Showing 162001 words to 165000 words out of 298130 words

Chapter 55 - KURKUKUN KADDARA (TAKUN KARSHE) BY BOSS BATURE.doc

ta duba sunan mai kiranta ba tai picking

"Unaisah! Ina kika shiga inata jaraba kiran layinki bana samu" wata irin zabura tayi aWan ruWe saboda bata gane wacece ba.

"Nasan baki gane mai magana ba, Aunty pretty ce"

Ajiyar zuciya ta sauke muryarta da kasalar bacci ta ce "Yanzu na gane, Ina kwana kin tashi lafiya"

"Ki yi hakuri na katse maki baccin ki, na damu da son jin awani hali kike a ciki kwana biyu ba ki neme ni ba"

Muryarta adidashe Tace"ba komai, nima kina araina"

"Ban yarda ba, meyasa baki kara kirana ba? Ni ay fushi ma nake dake, kin manta dani" muryar benazir da alamun 6aci rai tay maganar.

"Ba haka bane wallahi ban manta dake ba, nayi rashin lafiya ne amma yanzu naji sau?i, wayar ma bata a hannu na sai jiya na kar6e ta"

Tana jiyo sautin muryar aunty pretty tana zabga salati gaba daya ta ruWe jin bata da lafiya

"Inna lillahi! Yanzu ya jikin naki? da sauki?

Murmushi unaisah tayi jin yadda ta ruWe"ay na fada maki da sau?i yanzu"

Tana jiyo sautin ajiyar zuciyar ta
"Har naji sanyi araina, Allah ya ?ara maki lafiya, wallahi baki ji yadda naji ba saboda na damu dake, dan Allah Idan nan abuja kuke da zama, ki bani dama inzo gidan ku, dama yau nakeson fita anguwa"

waro idanu unaisah tayi da sauri tace"a'a ni ban ma ta6a zuwa abuja ba, a kano mu ke"

"Allah sarki, kinyi min nisa, in sha Allah wata rana zan kawo maku ziyara"

"Nagode da kulawarki a gare ni" sun jima suna waya kafin daga bisani su ka yi sallama, ta ajiye wayar tana faman sauke ajiyar zuciya, ita kanta tana son haWuwa da matar sai dai tasan ba abune mai yiwuwa ba, na farko batasan wacece ita ba? Idan har dagaske number da take amfani da ita ta sajeed ce me zai biyo baya?

da wannan tunanin ta sauko daga kan gadon ta kunna hasken dakin nasu

a hankali ta sauke idonta kan Deeja dake bacci tana jan minshari kwatsam taga ta fara mirginawa zata faWo ?asa daga kan gado, cikin zafin nama ta yi hanzarin tallabota a hankali ta wurga ta kan mattress din

Murmushi ta dan saki kafin ta juya ta shiga toilet, har yau tana mamakin jinin daya dauke mata tun bayan da ta sha bakar wahala bai dawo ba, har cikin ranta bata ji dadi ba, saboda taji ance alamun girma ne ga mace, kuma idan tanayi boobies Win ta zasu kara cukowa sannan hips dinta zai ?ara faWaWa komai ma na jikinta zai canza ta zama cikakkiyar budurwa, a gaban sink ta tsaya tana lalubar wurin don taga idan za'a samu ko da alamunsa ne sai dai bata ga komai ba...." fuskarta ayamutse ta kalli mirror kamar zata fasa ihu haka take ji, ita da take son ta zama house wife idan har bata fara wadannan abubuwan ba ina ita ina iya zama matar aure? ta faWa aranta, kafin ta sa hannu ta zame wuyan rigar baccin ta, ta soma le?en kirjin ta, murmushi tayi ganin sun ?ara girma ba laifi, wani irin dadi ne Ya lullu6e ta, har yau bata bari danish ya gan su ba, saboda kullum in zata sanya kaya sai ta Waure su tamau don karsu fito.

jujjuyawa ta yi agaban mirror din tana kallon qugunta, ni dai na rasa me angel take ma zumudi, da alama batasan meye ake azaman auran ba.

Gaba Waya matasan gidan sun tafi masallaci, bayan sun kammala sallah shiekh imam ya zaunar da su don suyi karatun da yake biya masu kullum.


Fitowa yai daga bathroom, waist dinsa daure da towel fari, gaban dressing mirror Ya tsaya zuciyarsa cike fal da tunanin halin da sajeed ke aciki, saboda Ya damu da yaran musamman wadanda ke acan gidan kurkukun ?addara sun tsaya masa a zuciyarsa, ayanzu baya da wani buri da ya wuce su kai masu Wauki, shaf shaf Ya shirya kanshi cikin dark jeans tare da v neck shirt ta Wame fatarsa.

Hayewa yai kan gadonsa ya daura kansa bisa pillow, hannunsa ruke da wayarsa, layin Boss Ya danna ma kira bayan yai picking suka gaisa da juna

"Inason ganinku, tare da salsabeel a room dina" amsa mashi boss yayi da toh"

Bayan wasu ?an mintuna, wayarsa tai alert, unclock Ya danna a hankali kofar ta buWe suka shigo su uku, cikin girmamawa suka gaishe da shi ya amsa masu

"Have a seat" ya fada Yana nuna masu couch, zama sukai suna fuskantar sa... Ya Wan dauki lokaci kafin ya dan bude idanunsa dake a lumshe ya dubesu daya bayan daya kafin ya tsayar da idanuna akan salsabeel

"me yakamata mu yi? bana son abun yadau lokaci, ko dan saboda sauran yaran dake fuskantar barazana da bu?atar mu kai masu dauki....." babu wasa akan fuskarsa yai maganar


Calmly Salsabeel Ya fara magana"yalla6ai, ni bani da hanyar da zan iya jagorantar mu zuwa gidan kurkukun ?addara, saboda garkuwar sihirina ta karye kuma ina da tabbacin daga wajen su ne suka yi min hakan, amma nasan Wan uwana zai Iya taimaka maku, shi kadai ne yasan hanyar da zai shigar daku Gidan kurkukun ?addara amma fa dole mu bi komai asannu kada muyi gaggawa saboda gidane mai hatsarin gaske, wani irin kurman ginine idan har baka da ilmi akansa kai kuskuran shiga kwakwalwarka zata iya ta6uwa"

Jin wannan maganar daga bakin salsabeel Yasa Taj da big guy suka kalli junansu da alamun rudani.

"Amma idan har Garkuwa ne zaiyi maku jagora shi ya san ta yadda zai shigar daku ba tare da kun sha wahala ba, amma fa da wuya danish Ya bamu haWin kai, mutum ne mai wuyar sha'ani yana da kafiya, kuma har yanzu shi garkuwar su ne zasu iya sarrafa shi daga can kurkukun, ni dai ashawarata tun yanzu ku fara jan shi a jiki kuna koya masa abubuwa masu mahimmanci kamar rubutu da karatu tun da baisan komai ba ta hakanne zai fara sakin jiki da ku har asamu abun da ake so" gaba Waya sun gamsu da bayanin salsabeel.

Numfasawa chief yai kafin ya ce"in sha Allah zamu yi ?o?arin jan shi a jiki,"

Big guy yace"ni abunda ke Waure min kai da yaron kwata kwata baya son mutane su rabe shi in ba yan uwansa ba, kuma baya son wani ya rabi yan uwansa, meyasa"? ya tambaya yana kallon salsabeel

"Rashin sabo ne, idan Ya saba da ku zai daina, amma fa da bu?atar ku guji bata masa rai, in har ya nuna baison abu to kada ayi masa in ba haka ba komai zai iya faruwa, idan ransa ya 6aci evil heart Winsa zata iya motsawa abun da bana fata" ta6e baki big guy shi dai har yanzu bai yarda da Danish ba.

Shiru sukayi na wani lokaci

"I understand that dealing with them won't be easy." gaba Waya suka maida duban su ga chief da yai maganar

"in sha Allah, zamu yi zaman tattaunawa tare da chief of army, da kuma commender na america, bayan haka za mu tuntubi rassan jami an ISOD da ke wasu kasashen, saboda taron ya shafi kowa da kowa. Dole ne mu hada kai kafin mu ci nasara a kansu. "

"Haka Yakamata yalla6ai" suka fada atare

Lumshe idanunsa yai gaba daya sun fahimci damuwar abunne ke addabar zuciyarsa

A lokacin da basuyi tsammani ba suka ji ya furta"na rantse da wanda raina ya ke a hannunsa wallahi duk wanda na kama da sanya hannunsa a kungiyar matsafan kurkukun ?addara sai ya WanWani kuWarsa ko da kuwa mahaifina ne bazan raga masa ba, ..., " yayin da yake yin maganar idanunsa sun kaWa jawur saboda tsantsar 6acin rai

"In sha Allah sir mahaifinka ba zai ta6a zama Waya daga cikin su ba..." kafin taj ya ?are maganar chief yai hanzarin katse sa yana huci yace"nima ina fatan hakan amma nasan mawuyacin abune, boss bana son na zurfafa bincike saboda fargaban kada inga wanda banyi tsammani ba, Ina jin tsoron ace akwai sanya hannun wani a family dina zuciyata zata karaya watakil ma hakan zaiyi silar da zuciyata zata buga...." ba su ta6a ganin tashin hankali tsantsa akan fuskar chief irin na yau ba, kwata kwata babu walwala atare da shi
Hada baki sukai wurin kwantar masa da hankali suna bashi baki, dakyar suka samu ya lafa yana faman sauke ajiyar zuciya ya kifa kansa jikin pillow... Bai sake dagowa ba, kamar bacci ne yai awon gaba da shi.

Mi?ewa sukai atare suka bar dakin, zuciyoyin su cike fal da tashin hankali, su kansu tsoron ranar da asiri zai tonu suke yi saboda sun san dole akwai na jininsa, a kwanakin baya ya ta6a basu labarin kiran sirrin da wani bawan Allah yake yawan yi masa akan Ya binciki danginsa akwai bara gurbi acikin su wadanda suke sadaukar da yaran family Winsu har faWa masa yai yaran da ake haihuwar su a mace ba mutuwa sukai ba suna nan da yaransu, bai ta6a maida hankali akan mutumin ba sai bayan da prisoners suka bayyana tukunna Ya fara gasgata maganar mutumin da har yau baisan wanene shi ba..."

Abakin kofar dakin nasa suka dakata da yin tafiya suna kallon junansu damuwa ce ?arara akan fuskokin su kowa da abun da yake sa?awa aran shi sam sun kasa magana daga bisani suka fuce.


Chief Har ya fara nutsawa cikin baccinsa Wayarsa dake ajiye kan drawer ta fara ringing kaitsaye sautin ya daki kunnansa

A hankali yadan bude idanunsa wadanda ke lullu6e da yalwar gashi ya kalli ceilling din dakin kafin mi?a hannu ya Wauki wayar

Motsa la66ansa yai tare da furta sunan Uncle hateem.

Picking call din yai

"Uncle am sorry, jiya na shiga bedroom dinsa na taras yana bacci shiyasa ban kira ka,"

On the other hand prime minister yace"Son ka hanani ganin maganin da zai warkar min da zazzabina....."

"Sorry uncle nayi laifi ay min afwa"

"It is okey, yanzu yana ina ya farka daga bacci"?

"Yanzu zanje bedroom dinsa na duba sa"

"Okey, akwai sako da za'a kawo masa daga company.." tun kafin ya ?are maganar chief ya furta"uncle wani sako kenan"?

"Idan an kawo zaka gani, nasan idan na fada maka ba zaka bari sakon ya iso ba, zaka hana ne"

"Haba uncle, ni na isa in hanaka yin alkhairi..."

"Hakane, amma bazan fada ba" ya faWa da zolaya

murmushi chief yai"andai hanani jin menene bakomai in an kawo zan gani, bari naje na basa ku yi magana"

"Video call zamuyi zanfi jin dadin ganinsa" amsa masa yai da okey, janye wayar yai daga kunnansa Ya nufi desk ya dauko ?aramar laptop dinsa Ya sauko down babu kowa sai masu aiki dake zaryar kai abinci kan dining, ta elevator ya hau ta sauke sa second floor........

Abakin ?ofar ya tsaya yai masa knocking, shiru ba abasa iznin shiga ciki ba, yanke shawarar shiga yai a hankali ya tura kofar a zaton sa bacci yake yi, yana shiga ciki yaji alamun motsinsa a toilet, har ya juya zai fita da niyar anjima zai dawo sai kuma yaji an bude ?ofar, fitowa yayi daga ci ki jikinsa asanye da kayan baccin sa

Ganin mutum adakinsa Yasa shi cin burki ya tsaya yana kallon bayansa cike da mamakin wanene ya shigo masa bedroom dinsa...

A hankali chief Ya juyo suka fuskanci juna, nan take danish ya ?ara daure fuskarsa tamau babu annuri.

Takawa yai zuwa gabansa Ya mi?a masa hannu don su gaisa, ma?e hannunsa yai alamar bazai bayar ba,

"Ba ay min haka" ya fada tare da sanya hannu ya janyo danish yayi huggin dinsa kamar zai maida sa cikin sa, kamar wani mugun abu ya rungumesa sai kankame jikinsa yake yi, bayan chief ya raba jikinsa daga nasa ya soma yi masa magana.

"Barka da safiya, Ina fata ka tashi lafiya" shiru yayi bai tanka masa ba, wani kallon ?asan ido yake jifa masa da ace chief baisan halinsa ba da sai yace ya tsane sa

"Ba magana? Ko da ya ke nima dalili ne Ya kawo ni roon dinka, kar6i nan uncle dina ke son magana dakai" ?in kar6a yayi,

"Ina nufin uncle dina Hateem, mutumin dana hada ka da shi shekaran jiya, ina fata ka tuna sa" zare masa idanu danish yayi, sarai ya fahimci wa yake nufi abun da bai gane ba ta ina za suyi magana da uncle din nasa?

In a low voice ya furta"yana ina"?

Mi?a masa laptop din yai" anan zakuyi magana da shi ta video call"

wani kallon rainin wayau danish yai masa arude ya furta"tayaya zanyi magana da shi ta wannan abun" Wan zaro ido chief yayi, can kuma ya saki fuskarsa tunawa da wanene shi

"Oh okey na fahimta lemme show you yadda zaku yi magana" bayan ya kira hateem video call fuskarsa ta cika laptop screen din, juyama danish ita yayi"look at him ku yi magana"

har saida danish Yaso Ya firgita lokacin da ya sauke idonsa kan laptop screen din ganin fuskar hateem mai Wauke da murmushi, muryarsa cike da nishadi Yace"my baby boy danish, ka tashi lafiya? Ya ka kwana jiya? Ka yi kewana kuwa ko kuwa ka manta dani" yatsun hannun sa na kerma Ya kar6i laptop din daga hannun chief Ya kura ma hateem ido yana kallonsa batare daya furta komai ba, shi mamakinsa tayaya har ya bayyana akan wannan abun?

"Ka zauna ku yi magana" chief ne Ya fada tare da nuna masa gefen gado, jiki na bari yaje ya zauna yaci gaba da kallon hateem dake ta faman sakar masa murmushi

"Ka yi shiru baka tanka min ba, ko dai kamanta dani ne? Fadamin sai in tuna maka" shiru yayi bai masa magana ba, mamakin duniya ya cikasa

Chief dake atsaye ya harWe hannayensa kan kirjinsa sai kallonsa yake yi zuciyarsa cike fal da tausayin rayuwarsa baiyi tunanin tsayawa ya kammala wayar ba sai ya juya ya fita daga dakin.

"Bazan damu ba, kallon da kake yi min ya tabbatarmin da ka gane wanene ni, shekaran jiyama da muka fara haduwa sai da nasha wahala kafin Ka yi min magana" ya faWa yana murmushi.

"Nakasa jurewa ka tsareni da wadannan kyawawan idanun naka please ko da zagina ne kayi ni dai burina naji muryar nan taka mai kwantar min da hankali, chief bai fada maka nayi zazzabin rashin ka ba"? Ya fada yana marairaice masa ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?fuska alamar zaiyi kuka...

Yana faman furzar da numfashi Ya dan motsa la66ansa kamar baison furta maganar yace"ina son ganin ka"

"Ba ga ni kana gani na ba" girgiza kai danish yai alamar a'a

"Ka fito kazo nan dakina"

"No bazai yiwu ba, ay bana kasar yanzu ina canada kai kuma kana nigeria, sai na hau jirgi tukunna zan iya zuwa wurin ka" hankali atashe danish Yace"a'a ni dai kawai kazo ka fito daga wannan abun ina son ganinka" waro idanu hateem yai da alamun ruWani akan fuskarsa.

"Ba yadda za'ae na fito, laptop ce fa, baka ga ?arama bace taya ni da nake babban mutun zan fito ta cikin ta" kamar zai sanya masa kuka yace"ni dai kazo ina son ganinka" ya fada yana shafa laptop screen din a kokarinsa naya gano kofar da zai buWe wa prime minister Ya fito waje.....

Chief owais Na awaje Yajiyo sautin fashewar wani abu daga dakin danish....



*Daga Al?alamin Boss Bature=؋?
'
'?*


*Littafin kurkukun ?addara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura*

3196407426

First bank

Bature Hafsat Muhammad,

*bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan layin 08169856268*_*~
'=؋?BOSSLADIESWRITERS=؋?*~_



3,F 'DB/=؋?=?%?=؞?


~Takun ?arshe=?%?~



Dedicated to Aunty Kubra=؋?=؞?



B5) -( 1HE'F3J) :J1 9'/J) (JF 'D3,F'! E9 *7H1'* E9B/)=؋?=ؘ?=??


An extraordinary romantic love story between prisoners with complex twists d'=؋?=ؘ?




Daga al?alamin Boss Bature=؋?
'






Chief na waje ya ji yo sautin fashewar wani abu daga dakin danish, a hanzarce ya tura kofar ya shiga kwatsam ya taras da abun da banyi tsammani ba

Gaba Waya ya fasa laptop din, ya raba ta gida huWu, hakan bai masa ba sai da Ya zu?unna a gaban pieces Win Ya sa hannu Yana tatta6a su kamar wani zararre komai ya kwance masa

Chief Ya jinjina ma lamarin, abun ya Waure masa kai tamau, ta inda ya gode ma Allah laptop ba wadda ya ke aiki da ita ba ce, da kuwa yaja masa babbar asara.

"Meyasa ka fasa ta? why pls ? Ko kallo bai ishe shi ba, damuwarsa akan Hateem ne da bai gani ba bayan yasha wahalar balla abun

Girgiza kai chief yayi"da ita ne zaka iya amfani wurin yin magana da shi saboda baya a Nigeria" Wagowa danish yayi fuskarsa a yamutse gaba Waya ya rasa sukuninsa, shi fa ya fasa ne da niyar ya buWe ma prime minister hanyar da zai iso gare sa.

"It is okey, koma ka zauna kan gadon ka, a hankali Ya koma kan gadon yana faman bin laptop din da kallo

?arasawa chief yai tare da kwashe pieces din ya fuce daga dakin Ya koma bedroom dinsa Yana shiga wayarsa ta fara ringing

Da sauri Ya Waura laptop pieces din kan couch kafin Ya Wauki wayar yai picking

"Owais meya faru ne? Muna cikin yin magama da shi naji Wuff ya katse kiran"

"Uncle mai kuke tattaunawa ne da shi"?

"Cewa yai yana son ganina in fito daga laptop din, nace masa bayadda za'ay amma ya matsamin shi ne fa naji shiru kiran ya katse"

"Uncle Ya 6alla laptop Win, gaba Waya ta tashi aiki, Allah Yaso ma ba wadda nake amfani da ita bane ay dayaja min asara"

Muryar Hateem da mamaki Ya furta"what? Ya fasata? Amma meyasa yayi haka"?

"Saboda ka ?i fitowa, may be yana nema maka hanyar da zaka fito daga cikin ta ne"

Kusan atare suka fashe da dariya daga hateem din har chief din saboda abun Ya basu mamaki da al'ajabi......

Dakatawa sukai da yin dariyar, kowan nan su yayi shiru na Wan wani lokaci, kwatsam sautin shesshe?ar kukan prime minister hateem Ya karaWe kunnansa lokaci Waya zuciyarsa ta buga saboda jin abun da bai zata ba, aruWe ya furta"uncle? Kuka kake yi? Ko dai kunne na ne suka ji min badai dai ba"?

Muryarsa araunace Ya furta"Ina tausayin rayuwarsa owais, ya karya min zuciyata yau, mutum har mutun baisan komai ba,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login