Showing 282001 words to 285000 words out of 298130 words

Chapter 95 - KURKUKUN KADDARA (TAKUN KARSHE) BY BOSS BATURE.doc

da muke jiran ?arasowar su, bayan haka yan uwanshi akagare suke da su koma gida, saboda sun gaji suna bukatar hutu"

cikin tausasa harshe ya ?are maganar yana duban chief, maganar big guy ta tuna mashi da nauyin baccin Danish, zai iya kai magrib bai farka ba, wrist watch din hannun shi ya duba kusan karfe Waya da rabi.


"Sir, Nima anawa shawarar Atada shi daga baccin" acewar COO,

Ci yace"nima na goyi bayan a tada shi daga baccin duba da lokaci"

gaba daya jami'an sun goyi bayan a farkar da shi daga bacci.

Duk abun da ke faruwa akan idanun su Unaisah suna kallon ko me ke faruwa.

Kamar za su tada jariri daga bacci cikin muryar raWa Taj ya furta sunan shi"Danish! Danish"! Kamar ya yi magana da bango, babu alamun zai farka


A hankali ya dan bubbuga kafadar"pls danish ka tashi" still bai farka ba


CI yace"amma dai yaro ne da jikin manya ko? Cos ni lokacin da aka turo mana hoton fuskar shi banyi tsammanin yakai haka girma ba"


Yar dariya Big guy yai"adinga hadawa da tubarkalla, dama nasan sai ka tanka, kai da baka iya gani ka yi shiru, to yaro ne shekaran shi 20" da zolaya yai maganar, murmushi Su ka yi tare da maida hankalin su akan Taj dake kokarin tada Danish.

Big guy yace"Dama na faWa ma ku Nauyin bacci ne da shi, a samu ruwa me sanyi a yayyafa masa a fuska watakil Ya farka" girgiza kai chief yayi"ban amince asanya mashi ruwa ba, bari na jaraba tada shi" mikewa taj yayi don ya bashi damar zama kusa da Danish.

Bayan ya zauna ya kai hannu ya Wan bubbuga kafadar shi"Danish? Ka tashi ina so zamu yi magana!.." a kalla ya ambaci sunan shi yakai sau biyar har Senior agents din sun fara jin fargaban anya lafiyar shi kalau.

Ba zato ba tsammani, suka ga ya fara motsa yatsun hannayen shi alamar zai farka, kusan atare suka sauke ajiyar zuciya, A hankali ya Wan bude idanun shi waWanda suka kaWa jawur ya dubi fuskar chief.

"Sannun da bacci, ka barmu muna ta jiranka" yamutsa fuskar shi yayi ba tare da ya furta kalma ba.


Ruko hannun shi chief yayi"ta shi mu shiga ciki, mun gama yi ma yan uwanka tambayoyi saura kai kadai ka rage, Ina fata zaka bamu hadin kai kamar yarda suka bamu" Cikin kulawa ya yi maganar yana duban shi.

Da wata irin kalasa Yake kallon chief dake masa magana, hanky din da ya rufe rabin fuskar shi tuni ya jima da warwarewa.

Tun daga kan yanayin shi Jami'an suka fahimci zaiyi ji dakai, Aransu suka ayyana kamar kanin chief saboda kamannin su da suka gani.

Sunyi mamakin ganin yadda chief ke lalla6a shi kamar zai durkusa mashi mutumin da suke ma biyayya sau da kafa suke tarairayarshi yau shi ne dakan shi yake tarairayar wani, ba komai ne yasa shi yin hakan ba face don ya samu ya shawo kanshi ya amsa masu tambayoyin su baya son Danish ya bashi kunya.


Dakyar Ya samu Danish Ya mi?e chief ya ruke hannun shi Yaja shi suka nufi Questioning Room Win yasan yadda yake da wuyar sha'ani shiyasa ya zabi kan shi a matsayin wanda zaiyi mashi tambayoyin yasan da wuya in wani ne Ya saki jikin shi.

Gaba Waya burin jami'an Suga tattaunawar chief da Danish, sun ?wallafa rai akan son jin bayanan da zai bayar, Suna atsaye gaban mirror din suna kallon su ta cikin Observation room din.

Bayan sun zauna kan Chairs dake fuskantar junan su, Chief Ya zuba masu juice a cup ya mi?a mashi.

kin dauka yayi har saida chief yace"na ka ne kadauka" kafin ya cira hannu ya dauki cup din Ya kur6i juice Win wani irin sanyi ne ya ratsa throat dinsa.

bayan ya kammala sha ya aje cup din ya mayar da hankalin sa akan chief dake kallon shi, bai ta6a jin fargaban tambayar wani dan adam a duniyar nan ba irin yadda yaji fargaban tambayar Danish sun kurama juna ido an rasa me magana a cikin su.

Jami'an dake kallonsu sunyi matukar ?agara, Yayin da taj da Big guy hankalunsu ke atashe saboda zullumin kada Ya basu kunya.

Idan muka koma 6angarensu Unaisah, tun da suka shiga da Danish ta rasa nutsuwarta, Hankalinta atashe Yake saboda ita tasan mawuyacin abune Danish ya basu hadin kai, idan ta tuna rayuwarsu ta baya yadda kwata kwata bai ta6a fada mata wani abu daya shafi kurkukun kaddara ba duk irin mutuwar son da ya ke yi mata, haka ya dinga boye mata ko ta tambaye shi baya fada mata ita da take kaddararsa balle su da har yanzu bai yarda da su ba kallon su kawai ya ke yi saboda ba yadda zaiyi da su.

Tun tana daga zaune har dai ta mi?e ta fara zarya a tsakar gurin da suke, hatta su Sajeed sai da suka lura da yanayin ta, ko da suka tambaye ta meke damunta sai tace masu ba komai ta kosa su koma gida ne.

"Zamu iya farawa"? Ya tambaya yana kallon sa, tamkar baisan furta maganar Yace"yeah..." ajiyar zuciya chief ya Wan sauke kafin ya fara magana

"Ka fara gabatar mana da kanka, muna son muji sunan ka da takaitaccen tarihin rayuwarka"

kalma Waya tak ya furta"Danish" daga nan bai ?ara magana ba, kuma baida niyar yin ta.


Hakan bai damu chief ba, yayi mashi uziri saboda yasan ba lallai yasan me ake nufi da gabatar da kai ba.

"Tun kana jariri ka tsinci kanka agidan kurkukun kaddara hakan na nufin kai rainon su ne, tun da a hannun su ka mallaki hankalin ka, kasan komai dangane da elders kuma kasan duk wani abu da suke aikatawa agidan kurkukun kaddara a matsayinka na prison shield dinsu..." ya faWa yana kallon fuskarshi, yadda kasan yana fahimtar shi ya nutsu yana sauraron shi.

Numfasawa chief ya yi kafin ya Waura da cewa"Wan uwanka Salsabeel ya fada min kafi shi sanin su wanene shuwagabannin kurkukun kaddara ka kuma san komai dangane da su, bayan haka kaima kana Waya daga cikin Giants masu babban mu?ami agidan kurkukun kaddara, saboda suna ji dakai kuma sun yarda da kai shiyasa har suka baka mukamin garkuwar su hakane"?

Ya tambaya yana bin shi da kallo, Waga mashi gira Danish yai alamar eh ba tare da ya furta ba.

"Bayan haka munji bayani daga bakin yan uwanka, kaine kayi masu hanyar da suka fita daga gidan kurkukun kaddara shima hakane"! Again ya Waga mashi gira.

Ran Big guy yayi mugun 6aci saboda a gurinsu disrespecting ne Chief Yana magana Ka amsa mashi da gira ji yake kamar ya fada dakin Ya kifa mashi mari dama shi akwai zuciya.

Chief kuwa bai kawo komai aran shi ba dangane da yadda Danish Yake amsa mashi.

"Who are the Elders? Do you know their faces? cike da sa ran zai amsa mashi yayi tambayar.

Girgiza mashi kai yai alamar a'a, Sai a lokacin Ya lura da yadda yake amsa mashi ba Wa'a kwata kwata ranshi ya sosu.

Muryarshi da sanyi ya furta"ba zaka iya yi min magana ba"? Waga mashi gira yai alamar eh, runtse idanun shi ya yi ranshi ya Wan baci amma sai yayi kokarin sarrafa temper dinshi saboda bayason ya bi shi ta karfi yafi son ya lalla6a shi su rabu lafiya.

"Kana nufin tsawon lokacin daka dauka agidan kurkukun kaddara bakasan su wanene elders ba? Ko fuskokin su baka sani ba"? Yamutsa fuska ya yi dakyar ya furta"nasan su amma ban san fuskokin su ba"

"Don't lie to me, Nasan ba halin ka bane"

"Why should I lie? If I don't want to tell the truth, I'll just shut my mouth." fuskarshi adaure yayi maganar.

Jinjina kai chief yayi"sunayen su fa? Ka sani"

Shiru yayi bai tanka mashi ba, hakan na nufin yasani baison fada mashi.

Bai matsa mashi ba Har cikin ran shi baiji dadi ba, daurewa yayi ya canza mashi wata tambayar.

"Ina so ka fadamin komai dangane da gidan kurkukun ?addara, da kuma abunda ake aikatawa a cikin sa"!

Wani kallo Danish Ya jefa mashi mai wuyar fassaruwa, A kalla sun shafe mintuna Danish bai amsa mashi tambayarba, kuma bai da niyar amsa mashi.

Jikinshi yayi mugun yin sanyi, bai ta6a zaton zaiyi mashi haka ba, duk irin yadda ya aje girman shi Ya kaskantar da kai agurinshi duk don ya samu ya basu hadin akai ashe shi ba ayi mashi gwanin ta.

Cikin karyayyar murya ya furta"Ka yi shiru ba ka amsa min ba ko baka ji me nace ba"? Kawar da kan shi gefe yayi alamar bazai amsa mashi ba

Softy chief yace"kada kayi min haka, idan ka fadamin ba iya mu zamu amfana ba, ku ma zaku amfana, Danish baka da burin daukar fansa akansu? Meyasa zaka rufa masu asiri? Mutanan da suka raba ka da iyayenka tun kana jariri suka sace ka, bayan haka suka tauye maka hakkinka na rayuwa tun baka mallaki hankalin ka ba, idan ma kana yi masu kallon iyayen ka masu kaunar ka toh ka dauna, Yakamata ka farka Danish! Mutanan da kake gani amatsayin wani naka basu ta6a sonka ba, sun raine ka ne saboda biyan bukatar kan su, duk ranar da ka mutu zasu manta da kai ne, tsawon shekara ishirin suka kuntata rayuwarka sun cutar dakai sun kuma raba ka da iyayenka saboda tsabar zalunci, kai baka tunanin ina nasu ya'yan suke? Nasan ba lallai kayi wannan tunanin ba amma inaso ka sani wallahi suna da ya'ya suna acikin mu suna rayuwar yanci cikin kulawa da gatantawar su, kai kuma sun wulakanta ka da sauran yan uwanka" a faWace ya faWa yana duban shi.

"Rayuwata ba ta ta6a burge ka ba? Lokacin da ka shigo cikin mutane amatsayin wanda baison komai ba, shin baka yi tunanin sun yaudare ka ba? Ya tambaya rai abace yana kallon shi, Maimakon yaga rauni atare da shi saima yaga ko ajikin shi, maganganun chief basu karya mashi zuciya ba, su Taj dake kallonsu duk sun fahimci hada jahilci ke damun Danish, Elders sun kashe mashi rayuwa sun yaudareshi ta yadda bazai iya gane cutar da shi sukayi ba. Sun riga da sun yi mashi hudubar su, sun gatanta shi sun nuna mashi cewa su kadaine gatan shi a duniya.


"ba gaskiya kake faWi ba, they've never hurt me. Suna sona kuma sune iyayena, bayan su bani da wasu iyaye a duniyar nan"

bai ?are maganar ba chief owais daya gama harzuka rai a6ace ya Waki gaban table din ko gizau Danish bai yi ba.

Muryarshi a kausashe Ya furta"kai wani irin bauWaWWan mutunne? Baka da tunanine? Ko bakasan ciwon kanka bane? Tayaya ina kokarin in fahimtar dakai kana kauce hanya? Meyasa kake yaudarar kanka? duk abunda mu ke yi munayi ne saboda mu daukar maku fansar cin zalunku da akayi mu kuma ceto rayuwar sauran yaran da ke a hannunsu sannan mu kawo karshen miyagun da suka kafa kurkukun ?addarar! Kai kadai zaka iya taimaka maka Danish! Don haka dole ka bamu hadin kai..." Ran shi yakai makura agurin 6aci baima san yayi mashi tsawa ba. idanunshi sun kaWa jawur saboda bai ta6a neman abu agurin wani ya rasa ba Danish shi ne mutun na farko da yayi rejecting din bukatarsa.

Jami'an dake kallonsu sun harzu?a Musamman big guy Yafi fusata ganin yadda Danish ke wahalar da chief duk basu ji dadi ba

Ga mamakinsu murmushin gefen fuska Danish yayi tare da furta"I'm respecting you, so please don't pressure me. If you want peace with me, stop asking about the prison of destiny and stop insulting the elders, bayan haka inaso ku sani bazan ta6a baku hadin kai ba indai akan su ne, saboda ku ba kowa bane agurina, ban hada alakar komai daku ba, duk da bani da ilmi amma nasan me na ke yi, Ina da hankali baku isa kuyi min wayau ba yan uwana kadai na sani su kadai zan bawa kariya kuma ina tare dasu babu wani wayau da za ku yi min"

maganar Danish ta yi matu?ar daure masu kai, Hankulansu yayi mugun tashi, gaba Waya chief ya rasa bakin magana saboda Danish Ya sagar mashi da gwiwa, yanayin fuskarshi ya nuna tsantsar mamaki da al'ajabi gaba daya ya fara sare da lamarin shi.

"Zan iya tafiya" ya fada yana kallon fuskar chief dake kallon shi kamar gunki haka Ya kame sam ya kasa magana, idan har ya biyewa zafin zuciyarshi ba karamin faWa zasuyi da junan su ba, sai dai bazai ta6a biye ma shi ba saboda shi ba ajin yin shi ba ne, bayan haka yana yi mashi Uziri duba da irin rayuwar daya taso still akwai tsantsar tausayin Danish a cikin zuciyar shi.

bai jira Amsar da chief zai ba shi ba, Ya mi?e Ya nufi hanyar fita daga room Win, yana ru?e handle din kofar yaji ta adatse.

juyowa yayi tare da kallon chief, bawan Allah Ya dafe kan shi da tafukan hannayen shi, tsabar bacin rai da takaici ne ya addabe shi, wata irin zufar 6acin raice ta fara tsastsafo mashi, la66ansa har kerma suke shima sam bai iya fushi ba, zuciya ce da shi.

"Ka buWe min kofar zan fita" babu wasa akan fuskarshi yayi maganar

A fusace chief yace"I'm not done talking to you! Come back and sit down. If you don't answer my questions, we'll spend the whole day here."

kwatsam Yaji alamun buWe kofar, aruWe ya Wago yana kallon shi yayi mamakin yadda ya iya bude kofar bayan computer ce ke controlling din ta, dole saida izninsu kofar zata buWe.

har ya Waga kafa zai fita kenan chief ya yi hanzarin mikewa ya bi bayanshi yana isa gaba daya ya faWa kan bayanshi yayi hugging dinshi tighly kamar zasu koma mutun Waya.

Cikin rauni na murya ya furta"Danish, I'm really disappointed in you.You embarrassed me, I never thought you'd do this to me you're hurting the heart that's trying to save your life. ban ta6a zaton za ka yi min haka ba"

ya faWa yana jan numfashi haWi da ?ara cusa jikin shi ana Danish, wlh tsabar bacin rai ne yasa shi yin hakan saboda gaba Waya ya fara sarewa da lamarin shi, kafin su baro gida adakin Danish sai da ya ro?e shi akan ya ba su hadin kai yace mashi ya amince amma sai gashi yanzu ya bijire ma su, Bai ta6a zaton zai kunyata shi ba.

Rungumar da chief yayi mashi ba karamin kashe mashi karfin jikin yayi ba, Zuciyar shi taso ta karaya sai dai baya jin zai iya amincewa da su, kalaman chief sun tsaya mashi aranshi sun kuma sanya mashi kokwanto a tunanin shi, ga wani irin yanayi da yake ji mara misaltuwa atare da shi yana ji kamar suna da connection da chief, sam ya kasa ta6u ka komai yanayin fitar numfashin shi sam babu kwanciyar hankali.

Lumsassun idanunshi ya Waura akan hannayen chief daya dafe flat tommy din sa, Har cikin ran shi baiji dadin bijire ma shin da yayi ba, baisan ya akai yake jin mutumin aran shi ba, Yana matu?ar ?aunar Chief baya son bacin ran shi.

Komai dake faruwa akan idonsu big guy, sun yi shiru suna jira suka ga martanin da zai mayar wa chief.

A hankali Danish ya daura tafukan hannayen shi akan na chief ya dam?e su sosai yana mai jin wani irin yanayi mara misaltuwa, In a weak voice Ya furta"Ka yi hakuri, bazan iya ba ku hadin kai ba, pls kada ku tursasa min akan abun da banyi niya ba.." yana faWan hakan ya 6an6are hannun chief daga ru?on da yayi mashi ya fuce daga dakin, wani irin jiri ne ya kusa Wibar shi da sauri ya dafe ?ofar da tafin hannun shi.

Da ?arfi Big guy ya ture kofar Observation room Ya futo Yana huci Ya nufi Danish dake kokarin komawa gurin su Sajeed, da sauri sauran Jami'an dake a tare da shi suka biyo bayan shi ganin yadda ya fusata, sun san halin shi yana da bad temper.

Taj dake abiye da su hankali atashe Ya ke danna wayar sa layin Salsabeel ya kira cikin sa'a ya Waga ko sallama baiyi ma shi ba ya faWa mashi abunda ke faruwa, salsabeel ya zabga salati dama sai da yai fargaban faruwar hakan, saboda shi yasan wanene Danish, mutum ne mai kafiyar tsiya ga girman kai da rashin yarda.

"Yanzu haka ina acikin head quarter din, wallahi nasan za'a rina shiyasa na yanke shawarar zuwa saboda shi" acewar salsabeel bayan sunyi sallama taj ya mayar da dubanshi ga big guy wanda tuni Ya cimma Danish wani irin kukan kura yayi tare da kai hannu Ya dam?i kwalar rigar shi, Jami'an dake a kewaye da su suka rurru?e hannun big guy suna kokarin su raba tsakanin su.

Tashin hankalin da ba'a saka ma shi rana, Kusan atare su Unaisah suka mi?e idanunsu azazzare suke kallon su cike da faduwar gaba.

Da wata irin kakkausar murya ya furta"Who the hell are you? Wan uban wanene kai a kasar nan? Me kake ta?ama da shi ne huh? Kana da wani gata ne daya wuce Allah da shi chief din ne? Saboda tsabar rainin wayau yana magana kana amsa mashi da gira tsaran wasan ka ne shi"? Ya faWa yana bin shi da wani ?as?antaccen kallo, big guy irin bauWadWun mutanan nan ne masu saurin fushi, wani lokaci sai daga baya su yi dana sani, shiru Danish ya yi batare daya tanka ma shi ba.

Big guy yaci gaba da fadin"Da kasan wanene chief da ba ka yi mashi haka ba, in ba dan aikin shi ba kai ka kai matsayin da zai kula ka ne? Ka rasa wa zaka yi disrespecting sai mutun mai kima da daraja a idon mutane, mutumin da ya ke hana idon shi bacci don ya taimaki rayuwar al'umma, mutun mai tausayin da jin ?an na ?asa da shi..." ya faWa A harzuke Yana kallon cikin idanun Danish wanda yayi kasa?e yana kallon shi, karfin halin mutumin ya bashi mamaki yadda ya dam?i kwalar rigarshi batare da jin shakkar yin hakan ba.

"Sir, ka yi hakuri ka daina yi mashi faWa, me zai hana mu lallashe shi ni inaga idan muka bi shi ta lallama zai bamu hadin kai kodan abunda muka ji wurin yan uwanshi dole muyi mashi uzuri" CI ne yai maganar cikin kwantar da murya

Agent zahra Yace"sir Please, ka kyale shi, He's still young, it's not your place to


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login