dayi yana fadin"am sorry my angel, ki yafe ni, nasan bankyauta maki ba, wlh kina araina, kamar yadda kike fadin kin yi kewata nima haka nayi kewarki, angel rashinki ba karamin gi6i yayi min ba rayuwata sai da nakusa zaucewa saboda haukan rashin ki a kusa da ni, Angel bana iya bacci batare da nayi mafarkin ki ba, duk dare na Allah sai na tashi nayi salla saboda inyi maki addu'a Allah ya kare min ke duk da bani da tabbacin kina araye ko kin mutu......" dakatawa yai da yin maganar, idanunsa acikin na Angel dinsa, sai da ya fara tattara nutsuwarsa kafin cikin sanyin murya ya fara basu labarin abun da Ya faru dashi bayan ya jefa Angel cikin ruwa.


_______________________________
'?


Abun da ya faru lokacin da wadannan migayun dattawan su ka ?yasta lighter bayan sun zazzaga mashi fetur a jikin shi, idan ba zaku manta ba, ba su kaiga jefa mashi lighter din ba, har sai da suka kusa shiga motocinsu tukunna suka cinna wutar, sannan ba su tsaya sunga wutar ta kone sa ba, suka shiga cikin motocinsu tare da fusgarsu suka bar dajin a guje, bayan tafiyarsu hucin wutar Ya daki fatar jikinsa wani irin radadin azaba ne ya ziyarci sassan jikinsa, nan take ya farfaWo daga suman da yayi ko da yaga wutar dake ci, cikin matsanancin tashin hankali ya yi wani irin kwakkwaran juyi da dukkan karfinsa gaba Waya ya rubza cikin Kogon ruwan daya jefa Angel, tsulundun Ya rubza cikinsa ya nutse can kasan ruwan kuma nan take ya sake sumewa.

Suna acikin ruwa Waya da Unaisah sai dai akwai tazara tsakaninshi da unaisah, wanda silar hakan yasa har danejo ta ceto rayuwar unaisah ba tare da tasan cewa akwai mutun acikin ruwan ba saboda ruwa daya ja shi... A kalla taj ya kwashe tsawon kwana uku acikin ruwan ba tare da ya samu taimako ba.

Ana haka cikin ikon Allah, Wasu fulanin daji dake kiwo daga can wata ruga dake a cikin dajin, su biyu matasa suka koro shanayensu zuwa wurin da ruwan nan yake, Anan suka yaWa zango, to Waya daga cikin su mai suna habu mayen ruwa ne duk in suka zo bakin ruwan sai ya shiga yin wanka, babu irin gargadin da Wan uwansa garbati baiyi mashi ba akan yadaina shiga ruwa saboda hatsarin dake gare shi amma yai kunnan uwar shegu da shi saboda taurin kansa da kafiyarshi, Abun ne yabi jikin shi tun suna kanana Yake shiga ruwa yin wanka har izuwa girmansa, shi kuma garbati mugun tsoron ruwane da shi, ko kusa da ruwa baison zuwa jikin shi kerma yakeyi saboda Labaran da yake ji daga wurin mutane dangane da mugayen halittun ruwa dake cinye mutun shiyasa yake jin shakkar kusan ta kanshi da ruwa, aranar da suka je bakin ruwan, habu na kokarin cire kayan shi don yashiga yayi wanka, garbati yayi saurin dam?ar rigarsa suka soma kokawa a tsakaninsu, cikin harshen fulatanci suke magana garbati yace wlh bazaka shiga ruwan nan ba, ka manta da gargadin da baffa yayi mana akan shiga ruwa? Ko so kake ka mutu ne kafin lokacin ka yayi?
Habu da ya gama hasala Ranshi a6ace yace"Aradun Allah garbati baka isa ka hanani shiga yin wanka ba, ko da kuwa sama da kasa zasu hade saina shiga, idan ma wani abu ya same ni, ni naja ma kaina kai dai naka kallone kawai" duk yadda garbati yaso ya hanashi amma yaki ji, a karshe sai yasa hannu ya hankaWe garbati gefe daya ya kife kan ciyayi da sauri habu ya bi ta hanyar da ya ke shiga ruwan ta cikin sauki yabi duwatsun dake kewayen da ruwan ya tsunbula cikinsa Ya cigaba da yin wanka yana raira waka cikin harshen fulatanci.

Mikewa garbati yayi zuciyarshi a 6ace yaci gaba da kula da shanayensu yana jiyo muryar habu dake acikin ruwa yana raira mashi wakar habaici har yana kiran shi da ragon namiji, zaifi dacewa ya koma Waura zani maimakon wando, har ma ya dinga taya su Inno surfen Gero, ranshi ya 6ace jin wannan maganar, amma saboda hakurin dake gare shi sai ya share shi yaci gaba da kula da shanayensu

Habu yana cikin yin nutso ya shige can kasan ruwan yana shawagi ba zato ba tsammani idanunsa suka sauka akan mutumin dake kwance kasan ruwa rai hannun Allah, kasancewar kasan ruwane idanunsa sunyi mashi biji biji sai ya dinga ganin kamar wata halittar ruwace me girman gaske, bakomaine ya fado mashi aranshi ba face gargadin da garbati keyi mashi akan ya daina shiga ruwa akwai mugayen halittun dake cinye naman mutun, nan fa hankalin shi yayi mugun tashi, zuciyarshi ta soma yi mashi dakan uku uku, Jiki na bari ya soma yin sama ya fiddo kanshi yana ihu na fitar hayyacin tamkar zai fasa makoshin sa, ko da garbati yajiyo ihun Habu abunka ga firgitacce bai tsaya tambayarshi menene ba, ya watsa aguje kamar karan farauta Ya nufi rigarsu.... Ya bar habu acikin ruwa Yana ta Zagba ihu tsabar rudu Ya hana ya fito daga ruwan gaba daya ya gama rikicewa.

Da gudun gaske Fulanin Rigarsu suka nufo wurin ruwan wasu ko takalma babu a kafafuwansu, wasu kuwa hannayensu ruke da makamai saboda su ceto dan uwansu, bayan sun karaso gaban ruwa wasu dattijai daga cikin kakanninsu irin wadanda suka daWe suna gwagwarmaya ne, basu da tsoro ko miskala zarratin, sun saba da duk wani abu daya shafi daji suna da kwarewa akansa
Basu tsaya bata lokaci ba suka afka cikin ruwan don su ceto rayuwar dan su, ko da suka shiga, Habu Ya kankame kakansu Yana sambatu iri iri, ya dinga nuna masu saitin inda yaga halittar da hannun shi, da sauri Waya daga cikin kakannin nasa mai karfin Hali ya kutsa kai cikin don ya kashe halittar, aikuwa yana shiga yayi tozali da mutumin dake a kwance kasan ruwan, lamarin ya daure mashi kai, ganin Wan mutun acikin ruwa, aranshi ya dinga tunanin mutunne ko aljan? Watakil aljanin ruwa ne" Wasi wasi yaci gaba dayi, har zai tafi sai kuma zuciyarsa ta dinga azalzalarshi akan ya dauko mutumin watakil tsautsayine ya afka da shi... Baiyi kasa a gwiwa ba yaje ya kinkimo tajuddeen abunka ga tsohon kashi na majiya karfi wadanda suke da shirinsu baiji nauyin taj ba akan kafadarshi ya sargafo shi, Ya fito masu da kawunansu daga cikin ruwa, ya Waga murya yana fadin"Ta mutunce ba aljani ba," Gaba Waya suka zaro idanu waje suna lekensu kowa da abunda yake sakawa aranshi, Bayan sun fito dashi daga ruwanne suka kewaye shi suna kallon shi, anan suka ga alamar bai mutu ba, da ranshi, wani abu daya basu tausayi game da shi, mummunan raunin da suka gani akan tafin kafarsa ta dama, fatar wurin ya rarake yayi rami, ba tare da sun 6ata lokaci ba suka tafi da tajudden can rigarsu, a inda suka cigaba da bashi kyakkyawar kulawa suka Waure masa raunin kafarsa bayan sunyi mashi ?an dabarun su na mutanan daji, tsawon kwanaki baya acikin hayyacinshi, ko bacci yake yi ya dinga farkawa kenan yanayi masu sambatu akan yarsa da ya baro cikin ruwa, sun rasa gane me yake nufi saboda basa jin harshen hausa, wani lokacin kamar zautacce yai ta kuka yana ambaton sunan Angel, a kalla taj ya shafe tsawon watanni ba tare da ya iya taka kafarsa ba, wannan dalilin ne yasa bai samu damar zuwa neman Angel ba, bayan haka ya yi loosing memory dinshi, sunanta ne kadai ya tsaya mashi aran shiyasa yake yawan ambatonshi....

Lokacin da ya fara samun sauki yaci gaba da rayuwa da su yana ta kokarin ya tuna miya faru dashi amma ya kasa saboda lalurar data sameshi a haka ya rayu a rigar su na tsawon shekara biyu cikin ikon Allah a daren wata rana yana tsaka da baccinsa yayi wani mummunan mafarki dangane da Angel dinsa wanda ya yi silar dawowar memory din shi, tun a cikin daren ya fara kokarin barin rigar don yaje nemanta gaba daya ya tada masu hankali duk wani mai bacci sai da ya farka yai ta ambaton sunan ?arsa da ya jefa cikin ruwa yana ta kokarin kwatanta masu sai dai sun kasa gane me yake nufi, lallashin shi suka cigaba dayi suna kwantar masa da hankali, a dole ya hakura bai fita a daren ranar ba,

A Washe garin ranar da sassafe kakansu habu ya bashi kyautar sandar da zai yi amfani da ita wurin yin tafiya, saboda har time Win kafarsa bata dawo dai dai ba, lokacin da su habu zasu tafi kiwon shanu sai yabi bayan su don ya nemo Angel dinsa, sai dai kash ita kuma a lokaci har wannan tsautsayin ya fada da ita, tana acan gidan kurkukun kaddara, kuma bata jima da barin rigarsu Danejo ba, shi kuma yafara zuwa nemanta, tunda yaga kogon ruwan ya ?afe babu ruwa acikinsa saboda damuna ta wuce, mutun na iya ganin komai dake a kasan ramin, yayi kuka na fitar hayyaci kamar ransa zai fita, har yunkurin fadawa yayi don ya kashe kanshi, da sauri su habu suka rirrike shi tare da jan shi suna lallashin shi, saidai sam baya fahimtar me suke cewa.

Sai da takai ga abakin ramin ruwan yake kwana tun safe har dare ya ritsa da shi baya motsawa anan fulanin suke zuwa kawo mashi abincin da zai ci, tunda ya ?i komawa rigarsu, yafi son zama bakin ruwa, hakika sunji tausayinshi duk da basu san meke damun shi ba, saboda son da kakansu habu keyi mashi, bukka ya haWa mashi a wurin saboda yaji dadin cigaba da kwana abakin ruwan, hada bargon lullu6a suka mallaka mashi, da duk wani abu da zai bu?ata......

Bayan wani lokaci, awata rana yana zaune abakin ruwan yayi zurfi a cikin tunaninsa, sai ga bafullatanar dajin da ta taimaki Angel, ta koro shanayenta zuwa kiwo, ita kanta bazata tuna rana ta karshe da ta zo bakin ruwan ba tun bayan da angel ta gudu tabar rigarsu bayan ta gama haukan jimamin rashinta gaba Waya danginta suka hanata fitowa kiwo, sai dai yan uwanta suka cigaba da yi, sai ranar ta samu suka barta, bata nufi ko'ina ba sai bakin ruwan da yabar tarihi a zuciyarta, tana cikin tafiya ta hango sabuwar bukkar da akayi abakin ruwan ga kuma mutun zaune ya zura kafafunsa cikin ramin, Kamar a mafarki haka take kallon shi, gaba Waya hankalinshi baya akanta....

Sautin kukan shanayenta ne suka dawo dashi daga zurfin tunanin daya shiga, firgigit yai tare dakai idanunsa gareta, duk a tunaninsa su habu ne suka zo yin kiwo, ko da idanunsa suka yi masa tozali da fuskar kyakkyawar matashiyar budurwa kamar aljana, da sauri taj ya mike yana kallon ta da tsantsar mamaki akan fuskarshi, babu wanda yayi ma wani magana acikinsu sai kallon kallo da suke jefawa junansu, ita dai danejo kallon sani take yima fuskarshi duk da tayi imanin wannan ne karo na farko data fara ganinshi, yayin da shi kuma tajuddeen baisan dalilin kallon da yakeyi mata ba, ya dai yi mamakin tsantsar kyawun dake gareta.

Jin shirun yayi yawane yasa ta soma yi masa magana da yaren fulatanci"wanane kai? Daga ganin bakuwar fuskarka ba fulanin dajin mu bane" fuskar ta da murmushi tayi maganar tana nuna shi da sandar hannunta.....

Bin ta da ido yayi don bai fahimci me tace masa ba.

Tamkar bazai tanka mata ba yace"bana jin yaren da kikai min magana shi," waro mashi dara daran idanuwanta tayi, wani irin annurin farin ciki ya gani akan fuskarta, cike da mamaki yake kallon ta ganin tana ta murmushi, bakomai ne yasa ta farin ciki ba face jin yayi mata magana da yaren Angel dinta, yarinyar da ta kwallafa rai akan son ta.

Bai yi tsammanin zatai mashi magana da hausa ba sai ji yai tace"Ya sunanka? Wanene kai? Me kake yi a rigar mu" dakyar hausar ke fita irin ta ?an koyo.

Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya bata amsa da cewa sunana tajudeen, bako ne a rigarku, ban jima da tsintar kaina a cikin ku ba," wani irin bugu taji kirjinta yayi mata, jin sunan daya ambata kamar ta ta6a jin sunan abakin angel, sai dai takasa tunawa

Cigaba tayi da janshi da fira saboda Ya kwanta mata aranta, wunin ranar danejo tana atare da taj, ba laifi ta Webe mashi kewar dake damun shi, yawo suka dinga yi acikin dajin suna tafiya suna fira kaWan kaWan saboda rashin sabo, da kuma ?arancin hausar dake gareta, bakomai ne take fahimta ba.

Tun daga ranar daya haWu da danejo, wata irin shakuwa mai karfi ta shiga tsakaninsu, kullum ne sai tazo kawo mashi abinci sau uku arana, wani lokacin gasassar masara zata kawo masu su zauna suna ci suna fira, har dai wata rana ta gayyace shi zuwa rigarsu, duk da ya nuna mata baisan zuwa, ro?ansa ta dingayi hada sanya mashi kuka, a dole ya amince mata suka je rigarsu, tashin farko danginta suna ganin taj suka tada 6alli akan basa son ganin shi tare da ita, hankalin danejo ba karamin tashi yayi ba, jin zasu rabata da mutumin da take sa ran zai maye mata gurbin Angel, akan idonshi suka rufe ta da fada kamar zasu bugeta cikin harshen fulatanci inna wuro ke ta faman zazzaga masifa tana fadin ta manta gargadin da sukayi mata akan kada ta kuskura ta ?ara kawo masu wani a cikin rigarsu! So take ta kashe kanta saboda taimakon bare ne? Ko ta manta da irin wahalar da tasha bayan tafiyar yarinyar da ta ?walla rai akanta ne?

Babban yayan su bawuro yace"tun wuri ta rabu dashi, idan ba so take su kashe shi ba" fashewa tayi da kuka hada bubbuga kafa tana fadin ita wallahi bazata rabu da shi ba, saboda zuciyarta ta kamu da kaunarshi," jin wannan maganar daga bakinta ba karamin fusata su yayi ba, Inna wuro tace"sai dai ta za6a ko su ko shi," abunka ga mai karancin hankali ga kuruciya dake damunta, da buWar bakinta sai cewa tayi zata bishi, aikuwa a fusace bawuro ya kifa mata mari, da sauri taj ya dakatar da su ganin abun nasu


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login