Showing 198001 words to 201000 words out of 298130 words

Chapter 67 - KURKUKUN KADDARA (TAKUN KARSHE) BY BOSS BATURE.doc

iya baku ita har zuwa time da ita patient din naku zata ji sau?i...." fuskarta babu fara'a tayi maganar.

kallon juna zahra da Aneelerh su ka yi jikin su yayi sanyi lakwas...
Cikin karyayyar murya Aneelerh tace"hakan ma yayi mungode sosai..."

___________________________________
'?

Firgigit ta farka daga bacci tana faman zazzare gray eyes dinta tamkar kwayar idanunta zata faWo kasa, hannun ta Waya dafe da goshin ta, numfashin ta na fita da sauri, kwata kwata babu kuzari a jikinta kamar wadda aka zarewa laka, ga wata kasala data baibaye sassan jikin ta, dakyar ta yunkura ta mi?e zaune tare da jingina bayanta jikin pillow, fuskarta ta kumbura suntum, kumatun sunyi jawur, haka la66anta ma sun dan kumbura, idanunta sun ?an?ance kwarmin idon yayi ja daga gani ta jigata ba kaWan ba...
Lokaci Waya ?wa?walwarta ta fara tariyo mata abunda Ya faru da ita adaren jiya, runtse idanunta tayi sosai kwallar da ta taru acikin su ta fara ?ar tseral kan kuncin ta, ta rasa gane meya faru? Shin mafarki ne ko gaske? Kokwanto ta soma yi saboda zuciyarta tagaza yarda da abun da ya faru, was wasi ta kama yi tana faman tariyo komai daya wakana adaren jiya, babu wata alama da zata tabbatar mata da abun ya faru dagaske, da sauri ta dubi yar rigar jikin ta, tayi uban squeezing kamar an ?watota daga bakin kura, da sauri taja rigar ta rufe santala santalan laps dinta, ta sauko daga kan gado tana faman bin dakin da kallo, mirror chair ta gani yashe ta jirkice kan floor
"Ina wandona Yake"? Ta jefa ma kanta tambayar,
Ringing din wayarta ne Ya doki dodon kunnanta, jiki na rawa ta nufi toilet saboda tana tunanin kamar anan ta cire wandon
Tana shuga ciki ta iske shi akan hanger, tunawa tayi da jinin daya dawo mata gadan gadan adaren jira aranta ta ayyana shima dagaske ne ko duk cikin mafarkin ne"? Ta kare maganar tare da buWe laps dinta ta laluba jikin ta, bata ga komai ba, sai dai wani farin ruwa mai yau?i yau?i dake gangarowa...
Gaba Waya ta gama rikicewa, tunaninta ya kasu gida biyu, ta jima a toilet din kafin ta fara tunanin yin wankan
Bada jimawa ba, ta fito sanye da rigar wanka, har ta kusa isa gaban mirror tajiyo bugun kofa,
"Wanene"? ta fada tare da kallon ?ofar
"Daddyn ki ne..." sanyi taji ya ratsa zuciyarta, da sauri ta nufi kofar ta buWe mashi
Tun daga kasa ta fara kallon shi, jallabiya ce a jikin shi maroon colour, sai kamshin turare ke tashi a jikin shi
"Daddy, Ina kwana..." bata ?are maganarba, ganin yadda yake binta da kallo mai tattare da ruWani
"Unaisah! Baki da lafiya ne? Meya faru naga fuskarki ta kumbura tayi ja, kamar kinyi kuka..." wani irin mugun bugu kirjinta yayi, babban tashin hankalinta kada ace abunda Ya faru jiya dagaske ne, ba mafarki ba
Muryarta adabarbace ta furta"da.. ddy.. lafiyana lou, meka gani ne."?

girgiza kai taj yayi"no ban yarda ba, fada min ko dai wani ya buge ki ne"?
"Wallahi daddy ba komai, watakil ko dan saboda firar da muka tsaya yi jiyane ban samu isasshen bacci ba shiyasa fuskata ta kumbura..." kwata kwata hankalinsa bai kwanta da yanayin ta ba, janyota yayi tare huggin dinta, ya daura hanneyensa akan bayanta
"Nayi missing dinki my daugher, ina fata kin tashi lafiya.."
"Lafiyalou daddy ..." dago da kanta yayi"baki jin ciwon kai? Ko zazza6i haka"
?a?aro murmushi tayi akan fuskarta duk don ta kwantar mashi da hankalin shi
"Bana jin komai daddy, ni yau da karfina na tashi..." ajiyar zuciya ya sauke
"Okey, ki shiga ciki ki karasa shiryawa, Chief Yana son ganin ki" waro idanu waje tayi alamar mamaki
"Daddy???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? ni kuma? Waga mata gira yai alamar eh
"Ki sanya kaya masu kyau, zan jira ki awaje" cike da mamaki ta amsa mashi da toh,
Bayan fitarshi cikin sauri ta nufi closet dinsu, ta dauko wasu hadaddun riga da wando ?an pakistan, rigar fara wandon yellow, veil din kayan yellow, ita kanta data sanya kayan saida ta jinjina ma kyan da sukai mata, gaban mirror ta zauna ta fara gyara sumar kanta dakyar take sharce ta da comb, bayan ta kammala gyara gashin, ta shafa powder da lipstick, kafin tayi rolling veil din akanta, takalma ta dauko masu tsini ta zura su a kafafunta,
Komawa tayi gaban mirror ta feshe jikin ta da turare
Har lokacin bata daina tunanin abun da ya faru a daren jiya ba, was wasi take tayi aranta.., kwata kwata bata so ya zamana gaskiyane abun da ya faru da ita....
A hankali ta zura kafarta ta fito daga dakin,
Walking slowly ta nufi daddyn ta dake atsaye yana jiran ta, babu kowa a falon da alama basu kaiga fitowa ba
"Daddy yunwa nake ji, Ciki na babu komai.." ta fada yayin da ta ruko hannunsa acikin nashi
"Kada ki damu, nima banyi breakfast ba, idan munje wurin chief din zamuyi atare da shi..." amsa mashi tayi da toh
Kaitsaye suka nufi walkway bata san ina za su bula ba
"Daddy ba part dinsa zamuje ba"?
"Eh, yace mu same shi a backyard..

Zazzaune suke akan wasu jigunannun sofas ?an ubansu, backyard din ya HaWu an ?awata shi sosai, chief da hajiya saratu suna a zaune kan sofa daya, Aneelerh da zahra suna fuskantar su, tun da suka zauna Aneelerh take ta jinjina ma haduwar gidan da shi kanshi mamallakin gidan wato chief, kallo Waya tayi mashi saida gabanta Ya faWi, ya Wauki wankan suit navy blue sunyi bala'en yi mashi kyau

Zahra dake satar kallon shi, gani take kamar a mafarki yau gata ga director general na isod, crush Winta, mutumin da tayi haukan son shi a lokacin baya..

Round table din dake a tsakiyarsu, cool drinks ne da Snacks asaman hadadden wooden tray

"Idan muka baku aron yarinyar sai yaushe ne zaku dawo mana da ita.."? Hajiya saratuce tayi masu tambayar
"Idan da hali har zuwa lokacin da benazir din zata ji sau?i, dan Allah ayi mana alfarmar nan..." gyaWa kai hajiya saratu tayi"okey, amma fa zaku bani tukuici tun da ni nayi maku hanya a wurin chief..." ta faWa da yar zolaya tana kallon su
Murmushi suka saki zahra tace"bakomai mommy, ay duk abunda kikeso zamu baki.." yar dariya tayi"zolayarku nakeyi..." dariya sukai su kansu sun san tafi karfin tukuici, ta dai faWi ne don ayi raha...

Kwas kwas sautin takalmanta Ya ratsa kunnuwansu, kusan atare su Aneelerh suka dago tare da kallon inda sautin ke fitowa....S'


*Daga alkalamin Boss Bature mu haWu next page on monday idan Allah yakaimu da rai da lafiya
'?*

*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne dukanshi za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440*____________________________
'?



Kwas! kwas !! sautin takalmanta Ya ratsa kunnuwansu, kusan atare su Aneelerh suka Wago tare da kallon inda sautin ke fitowa...


?ura idanu sukayi suna kallon su, kafin Aneelerh tayi wani irin yunkuri ta mi?e jikin ta na 6ari, zuciyarta na dakan uku uku, gaba Waya tabi ta rikice gani take kamar a mafarki take kallon su!! Kokwanto ta farayi anya kuwa sune? Tajudeen da Angel? Ko dai idanunta ne suke nuna mata badai dai ba? Tayaya mutanan da suka 6ace almost 16years yau kwatsam ta gansu, da ransu da lafiyar su, kanta ne ya wani irin sara mata da sauri ta dafe goshin ta, ganin hakan yasa Zahra ta mi?e a matu?ar ruWe take kallon Aneelerh...

Lokacin da unaisah ta Waura kwayar idanunta akan fuskar Aneelerh, Ras taji gabanta Ya faWi, wani irin burki taci ta dakata da yin tafiyar, idanunta azare take kallon ta, wlh ko amafarki taga fuskar Aneelerh sai ta shaida ta balle kuma azahiri, La66anta na kerma ta furta"Aunty Aneelerh? Daddy! Auntyna ne? Ita ne nake gani azahiri ba mafarki ba? Daddy wallahi itace aunty Aneelerh ce...." kalamanta ne suka dira akan kunnan Aneelerh, baiwar Allah jiki na 6ari ta watso da gudu mayafin ta har yana ?o?arin zamewa, da gudu unaisah ta nufe ta, takalman kafarta suka kusa kayar da ita kasa, amma ahaka ta jure don bazata iya jira aunty Aneeleeh ta karaso gareta ba, zubewa Aneelerh tayi akan gwiwowinta tare da ware hannayenta biyu ta rungume unaisah, tayi hugging dinta tightly lokaci Waya suka fashe da matsanancin kukan farin ciki mai tsuma zuciya =??


A hankali taj ya ?araso Ya tsaya daga bayansu, tare da goya hannayensa bisa kirjinsa.

A sukwane hajiya saratu da chief suka mi?e tsaye suna kallon su, fuskokin kowan nan su Wauke da murmushi su kansu da suka sake haWa wannan zumunci ba karamin dadi suka ji ba, farin cikin da suka gani akan fuskar Aneelerh da unaisah ba zai misaltu ba.


Yadda Aneelerh ta rungume unaisah, kamar zata mayar da ita cikin cikinta, a kalla sun shafe mintuna goma manne da juna, kafin Aneelerh ta raba jikin ta daga na Angel, a lokacin itama ta dur?usa kan gwiwowinta, Aneelerh ta sanya tafukan hannayenta biyu ta tallabo fuskar unaisah da su, itama unaisah ta tallabo fuskar Aneelerh da nata tafukan hannun, suka kurawa juna ido yayin da hawaye ke sintiri kan fuskokinsu, cikin shesshekar kuka Aneeleeh take fadin"Angel dina! Kece nake gani? Dan Allah ki fahimtar dani nagaza yarda da abun da idanuna suke gane min! Wayyo Allahana.." ta fada tana jan numfashi.

"inna lillahi Ya Allah Idan Mafarki nake kada ku tada ni, kubarni kawai inci gaba da yin shi, Ya ilahi Angel dina ce..Ina kika shiga? Kika bar auntynki da ciwon rashin ki? Angel wayyo Allah...duk tabi ta susuce


Cikin muryar kuka unaisah tace"Aunty Aneeleeh, ni ce Angel dinki, ?arki, Aunty Aneeleehna, ba mafarki kike Yi ba, ni ce dagaske, Angel dinki abokiyar firarki, mai sanyaki nishadi..." ?ara rungumeta Aneeleerh tayi.

Gyaran murya taj yayi cikin karayar zuciya ya firta"Aneelerh!.." kamar jira take yayi magana, a zabure ta mike ta tsaya agabanshi idanunta jawur ta furta"taj! kasan irin haukan rashin ku da nayi? Me nayi maka dana tsantsanci haka daga gareka?..." kwalar rigarshi ta dam?a da hannayenta biyu ta jijjiga shi kamar zata rufe shi da bugu taci gaba da fadin"taj meyasa kayi min haka? Meyasa ka gudu da unaisah kuka barni da kewarku? Taj kasan irin kunci da radadin dana naji a lokacin dana farka naga babu ku"?

Kalamanta sun karya zuciyarshi baisan sa'adda hawaye suka wanke fuskar shi ba, Zahra dake kallon su tuni hawaye sun wanke fuskarta ga wani farin ciki da ya lullu6e ta na ganin Unaisah, Jikin chief owais yayi sanyi lakwas tsantsar tausayinsu ne ya kama shi, ba shi ba hatta Hajiya saratu sai da taji tausayinsu duk da bakomai ta sani ba dangane da rayuwar su ba.

"Taj Ina mijina? Ina uzair! nasan Yana atare ku? Ka faWa min taj meyasa kuka gudu daga gida? Tsawon shekara da shekaru baku ta6a waiwayena ba? Laifin me nayi maku taj? Idan wani abu ne yasa kuka gudu meyasa baku sanar dani ba? Harga Allah bakuyi min adalci ba taj! dai dai da rana Waya baku ta6a nema na ba ko da awaya ne...." Da?yar ta ?are maganar, Lokaci Waya ta yanke jiki zata faWi da sauri taj ya tarota ta faWo kan kirjinsa.

Da sauri zahra ta karaso gabansu tana kuka, zu?unnawa taj yayi a hankali ya kwantar da kanta bisa laps din sa, har lokacin Angel tana a durkushe kan gwiwowinta da karfi take furta"Aunty aneelerh ki tashi! Dan Allah ki tashi wayyo Allahna daddy ka ce mata ta tashi" duk tabi ta rude zahra ma kukan take tana ambaton sunanta, Hajiya saratu ta kasa furta komai, lamarin ne da ta6a zuciya..


robar ruwa mai sanyi chief ya dauko daga kan table, Ya nufo wurinsu Ya buWe murfin tare da mika ma Taj, Hannunsa na kerma Ya kar6a Ya tarfa ruwan a tafin hannu Ya watsa mata kan fuskarta, nan take taja mumfashi tare da furzar da shi...
Cikin karyayyar murya ya furta"Anila! dan Allah ki saurareni, wallahi bada son ranmu muka gudu ba, mummunar ?addara ce ta afka mana wadda tayi silar barinmu gida..., na rasa komai nawa Aneeleeh..." ya faWa yana kallon cikin idanunta, dakyar take kallon shi, wani irin azababben ciwon kaine Ya far mata, ita kadai tasan halin da take a ciki.

"Nasan zaki fahimce ni Aneeleerh, har abada kinsan bazan Iya gudunki hakanan ba tare da wani ?wa??waran dalili ba, dukan mu babu wanda baiyi kewar rashinki ba, kuma ko bayan da muka gudu kina aranmu bamu manta dake ba....."

"Taj ina mijina...."! Gabansa ba karamin faduwa yayi ba, kallon chief yayi da sauri ya girgiza mashi kai alamar kada Ya faWa mata, saboda a halin da take ciki muddin suka sanar da ita tsaf zata iya zaucewa.

"Aneelerh, bansan Ina uzair Yake ba! Idan ba zaki manta ba, ba atare muka bar gida ba, adaren ranar da abun ya faru kinzo har gida kin same ni kina kuka kika ce uzair bai dawo ba, har na kwantar maki da hankali, tun daga wannan lokacin ban ?ara sanya uzair a idona na, amma muna nan muna bincike akanshi, in sha Allah shima zamu gano shi.

zuciyarta ba karamar karaya tayi ba, tuni ta sake fashewa da wani sabon kukan.

Kafin wani ya sake magana a cikin su, wayar Hajiya saratu ta fara ringing, da sauri ta zaro wayar daga cikin handbag dinta, ta duba mai kiran ta, p.a din tace, picking call din tayi"Okey, Gani nan zuwa yanzu nan.." ta faWa tare da katse kiran ta dago ta dubi chief.

"My son yakamata na tafi, naso in tsaya amma kirane na gaggawa, duk halin da ake ciki pls ka sanar da ni..." ta fada cikin saurin murya, kafin ta dubi su Zahra.

"Zahra, Ni zan wuce, in sha Allah idan na samu time zanzo asibitin in duba mara lafiyan..." tayi masu fatan Alkhairi, godiya suka dinga yi mata, Har bakin mota chief tare da zahra suka rakata, akan idonsu motar ta fice daga gidan.

Dawowa sukai wurinsu Taj dake a durkushe ?asa.

"Taj baka fadamin meyasa kuka gudu ba..."? Cikin jin ?unar rai ta jefa mashi tambayar.

Atakaice ya labarta mata abun da ya faru da su, tun farkon da suka fara yi ma Alhazawan nan le?en asiri da kuma farmakin da suka kawo mashi atsakar dare harya gudu da Angel....."

sai dai bai sanar da ita wayar da uzair ya kira shi ba ya dai ce shi baisan meya faru da uzair ba, har yau suna neman shi ba su gan shi ba, hankalinta yayi mugun tashi jin wannan musifar data afka masu, hatta zahra tayi matu?ar firgita jikin ta sai tsuma yake abun ya bata tsoro...

"Shiyasa bamu neme ki ba, saboda rayuwarmu tana a cikin hatsari, idan har miyagun suka san muna raye ba za su kyale mu ba, don dole muka killace ce kanmu kafin Allah ya tona asirin su"

"Inna lillahi wa'inna ilaihirraji! taj wannan wani irin tashin hankaline! Ni dama saida raina ya bani ba hakanan kuka gudu ba, Allah Yasa basu kashe uzair ba, nama san mawuyacin abune uzair ya rayu watakil sun kashe min shi...." bai bari ta ?are maganar ba, Ya fara lallashin ta dakyar Ya shawo kan ta....

Zafafan hawayene suka cigaba da wanke kuncin ta,

"Boss!" chief ne Ya kira sunan shi
"Na'am yalla6ai"
"Ina son magana daku, ban da unaisah"

A hankali Ya Wago da Aneeleeh, da sauri zahra ta zu?unna tare da tallabo ta don gaba Waya jikin ta ba kwari dakyar ta samu ta mi?e.

Unaisah dake kallon su ta shiga ruWani tunda chief Yace Yana son ganin su ban da ita...
Ru?o hannunta taj yayi, suka nufi sofas din wuri ya zaunar da ita
"Daddy meya faru"?

"Kada ki damu, magana ce mai mahimmanci zamuyi, Idan muka gama zamu sanar dake, cike da gamsuwa tace toh

"Wazu Kin faWa min kina jin yunwa, ga snacks nan da juice ki sha kafin mu gama magana" yatsun hannunta har kerma suke wurin daukar burger ta fara cin ta.

idanunta akan su Aneelerh dake tafiya suna nufar can nesa da ita, zuciyarta cike fal da farin ciki, kamar wadda akaiwa albishir da gidan Aljanna, bakinta yaki rufuwa sai faman tariyo fuskar aunty aneeleeh takeyi, burinta su gama maganar don ta tambayeta ina ?anin ta da daddynta ya bata labari ta haifa mata....


Bayan kowan nan su ya zauna kan kujeru suka nutsu suna jiran jin me chief zai sanar da su

"Inaso ku faWa masa abun da ya kawo ku neman ?ar sa"! Ya faWa batare da ya Wago ya kalli waninsu ba, aWan ruWe Taj Ya kalli su Aneeelerh.

Baiwar Allah tama rasa ta ina zata fara, saboda tasan ba lallai Ya amince masu ba.

"Aneelerh kinyi shiru! FaWa min meyasa ku ka zo neman Angel? Tun jiya chief yayi min bayanin zuwan ku amma bansan cewa ku bane, nayi mamakin ganin ku! Tayaya har kuka gano inda mu ke!? Ya fada cike da son jin ?arin bayani.

Cike da fargaba Aneeleeh ta fara zayyana masa abun da ya faru na bayyanar benazir, bata 6oye mashi komai.

tunkafin ta ?arasa maganar yanayin fuskar taj ya canza zuwa tsantsar 6acin rai, kwata kwata baiji dadin bayyanar benazir ba, saboda tafi ta aransa baya bu?atarta arayuwar shi, wani irin Waci yaji aran shi, Aneeelerh ta fama mashi tsohon raunin dake a zuciyar shi.

ko sunan ta baison ji, aranshi ya arayyana da ranta da lafiyarta tsawon shekara da shekaru bata ta6a neman su ba? Idan har shi bata neme shi ba ay yakamata ko yarta ta nema baisan wata irin zuciya bace a kirjin benazir ya riga da yasan halinta domin kuwa ba zai ta6a manta irin rayuwar auran da sukai da ita ba, macace mara kunya batasan darajar aure ba, ta azabtar da shi da soyayyarta.

gaba Waya sun lura da yanayin shi, kamar baya atare da su, Aneeleerh duk tasha jinin jikin ta, dafa kafadarsa chief yayi a hankali ya kallesa idanunshi sun kaWa jawu"dan Allah kada kace inyi hakuri, saboda bana jin zan iya yafewa benazir, hasalima ban yarda cewa dagaske ta damu da mu har haka ba, Allah kadai kasan manufar da take da ita akan mu, ba zan ta6a yarda da benazir ba, matar da ta tafi tabar yarta a kwamin wanka, taje can tana yawon biWiWin ta tsawon shekaru bata ta6a neman mu sai yanzu"? Hawayen dake taruwa a cikin idanunsa tuni sun wanke fuskarshi hakan ba karamin Waga hankalin zahra da Aneeerh yayi ba..

Shi kadai yasan ?unar da zuciyar shi take yi mashi
Shiru chief yayi sam ya kasa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login