Showing 150001 words to 153000 words out of 298130 words

Chapter 51 - KURKUKUN KADDARA (TAKUN KARSHE) BY BOSS BATURE.doc

kaji kana bukatar abokiyar rayuwa ka sanar dani, zan goyi bayanka kuma zan nema maka dattijuwa dai dai da kai" dariya baba obie yayi "Allah ya kiyaye In auri tsohuwa, Haba owais Ina laifin Yar sha takwas mai jini a jika, wadda zata sangarta ni, kasan mu tsoffi munfison adinga tarairayarmu kamar irin new born baby, Yanzu ni owais idan na auri dattijuwa kamana me zata min"? da mamaki chief ya Wago yana kallonsa kai kace ba daga bakinsa kalaman suke fitowa ba.

Kafin Ya bashi amsar maganarsa, Wayar baba obie Ta fara ringing, da sauri ya zarota daga aljihu tare da picking call in ya kara a kunnansa.

Chief owais sai kallonsa Yake yi har yau yana mamakin tsufan kakan nasa, kwata kwata babu rudin tsufa atare da shi, yana da karfi ga kaifin basira, idanunsa kuwa kona matashi albarka saboda yadda yake gani da su ko bai sanya glass ba, harta sandar da yake rukewa ta gayu ce ba dan ya gaza taka kafarsa ba.

"Alhamdulillah Alhamdulillah, almost 3 time baba Obie Ya furta hakan, Hannunsa Waya dafe da saitin zuciyarsa alamar Yaji sanyi aransa.

"Ina fata kun sauka lafiya, Ubangiji Allah Ya huta gajiya, Ina ?an jikokin nawa da surukar arzikin Ina fata duk suna lafiya"? Ya tambaya yana sauraron muryar wanda suke magana da shi.

"Madallah, naji dadin jin hakan, Hateem ka kula min da kanka, tun da ka haura kabar kasar nan nake ta zullumi duk bayan yan mintina saina duba Onn news inga ko kun sauka lafiya don nasan sune nafarkon da zasu fara buga labarin yadda jirginku yayi landing sai gashi cikin ikon Allah Ka kirani...' yai maganar fuskarsa dauke da murmushi

"Muna atare da owais, watakil Ya manta wayarsa agidane, wuni yayi awurina yanzu haka muna a garden..."

mi?a ma owais wayar yayi"uncle dinka ne ke son magana dakai, kar6i kuyi magana kai masa bangajia jirginsu Ya sauka lafiya...."

da sauri chief Ya kar6i wayar tare da karata a kunnansa
"My uncle, Ykk Ina fata kun sauka lafiya"?
On the other hand muryar prime minister ta amsa da cewa Alhamdulillah Myson, tafiya tayi kyau yanzu haka Ina a bedroom dina dakyar na samu jama'a suka ?yale ni"
"Sunyi kewarka ne, Kai dinne badai farin jini ba,
Yar dariya hateem yai kafin ya numfasa Yace"Ina yarona? tun ina a cikin jirgi nake ta tunaninsa, owais Yanzu haka da nake maka magana zazzabi nake ji a jikina saboda kewar sa, ina ta kiran layi ka donka bani shi mu gaisa bana samu" dagowa yai ya saci kallon baba obie Ganin sun haWa iso yasa shi saurin canza yare zuwa larabci saboda baison Yaji me zai furta.

"Uncle, zazza6i saboda shi"?

"Hmm ba zaka gane ba, dan Allah Ka hadani da shi"

Hankalinsa adan tashe Yace"pls uncle, ka daina sanya damuwa aranka, bana jin dadi, na manta wayana agida ne shiyasa baka same ni ba, amma in sha Allah idan na koma zan yi kokarin hada ka da shi ko hankalinka Ya kwanta amma kafin nan pls ka sha magani kada zaza6in yai yawa"

"Owais babu wani magani da zai warkar da zazza6in nan kawai ka hadani da shi, saboda shi kadaine warakana" baba obie dake kallon owais ya kura masa ido ba tare da ya fahimci me suke cewa ba.

"Okey uncle, zanyi abun da kake so"
"Nagode owais, and pls abashi kulawa ta musamman, bana so ya nemi wani abu ya rasa, na yarda dakai kuma nasan zaka Iya min abun da nake so" cikin girmamawa ya amsa masa da toh uncle.

Sun Wan jima suna waya kafin sukai sallama Ya mika ma baba obie wayar, harara Ya galla masa"fadamin me kuke tattaunawa ne naji ka canza yare don kada naji ko"

Girgiza kai owais yayi"ba haka bane....." bai ?are maganar ba, sallamar Hajjaty ta katse su, ba karamin dadi owais yaji ba saboda bay da amsar da zai ba baba obie akan tuhumarsa da Yakeyi

Tuni kamshin turarenta Ya gauraye hancinansu, Hannayenta ruke da tray ta shigo garden din, Tea set ne akan tray din tare da fresh fruit, bayan ta ajiye masu fuskarta da fara'a ta gaishe sa su,a mutunce suka amsa mata
"Idan kin shiga ciki, Ki sanar da mutanan gidan su prime minister sun sauka lafiya yanzu ya kirani awaya ya fadamin nasan ba lallai suji ba"
Murmushi tayi"in sha Allah zan sanar da su" ta fada tare da mikewa ta fuce daga garden

"Kana sonta ne? Naga kana kallon ta" muryar chief ce Ta ratsa kunnansa da sauri ya kau da idonsa daga kallon bayan hajjaty ya wurga masa hararar zolaya"dan Allah ka daina wannan maganar, kawai daga na kalle ta? Ta6e baki owais yayi batare dayace komai ba, Ya dauki Tea pot Ya tsiyaya masu a cups, atare suka zauna suna sha gwanin ban sha'awa

___________________________________BossBature
'?


A6angaren Aneelerh wunin ranar da farin ciki tayi shi, babu wanda baisan da zancen bayyanar benazir ba, Harta su mami da abie sai da ta sanar da su, sunji dadi har addu'a sukai mata akan Allah ya ?ara tsareta daga sharrin wadanda sukai mata kurciya da kuma fatan Allah Yasa suma su Taj su bayyana kamar yadda benazir ta dawo.

Tun bayan da ta kammala sallar la'asar ta du?ufa tana kallon hotunan benazir da ta tura mata awaya, kamar yau tafara ganin ta, gaba daya zumudin son ganinta takeyi, akwai abubuwa da dama da take son taji daga gare ta, tana son tasan meya faru da ita bayan guduwarta? Sannan A wani hannu ta faWa? Murmushi tasaki yayin da take yin zooming fuskar benazir tayi haske jawur ta ?ara jiki ta zama big mama..

"Ya Allah kamar Yadda Ka nuna min benazir da ranta da lafiyarta Ya Allah ka nuna min su Uzair haka, har Yanzu ban fidda rai da su ba, saboda Inaji araina suna araye, Ya Allah ka tsare min mijina da dan uwansa da angel dina aduk inda suke, Ya Allah Idan sun riga mu gidan gaskiya kaji?ansu ka gafarta masu alfarmar annabi muhammd SAW......"

muryarta na rawa ta ?are maganar saboda kukan daya ciyota.....

"Aunty Aneelerh" muryar zahrace ta katse mata kukan nata, da sauri ta sanya tafin hannu ta share hawayen don batason zahra taga kukan ta, hakan zai iya sanyata damuwa, murmushi ta kakaro akan fuskarta ta dago ta kalli zahra dake shigowa.

"Na'am Sisterna"

"Auntyna Ina ?ara tayaki Murna, Aunty benazir ta bayyana saura Angel dinmu in sha Allah itama zamu ganta, Ni nasan yau dakyar zaki iya runtsawa saboda zumudin haduwa da Aunty benazir" cike da nishadi zahra tayi maganar, tare da samun wuri gefen Aneelerh ta zauna tana dubanta.

"Nagode zahra, ki cigaba da tayani addu'a Allah Ya bayyana su uzair, bana jin zan ma Iya bacci adaren yau, in sha Allah zanyi nafilfili akan su..." ta fada tana Wan yamutsa fuskarta dake a kunshe da damuwa.

"Lokacin da yayan benazir Ya fada min cewa kurciya akai mata har ta gudu tabar gida, wallahi bakomai ya fado min araina ba face 6acewar su taj, farat Waya aka neme su aka rasa, a tsakar dare, zahra baki tunanin suma kurciyar akayi ma su"? Idanunta Jawur ta jefa mata tambayar, shiru zahra tayi jimm alamar tana nazari kafin taWan jinjina kai tace"nima nayi tunanin hakan, zai iya yiwuwa, amma kada mu dogara akan hakan tunda bamu da tabbaci"
"Kin fadi gaskiya zahra"
Shiru suka danyi na wani lokaci..

"Zahra, dazu muna cikin yin magana bamu ?arasa ba abie Ya kira ni..." murmushi zahra tayi

"Ni ma sham na shafa'a...." labari ta fara bata na dinner din hateem tun daga farko har karshe ta dire mata.

Bakomai ne Ya tsaya ma Aneelerh arai ba face yarinyar da zahra ta bata labarin sun haWu har sunyi hotuna.

"Ki nuna min hoton in gani" zumbur zahra ta mike tana fadin inna lillahi na manta wayar a hannun baby junaid tun Wazu tana a wurinsa, Allah Yasa bai yi min barna ba" da sauri ta fuce daga dakin ta shiga neman baby junaid itace har dakin ummi da mamie duk baya a ciki, har falo bata gan shi ba, da sauri ta nufi dakin abie nan ma babu shi ta dawo ta shiga dakin uncle still ba junaid

Sai da ta gama shan wahalar nemansa har zata juya ta koma daki ta jiyo sautin muryarsa a kitchen shi da Ana suna magana.

"Kinga wannan itace Angel dina aunty zahra ce ta dauko min hotonta"

Adai dai lokacin zahra ta shiga kitchen din kafin Ana Ta kar6i wayar don taga hoton Angel din motsin shigowar zahra ya firgitar da junaid aruWe Ya saki wayar ta kife kan floor, wani irin bugu zuciyar zahra tayi ba ita ba hatta Ana hankalin ta, sai da Ya tashi idanunsa azare suke kallon junaid wanda tuni yasha jinin jikin shi.

Muryarsa na rawa ya furta"aunty zahra bani bane, Ana ne ta kada miki waya...' yana magana yana girgiza kansa duk yabi ya rude, Jikinta na tsuma Ta nufi wayar ta dauko ta tare da juyo da ita, gaba Waya screen dinta ya tsastsage fatsa fatsa baka Iya ganin komai.....

Kamar ta fasa ihu haka Taji tsabar bacin rai, a fadace tace"junaid hankalinka Ya kwanta ko? Ka fasa min waya! daga abun arziki na baka ita don ka kalli hotuna" ta fada tana zare masa ido fuskarta adaure tuni Ya ?ara firgita.

"Sister zahra kiyi hakuri shima bada son ransa hakan ta faru ba, kada ki tsorata shi" Ana ce ta fada cikin kwantar da murya.

Bata tsaya sauraronta ba, Ta ruko wuyan rigar junaid"don kaga ina maka wasa da dariya ko? Shiyasa har ka samu kwarin gwiwar fasa min phone, muje daki yau saika yaba ma aya zakinta Wan rainin wayau, dallah jibarka ko kunya babu" la66ansa ya fara ta6ewa alamar zaiyi kuka"kar na kuskura naga hawaye a idonka, wayar wuta zan sa maka" shiru yayi can kuma ya fara mata magiya"bazan ?ara ba aunty zahra, dan Allah kada ki buge ni, na tufa Allah" kiris Ya rage ta fashe da dariya ganin yadda Ya tsorata kamar ta ta6a bugunsa Alhalin tun da ya taso babu wanda Ya ta6a bugunsa


Janshi tayi har zuwa bedroom dinta, Ta zaro wayar charger a jikin socket, kafin ta dawo gare shi da gudu ya fuce waje yana kuka, biyo shi tayi aguje tana kwala masa kira.

Bai nufi ko'ina ba sai dakin mommynsa Yana shiga Ya faWa kan laps dinta Ya ?an?ameta yana fadin"mommy kice ma aunty zahra kada ta bugeni, bana so..." duk yabi ya dabarbace, a rude Aneelerh ke kallon bayansa Jikinsa sai kerma yakeyi"fadamin kaida wanene"?

"Aunty kibarni da babyn nan, Allah Yau sai yaji ajikinsa, Har ni zai fasa ma screen din waya? daga abun arziki na bashi aronta don ya kalli hoton Unaisah shine zai fasa min phone"

"Amma banji dadi ba junaid, meyasa zakai mata haka? Ka kyauta abun da kaima aunty zahra"? Ba tare daya dago dakansa ba yace"tayi hakuri bajan ?ara ba, mommy ki siya mata wata wayar cikin kudina da nake tarawa a wurin ki" dariya sukayi gaba dayansu jin abun da Yace.

"Aunty aneelerh yanzu ya zanyi? Ni takaicina hotunan da baki gani ba"
Mika mata hannu Aneelerh tayi muga wayar da sauri ta bata, duddubawa tayi kafin tace"zanyi magana da mahboob yakai maki ita wurin gyara, kada ki damu idan an dawo da ita sai ki nuna min hotunan" ajiyar zuciya zahra tadan sauke"shikenan amma duk da haka saina tsala masa wayar nan" ta fada tare da yunkurawa zata zane bayansa fashewa yayi da kuka yana fadin"aunty zahra kada ki bugeni, Allah Yana sama Yana kallon ki..." dariya zahra tayi"kasan da hakan shine ka fasa min wayar"? Muryarsa da shesshekar kuka Yace"ay mommy zata canza maki wata cikin kudina" tuntsirewa tayi da dariya cike da zolaya tace"ban ta6a sanin kai matsoraci bane sai yau, ay ko daga yanzu tun da na gano lagwonka, da zarar kamin rashin ji zan zane maka baya da wayar cazana" ma?e mata kafaWa yai, ba tare daya tanka mata


*HAJIYA ADAMA>?
?*

A hankali tai parking motarta, fitowa tai cikin shiga ta lace, ta yafa mayafi kan kafadarta, fuskarta manne da farin glass, Shopping bags ta Wauko a back seat na motar, kafin ta Nufi cikin gidan tana gab da zata shiga bedroom din su ta tsinkayi Muryar Uncle abdallah yana waya

"Kayi hakuri nasan ba haka mukai dakai ba, na saba alkawari amma ka dubi halin da nake aciki, lokaci Waya na rasa Wana bayan haka na rasa Wan yayana tare da yarsa, na rasa yayana da kakata kai kadaine zaka Iya taimakona a halin da nake a ciki, wlh ni zan iya maida maka adadin kudin dana kar6a a wurin ka saboda ka dawo mun da su indai suna araye na ?wammace na ?are rayuwata a talauci akan inci gaba da ganin damuwarta akan rashin haihuwa..."

Muryarsa amarairaice yayi maganar kamar zaiyiwa mutun da suke yin wayar sujjada tsabar yadda yake lalla6a shi yana yi masa magiya


Cak Ya tsaya da yin maganar ba tare daya ?arasa ta ba, sakamakon kamshin turaren hajiya adama da hancinsa ya sha?o masa, a hankali Yai rejecting call din yana kokarin dai daita nutsuwar shi

"Ba halin ki bane Yi min la6e,"! Taji Ya faWi fuskarshi ba fara'a

Bata tanka mashi ba, har sai da ta ?arasa gaban gado ta daura shopping bags din kafin ta juyo ta dube shi da alamun rudani akan fuskarta

"Gaskiya ka faWa ba halina bane, amma wannan wayar da kayi yanzu ta Wan Waure min kaina, dear wani kudi ne naji kana fadin zaka mayar adawo maka dasu idan suna araye!? Har kake fadin ka ?wammace ka ?are rayuwarka a talauci akan ganin damuwana na rashin haihuwa? Su wanene kake yin magana akan su?

da wani irin kallon tuhuma take duban shi.

Hannu Yasa yaWan shafa keyar shi, daga ganin fuskarsa babu kwanciyar Hankali, tsufansa Ya ?ara bayyana musamman fuskarsa duk tayi tamoji tamoji.

Maimakon Ya bata amsar tambayarta sai cewa yai"Har Kin kammala siyayyar?
Dame dame kika siyo mana ne" A waske Ya faWa tare da nufar Shopping bags din da ta ajiye kan gado, Ya buWe Yana dudduba kayan ciki.

Kamar sakarya Haka Ya barta a tsaye Tana kallon Ikon Allah.

"Hajiyata, Yunwa nake ji, pls Ki dafa min abunda zan dan ci"

gyaWa kai tay aranta ta ayyana koma menene zan bincika duk da ba halina bane amma da bu?atar nasan dawa kake waya akan su wa kake magana

Cire mayafin tayi, ta daura sa kan gadon, Kafin Ta juya tana fadin"Sorry dear, nabarka da Yunwa, bansan lokaci Yaja har haka ba, bari naje kitchen na shirya mana abun da zamu ci"

Bayan fitarta daga dakin ajiyar zuciya ya sauke, kamar wanda Ya ku6uta daga hannun dogarawan sarki, kwantar da kansa yai kan pillow idanunsa sun kaWa jawur bakomai Yake tariyowa ba face nasihar yayansa Malam Zaheer ha?i?a yayi babban rashin da har abada bazai ta6a samun makancinsa ba

Agogon Wakin Ya kalla kusan ?arfe Biyar Na marece, lumshe idanunsa yayi zuciyarsa nayi masa wani irin radadi daga gani yana acikin matsananciyar damuwa, Muryoyin su Uzair ne suka fara yi masa gezau acikin kan shi bazai ta6a manta ranar da suka shigo Wakinsa da zumuWin sanar dashi sun samu matayen da zasu aura.

"Kunyi shiru bakuce min komai ba"
"Taj ka fara fada masa" harara Taj Yai ma uzair ay kai yakamata ka faWa masa ni kunyar shi nake ji Allah, acikin kunne sukeyin raWar

Murmushi Uncle abdallah yai sai yake ganin kamar komai A yanzu Yake faruwa.

"Mijin mace Waya, abincin Ka Yana jiran ka" kamar daga sama ya tsinkayi muryar Hajiya adama, da sauri Ya mike Ya shiga toilet jim kadan Ya fito Ya nufi dinning din, A tsaye Ya same ta tana karasa jera masu abincin

Murmushi suka sakarma Juna"Bismillah, babyn Hajiya adama" atare suka zauna suna fuskantar Juna.

"Sannu da kokari matar mutun Waya, nagode da kulawarki agare ni, Naji dadin girkin nan" ya fada Yana kokarin tura jallop rice din daya debo a spoon"Shiyasa nake alfahari dake saboda kin Iya girki"
Murmushi tasaki Jin Yabon da yai mata"nima ina alfahari dakai," shiru suka danyi kowa yana cin abincinsa can ya ?ara dagowa ya saci kallon fuskarta karaf suka hada ido duk saiya rasa sukuninsa
"Wai lafiya naga kamar wani abu na damunka"?
Girgiza kai yai"ba wani abu, kawai ina tunanin ranar da zamu rabu" ras taji gabanta Ya fadi arude tace"Abdallah? Meya kawo maganar rabuwa? Anya kuwa kasan me Harshen Ka ya furta"?

Ya Wan tsorata da ganin Yadda Ta Waga hankalin ta.

"Kaga In baka lafi????































!
"
#
$
%
&
'
(
)
*
+
,
-
.
/
0
1
2
3
4
5
6
7
8
9
:
;
<
=
>
?
@
A
B
C
D
E
F
G
H
I
J
K
L
M
N
O
P
Q
R
S
T
U
V
W
X
Y
Z
[
\
]
^
_
`
a
b
c
d
e
f
g
h
i
j
k
l
m
n
o
p
q
r
s
t
u
v
w
x
y
z
{
|
}
~

?
ya muje nakaika asibiti bawai ka kama Yi min sambatu ba"
babu wasa akan fuskarta tayi maganar.
Cikin sanyin murya yace"kiyi hakuri hajiyata, Nima zolayarki nakeyi, maganar rabuwa da nayi kinsan akwai mutuwa ko kuma wata kaddarar ta rayuwa da zata iya sanyawa mu juyawa juna baya!

Harara ta galla masa, tuni idanunta sun ciko tab da ?walla mikewa tai da sauri tana fadin"banji dadin maganar nan ba, eh nasan mutuwa dole ce amma meye na kawo maganar rabuwa muna tsaka da cin abincin mu"? Ta jefa mashi tambayar hawaye nabin fuskarta shiru yayi sam ya rasa amsar da zai bata

"Na rasa uzair da taj, na rasa unaisah, haba kabarni inji da wannan radadin mana, akan me zaka tada min maganar rabuwa...." rai a6ace Ta bar dining din ta nufi bedroom dinta

Da sauri Ya mi?e yabi bayanta jiki na rawa saboda baisan bacin ranta, lallashin ta Ya dinga yi kamar zai mata sujjada dakyar Ya samu ya shawo kanta har ta daina fushin da shi


*=ؘ?EX-PRISONERSd'*

Wuraren ?arfe takwas na dare Gaba Wayansu sun hallara A main falo din gidan yadda kasan gidan biki ko suna, sai surutu sukeyi suna yin firar yaushe rabo abu Ya?i ?arewa kamar Yauce rana ta farko da suka fara sanin junan su, da alama dai gidan Chief Ya zama Gidan marayu kowa ka kalli fuskarsa annurin farin ciki ne, ummi tana azaune kan sofa tare da batool hannun ta ruke da waya video take daukar su ba tare da sun sani ba.

Mutun Wayace babu acikin su, Unaisah dake a daki Tana shiryawa, kamar yadda sukai da daddynta zai kaita Part dinsa dake agidan, wata hadaddiyar abaya ta sanya launin black and white ta Wauko mayafi tayi rolling nasa akanta, tabi ko'ina na jikinta ta feshe shi da turare yarinya fa ta zama budurwa wani irin gayu take ji,

Bayan ta sanya takalma, ta soma tunanin Ina ta jefa wayarta, sai yanzu ta fado


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login