Showing 90001 words to 93000 words out of 298130 words

Chapter 31 - KURKUKUN KADDARA (TAKUN KARSHE) BY BOSS BATURE.doc

dinner din Ya kusa Cika

Har ta nufi stairs zata hau, kunnuwan ta suka soma jiyo mata Gunji gunjin kukan unaisah, Lokaci Waya taji gabanta yai mugun faWuwa, tsabar rudanine akan fuskanta, fasa sauka tayi cikin takun sauri take bin hanyar da take jiyo sautin kukan cike da was wasin kodai kunnuwanta ne suke jiyo mata badai dai ba

A hanzarce takarasa Bakin kofar, ta soma bubbugata tamkar zata 6alleta, muryarta da sauti mai karfi take ambaton sunanta"Unaisah!! Unaisa!! Unaisah"

Kofar tamkar an datse ta da key taki buWewa ta rufe gam, kware murya ummi tayi tana ambaton ba kowa ne akusa? Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un unaisah idan kinaji na ki yi min magana! Meke faruwa dake ne'?_

Ta faWa jiki na tsuma ta zura hannu Waya ta dauko wayarta daga cikin aljihun skirt dinta.

Layin boss man ta danna ma kira bugu biyu yayi picking ko sallama babu tace"yalla6ai kazo gida an samu matsala, na fito daga daki na na ji yo sautin muryar unaisah a dakin danish tana kuka na tashin hankali, nayi kokarin buWe kofar ta datse..."

Muryarshi a ruWe Ya furta"Chief bai dawo ba"? Yarfa hannu ummi tayi "bansani ba, yanzu na fito daga daki.... bai bari ta ?are maganar Ba, Yayi rejecting kiran ranta ne ya 6ata cewar zai zo, tsayawa tayi abakin kofar Idanun ta sun kaWa jawur ta tsorata dajin ihun unaisah, lokaci daya taji shuru babu ihun nata nan fa hankalinta ya kara tashi tadinga buga kofar da hannu da kafa Tana Ambaton"Unaisah dan Allah Kiyi min magana? Danish Ya farkane? Me yake yi maki? Meyasa kike kuka, Nashiga ukuna, Unaisah kada ki bari Ya cutar dake, Kiyi kokarin kare kanki! Unaisah kina jina? Naji kinyi shiru inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un..." hawaye har sun fara wanke fuskar ummi saboda ta gama gigita Zuciya da sake sake gani take kamar Danish Ya kashe ta ne shiyasa tajiyo shirunta.

Kamar an jeho shi Ya faWo falon A fujajen, wuyan jallabiyar shi ma akarkace take sam baya a hayyacinsa, da gudu Ya falfala Ya haye up inda ummi take atsaye tana faman buge bugen ?ofa, yana karasawa Ya daddage da iya karfin shi na karshe Ya bangaje ta da kafadarsa nan take kofar Ta zuge kanta da gudun gaske, Tsabar saurin su shiga suga meke wakana har suna bangaje juna shi da ummin america, duk wannan budurin da ake sauran yan uwan su basu san meke faruwa ba.

Shigar su keda wuya, suka taras da abun da ya daure musu kai, Yana azaune bakin gadon Ya du?ar da kanshi kasa, Sumar kanshi Ta lullu6e fuskar Unaisah wadda kanta yake abisa cinyoyinsa' basa iya ganin fuskarta sai ?an kafafuwanta, cike da fargaba da karyewar zuciya boss Ya furta Sunan shi"Danish! Unaisa meya faru ne? Ka yi mata wani abu ne? Ha?i?a sun yi mamakin farkawarsa babu wanda yayi tsammanin zai tashi a cikin ?an kwanakin nan.

Adabarbarce ya kare maganar, tamkar yayi magana da bango babu alamun danish zai saurare su duk sun bi sun rude mutun kamar Ifritun aljani gashi ya damki yarinya a hannun shi

Cikin shesshe?ar kuka Ummi take rokonshi akan Ya saketa, kada ya kashe masu ita.....'

Karfin Hali taj yayi da sauri Ya nufi gefen gadon inda su ke a zaune Ya mi?a hannayenshi biyu da niyar ya kawar da ita, Dam?ar hannunsa Danish yayi tare da dagowa yana faman lumshe idanun shi tamkar na wanda yasha giya, muryar shi da kasala Ya furta"ina bukatar ruwan da zan yayyafa mata" kusan atare ummi da Taj suka sauke ajiyar zuciya, saboda sunyi tsammanin baya ahayyacinsa ne.

juyawa ummi tayi da sauri ta fita daga dakin sai gata ta dawo hannunta ru?e da robar ruwan da ta Wauko a fridge ta mi?a ma taj, shi kuma Ya kar6a ya Mi?a ma danish, a hankali Ya sanya hannu ya kar6a bayan ya cire murfin ya tarfa hannunsa dake Wan kerma Ya Webi ruwan ya watsa mata akan fuskarta, lokaci Waya ta zabura zata fara buge buge da sauri boss Ya dam?i hannunta, tare da dago da ita ya zaunar.

Wani jiri jiri take gani a idanunta, hannu tasa ta dafe makoshinta tana fadin ruwa ruwa zan sha.

Kwafa mata ruwan yayi abaki ta rurruke robar duka ta shanye shi, ta dago da luhu luhu idanunta wadanda suka kada jawur da su Sam ta manta a ina take zaune, gani take kamar amafarki lamarin Ya afku, Kwata kwata bata lura da danish ba, wanda ke a gefenta kuma shi ya bata ruwan da ta sha.

"Unaisah, are you okey? Ina fata bai ta6a lafiyar jikin ki ba"! Cikin kulawa ummi keyi mata magana

Kallon ummi tayi murya na Wan rawa ta furta"nayi mafarki danish Ya farka, Har Ya sha?e min wuyana" ta faWa tana shafa wuyanta

"Ba mafarki ki ka yi ba, dagaske ne Ya faru, danish Ya farka sai dai baya a hayyacinsa ne lokacin daya sha?e ki" boss ne ya bata amsa, da wani irin Hanzari ta dubi danish da ke gefen ta, idanunsa suna a lumshe numfashin sa na fita a hankali.

Lokaci Waya ta fashe da matsanancin kukan farin ciki, ta kamo yatsun hannayensa acikin nata, Muryarta cikin shesshe?ar kuka take fadin"My man...kana lafiya? jinjina mata kai ya danyi alamar eh.

"Alhamdulillah Ya Allah, Alhamdulillah..." sakin hannunsa tayi ta sauko daga kan gadon ta zube saman gwiwowinta tare dakai goshi kasa tayi sujjada tana mai nuna godiyarta ga Allah.

Murmushi taj ya soma saki yana kallon danish, Wani irin farin ciki ne Ya lullu6e shi mara misaltuwa Yaji dadin farfadowar nan tashi, Har ya fara tunanin haduwar shi da Prime minister.

Har yanzu Danish babu fara'a akan fuskar shi, jefi jefi Ya ke kallon su da lumsassun idanunsa, ganin lokaci na shirin kure masu yasa ummi ruko hannun unaisah tace su tafi su fara shiryawa, kamar karta baro dakin tana tafiya tana waiwayon danish gani ta ke kamar in ta fita zai koma yar gidan jiya, har sai da boss yace mata zai kira chief yanzu awaya tare da sheikh imam tukunna ta Wan samu kwarin gwiwar barin dakin.....

Batare da 6ata lokaci ba, Taj Ya kira chief awaya ya sanar da shi dangane da farfaWowar danish, A lokacin chief Har Ya kira likitan da zai duba shi, yayi murnar jin zancen tashin danish, kafin ma karasowar su dakin sai da ya Kira Shiekh Imam suka jira Ya zo falon Kafin suka sauko shi da likitan dayazo duba dashi a tare suka nufi dakin shigar su keda wuya Chief owais ya nufi danish, tamkar dan uwansa na jini Ya mi?a mashi hannu ya taimaka mashi ya sauko daga kan gadon gaba Waya yayi hugging dinsa a jikin shi, ya Waura hannayensa abayansa yana dan bubbuga shi, har rada yai mashi a kunna ya furta"nayi farin ciki da samun lafiyar ka, Ina fata babu abun da ke yi maka ciwo ayanzu..." ya fada tare da dafe kafadun danish ya dago da shi.

Babu wanda baiyi farin ciki acikin su ba, Musamman sheikh imam Ya ambaci kalmar alhamdulillah tafi sau a kirga, ya Waga hannayensa sama ya dinga zubawa Allah kirari HaWi da nuna godiyarsa ga nasarar da suka samu, Bayan ya gama ya janyo danish din duk da bai sakar masu fuska ba wannan bai shafe su ba, dama su burinsu ya farfado kuma Alhamdulillah kwalliya tabiya kudin sabulu, Rungume shi shiekh imam yayi tamkar zai mayar dashi cikin sa, ya dinga shafa sumar sa yana karanto addu'o'i yana shafe mashi ko'ina na jikinsa.

Ko da likitan ya duba danish baiga komai ba sai ma wani abun ban mamaki daya gano wato Lafiyar dake gare shi, har ta wuce wadda hankali zai dauka, babu ko ciwon kai a tare da shi.

Bayan tafiyar likitan shawarwari suka tsaya sunayi atsakanin su, kafin daga bisani chief ya raka shi bathroom don yayi wanka, Kafin ya fito aka shirya mashi lafiyayyan abinci a daki aka shigo mashi da shi, atare da chief suka ci abinci, gwanin ban sha'awa kamar wasu yan uwan juna sai daya tabbatar danish Ya cika cikinsa tukunna ya samu kwarin gwiwar sanar da shi dangane da uncle dinsa dake son ganinsa, ya nemi alfarmar yana so su tafi atare, shiru danish yayi mashi dama ya?i furta masu magana tun da ya farka kamar wani kurma sai dai yabi su da ido.

Tarairayarsa suka dinga yi suna lalla6a shi, duk don ya amince, amma Wan tahalikin nan yai shiru, dabara ce ta fadowa taj da sauri yace mashi a tare da su unaisah zamu tafi da sauran ?an uwan ka, kuma duk sun amince zasu je.

Jin ya ambaci zasu tafi da su unaisah ne yasa shi saurin amince masu ta hanyar jinjina masu kai, domin kuwa bazai bari su tafin masa da yan uwansa ba, Murmushi sukayi gaba dayansu ganin sunyi nasara akanshi... Nan fa suka fara shirya shi, kamar wani yarima.

Lokacin da su sajeed suka ji labarin Farkawar danish, Aguje suka watsa da gudu suka nufi bedroom dinshi, Tsabar farin ciki maimakon suyi dariya saima suka fashe da kuka suka dinga rungumar shi, Dadi kamar zai kashe su, Shi kanshi yayi farin ciki da ganin su duk da yaki tanka masu sunyi sunyi dashi akan ya bude baki yayi masu magana amna yakiya sai dai fa kallo ko irin sakin fuskarnan babu
Hakan bai wani dame su ba, tun da ya farka falillahil hamdu, duk wannan mai saukin ne, dama sun riga da sun san halin kayan su, bayan sun gama murnar samun lafiyan dan uwan nasu, Ummi ta tattarasu suka koma dakunansu, kowan na su yayi wanka, Suka soma shiryawa cikin kayan su cike da zumudi, bayan haka dangane da abun da ya faru a hall na kashe Hasken lantarki aikin chief owais ne shine ya tsara komai, tare da interior designers da sukayi decoration na hall din saboda yana son yaga reaction din family nasa, bayan ya gama tsara komai, Shi yafara halartar dinner din, ya riga su Unaisah tafiya kamar yadda ya tsara saboda yana son ya fara yi masu hanyar shiga batare da an samu matsala ba, tun da wurine mai tsaron gaske, su boss da big guy ne da wasu daga cikin jami'an isod sukayi jigilar daukar su Unaisah a cikin motocin su, suka kawo su bakin hall din, bayan tafiyar su tuni Ummi ta shirya saboda ta samu amincewar chief akan fitar da za ta yi, taje ne ya nema mata alfarma, Jami'in isod ne yayi driving dinta zuwa gidan da tace zata je na kawarta.

(Wannan shine abunda ya faru kafin zuwansu dinner hall din)

(CIGABAN LABARI)

HaWa ido su kayi da prime minister, cikin sanyin murya ya furta"shi ne...?
Jinjina mashi kai chief owais yayi alamar eh, wata nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke, fuskarshi dauke da wani irin annurin farin ciki mara misaltuwa da tafukansa ya tallabo fuskarshi yana bin shi da kallo mai nuni da tsantsar ?aunarsa, kasa jurewa yayi baisan sa'adda Ya janyoshi zuwa ga faffadan kirjinsa yai huggin insa tightly kamar zai mayar da shi cikin cikinsa, hannayensa biyu dukansu ya tallabe bayan danish dasu, yayin da zuciyoyinsu ke harbawa da bugu mai tsanani, wani irin yanayi mara misaltuwa....

Hakan ba karamin Waga hankulan mutanan dake a hall din yayi ba, gaba Waya sun ?ara rudewa da ganin rungumarshi da prime minister yayi.

Muryar Hajiya saratu tamkar zata fashe da kuka ta furta"wai ba zakuyi mana bayanin su wanene ba? Kun barmu atsaitsaye cirko cirkon kamar sakarkaru" ta fada tana kallon chief owais don ta fahimci yasan da zamansu tun da taji Pm hateem ya tambaye shi shine....
"Owais su wanene wadannan Yaran! "? Baba obie ne ya furta maganar

Sai lokacin chief Owais ya soma takowa yana tunkaro wurin da su ke atsaitsaye, cikin dakakkiyar muryarsa ya soma magana genlty

"A gafarce ni, nayi laifi ban sanar da zuwan su ba....' ya faWa awayance yana bin kowan nan su da kallo.

"Idan ba zaku manta ba, na ta6a baku labarin Yaran da Sojin america suka tsinta a evil forest, suka dam?a case dinsu ga hukumar mu ta Isod, ga wadanda basu san da zaman su ba, to ga su nan, sune yaran da nake ru?o a hannuna, na gayyace su ne don su gana da dangina saboda sun zama tamkar ?an uwa agare ni"

Lokacin da ya ?arasa maganar, hajiya saratu ta zabga salati tana huci ta furta"wlh baka isa ba Owais! Ka haukace ne? da Zaka kwaso mana tsintattun Yaran da ba'asan asalin su ba, ka kawo mana acikin dangi? Anya kuwa kana a hayyacin ka? Rai amatu?ar 6ace tayi maganar, Hankalin su Unaisah ba karamin tashi yayi ba, Masu tsoro acikin su har sun fara Ja da baya jiki na kerma...

A matu?ar firgice Senate Lateef Yace"kana nufin ?an uwan yaron nan da ya rikiWa ya koma maciji"? Wannan maganar da senate lateef Ya furtane Yaja hankulan mutanan Hall din, Tashin hankali ne tsantsa akan fuskokinsu, Muryoyinsu a kidime suke maimaita kalmar maciji ga wadanda basu san da zancen faruwar lamarin ba, nan take Pravin yayi wuf ya kwashe komai daya faru ya sanar da su, Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un shine abunda suke furtawa a bakunansu....

Prime minister sam baya gane me su ke cewa saboda idanunsa sun makance, Ya kurmance baya ji baya gani tunda ya rungumi danish a jikin shi bai ?ara Wago da kanshi ba, Kamar daga sama yaji an dam?i damtsen hannunsa da ?arfi aka raba shi daga jikin danish wanda bakowa ne yayi hakan ba face Senate Lateef, ya janye shi gefe guda, Yana faman zazzaga masifa"wlh bazamu lamunta ba! Don Na fahimci bakasan ciwon kan ka ba, taya zaka kwaso mana mugun abu ka kawo mana a cikin dangi? Wannan wata iriyar masiface? So kake ka tarwatsa mana farin cikin mu? Ko kuwa so kake ka ?arar mana da dangin mu ne!? Wai ma wanene ya baka shawarar ka kawo su wurin nan....."?

Tunkafin Senate lafeef ya kare maganar, sautin shesshe?ar kukansu Ya soma karaWe hall din, sun girgiza da jin munanan kalamin da ake fada akansu, bayin Allah da farin cikin su da zumudi su ka zo ganin dangin chief owais sunyi tsammanin suma zasu sosu kamar yarda shima yake son su ashe ba haka bane......'

"Wallahi sai dai ka za6a, ko dai ka tattara su ku koma can gidanka, ko kuma mu mu fita mubar maka hall din ka ?are dinner din tare da su, don wlh baka isa ka jazamana masifa ba, wannan ay annobace ka kwaso mana" acewar hajiya saratu ta faWa tana watsa hannayen ta.

Chief owais dake sauraronsu Waya bayan Waya yake binsu da kallo daman yasan za'a rina ba lallai su wanye lafiya ba, sai gashi ta tabbata, kowa da abun da yake tofawa, mutane ?alilan ne basu tanka ba.

Hankalin Hateem yafi na kowa tashi, ganin za'a raba shi da muradin ranshi, Ga samu ga rashi, Ji yake tamkar Ya fasa ihu, ?iri ?iri su Senate lateef sun rurru?e hannayenshi gudun kada Ya ?ara tunkarar Danish.

Security advisor din Hateem ne ya tambayi meke faruwa ne? Muryarsa a bubbuWe yasha ya bugu baya gane komai sama sama yake jin kan shi, Kasancewar basa jin yaren hausa basu san takan zancen ba, da sauri pravin uban ?an zigi Ya buWe baki da niyar Ya sanar dasu, wata irin tsawa mai kama da saukar aradu chief owais Ya sakar mashi, wadda tay matu?ar gigitasu a hanzar ce yaja baki ya yi shiru.

Dalilin dayasa ya yi mashi hakan gudun kada ya sanar da su, don muddin sukaji da zancen Yaron daya rikida ya koma maciji to kuwa nan take zasu sa a dakatar da taron bayan haka zasu sanya jami'ansu su kori su unaisah don ba zasuyi ganganci da rayuwar hateem ba...

Cikin sanyin murya prime minister yayi ma mutanansa bayani da yaren da zasu gane ya kwantar masu da hankalin su, da cewa family issue ne kuma in sha Allah zasu shawo kan matsalar yanzu, iya abun da ya fada masu kenan, dama kuma ba ahayyacin su suke ba, shiyasa abin yazo masa da sauki da tuni sunsa an tada taron gaba Waya.

Da kakkausar murya chief owais Ya soma magana babu annuri akan fuskarshi.

"ni ne silar dana kawo su wurin taron nan, bawani ya bani iznin in gayyace su ba, kuma basu suka nuna suna son zuwa ba, face don ni nake so su zo...." bai ?are maganar ba, Hajiya saratu tayi yunkurin dakatar dashi aikuwa a fusace Ya Waga mata hannu alamar tayi shiru, Waro idanu waje tayi ba ita ba hatta sauran mutanan hall din sunyi mamakin rashin kunyar da owais yayi.

"Suma ya'yane kamar kowa! Yaro kuma da bashi da lafiya, Bayin kanshi bane, Aljanu ne suka shafe shi, kuma ya samu lafiya bayan da shiekh Imam ya dau kwanaki Yana duba shi.....' bai ?are maganar ba, muryar sheikh imam ta karaWa kunnuwansu a yayin da yake shuowa dakin taron.

"Tabbas maganar owais gaskiya ne, Yaran nan ba masu cutarwa bane, mutanene kamar kowa, kuma abin a tausayamawa ne....." a tsanake cikin hikma sheikh imam ya fayyace masu komai dangane da halin da danish yake a ciki, wasu sun fahimta yayin da wasu sam kamar kurame basa gane komai.

Gaba Waya hall din Ya rikice da maganganunsu, wasu suna hura wutar akore su daga hall din yayin da wasu sukayi shiru basu tanka ba irin su mai girma sharafudden, sun natsu suna bin duk wani mai magana da kallo, ga dukkan alamu akwai abun da suke jira shiyasa suka yi shiru.

Cikin sanyin murya prime minister yace"dan Allah kowa yakwantar da hankalin shi, Idan har saboda ni aka shirya dinner din nan, to ina rokon alfarmar ku bar su na yau kawai su zauna, in sha Allah ba abinda zai faru" idanunshi akan danish ya ?are maganar, wanda tun shigowarshi hall din idanunsa suke alumshe tamkar ma baisan sunayi ba, su batool daine suka ruWe jikinsu sai


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login