Showing 120001 words to 123000 words out of 298130 words

Chapter 41 - KURKUKUN KADDARA (TAKUN KARSHE) BY BOSS BATURE.doc

family dinsa bane to baya picking sai anfara neman iznin yin magana da shi......

Amma a lokaci sai zuciyarsa ta kwallafa rai akan son sanin wanene ke kiransa...
Baisan sa'adda Ya danna answer call ba, ko da yai picking ya kara phone din a kunnansa shiru yayi baice komai ba tsabar miskilancinsa jira yake yaji wani isasshen ne ya kira shi batare da iznin shi ba.

Lamarin ya daure masa kai jin anyi shiru ba'ayi mashi magana ba, ko wanene wannan mai karfin halin? Har zaiyi rejecting call din sai kuma Ya fasa calmly ya furta "who is on the line"?

Sautin muryar karamar yarinya yaji ta ratsa kunnansa "Angel ce,"

Yayi mamakin jin muryar karamar yarinya, aransa ya ayyana ko yar wacece ta kirasa,
"kinsan dawa kike magana"?

"a'a," ta bashi amsa atakaice

"Ur age"?

"7yrs" voice Win shi da alamun mamaki ya maimaita"7yrs? ina mai wayar yake'?

"Daddyna ne, ya tafi masallaci ni kaWai ce agidan, shine na hada numbobi na kira don in gaisa da mutanan duniya"

Murmushin gefen fuska yadan saki har dimple dinsa ya lotsa, don ya fahimci ba'asan ta dauki wayar ba, tun daga kan muryarta ya gane irin yaran nan ne masu tsiwa

"Can i call u video"?

Da sauri tace eh,

Nan take ya mayar da kiran Video call, da sauri ya sanya yatsan hannunsa ya rufe front camera din wayar saboda baison taga fuskarshi, baisan ko tarko aka Wana masa da ita ba, lokacin da fuskar Angel ta bayyana akan faskeken screen din wayarsa wani irin bugu zuciyarsa tayi, bai yi tsammanin zai ganta kyakkyawa ba, fara sol ga manyan idanu launin gray dara dara da su, gaba Waya ya kasa kyafta idanunsa daka kallon fuskar ta, a sukwane ya koma gefen gadon shi ya zauna yana ci gaba da kallon ta...

"I can't see u" ta yi maganar tana faman gwale masa ido, murmushi yasaki yana kallon ?ananun la66anta tausasan gaske launin pink, chief Ya shagala da kallonta, tamkar a mafarki yake bin fuskarta da kallon ?urulla kamar zai haWiyeta, A can 6angaran Angel taji shiru ba'ayi mata magana ba, a tunaninta rashin network ne, yasa bata ganin shi a video din, batasan cewa shine ya toshe front camera din wayarsa don kada tagansa, da sauri yayi screenshort din fuskarta ba tare da sanin ta ba...

Zuciyarsa ba ?aramin sosuwa tayi ba, ganin tayi rejecting call din, sam bai gaji da kallonta ba, da wata irin kasala ya kwantar da kansa bisa pillow, Ya bude hotonta yaci gaba da kallon fuskarta....

Baiyi tunanin kiran layin ba, haka ya wuni da tunaninta aranshi, tsawon kwana uku baya iya bacci batare daya kalli hoton fuskarta ba, sometimes a rungume da wayarsa yake kwana, sai da takaiga harta daddynsa da mommynsa sunsan da hoton yarinyar daya kwallafa rai akai, mahafinsa ne Ya bashi shawarar Ya nemo ta idan hakan zai kwantar masa da hankalinsa, Ya ji dadin shawarar daddynsa, maimakon ya tuntu6i layin tajuddeen kaitsaye su yi magana da shi, sai ya fara bincike ta hanyar amfani da phone number din da Angel ta kira da shi, anan ya sami bayanan taj hada shafukansa na social media da yake amfani da su wurin yaWa aikinsu na ?an jarida, cikin sa'a ya gano address din gidan radion da taj yake aiki, bai samu damar zuwa joss ba saboda kiran gaggawa da akayi masa tafiya ce ta kama shi zai bar kasar ba don yaso ba.

Gaba Waya ya tattara komai ya damka a hannun Big guy, wanda ya kasance Waya daga cikin na hannun damansa, amintattunsa, Ya fada masa komai dangane da yarinyar data kirasa a wayar sannan yace mashi yana son yaje har can joss din Ya bincika mashi inda suke rayuwa, saboda yana son sanin komai dangane da ita........

Atakaice big guy shine mutumin da ya siya ma angel piano da kayan zane, a ranar da sukaje kasuwa da su taj ta sanya masu rigima sai ansiya mata su gashi basu da kudi, ashe shine ke bi biyarsu duk wani motsinsu akan idanunsa, chief shine ya bada umarnin komai suke bukata yayi masu shi sannan bayaso su san cewa shine yake bibiyarsu har zuwa lokacin da zai dawo kasar.

Duk wani abu da unaisah tayi sai big guy ya turama Cheif ta wayarshi, hakan ba karamin dadi yake yi mashi ba ....

Kafin chief ya dawo Nigeria wannan tsautsayin ya ritsa da su tajuddeen wanda yayi silar 6acewarsu, hankalin big guy ba karamin tashi yayi ba, lokacin da labarin ya riske shi, har sai da yaji fargaban sanar da chief saboda yasan yadda ya ?walla fa rai akan kaunar yarinyar, gashi saura kwanaki kalilan ya rage mashi ya shigo nigeria, Yaci burin haduwa da ita tare da mahaifinta, Allah bai nufa ba . ...

Dakyar Big guy ya sanar da shi abunda ke faruwa na 6acewarsu, tsabar tashin hankalin daya fuskanta na jin mummunan labarin har zazza6i sai da yayi, duk da haka bai karaya ba, yabar komai nashi, ya dawo nigeria bai sauka a abuja ba, kaitsaye ya sauka a joss, big guy ne yaje tarbo su a airport, tare da jami'ansu dayazo da su...

A katafaren gidan da big guy din yake da zama suka sauka, dama chief ne ya biya kudin gidan a lokacin daya tura shi neman gidan su Angel.

Kwana uku da zaman su agidan kafin suka fara nasu binciken, basu tsaya bata lokaci ba suka nemi alfarmar Inspector General of CID da ya damka masu case din su tajudeen a hannun su, tuni suka amince masu saboda sunsan hukumarsu ta musammance, duk wasu bayanai nasu tajudeen saida suka tura ma chief hada makullan gidajensu da suka kar6a.

Muhsin yana Waya daga cikin wadanda jami'an isod suka tuntu6a har gida suka kai mashi ziyara don jin cewa shi Wayane daga cikin aminnan tajuddeen bayan sunyi mashi tambayoyi ya amsa masu wanda ya sani sai kuma sukace mashi ko bayan tafiyarsu idan yaji Wuriyar tajudeen ko abokinsa uzair yayi gaggawar sanar da su, saboda sunsan zasu iya tuntubarsa tun da shi amininsu ne, contact dinsu suka bashi kafin sukayi mashi sallama kun ji yadda akai har muhsin ya samu damar sanar da jami'an isod zancen zuwan tajuddeen ba tare da shi taj din Ya sani ba, saboda ya fahimci baya son kowa yasan da zamansa, shiyasa bai sanar da shi dangane da jami'an isod dake nemansa ba...

Bayan chief owais ya kammala bashi labarin, saukko yayi daga kan sofa din Ya zube saman gwiwowinsa hawaye nata sintiri akan fuskarshi cikin sanyin murya yace"dama angel itace silar da kasan da zamana"? Muryarsa na rawa ya furta maganar, baisan sa'adda ya fashe da kuka ba, dama zuciyarsa a raunace take,
"Allah sarki angel, ashe da rabon wata rana rashin jin ki ya yi min amfani...." kasa karasa maganar yayi,
Da sauri chief ya ruko hannunsa acikin nashi, cikin sanyin murya yace"ka yi hakuri, ni banzo don na fama maka raunin dake acikin zuciyarka ba, nazo ne don na tallafi rayuwarka, idan har ka bani hadin kai nayi maka alkawarin zan yi iyakar bakin kokarina don ganin na baka kariya, na kuma tallafa maka da duk abunda nake da shi, Allah shine Ya hadani dakai ta silar yarka, Ina jinta tamkar kanwata, muhsin Ya sanar dani komai dangane da abun da ya faru dakai wanda yai silar bacewarku, in sha Allah mutanan da suka yi maku wannan aika aikar sai sunyi danasanin kasantuwarsu a doron duniyarnan......."

kwantar masa da hankali chief ya cigaba da yi har saida yaga ya fara samun nutsuwa tukunna yace mashi zai jira ya yanke shawara...." ai tunkafin ya karasa maganar taj yace mashi ya amince, zai basu hadin kai, babu wata shawara da zaiyi, saboda shi bashi da mafita kwara su tallafa masa ya nemo yarsa.....

Sunji dadin yadda taj ya amince masu batare da 6ata lokaci ba chief, Yace mashi su fara shiri zasu tafi abuja tare da shi, saboda Yana so ya sama masa muhallin da zai zauna akusa dashi sannan yace zai sama masa gurbi a hukumar su ta Isod bayan ya kar6i training dinsu, bayan tafiyarsu tajudeen abuja, rayuwarshi ta sauya, chief owais ya gatanta shi, a cikin gidansa ya ware masa part Waya, inda zai zauna tare da danejo bayan haka ya bashi kyautar mota, cin su da suturarsu gaba Waya shine yake daukar nauyin su, Kafin taj Ya fara kar6ar training din Isod sai da yafara auran danejo saboda yana son su ?ara kusanci da juna, bayason tayi kewar rashin wani nata.

Big guy shi ne mutumin da ya shiga gidan Uzair, aranar da Aneelerh taje gidan har ya Wauke mata baby junaid, bayan haka sune jami'an sirrin da suka kaita gidansu har su ka yi mata tambayoyi da suka shafi 6acewar su Angel.

Sauke numfashi yayi bayan ya gama basu labarin cikin sanyin murya yace

_"Kunji yadda akai na tsira daga hannun mutanan da suka so rabani da rayuwana, hakika cheif yayi min halaccin da bazan ta6a mantawa ba, ya kyautata min, ya faranta min a lokacin da gwiwata ta sage na fidda rai da rayuwar duniyar nan, badan Allah ya ?addarar haduwata dashi ba, da yanzu bansan awani hali zan tsinci kaina ba"_



*Daga Al?alamin Boss Bature=؋?
'
'?*


*Littafin kurkukun ?addara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura*

3196407426

First bank

Bature Hafsat Muhammad,

*bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan layin 08169856268*_ *~
'=؋?BOSSLADIESWRITERS=؋?
'~*_



3,F 'DB/=؋?=?%?=؞?


~Takun ?arshe=?%?~



Dedicated to Aunty Kubra=؋?=؞?



B5) -( 1HE'F3J) :J1 9'/J) (JF 'D3,F'! E9 *7H1'* E9B/)=؋?=ؘ?=??


An extraordinary romantic love story between prisoners with complex twists d'=؋?=ؘ?



Daga al?alamin Boss Bature=؋?
'





__________________________
'?




Shesshe?ar kukan su ta cika Wakin, babu mai lallashin wani a cikin su, tsananin tausayin taj ne ya kamasu jin irin kalubalen da ya fuskanta, A hankali unaisah ta Waura tafukan hannayenta dake kerma kan fuskarshi ta share mashi hawayen shi, cikin sanyin murya tace"daddy, ka yi ha?uri, ka daina zubar da hawayenka, bana son ganin su, kallonta yai da rinannun idanunsa muryarsa na Wan rawa yace"My Angel, ni nawa ?aluban dana fuskanta bakomai bane akan naku! Ku ne kuka ga rayuwa, ku yakamata a jajanta mawa, a kuma tausayama rayuwarku....." gaba Waya hankulansu Sajeed na akanshi, da ruWani unaisah tace"daddy, kasan abun da ya faru dani bayan na gudu daga rugar su danejo"?
Lumshe idanunsa yai hawaye na sintiri ya Wan jinjina kanshi kafin ya motsa la66ansa"na san abun da ya faru dangane da rayuwar kullan da ku ka yi a GIDAN KURKUKUN ?ADDARA, da kuma irin ba?ar izayar da suke yi maku, ranar da mu ka fara ji daga ni har chief duk irin juriyarmu sai da muka zubar da hawayen mu saboda abun ya Waga hankulanmu, ya razanar da mu, bazan iya misalta maku halin da muka shiga a lokacin da muka ji labarin abun da ake aikatawa a GIDAN KURKUKUN ?ADDARA.

Kallon kallo Su Naufal suka soma jifar junansu da shi idanuwan kowannansu sunyi jawur da su, saboda kukan da suka sha, bakomaine yasa su kallon juna ba face mamakin yadda akai daddyn Angel Yasan abun da ake aikatawa agidan kurkukun ?addara, Unaisah ce kadai batai mamaki ba saboda tasan dama sun sani watakil abakin salsabeel suka ji komai.

Murya na rawa Batool Tace"daddy dama kunsani? Meyasa baku kawo mana dauki ba? Kunsan kuwa irin ?untatar rayuwar kullan da mukayi a gidan kurkukun ?addara? Ta fada hawaye masu Wumi suna sintiri akan kuncin ta, muryarsa a raunace ya furta"mu kan mu ba mu jima da sani ba, da ace tuntuni mun san da zaman ku da har rayukanmu zamu iya sadaukarwa don mu ceto rayuwarku"

Ummin dake kallon batool jikin ta har tsuma yakeyi saboda tsabar ?agara da son jin tarihin rayuwarsu babban burinta taji menene ma'anar gidan kurkukun ?addara da taji sunata ambato a bakunansu.

Jan numfashi batool tayi kafin ta Waura da cewa"mun rayu tun kafin mu mallaki hankulanmu, bamu ta6a ganin hasken rana ba, babu shige babu fuce, a Waki Waya muke a kulle, kullum cikin uniform Waya, abinci sau Waya arana, bamusan dadin rayuwar duniyar nan ba, duk wani hakkinmu na rayuwa an tauye mana shi, mu bamu san dadin iyaye ba, sannan babu mai jin kukanmu, balle a kawo mana dauki, anjuye mana tunaninmu balle musan cewa muma mutane ne masu ?an ci kamar kowa.... ..." bata ?arasa maganarba saboda kukan daya tokare makoshinta, tamkar zatayi kakarin amai.

Cikin karyayyar murya Unaisah tace"tsohuwa tamira ta ta6a fada min cewa na jininmu ne kadai zai Iya sadaukar damu, har yau nagaza yarda da maganar nan, Ina kokwanton tayaya za'ay iyayen da su ka yi silar zuwanka duniya ko wani naka ya sadaukar dakai inda za'a azabtar da rayuwarka? Daddy wanene ya sadaukar daniS'

A matu?ar ruWe ta jefa mashi tambayar tana kallon shi.

Cikin sanyin murya yace"unaisah ni kaina a rude nake, bansan wa zan zarga ba Allah shine yasan wanene mugun da yayi maki wannan aika aikar"
Muryar ummi araunace tace"dan Allah ku fahintar dani, tun Wazu inata magana kunki bani amsa! Inaso naji meya faru da ku? Sannan Ina ne GIDAN KURKUKUN ?ADDARA"!?

Da?yar Unaisah ta lallashi zuciyarta dake yi mata radadi, kafin ta Waura idanunta akan fuskar ummi"zan fada maki komai da kikeson ji aunty ummi" A hankali ummi ke kallon fuskar unaisah

Lokacin da tafara bata labarin rayuwarsu wata irin zuface ta soma wanke fuskar ummi, jikinta ya hau yin kakarwa saboda razanar da tayi, ko a mafarki bata ta6a jin labari mai matu?ar firgitarwa irin wannan ba tuni hawaye sun soma yar tseral kan kuncinta.

Abunda yafi tsaya mata arai cikin labarin da Unaisah ta bata shine mutuwar Unaizah yar gidan daddy, ba ita ba harta taj Jikin shi Ya gama mutuwa saboda bakomai suka sani ba dangane da rayuwarsu saida unaisah tafara basu labari, chief dake atsaye bakin door yana sauraron su kasa jurewa yayi, wani irin jiri jiri Yake gani acikin idanunsa, zuciyarsa har wani tafarfasa take yi tamkar zata kone kanta tsabar 6acin rai da fusata, jijiyoyin wuyansa tuni sun fito rudu rudu kan goshinsa, juyawa yai da sauri Yabar kofar dakin, A hanzarce big guy yabi bayansa gudun kada zuciya ta debe shi Ya je yai ma kanshi Illa.

Zuciyar ummi dake hauhawa tana harbawa da wani irin mahaukacin bugu na tashin hankali tama rasa ina zata jefa kanta taji dadi gaba Waya taji ta tsani rayuwar duniya, Hakika Labarin su Unaiza Ya karya mata zuciya, ya ?ara mata karfin imani sai yanzu ta gane babban kuskuran da tayi nagaza daukar ?addarar rayuwarta, cikin shesshekar kuka mai haWe da gunjin kuka ta furta

"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!! Wannan wata irin musibace? Ku fadamin Tayaya akai har kuka Iya jure wannan ukubar da ?ananun shekarun ku batare da zuciyoyinku sun buga ba? La66anta na kerma ta fada tana dubansu kafin taci gaba da cewa "Zuciyata tagaza yarda da abun da kunnuwana suke jiye min! hankalina Ya tashi! Zuciyata ta karaya! Wannan wani irin zaluncine? Su wanene wadannan Fasikan mutanan mugaye azzulamai marasa imani da tausayi, wadanda basu Wauki ran dan adam abakin komai ba, wai su wanene su dan uban su? Wasu irin dabbobine su jahilai, Masu matattar zuciya, Anya kuwa suna da zuciya a kirjinsu? Anya kuwa mutanene su kamar kowa? Ina kokwanto akansu..." gaba daya ummi ta burkice masu sambatu kawai takeyi kamar sabon kamu ahauka, da alama abun ya razana kwakwalwarta.

Rashin imanin da akai ma yaran ya Waga hankalin ta, fashewa ta kuma yi da kuka kafin taci gaba da fadin"sun manta cewa zasu mutu su koma ga Allah? Wai su basa tunanin makomar su ne? Duniya kaWai suka sa agaba, ko Sun manta cewa duk wani abu da suka mallaka aduniyar nan zasu barshi? Daga su sai halin su za'a binne su!?...."

Waya bayan Waya take kallon su jemimah dake ta kuka aranta ta ayyana yanzu gaba dayansu nan an lalata rayuwarsu har da yan ?ananan cikin su wani irin yunkurin amai ne yazo mata da gudun gaske ta mike ta fuce daga dakin, Har batool ta yunkura zata bita taj yai saurin ru?e hannunta,
"ku barta tayi kuka ta hakanne zata samu saukin abunda take ji aranta" jiki asanyaye batool ta zauna.
Shi kanshi bazai Iya misalta irin kunar da zuciyarshi take yi mashi ba
Cikin muryar lallashi Yace da su"Idan na ce kuyi hakuri kamar na cuce ku ne, saidai ba yadda zakuyi hakurin nan dai shine yakamace ku, Allah Baya barin hakkin wani akan wani, wadanda suka azabtar da rayuwarku In sha Allah za su ga mummunar sakayyar da Allah zai masu tun agidan duniya zasu fara WanWana kudarsu kafin su koma ga mahaliccinsu su fuskanci makomarsu......." da?yar Ya samu ya shawo kansu, kafin ya bi su daya bayan daya yayi huggin dinsu duk don ya kwantar masu da hankalin su, sai da ya tabbatar ya share masu hawayensu tukunna yace

"Dan Allah kada ku sanya damuwa aranku, ku kwantar da hankulanku in sha Allah komai yakusa zuwa karshe, yanzu ku koma dakunanku ku yi wanka ku kwanta ku huta, nasan baza a rasa masu fama da ciwon kai a cikin ku ba, zanyi magana akawo maku breakfast har bedroom dinku"

muryoyin su adisashe suka amsa mashi da toh,

kafin suka mike kamar wadanda aka zarewa laka haka suka nufi kofar dakin suka fuce.

Bayan fitarsu Ya rage daga Unaisah sai batool sai kuma Taj,
Mikewa batool tayi jikinta tamkar na wadda tayi zazza6i ganin ta nufi kofar dakinne Yasa taj yi mata magana"Ina zaki je ne"?

"?akin Aunty Ummi" amsa mata yai da okey, bayan ta fuce ya maida dubanshi ga unaisah, janyota yai tare da kwantar mata da kanta kan kirjinsa hannunsa akan kafadarta
"Ina fata yanzu babu abunda ke maki ciwo"? muryarta kasa kasa tace"eh daddy,"
Da yar zolaya yace mata"ya rashin ji ko da yake naga kin daina Yanzu"? ?ara shige mashi tayi tana yar dariya, bubbuga bayanta yai da hannunshi, kafin ya janyeta, ya mike kan gwiwowinsa ya fuskanci alkibla yakai goshinsa kasa yai sujjada murmushi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login