Showing 18001 words to 21000 words out of 298130 words

Chapter 7 - KURKUKUN KADDARA (TAKUN KARSHE) BY BOSS BATURE.doc

daga tunanin da yake sa?awa aranshi, Murmushi ya saki, Hateem Ya ruko hannunshi suka nufi jigunannun royal sofas din Falon masu numfashi ?an ubansu afagen haWuwa.

Yazrin ta ru?e hannun chief Owais acikin nata, Har suka samu wuri suka zauna saman sofa, Lokacin da Taj yai tozali da Nazli Har saida gabanshi Yadan fadi, aruWe Yake kallonta sai ya dinga ganin fuskar Danish akan fuskarta, Prime Minister ya lura da rudanin dake akan fuskarshi, gyaran muryar da yayi mashi ne yasa shi yin saurin kallon shi, da ido yai mashi alamar ya yaganta, jinjina mashi kai Taj yayi, suka sakar ma juna murmushi.

"Nazli" Prime minister ne Ya kira sunanta, A hankali Ta dago da fararen idanuwanta ta daurasu akan fuskarshi.

"Dad, welcome back" ta fada ba tare da ta kau da idonta daka kallon shi ba.

"Yawwa, Baki ga mutanan da nazo da su ba" sai lokaci ta kalli Boss man tamkar bata son yin maganar ta furta"Hey, How are you"

Fuskarshi da fara'a yace"lafiya lou fatan na same ki lafiya"
Amsa mashi tayi, harzata dukar da kanta Yazrin tayi saurin cewa"Sister, baki gaishe da big bro ba" ba tare data kalle shi ba tace"Okey" Iya abunda ta furta kenan.

Tsantsar mamaki ne akan fuskar Boss man, ko a mafarki bai ta6a ganin mace mai izza irinta ba, bai ta6a tunanin za'a Iya samun macen da zata kau da idonta daga kallon chief owais, sai akan Nazli.

Chief owais tamkar shima baisan da zamanta ba, hankalinshi na akan wayar hannunshi daya ru?e Yana daddanawa

"Nazli, ki gaishe da Yayanki" babu wasa akan fuskar Hateem Yayi mata maganar, tun daga kan Yanayin yadda ya furta mata maganar zaka fahimci ranshi ya sosu da abunda Nazli tayi

Batare data dago ta kalli chief owais ba ta furta"ya kake"

Banza yayi da ita, har saida prime minister Ya ambaci sunanshi tukunna Yace"Uncle kada hakan Ya dame ka, ka bar ni da ita, dai dai nake da ita" cikin nuna isa Yayi maganar.

Daure fuska Yazrin tayi, ranta ya 6aci bata ji dadin abunda Nazli tayiwa Chief fa, Kodan saboda ba?on da suka zo dashi aganinta bai kamata tayi hakan ba.

Mi?ewa tayi tare dakai hannu ta dauki laptop dinta, ko sallama babu ta nufi upstairs, sautin takalmanta har cikin kunnuwan su.

Bayan tafiyar Nazli, Gimbiya Mujeedat ta sauko down cikin shiga ta alfarma, tunkafin ta ?araso take sakar masu murmushi.

"Marhaban bika, My Son In-law, Long time bamu haWu ba, dama kana a kasar," ta jefe mashi tambayar tare da samun wuri ta zauna tana fuskatar su.
?agowa chief Owais Yai tare da kallonta, da murmushin gefen fuska ya furta"ban jima da dawowa ?asar ba, nayi laifi ban le?o mun gaisa ba, sai yau Allah Ya nufa" taj dake kallon gimbiya mujeedat afakaice Ya jinjinawa haduwarta, mace kamar kanta aka fara tsara kyau ta haWu ga Iya dattako.

"Sannu da dawowa Mijina, Ina fata anyi nasara"cikin kulawa tayi maganar tana kallon Hateem, lumshe mata ido yai tare da Wan jinjina mata kai alamar eh
Dauke idonta tayi daga kan fuskarshi ta dubi Taj, baiyi tsammani zata kula shi ba, amma sai yaga ta sakar mashi murmushi tana fadin"barka da zuwa" yace mata yawwa.

"Mijina baka fadamin wanene wannan ba"?
"Sunanshi tajudeen, abokin aikin Owais ne"
"Masha Allah, malam Taj, naji dadin haduwa dakai, Ya aiki"?
Yace mata lafiyalou," sun Wan Wauki lokaci suna tattaunawa kafin daga bisani,
Prime minister Yace da ita"Sheikh Imam Yana aciki"?
"Eh, tun Wazu daya zo, na kaishi masaukin da aka tanadar masa,"

"Okey, bari na shiga wurinshi" ya fada tare da mi?ewa ya nufi Hanyar zuwa part din da shiekh Imam Yake.

Kafin dawowarshi, Biyu daga cikin masuyi masu hidima suka shigo falon, Hannayensu ru?e da ?ayatattun trays, daga saman an jera kayan abinci kala kala da drinks"

Cikin girmamawa suka gaishe da su tajudeen, kafin suka sauke farantan kan lallausan carpet din dake awurin.

"Big bro, fadamin me kake son ci, zan zuba maka da kaina" yazrin ce tayi mashi maganar, girgiza mata kai yai alamar a'a, zuciyarta ajagule tace"Pls, kada abunda sis nazli tayi maka Ya 6ata maka rai, kariga da kasan halinta" calmly ya furta"okey" daga haka bata ?ara yi mashi magana ba, zu?unna tayi batare da girman kai ba tace da masu hidiman da suka kawo abincin ku tafi ni zan yi serving dinsu, tafiya sukayi, Ita kuma ta zauna ta dauki lemu me sanyi ta tsiyaya shi a cup ta zuba ma Taj ta mi?a mashi.

Har cikin ranshi yaji dadin hakan, kuma ya yaba da hankalinta, tun anan Ya fahinci tafi sau?in kai Akan ?ar uwarta Nazli, nan take Ya tuna da Halin Danish miskilancinshi sak kalar Na nazli ne, Aranshi yace Komai nasu kala daya kamar Wan uwanta"

"ya owais, zan je na dawo" yazrin ta fada Tana kallonshi, amsa mata yai da ok, da sauri ta nufi upstairs.

Bayan taj Ya kammala shan lemun, ya fara shan fresh fruit din da aka kawo masu.

Elevator Yazrin Ta hau, ta sauke ta a second floor, moving quickly Ta nufi Wakin Nazli, a buWe ta samu ?ofar, zura ?afarta keda Wuya ta fara Cin karo da takalman Nazli a tsakar daki, Ga mayafinta kan floor, Da sauri takai idonta kan katafaren gadonta, tana daga kwance doguwar sumar kanta ta lullu6e mata bayanta.

Cikin sanyin murya Yazrin ta soma Yin magana tana tunkararta.

"Sister, Meyasa kika za6i ki ?untatawa zuciyarki? kina sonshi amma meyasa kike ja mashi aji"? Shiru Nazli bata tanka mata ba, babu lamun zata motsa.

"Ni banga amfanin 6ata mashi rai da ki ke yi ba, da hankalinki da tunaninki, gaban ba?on daddy, kike nuna ba'a isa dake ba, wannan ba Wa'a bace, shi kanshi daddy ranshi ya 6aci da abunda kikayi," dakatawa ta danyi da yin maganar tana kallon Nazli dake kwance tamkar maiyin bacci.

"Nasan kina jina, ban damu ba dan kin share ni, Nidai shawara nake baki a matsayina na ?ar uwarki mai son farin cikinki, kada kiyi wasa da damarki, mata dayawa suna hauka akan son Ya owais, basu ta6a samun damar yin tozali dashi ba, amma ke cikin sau?i Kin same shi, Kina ?o?arin Yin watsi da damarki, bana son kiyi danasani sister," har cikin zuciyarta take furta kalaman.

"I thought when you saw him, you would rush to hug him and tell him how much you missed him, but sai naga akasin hakan, wai yaya owais kika share kamar wani tsaran wasan ki, ki daina ganinshi kamar wani tsaranki, kafin a haife ki shi aka fara haihuwa"

Shiru Nazli bata motsa ba, Yazrin taci gaba da cewa"Ki cigaba da ja mashi aji, wata rana zakiyi danasani, Allah yasa Ya auri wata bake ba...." kafin Ta ?are maganar A fusace Nazli Ta yun?ura ta mi?e zaune Ta rarumi laptop dinta dake agefenta, daga Inda take ta daddage ta wurga ma Yazrin ita, da sauri Yazrin Ta tarbe laptop din da hannu biyu, fuskarta dauke da murmushi tace"kinji haushin magana ta ne"? KaWan kika gani, sai ma ranar da za'a shafa fatihar auranshi, Haukan da za ki yi sai yafi wannan" wurga mata laptop din Yazrin tayi kafin ta juya da gudu ta fuce daga dakin ganin yadda Nazli take huci.

A hankali ta Waura kanta saman pillow, haWi da lumshe idanuwanta, red lips dinta sun ciza launinsu, ita kadai tasan irin radadin da take ji aduk lokacin da tayi ma owais haka, ita aganinta batayi laifi ba, shi yakamata yazo inda take don ya nemi afwarta akan tsawon lokacin daya Wauka ba tare daya je canada ba, Al?awari ne ta Waukarwa kanta idan har baizo wurinta Ya wanke kanshi ba ita kuma har abada bazata ta6a kula shi ba, koda an shafa fatihar auran su!!!
Don ita ba irin matan da namiji Yake juyawa bace, macace mai aji, mai kuma Ji da kanta, zata iya ha?ura da komai akan izzarta.

Idan muka koma Falo, Bayan ?an mintuna, Prime Minister Ya shigo falon tare da Shieikh Imam, sai kuma gimbiya Mujeedat, mi?ewa Chief Owais Yai shima Taj Ya mi?e, suka yima Gimbiya mujeedat sallama kafin suka dunguma zuwa harabar ajiye motocin gida, jami'ae suka buWe masu ?ofa suka shiga, Ajere motocin suka nufi gidan baba Obie.


*BABA OBIE*


Bai jima da farkawa daga bacci ba, jikin shi yayi tsauri, wani irin azababben zazza6i ne Ya lullube shi, har sai da Senator Lateef ya kira family doctors din su, domin duba lafiyar mahaifinsu, a ?alla likitocin sun Wauki tsawon mintuna talatin akan shi suna ?an bincike binciken su, kafin daga bisani suka tabbatar masu da cewa Firgici ne da tsoro ke damun shi, Idan Har ba'ayi gaggawar kawar mashi da abunda ke razanar da shi ba, zuciyarshi zata Iya bugawa, Jin wannan maganar daga bakin likitocin yayi matu?ar ?ara Waga hankulansu, musamman Hajiya saratu duk tabi ta ruWe, hannayenta biyu asaman kanta take ambaton Inna lillahi wa inna ilaihirraji'un, mun shiga Uku, ?iri kiri ana so aga bayan uban mu.

Bayan tafiyar Likitocin, gaba Wayansu suna adakin Obinna, zuciyoyinsu cike da jimamin sakamakon ciwon shi, ya kasa ta6uka komai, duk ya yamutse tsufanshi Ya ?ara bayyana, Senate lateef ne ya taimaka mashi ya shiga bathroom yai wanka, ya fito ya canza suturar jikinshi, Kafin Ya shimfiWa mashi darduma, acikin dakin yai sallar da bai samu damar yi ba, sam babu natsuwa atattare da shi, bayan Ya kammala Yin sallar ne, senate Ya ru?o hannunshi, Ya zaunar dashi kan lallausan carpet, da sauri His excellency abdul razak Ya mi?e daga kan arm chair din da Yake azaune Ya nufi Kayan abincin da Hajjaty ta kawo mashi, Ya sanya hannu biyu ya Wauko su yaje ya ajiye farantin gaban Baba obie.

Saukowa Hajiya saratu tayi daga gefen gadonshi, ta zauna gefenshi idanuwanta acike tab da hawaye take yi mashi sannu.

"Babana Allah Ya baka Lafiya, Ka daure ka ci abinci, sai kasha maganin zazza6in da likita Ya bada abaka" cikin kulawa tayi mashi maganar, a raunace ya Wago da idanuwanshi waWanda suka kaWa jawur dasu Ya Waura su akan fuskar Saratu na tsawon mintuna biyu, kafin ya kau da idon Ya dubi Senate Lateef da ke ?o?arin zama gefen gadonshi, A hankali Ya maida idonshi akan fuskar His excellency deen da Pravin waWanda ke A zaune kan carpet.

Lumshe idanuwanshi ya Wanyi, kafin ya ware su kan fuskar Twins dake zaune kan carpet kamar wasu mutanan kirki, sun yi zaman cin tuwo kowa da abun da Yake sa?awa aranshi.

"Sannu baba, Allah Yabaka Lafiya," su twins ne sukayi mashi ya jiki, kafin sauran mutanan dake adakin suma sukayi mashi Ya jiki, bai samu damar amsa masu ba, Sai dai bin dakin da yake yi da kallo.

Muryarshi adisashe Yace"Hateem baizo bane ko baku fada mashi halin da nake aciki ba"?

Shiru su ka yi jin, kowa yana jin fargaban fada mashi abunda Prime minister Yayi.

"Kunyi shiru bakuce komai ba! ina Owais? Yace min zaizo yau ya akai ban gan shi ba"? fuskarshi Wauke da matsananciyar damuwa Ya furta maganar.

Hajiya saratu ce tayi ?arfin halin buWe baki, ta labarta mashi abunda Pravin Ya fada mata dangane da tura jirgi da hateem yayi zuwa Sudan dan adauko Sheikh imam Ya duba jikin Yaron daya rikiWa Ya koma maciji.

Tsabar 6acin raine tsantsa akan fuskar Obie,

Senate Lateef yace"tun safe babu wanda ya kira awaya cikin su don ya tambayi ya ka kwana, Gaba Waya sun Waura burin duniya akan Yaron da muke zargin Abokan hammayar mu ne suka turo shi donsu tarwatsa zuri'armu" afaWace senate Lateef Yayi maganar
His excellency deen Yace"gaskiya bamu ji daWi ba, Hateem bai kyauta mana ba, yayi abu gamon kanshi batare daya nemi sha'awar mu ba, ni narasa gane meke damunsu daga shi har Owais din idanuwansu sun makance basa ji basa gani indai akan taimako ne, toh gashinan dai suna ?o?arin jefa rayuwar mahaifinmu cikin matsala, Fisabilillahi Ina amfanin hakan"? Ya ?are maganar tare da jan dogon tsoki.

Tun da suka fara magana, Pravin Yake ta tsuma, tsabar zumuWun su ?are maganarsu don ya samu damar tunzura su, ganin Deen Ya dasa aya a maganarshine ya samu ?warin gwiwar cewa
"Yakamata ayi gaggawar Waukar mataki akan Yaya Hateem, Shina fi ji, duk da ba fata nake Yi ba, amma idan wani abu Ya same shi, Ba iya family din mu Ya shafa ba, Nigeria gaba daya ya shafa, ?asar da yake mulka bazasu ta6a sassauta mana ba idan wani abu ya samu shugabansu, koda kuwa kwarzane ne Ya fito akan fatarshi sai sunji ba'asi" maganar pravin ta ?ara Waga masu hankulansu, babu wanda yai wannan tunanin saida Ya furta tukunna suka ankara da gangancin da suka Yi.

Ganin yadda suka Waga hankalinsune Yasa shi ?ara samun kwarin gwiwar cigaba dayin magana.

"Ga kuma mahaifinmu babu ?oshin lafiya, ba zamu zuba ido muna ganin wani bakon abu na neman yi mashi illa ba, dole mu dauki mataki, wallahi indai akan baba ne sai inda ?arfin mu Ya ?are, dole Yaron Yabar estate din nan, ai nan ba gidan marayu bane" ya faWa yana mai nuna 6acin ranshi
Senate Lateef Yace"Sannan, shi kanshi Owais din zamu Yanke ala?arshi da Yaran! Babu shi babu su, shi kuma Hateem tunkan Aje ko'ina, acikin satin da zamu shiga Ya tattara Ya koma canada, don ba zamu bari Yaja mana bala'e ba, Idan muna son ganinshi koda duk weekend ne zamu iya zuwa canada wannan ba damuwarmu bace, awurinmu tamkar zuwa kano ne"

Duk maganar da sukeyi akan kunnan Baba Obie, yayi shiru Yana sauraronsu, abincin ma Yagaza cin shi, hajiya saratu sai lalla6a shi takeyi akan yaci amma Ya?i Ya, Ranshi Ya 6aci matu?a, bakomai yafi ?ona mashi rai ba face rashin zuwan Hateem da Owais, bayan sunga halin daya shiga adaren Jiya, maimakon su mayar da hankali wurin kwantar mashi da hankalinshi, sai suka ta'alla?a wurin Kula da abun da Ya cutar da rayuwarshi, me hakan Yake nufi?

"Baba dan Allah kaci abincin idan ba haka ba Hankalina bazai kwanta ba" hajiya saratu ce tayi mashi maganar yayin da take mi?a mashi abincin data Webo a cokali, kawar da kanshi gefe Waya yai batare daya furta mata magaba ba.

"Grandfa, please kaci abinci, gaba Waya mun damu da halin da kake aciki" zaid ne yayi maganar.
Kafin wani Ya kuma furta magana, Suka soma Jiyo dirar motoci acikin Estate din
"May be sune suka ?araso" Acewar His excellency abduk razak.

"Anya kuwa sune? Naji Wazu Yaya deen ya kira Yaya sharafuddeen nafi tunanin shine Yazo" Pravin ne yai maganar, dakatawa su ka yi da yin magana, gaba Waya hankalin su ya koma akan ?ofar dakin, sunyi matu?ar ?agara da son ganin wanene zai shigo.

Knocking ?ofar dakin Akayi, Pravin Ya Waga murya tare da cewa"ku shigo daga ciki"

Lokacin da ?ofar Wakin ta buWe, Prime Minister Hateem Ne Ya fara shigowa yana maiyi masu sallama, Chief Owais Yana abiye da bayanshi, su kadai suka shigo, Boss man da sheikh Imam suna acan babban falon gidan suka zauna saman sofa.

Tun da suka shigo dakin kowa yayi shiru yana binsu da kallo, su kansu sun fuskanci babu Lafiya, cikin girmamawa Hateem yabi ?an uwanshi Waya bayan Waya ya gaishe da su, fuskokinsu babu walwala suka amsa mashi, chief Owais ma Haka yabi kowan nan su ya gaishe da shi, banda Pravin, baya acikin jerin mutanan da suka kai matsayin da zai iya gaishe da su, tunfil azal basu jituwa, shiyasa hajiya saratu take matu?ar jin haushin Owais, saboda ?iyayyar da yake nunawa mijinta, ko yanzu daya gaishe da ita da?yar ta amsa mashi tana faman yamutsa fuska.

A hankali ya zauna daga gaban farantin kayan abincin baba Obie, wanda tun da suka shigo Wakin idanuwanshi suke akan fuskokinsu, Idan ya kalli prime minister sai Ya kalli Owais, har gaishe da shi su kayi bai amsa masu ba, hakan ba ?aramin Waga hankalin prime minister yayi ba, don wannan alama ce dake nuna cewa mahaifinshi yana fushi da shi.

da sauri Zayn da zayn suka haWa baki wurin gaishe da Prime minister, bayan ya amsa masu suka gaishe da chief Owais, shima ya amsa masu fuskarshi babu walwala, daga haka babu wanda ya ?ara furta magana, munafuki pravin a fakaice yake sakin shu'umin mirmushi, wato ha?arsa ta cimma ruwa

Baba Obie, Ya tsayar da idanuwanshi akan fuskar Owais, kamar yadda yake kallon shi shima haka yake kallon shi

"Hateem, meyasa tun safe bakazo gida ka duba ni ba"? Baba obie ne Ya jefa mashi tambayar.

Da?yar Ya iya buWe baki Yace"Kana araina baba, nasan ban kyauta ba na rashin zuwana, ka gafarce ni"

"Baka fada min me ya dakatar dakai daga zuwa ba? Shi nake son ji"

Da sauri Zayn da zaid suka mi?e ganin irin kallon da hajiya saratu tayi masu alamar su tashi su tafi, salin Alin suka fuce daga dakin

A tsanake Prime minister Ya labarta mashi abun da Ya faru.

"Saboda wa kazo ?asar nan"?

Jim ya Wanyi kafin Ya furta"saboda kai babana"

"Taya za'ai nayarda da maganar ka Hateem? Abun da Ya cutar dani daren Jiya shi ka tsaya taimako, tun safe kana can kana yi mashi hidima, yayin da ni kuma nake kwance ba lafiya"

Tuni prime minister Yasha jinin jikinshi, duk sai yaji ba dadi, zuciyarshi ta karaya
"Baba bansan baka da lafiya ba, dan Allah kayi hakuri idan na 6ata maka rai, amma ka riga da kasan halina kuma kaine kake ?arfafa min gwiwa akan yin taimako, ka sha fada mana tun muna yara idan muka ga mutun na bu?atar taimako to mu taimaka masa da abun da muke dashi, kada mubarshi hakanan, Yaran nan bayin kanshi bane, ?addarace ta afka mashi, baida kowa marayane, Yana bu?atar waWanda zasu tallafi rayuwarshi.... "Kafin Ya ?are maganar, Pravin yayi kuskuran katse shi da cewa "yaya kai ne baka fahimta ba, Yaron nan ma?iya ne suka turo shi don su tarwatsa zuri'armu, idan ba haka ba ta ina mutun zai Iya rikiWa ya zama maciji? Sannan ya rasa inda zai faWo duk gine ginen dake a estate din nan na kusa da gidan Owais din bai shiga cikin su ba sai nan zai


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login