Showing 192001 words to 195000 words out of 298130 words

Chapter 65 - KURKUKUN KADDARA (TAKUN KARSHE) BY BOSS BATURE.doc

wani bai isa Ya cutar min dake ba! ...." bai kare maganar ba, tace"bansan ya zanyi ba, wallahi ina jin tsoron ranar da asirinmu zai tonu, pravin bana son abunda zaija mu rasa kimarmu da darajarmu a idon mutanan gidan nan, saboda ina ji araina akwai wanda ke son ya tona mana asiri shiyasa aka fara bibiyana.." ta faWa tana jan numfashi kafin taci gaba da cewa"saboda fargaban abunda Ya faru daren jiya, ko abinci banci ba tun safe har yau kamar mai azumi, wanka ma nakasa yin shi...."

Ta ?are maganar, tana kallon cikin idanunshi

"Tuntuni saida naso In siya maki gida daban inda zakiyi rayuwarki cikin kwanciyar hankali, amma sai kika nuna bakison rabuwa da su....abunda nake jiye mana kenan...

"Duk laifinka ne, Abunda kayi min awurin dinner din hateem shine Yaja har wasu suka fara zarginmu, kuma ni gaskiya bazan bar gidan nan ba, kawai ka nema min mafita ..."

Jinjina kanshi yayi tare da ruko hannayenta acikin nashi"zan tambaye ki wani abu" daga mashi kai tai alamar toh

"Idan kika kama 6era adakin ki Yana yi maki 6arna, kuma kinsan zai iya haifar maki da gagarumar matsala wani hukunci zaki masa"?

"Meyasa kayi min wannan tambayar"?

"Kedai ki bani amsa"!

Shiru tayi jim kafin tace"hannayen da yake yin amfani da su wurin yin 6arnar su zan na?asa, sannan in murje bakin shi ta yadda bazai iya daukar komai da shi ba...." murmushi pravin ya sakar mata"kin kawo shawara mai kyau.." arude tace"bangane me kake nufi ba"
Bai bata amsar tambayarta ba, sai cewa yai muje bathroom In taimaka maki kiyi wankan da kika kasa"

Ajiyar zuciya ta sauke tare da mikewa suka nufi toilet atare almost 18 mins Ya fito dauke da ita a hannunshi, dukansu sun daura towel a waist dinsu,
Taimaka mata yayi ta sanya kaya, shima ya maida nashi

"Tashi ki je kitchen ki shirya mana abinci mu ci atare" amsa mashi tayi da toh,

Bayan fitarta da yan mintuna ta dawo hannunta ruke da try na kayan abinci, ta ajiye masu kan rug, saukowa yayi daga kan gadon suka zauna atare suna ci.....

___________________________
'?

Bayan kammala sallar Magbrib, Owais Ya nufo pool yard din gidan baba obie, Jikin shi sanye da farar jallabiya, tunkafin Ya ?arasa Ya hango Hajiya saratu zaune kan kujera ta Waura ?afa Waya bisa Waya, Hankalin ta na akan wayar hannunta da take dannawa


Cikin kunnanta ta tsinkayi muryarsa"Assalamau alaikum" ba tare da ta kalle shi ba tace"wa'alaikum salam,"
Zukunnawa yayi daga gaban kujerar da take Cikin girmamawa Ya gaishe da ita, Har cikin ranta taji daWin hakan da yayi mata sai dai bata nuna a fuska ba, wai don kada ya raina ta
"Lafiyalou My son, ina fata Ka wuni lafiya? Ya aiki"?
"Alhamdulillah.."
"Bismilla ka zauna" ta fada tare da nuna masa chair din dake facing dinta, mi?ewa yayi bayan ya zauna ya Wago da ido ya kalle ta, babu alamun zata kalle shi

"Mommy, kince kina son ganin na, zamu yi magana" sai da ta mula ta sha iska kafin tace"eh, magana ce mai mahimmanci, Ina fata zaka bani aron hankalin ka.."

Amsa mata yayi da toh, tsawon mintuna biyar ta shanya shi, kafin ta fara kora mashi jawabi dangane da zuwan su Zahra, da alfarmar da suka nema a wurin ta...." tun da ta fara maganar, Yake dubanta da alamun rudani akan fuskarshi.


"Ita zahran da ta kawo min maganar, tana Waya daga cikin interior designers din da suka yi mana aiki aranar dinner din hateem a hall dinne taga yarinyar, sunan yarinyar ta wurinsu Angel amma asalin sunan ta Unaisah, har hotonta sun nuna min, sunyi kama sosai da yarinyar wurin ka,"

Cike da son jin ?arin bayani yace"ko ta fada maki sunan Baban Yarinyar da sunan mahaifiyar ta"? Shiru tayi tana kokarin tariyo sunan su ....can tace"na tuna, sunan mahaifin yarinyar zaheer tajudeen, mommynta kuma sunanta benazir"

." Bari na kira Daddyn nata, naji idan Ya san su" da mamaki hajiya saratu tace"oh dama mahaifin yarinyar yana atare da ku"?
"Eh," ya bata amsa atakaice, har cikin ranta taji dadin jin hakan....
Phone dinsa Ya curo daga aljihu Ya danna ma Taj Kira, Tana fara ringing Ya saka wayar a handsfree don taji abunda zasu ce

"Yalla6ai barka da marece, Na shigo gidan na taras baka nan.."

"Ina agidan grandpa, zuwa anjima zan shigo"

"Allah ya dawo kai lafiya"

Am so nake na tambaye ka, Wa cece Aneelerh! Kamar na ta6a jin sunan abakin ka"

"Yalla6ai ka kamanta ne halan, matar aminina ce uzair, kamar mahaifiya take awurin Angel Wina..." murmushi hajiya saratu tasaki jin abun yazo mata cikin sauki

"Zamuyi magana idan na shigo gidan" amsa mashi yayi da toh, bayan yayi rejecting call din Ya Wago Ya kalli hajiya saratu dake kallon shi

"Yarinyarsa ce..."

"Alhamdulillah, Yanzu gobe da yaushe zasu zo ganin ta? ta tambaya tana kallon shi

"Duk lokacin da yayi miki, su zo kawai" murmushin gefen fuska tasaki, Taji dadin yadda yake bata girma
"Nagode my son, bari nasa akawo mana abun sha" da sauri yace"ina so zan shiga wurin baba"
"Okey, mu tafi tare" mikewa sukayi atare suka jera suna tafiya, abun ba karamin dadi yayi mashi ba, tsawon lokaci basa jituwa da juna, sai gashi silar neman unaisah da yan uwanta sukazo yi Allah Ya haWa kan su, Har fira ta fara jan shi da ita, a haka har suka karasa dakin baba obie...

Idan muka koma 6angarensu Hajiya Layla dake a asibiti, wuraren ?arfe 8 na dare, Hospital staff suka fara sallamar mutanan da ke zuwa dubiya, saboda a dokar asibitin karfe takwas na safe visitors suke zuwa da zarar takwas Na marece Yayi kowa zai tafi za'abar majinyaci karkashin kulawar nurses
Hajiya layla tace ita fa ba inda zataje, dole ta kwana don ta kula da yar ta, dr shureim ma ya goyi bayanta, tunawa da barazanar kashe benazir da ake ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????Yi, Idan suka tafi ba lallai nurses su san lokacin da za'a farmake ta ba, duk da akwai cctv camera a kowani daki na marasa lafiya, bayan hakan asibitin Yana da tsaro sosai, kawai dai bai yarda subar benazir ta kwana ba tare da wani nata akusa ba
Hospital staff din basu Yi masu gardama ba, ganin sanannu ne a idon jama'a, kuma da ma ire irensu sunayi masu alfarma, kodan saboda matsayin dake gare su, musamman hajiya Saratu da takasance former firstlady ta kasar, tun da ta sanya baki a maganar suka amince hajiya layla ta kwana tare da ita.

Gaba dayansu sun hallara a harabar ajiye motocin asibitin, Sun fito domin tafiya gidajen su,
Mami da abie suna atsaye, Ga Aneelerh da Zahra da mahboob, Aneeleeh taso abarta tayi jinyar benazir,
"Mu zamu wuce, Ubangiji Allah Ya bata lafiya, Allah Ya tashi kafadunta, in sha Allah zamu cigaba da tayata addu"a" abie ne yai maganar tare da mi?a ma Alhaji ubaid hannu suka yi musabaha
"Mungode sosai, Allah yakaiku gida lafiya,"
Mami tace"dan Allah duk halin da ake ciki game da rashin lafiyarta ayi kokarin sanar damu"
Hajiya sarah tace"in sha Allah zamuyi kokarin hakan"
bayan abie da mami sun shiga mota, Hajiya layla ta ruko Hannun Aneelerh acikin nata fuskarta dauke da matsananciyar damu tace
"Dan Allah kiyi kokari Aneelerh, Zuwa gobe, Ku tuntu6i iyayen yarinyar da kikace tana kama da yarta, ku rokar mana alfarma awurinsu, su ara mana ita, idan ma suna bukatar mu biyasu kudi su faWi nawa suke so, ko nawa ne zamu biya, wallahi bana so na rasa benazir, ina matu?ar jin tausayinta...." la66anta na kerma ta ?are maganar, tuni taji hawaye sun wanke fuskarta
Wani irin tausayinta ne Ya kama Aneelerh, bata san sa'adda itama ta fara share kwallar ba, Yau dai sun sha kuka bayin Allah
"Mommy in sha Allah zanyi kokarin ganin sun bamu yarinyar, Indai akan benazir ne wallahi sai inda karfi na ya ?are...."
"Pls kukan Ya isa haka, Ku yi hakuri, mu cigaba dayi mata addu'a Allah Ya bata lafiya..." acewar hajiya sarah
Dakyar sukayi sallah da juna, bayan sun aneelerh sun shiga motarsu, A jere motocin suka fuce daga asibitin,

"Zan tafi ba dan naso ba, amma In sha Allah, gobe da wuri zan shigo asibitin"
Fuskar hajiya layla a yamutse tace"Sai Allah Ya kaimu.."
"Duk halin da ake ciki, pls ki sanar dani" ta amsa mata da toh,
"Allah Ya bata lafiya" ta amsa mata da ameen, dr shureim ne ya buWe mata murfin motar, Ta shiga daga ciki, kafin Ya datse mata, akan idonsu motar hajiya sarah ta fuce daga asibitin
Ya rage saura su uku dake atsaye suna kallon juna,

"Shurem muje ko"? Alhaji ubaid ne yayi mashi maganar, Sam baya son tafiya, Gani Yake kamar in ya tafi wani abu zai faru da benazir,
"Toh daddy" Yayi maganar, Tare da ruko hannun hajiya layla
"Mommy, nasan ko ban fada maki ba, zaki kula da ita, amma inaso ki sanya ido sosai, dole sai kin hana idonki bacci in ba haka ba..." bai kare maganar Ba Alhaji ubaid Yace"meyasa kace haka"?
"Daddy akwai wani abu da nake zargi akan benazir, zan sanar daku amma ba yanzu ba, saboda bana son Waga maku hankali, kawai abinda nakeso mommy kada kiyi gangancin kula da ita, in ba haka ba za'a iya samun matsala, duk da munsan Allah ke tsare bawansa amma da bukatar muma mu kula"
Hankali atashe Hajiya Layla ke kallon shi, Muryarta na rawa tace"Shureim dan Allah ka fada min meke shirin faruwa da Benazir dina, ni dama najima ina zargin akwai wanda ke bibiyar rayuwarta, so ake akashe min ita, ko faduwar da tayi a toilet sai da raina ya bani wani mugun abunne Ya faru da ita, in ba haka ba taya za'ace ta fita hayyacin ta? Bata gane kowa dake akanta?..." maganganunsu sunso rikita Alhaji ubaid Ya rasa gane inda zancen su Ya dosa
"Dan Allah kuyi min bayani meke faru ne"?
Da ido Hajiya layla tayi ma dr shureim Alamar yayi shiru saboda tana zargin ba hakanan Aka kyale Alhaji ubaid ba, kada su saki baki su sanar da shi zargin da suke Yi Yana iya zuwa ya sanar ma Alhaji musa, tunda Ya zama kamar ubansa komai zaiyi sai ya nemi shawarar shi
Jinjina kai dr shureim yayi alamar Ya fahimce ta,
"Daddy, Muje gida zan sanar da kai komai" Ya faWa tare da ruko hannun shi, Hajiya layla tayi masu Allah Ya kiyaye hanya, tana atsaye tana kallon motarsu har suka fuce daga hospital din,
Da sauri ta koma Wakin benazir, tana shiga, ta iske Nurse agaban gadon ga benazir zaune jikin ta sai kerma Yake tana ta sambatu
"Daddy, mommy, ku kira min taj, Ya kawo min babayna dana bar mashi, dan Allah ku bani ?ata, kada na mutu ban ganta ba...." lallashinta hajiya layla ta cigaba da yi sam bata fahimtar komai, sunan ?arta da mijinta kadai take ambato,
Har abinci nurse ta kawo mata, kwata kwata ta kasa cin shi, duk yadda mami takaiga lallashinta abun Ya faskara, Addu'oi ta koma tana tofa mata, har dare Ya tsala mami tana zaune kan kujera tana kallon ta, Har dr ya shigo ya kara duba jikinta, Ya bata magungunanta dakyar suka samu ta sha, daga bisani bacci Yayi awon gaba da ita, lokacin da aka fara kiraye kirayen sallar ishai'a, mami ta shiga toilet cike da zullumin kada wani ya shigo dakin Ya cutar da benazir, saboda ta razana da jin kalaman dr shureim, jin motsin mutun adakin yasa tayi wuff ta bangaje kofar toilet din ta fito tana haki, Ko alwalar bata karasa ba..

*Daga alkalamin Boss Bature mu haWu next page
'?*

*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne dukanshi za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440*_________________________
'?


Dafe kirji tayi tare da sauke ajiyar zuciya, ganin likitan dake kula da benazir ne

"Are you okey"? Daga mashi kai tayi alamar eh,

Ganin tana mashi kallon kamar bata yarda da shi bane yasa shi cewa"zan tashi daga aikine, Na shigo na kara duba lafiyarta ne, kafin na tafi...." murmushin Ya?e ta sakar mashi"mungode dr, Allah Ya saka da alkhairi, agaida gida" ya amsa mata da toh, harya fuce daga dakin Yana mai mamakin Hajiya layla, abun ya daure masa kai yadda ta fito daga toilet a haukace anya kuwa tana da lafiya"?

Komawa cikin toilet din tayi, sam babu nutsuwa atare da ita, shaf shaf ta ?arasa alwalar ta fito da sauri ta nufi closet din dakin ta dauko darduma ta shimfiWa tare da kabbara sallah.
Da zarar taji motsi adakin sai gabanta Ya faWi, bayan ta ida sallar, ta zauna tayi addu'o'i ta kai kukanta wurin Allah,
Kafin ta mike ta koma kan chair din dake fuskantar gadon benazir ta zauna tana kallon ta, patient gown din dake ajikinta launin light blue tayi mata kyau, A hankali ta kai hannu ta shafa gefen fuskarta, tuni taji ?walla sun cika idanunta.

Idan muka koma bangaren su Aneelerh, bayan komawarsu gida, A falo suka zauna kowa Yana jimamin halin da Benazir take a ciki, Ummi ta fito daga daki hannunta dauke da Baby junaid bawan Allah tunda Mahboob ya dauko shi daga makaranta, Ya dinga kuka Yana ambaton mommynsa, dakyar mami ta samu ta shawo kanshi Har yaci abinci tayi mashi wanka, har bacci Yayi, sauke shi ummi tayi da gudu Ya nufi Aneelerh ya faWa jikinta Yana kuka, Ta rungune shi tana lallashin shi, dakyar ta shawo kanshi har suka sasanta junansu...

Lokacin da hajiya sara ta shiga falon gidan, kasa yin sallama tayi saboda fargaban hukuncin da Alhaji musa zaiyi mata, Cikin sanWa ta nufi bedroom din su ko sallama batayi ba, ta shiga ciki,

A kwance ta same shi kan shimfiWeWan gadon shi, Ya tada kanshi bisa pillow, zeenatu na arungume da shi, ta daura kanta bisa kirjinsa, daga ita har shi kayan bacci ne a jikin su

Tayi tsammani bacci suke Yi, ajiyar zuciya ta sauke, ta lalla6e ta nufi cikin dakin, ta daura key dinta akan mirror, ta nufi toilet ta shiga, alwala tayo tana kokarin fitowa daga toilet din suka ci karo da shi, wani irin bugu kirjin ta yayi, tuni gumi ya lullu6e fuskarta, la66anta na kerma tace"yanzu na shigo, nayi tunanin bacci kake Yi, fatan na same ka lafiya..." tsare ta da idanunsa yayi masu matukar gigitata, gaba daya yayi mata kwarjini

"Ki faWa min wani hukunci Ya dace Inyi maki"! Rass taji gabanta Ya fadi, marairaice mashi fuska tayi"am sorry bazan ?ara ba, wallahi bansan na Waga maka murya ba, dan Allah Ka yafe min.."
Fuskarshi babu annuri Ya furta"cewa nayi ki fada min wani hukun ci Ya dace nayi maki"?
Shiru tayi batare da ta furta kalma ba, duk tasha jinin jikinta....fargabanta kada Yace zai turata U.s
Saboda bata son duk wani abu da zai rabata da shi, shiyasa take yi mashi biyayya sau da kafa, duk wani abu da tasan zai bata masa rai, tana kokarin ganin tayi takatsantsan da shi
"Daddy kayi mata hakuri tun da ta gane kuskuranta," muryar zeenatu ce ta ratsa kunnuwansu,
"Kinci sa'a, da yau sai kin yaba ma aya zakin ta" nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke, har zata wuce ya sake shan gabanta, a rude ta kalle shi
"Ya jikin benazir din?
"Jikin nata yayi tsauri, kwata kwata bata a hayyacin ta, baiwar Allah tana jin jiki"

"Allah Ya bata lafiya, in sha Allah gobe da safe zanje dubata" har cikin ranta taji dadin jin zaije dubata,
"Allah ya kaimu lafiya.."
"Kije kiyi sallar, kafin kin kammala zan kira tani ta shirya maki dinner dinki, nasan kina jin yunwa, kin wuni baki ciki komai ba" ya fada tare dakai hannu Ya shafa flat tommy dinta, aruWe hajiya sarah take kallon shi, kamar ba Alhaji musa ba,yadda kasan badaga bakinshi kalaman suke fitowa ba,
Kamar sakarya haka ta kura mashi ido tana kallon shi, murmushin gefen fuska ya sakar mata, gaba daya ya nemi zautar da ita, dakyar ta samu nutsuwar sanya hijabi ta kabbara sallah,......"
Sallamar su Alhanji ubaid ce ta karaWe kunnuwansu, da gudu Zeenatu ta diro daga kan gado ta fuce kamar walkiya, tunkafin ta karaso dr shuriem Ya hangota, murmushi ya saki tare da bude mata hannayenshi ta faWa kan kirjinshi tana dariya
"Yaya shureim sannu da dawowa, naji dadin ganinka, dama ina ta zullumin kada kaki dawowa gida.." bata ?are maganarba, Alhani ubaid Yayi mata gyaran murya, waro idanu tayi don gaba daya ta manta da shi awurin cike da jin kunyarshi ta rufe fuskarta da tafukan hannayenta
Dariya Alhani ubaid Yayi"zeenatu, meya hanaki yin bacci..." muryarta da yar shagwa6a tace"yaya shureim nake jira ya dawo..." kafin ta kare maganar Alhaji musa Ya shigo falon Ya nufe su cikin takun nan nasa na isa
"Sannunku da dawowa, ya mai jikin"?
Alhaji ubaid Yace"da sauki, kafin mu dawo ta farka sai dai bata ahayyacin ta...." cikin nuna tausayawa ya furta"Allah Ya bata lafiya, gobe zanje asibitin, Ina Hajiya laylan ne"?
Dr.shureim yace acan zata kwana" shiru yayi bai ce komai ba.

wani abu daya daurewa dr shureim kai tun da ya dawo gidan zeenatu bata tambaye shi Ya jikin benazir ba, kwata kwata kamar irin ta manta da zancen ta, bayan tafi kowa nuna damuwa akanta, har magana yayi mata banji kin tambayin auntynki benazir ba, sai tayi shiru bata tanka mashi ba kamar bataji me yace ba, kusan sau uku yanayi mata maganar tana share shi, amma idan yayi mata wata maganar daban saita amsa mashi.

Bayan shigar shi daki, kasa runtsawa yayi, har saida Ya kira mommynsu a waya ya tambayeta awani hali suke ciki? Ta tabbatar masa da komai lafiya kafin ya samu nutsuwar Yin bacci.

*EX-PRISONERS*

Around ?arfe 10 na dare, ummi ta sauko down, har ta shirya cikin kayan baccin ta,
Tunkafin Ta karasa Ta hango wasu daga cikin su kwance ka lallausar carpet din falon suna bacci, tun da zu tabarsu suna ta shan fira atsakaninsu tayi tunanin in sun gama zasuje su kwanta sai kuma ta taras da su kwance suna sharar bacci, wasu asaman sofas wasu akan carpet

Murmushi tasaki haWi da girgiza kanta, tama rasa tayaya zata fara tada su,duk sun sanya kayan baccin su..., Waya bayan Waya ta fara farkar da su

"Batool My baby, wake up, Parveen! Hannah ku tashi dan Allah....! Ni bansan ya akai kuka bari bacci Ya dauke ku a falo ba, salon kawai ku wahalar da auntyn naku..." dakyar ta samu batool ta mi?e tana ?an soshe soshe

"Wuce kije daki" ta amsa mata da toh,
"Praveen ku tashi..." cikin magagin bacci ta buWe ido bakinta cunkushe da apple din da bata


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login