Showing 12001 words to 15000 words out of 298130 words

Chapter 5 - KURKUKUN KADDARA (TAKUN KARSHE) BY BOSS BATURE.doc

ke yi, amma dana kira sunanta na bubbuga jikinta ta?i farkawa nan fa na gane babu lafiya atare da ita"
A faWa ce Benazir tace
"Tayaya za ki ce bakisan meke damunta ba? Bayan ke ce kike kula da bedroom dinta"
Tani dake kallon Benazir duk tasha jinin jikinta
"Bansan ya zanyi maki bayani ba, ba laifi na bane, tun safe nake fama da ita akan ta fadamin meke damunta ta?i ta sanar dani, na rasa gane kanta ta ?untata kanta aWaki, ta hana kanta sukuni yinin yau" hawaye har sun fara sauka kan fuskar Tani.

Jiki asanyaye Benazir tace"bari naje na faWa ma su Mommy abinda ke faruwa" A firgice Tani tayi hanzarin dakatar da ita ta hanyar shan gabanta muryarta na rawa ta ke ambaton" inna lillahi wa inna ilaihirraji'un, dan Allah ki rufa min asiri kada ki faWa masu abunda ke faruwa, wlh zasu Iya korata daga gidan nan, ba lallai su fahimce ni ba, Alhaji musa baya raga mana akan Zeenatu, Idan yaji wannan maganar babu makawa zai kore ni ne"

Cikin rashin fahimtar kalaman Tani, Benazir tace"dan Allah malama ki bani hanya in wuce, kina ganin yarinya babu numfashi sannan ki hana in fadama Iyayenta, hakan bazai yiwu ba dole suji ko dan akira likitan ya duba ta" a tsiwace Benazir tayi maganar, tare da bi ta gefen Tani ta nufi ?ofar fita dakin.

Zubewa Tani tayi saman gwiwowinta hannayenta biyu asaman kanta, yayin da hawaye ke yin sintiri akan kuncinta.

"Dr shureim nasan kai zaka fahimce ni, dan Allah ka hanata fita daga dakin nan, wallahi idan ta faWa masu halin da ake ciki, bani kadai zata ja ma bala'e ba, duka ma'aikatan gidan nan zata shafa"

?agowa dr shureim yayi, launin idanuwanshi har sun canza kala, muryarshi adidashe Ya ambaci sunan benazir, Harta Waga ?afa zata ?etare kofar Wakin tayi saurin cin burki jin kiran shureim.

Juyowa tayi miryarta da faWa tace"yaya shurem kada ka biyewa matar nan, akan me zata hana afada masu halin da ?arsu take aciki, so kike mu rufa maki asiri, mu zuba ido muna ganin yarinya bata motsi har wani abin da ba'a fata ya faru da ita ko"?

Fashewa Tani tayi da kuka, abun duniya ya isheta.

Cikin sanyin murya dr shureim yace"Sister calm down ur mind, Zeenatu suma tayi ki mi?o mun ruwa in yayyafa mata, sannan kada ki sanar da kowa, mu jira muga awani yanayi zata farka, Idan ba lafiya dole mu sanar da mutanan gidan don akira mata doctor" amsa mashi tayi da toh, da sauri ta nufi ?aramin fridge dake a dakin ta buWe ta Wauko bottle water taje ta mi?a ma shureim yasa hannu ya kar6a.
Kowan nan su fargaba ce azuciyarsa, musamman Tani jikinta ya?i daina yin kakarwa
Kusan sau uku dr shureim Yana yayyafa mata ruwa a fuskarta batare da ta motsa ba, Har sun fara fidda rai a lokacin da ba su yi tsammani ba suka ga Taja dogon numfashi tare da sauke shi, da wata irin kasalalliyar murya ta firta"innalillahi wa'inna ilaihirraji'un"

Atare suka hada baki suna ambaton sunanta"Zeenatu! Zeenat"
Firgigit ta ware blue eyes dinta akan fuskokinsu, launin farin idon ya canza sosai
Wata irin nauyayyar Ajiyar zuciya kowan nan su ya sauke
"Zeenatu, fada min meke damunki"? Tani ce tayi maganar
Cikin kwantar da mirya Benazir tace"Sister Wina, baki da lafiya"? Da ?yar zeenatu take buWe idanuwanta sunyi mata nauyi saboda kukan da tasha, fuskarta tayi jawur.

"My zeenat" jin miryar dr shureim yasa tayi saurin wurga eye balls dinta akan fuskarshi, wani sabon kukan ne ya kufce mata tamkar ranta zai fita, duk tabi ta rikitar da su.

Hada baki su ka yi wuri lallashinta da kwantar mata da hankali da?yar su ka shawo kanta, tayi shiru tana faman ?yaf?yafta masu idanuwanta waWanda ke aji?e sharkaf da ruwan hawaye.

"Please faWa min meke maki ciwo"? Dr shureim ne yai maganar,
Duk sun tsareta da ido
Da?yar ta iya buWe baki ta furta"Yunwa nake ji" sunyi mamakin jin abunda ta fada masu badan sun yarda da maganarta ba,
"Tani, dama zeenatu bata ci abinci ba? Shiru tani tayi tana faman zare idanuwanta, banezir ta jefa mata kallon tuhuma kafin tace" ?azu da safe ke kika ce tace akai mata breakfast dinta a Waki Kenan baki kai mata ba "?
Girgiza kai tayi Tani tayi"Na kawo mata abincin, Itace ta?i ci, ba yau ta fara yi min hakan ba, Idan wani abu na damunta bata cin abinci, kona tursasa mata akan dole taci, sai tace min in tafi zata ci, da zarar nabar Wakin take daukar abincin ta shiga toilet da shi tayi flushing dinshi" har saida Dr shureim ya Wan zaro ido jin abunda Tani tace, Zeenatu ta haWe fuska ga dukkan alamu bata da gaskiya, Mi?ewa benazir tayi da sauri ta nufi toilet jim kaWan sai gata ta fito daga ciki fuskarta adaure babu walwala tace"Zeenatu baki kyauta mana ba, Fisabilillah haka ake rayuwa? Don wani abu na damunka sai ka?i cin abinci? Maimakon ma in ba ci zakiyi ba ki bata ta mayar a kitchen sai ki zubda lafiyayyan abinci, kinsan fa ba kyau Almubazzaranci"

Rufe ido zeenatu tayi, har lokacin bata Wago da kanta daga kan laps din dr shureim ba.

"Tani ki ci gaba da yin ha?uri da ita, In sha Allah zata daina very soon yanzu ki koma kitchen ki haWa mata wani abincin ni zan bata da kaina"

Muryar Tani asanyaye tace"To" kafin ta juya da sauri tabar dakin
"Sister, nabar wayata daki ko zaki dauko min"
Benazir ta amsa mashi da toh, kafin ta fuce daga dakin, Ya rage da ga shi sai zeenatu, dama da biyu ya aiki benazir ta Wauke mashi waya.

A hankali ya tallabo kanta ya Waura shi kan ?irjin shi, tamkar ?ar baby haka ya ru?e ta.

Wata irin kunyarshi ce ta kamata, ta?i bari su haWa ido.

"My zeenat, haka za mu yi aure kina yin min rigima? Ya kikeso inyi da rayuwata idan baki gyara halin nan naki ba"?

Turo mashi pink lips dinta tayi batare da tace komai ba, murmushi yasaki yana mai mamakin ?uruciyar zeenatu.

"FaWa min waya ta6a min ke"? Da?yar ta Wan iya buWe ido ta harare shi kafin tayi sauri kau da idonta gefe, nan take ya fahimci wani abu.

"Hakan na nufin ni na 6ata maki rai? Ko kinji maganganun da muka tattauna nida sister benazir Wazu da safe"?

Muryarta da shagwa6a tace" I heard everything, ya Shuraim! I won't marry you, because you lied to me. You told me that you had never been in love, bayan ba haka ba ne, sannan ka nuna min hotona amatsayin hoton da ka ke yawan kallo a phone din ka, ashe ba haka bane hoton wata ne daban, Why ya shureim? What did I do to deserve that?' she said, giving him a suspicious look.

Aranshi ya ayyana zeenatu matsala, tun yanzu ya fara jin shakkar kishinta .

"Ka tsare ni da ido baka ce komai ba Sannan har fadi kake yi wai ba zaka ta6a samun madadinta ba even if u get married" ranta a6ace ta ?are maganar hawaye nabin fuskarta, hannunta Waya dafe da saitin zuciyarta.

Tun da take yin magana ya natsu yana bin fuskarta da kallo har saida ta gaji don kanta ta dakata da yin maganar tukunna ya samu damar bata amsa
Calmly ya furta"My zeenat, baki fahimci kan zancen namu ba, shiyasa babu kyau yiwa mutun la6e, kalli yadda kika takura kanki akan abunda baki da tabbaci kansa" harara ta jefa masa"yaya shureim ni fa ba kurma bane, Ina ji ai," ta faWa tana nuna mashi kunnanta da hannu.

Murmushi yayi mata, ita ko sai ?ara haWe mashi fuska take yi.

"Bana son 6acin ranki zeenatu, don haka zan faWa maki gaskiyar abunda na 6oye maki, saboda ina burin na aureki duk wani sirrina ya kamata ki sani, amma bana so ki faWa ma kowa"

Jinjina mashi kai tayi alamar Toh, shiru yai yana yanke shawara da zuciyarshi, ?wara ya faWa mata gaskiya idan ba haka ba zata ci gaba da yi mashi kallon ma?aryaci kuma ba sonta ya ke yi ba tun da yana da wadda yake kallon hotonta kullum bayan haka zata cigaba da yin jinyar zuciyartane tun da ita haka Allah ya halicce ta da kishin tsiya.

"Dangane da hoton dana nuna maki naki, tabbas bashi nake kallo ba, hoton ?ata ne nake kallo....." tsabar firgita da jin maganarshi yasa zeenatu ta zabura ta sauka daga jikinshi ta koma tana fuskantar shi, idanuwanta azazzare, maganar ta daki kunnanta tamkar a mafarki taji ta.

"Yaya shurem na shiga uku, ?a fa kace, dama ka ta6a yin aure hada baby"
Girgiza mata kai yayi"a'a, Ni ban ta6a yin aure ba, na samu yarinyar bata hanyar aure ba...." bai kai ga ?are maganar ba yaga ta Waura hannayenta biyu saman kanta alamar ta shiga uku.

"Ya shureim dama kai Wan iskane" dafe kanshi yai da hannu Waya

"Idan ba zaki natsu ki saurare ni ba, zan tashi nabar Wakin nan" da sauri taja baki tayi shiru.

Tuni yanayin fuskarshi ya canza sam baya son tuna abunda ya faru a rayuwar shi, tamkar yana faman raunin dake a zuciyar shi ne

Numfasawa yai kafin ya Waura da cewa "Bayin kai na bane, zan Iya cewa ?addarace ta afka min har hakan ya faru, a yanzu haka da nake baki labari, Yarinyar bata araye tun tana jaririya ta rasu, Tsakanina da mahaifiyarta bamu ta6a yin soyayya ba, daga ni har ita ba mu ta6a tsammanin zamu yi mu'amala da junan mu har takai mu ga aikata sa6on Allah, mun fuskanci matsanancin tashin hankali, abun da ya faru zeenatu shine silar ?uncin rayuwar da na shiga..... '

Du?ar da kanshi ?asa yayi tamkar mai neman gafara, hawaye tuni sun cika idanuwanshi, sam bayason tuna baya saboda tsohon raunin dake acikin zuciyarshi.

Jikin zeenatu yayi mugun yin sanyi, har cikin ranta ta yarda da maganar shi, ta kuma ji tausayin shi.

"Yaya shureim na yarda da kai, please forgive me for what I said. Rashin sani ne kuma nayi danasani, dan Allah ka daina zubar da hawayen ka, I know it's hurting your heart, amma kayi ha?uri"

Matsawa tayi kusa dashi ta sanya tafin hannayenta biyu ta share mashi hawayen dake akan fuskarshi, wani irin tausayinshi ne ya kamata, da sauri ta rungumoshi ya Waura kanshi saman kafaWarta itama ta Waura nata kan asaman tashi kafaWar.

"Yaya shureim ita babyn taka an riga haihuwarta kafin Ni"?

Cikin rauni na murya ya furta"da ace tana araye da yanzu ta girmeki" cikin sigar lallashi take Wan bubbuga bayanshi da hannayenta, ba tare da sun raba jikinsu ba taci gaba da tambayarshi Ya sunanta"?

"*FATIMA*" atakaice Ya bata amsa
"Allah sarki ?ar uwata fatima, Allah yaji?anta"
"Ameen"
"Ita maman babyn naka, meye sunanta" shiru yayi don baison furta sunan.

Fahimtar hakan yasa tayi saurin canza akalar zancen nata

"Yaya shureim idan aunty benazir ta kawo maka wayarka zaka nuna min hotonta dan Allah"
"Zan nuna maki"
A hankali ta Wago da fuskarta, haWi da daura idanuwanta akan fuskarshi, ta dafe kafadunsa da hannayenta
Ido cikin ido suke kallon juna
"Idan mukayi aure nima zan haifa maka Wiya, bama Waya ba ?an biyu zan haifa maka, sai mu sanya masu sunan Fatimarka" tunkan ta ?are maganar tayi saurin dukar da idonta ?asa
Shi kanshi yayi mamakin maganar data furta mashi, saboda kunyar dake gareta amma ya fahimci tausayin shi ne Ya kamata.

Shafa sumar kanta yai da hannun shi Waya"nagode da kulawarki agare ni,"
da buWar bakinta sai cewa tayi"ya shureim pls ka sanar da daddyna da daddynka maganar auranmu, suyi sauri su daura mana aure, don in haifa maka fatima"

Dariyace ta kubce mashi, cikin jin kunyarshi Zeenatu ta yi saurin mi?ewa ta nufi gado ta haye ta kwantar da kanta
Abun da basu sani ba, benazir tana la6e tana sauraronsu, hannayenta biyu ru?e da Tray din abincin zeenatu data kar6a a hannun Tani
Hankalinta idan yai dubu toh ya tashi, har sai da gabanta ya fadi, Jin zeenatu nayiwa shureim zancen aure, aranta tace"taya ma haka zata yiwu? Soyayya tsakanin Ya shureim da zeenatu ?ar cikinsa? Anya kuwa zeenatu tasan ainihin shekarun dr shureim? Lamarin ya Waure mata head.
Shiga dakin tayi da sallama abakinta, dr shurem ne ya amsa mata sallamar, ta ?arasa kan carpet din gefen gadon ta Waura mata tray din
Idanuwanta akan fuskar Dr shureim, ya lura da kallon da take yi mashi sai dai bai kawo komai aranshi ba
"Ina wayar"
Cikin aljihun jallabiyar jikinta ta zaro wayar ta mi?a mashi, Ya kar6a yana fadin"nagode sister,"
"Yayana, wani abu ya farune bayan fitana? Naga zeenatu a kwance kan gado"
"Taji sau?in abunda ke damunta, dama ba wani ciwo bane" gyaWa kai benazir tayi"Okey, mu taimaka mata taci abincin"
Atare suka zauna da zeenatu suna bata abinci abaki, Hankalin benazir yaki kwanciya sai satar kallon dr shureim da zeenatu takeyi afakaice batare da sun ankara ba, har wani kallon ?auna taga suna jefawa junansu, ita dai abun ya tsaya mata aranta, ya girmi tunaninta.......


*d'HAJIYA ADAMA>?
?*


A zaune take kan mirror chair, ta Wauki wankan riga da zane na zallar leshi launin ruwan toka rigar tayi matu?ar yi mata kyau, ta ca6a adon zabba da awarwaro a hannunta, head dinta kala Wayane da takalman ?afarta black colour, Hand bag Winta tana ajiye saman gadonta itama launin takalmanta ce.

A tsanake take shirya kanta, bayan ta gama shafe shafenta, ta kai hannu ta Wauki turare tabi ko'ina na jikinta ta feshe, mi?ewa tayi ta nufi gadon inda ta ajiye mayafinta, ta Wauka ta yafa shi a kafaWa, kafin ta ru?o handbag din.
Tana ?o?arin juyawa Uncle abdallah Ya doko sallama hannunshi Wauke da baby junaid sunyi shiga kala Waya ta shadda blue sky.
Murmushi tasakar mashi, da fara'a akan fuskar uncle abdalla yace"madam shanyar da ki ka yi ta bushe tun Wazu ba ki je kin dubo ta ba"

Farfari tayi mashi da ido"am sorry my husband, nabarku kunata jirana awaje"
From head to toe yake binta da kallo har zuwa kan head din data Waura, komai nata burgeshi yake yi, Hajiya adama ta Iya Waukar wanka.

Baby junaid sai faman lumshe idanunsa yakeyi sam baya fahintar komai biji biji yake ganinsu baccine ke neman yaci ?arfinsa
"Kullum ?ara kyau kike yi, faWamin menene sirrin"?
Still fuskarta da murmushi tace"bani da wani sirri daya wuce kai, Mijina, saboda kulawar da kake bani da tarairayata da kakeyi sune suke ?aramin kwanciyar hankali da natsuwar da nake samu har kake ganin ina ?ara kyau"

Lumshe idanuwanshi yayi tare da waresu kan fuskarta.

"Shiyasa nake ?ara ?aunarki acikin zuciyata, samun mace irinki abune mai wuya a duniyar nan, kin haWa komai hajiyata, kyau, nasaba, ilmi, abu mafi jan hankali agare ki, tsaftarki, da Iya girkinki, idan nace zan lissafa maki kyawawan Wabi'unki da halayanki to kuwa zamu kwana batare dana kammala karanto maki ba"
Tsabar jin dadin maganarshi ce tasata yin dariyar farin ciki
"Kana ?ara huramin kaina fa,"
"Ba hura maki kai nakeyi ba, Kin cancantane my wife"
"Thank u dear, for loving me and for everything" har cikin zuciyarta take fada mashi kalaman
"Yakamata mu tafi, baby junaid fushi yake yi damu, mun?i kai shi wurin mommynsa" ya fada yana dariya
Kallon fuskar baby junaid hajiya adama tayi, tuni bacci yai awon gaba dashi, Ya langwa6e kansa saman chest din uncle abdallah.

"We will miss him. I love my grandson bana son rabuwa dashi sai dai ba yadda zanyi dole na maida ma mamansa" yanayin fuskarta ne ya canza zuwa damuwa,
" jin kaina nakeyi tamkar ban ta6a haihuwa ba saboda rashin Uzair, abun yana ta6a min zuciyata, shi kaWai nake gani inji dadi, da kuma Wan uwansa tajuddeen da baby angel dinmu Yanzu duk babu su ..." cikin jin ?unar rai ta furta maganar, jikin uncle abdallah yayi sanyi, Shi kanshi abun yana damunshi.

"Tunda na haifi uzair ban sake samun damar da zan haihu ba, saboda matsalar dana samu, mijina meyasa ba zaka kar6i shawarata ba? Nifa inason ganin jininka" idanuwanta sun cika tab da ?walla.

?aure fuska uncle abdalla yayi, tamkar bai ta6a yin dariya ba

"That's enough! Bana so kina min maganar nan! Stop trying to pressure me into getting married. I have no intention of doing it, ke kaWai kin ishe ni, kada na kuskura naji kin sake tada maganar," Yana ?arasa maganar ya juya da sauri ya fuce daga falon, Bin bayanshi tayi, a harabar ajiye motocinsu, ta same shi tsaye ya jingina bayanshi jikin motar, harya kwantar da baby junaid, a back seat.

Agabanshi ta tsaya tana ?o?arin shanye damuwarta tace"am sorry, idan ranka ya 6aci, bazan ?arayi maka maganar ba,"
Batare dayace mata komai ba ya nuna mata murfin motar, buWewa tayi ta zauna a front seat, Ya zagaya ta other side ya zauna a driver's seat, key yayi ma motar, a hankali yayi reverse ya karya kwana ya fitar dasu daga cikin gidan, tunda suka haura kan titi babu wanda yayima wani magana acikinsu, kowa da abunda yake sa?awa aran shi, idanuwan hajiya adama sun kaWa jawur dasu, jefi jefi takan kai idonta ta cikin mirror din motar ta kalli baby junaid dake akwance yana sharar baccinsa, mutuwar son yaron takeyi, sam batason rabuwa dashi sai dai ba yadda zatayi.

A hankali motarsu ta ?araso bakin gate din gidan Uncle Wan Iya, Horn su ka yi Baba mai gadi Ya buWe masu ?ofar su ka shiga daga ciki, bayan uncle abdallah yayi parking din motar, cikin kulawa ya dubi fuskar Hajiya adama
"My wife," kallon shi tayi fuskarta a yamutse babu walwala
"Kinsan ina sonki, and bana son 6acin ranki, zan Iya yin komai danganin na faranta maki rai, dalilin dayasa bazan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login