Showing 213001 words to 216000 words out of 298130 words

Chapter 72 - KURKUKUN KADDARA (TAKUN KARSHE) BY BOSS BATURE.doc



Bayan kowan nan su Ya zauna kan sofa, Uncle dan Iya yace"masha Allah, kunsan ni bani gani inyi shiru, abdalla kayi kokari wannan dankareran gida haka kamar dubai"? ya fada Yana bin falon da kallo, hakan ba karamin dariya ya basu ba,
Mami tace"naso ace tuntuni mukazo ganin gida Allah bai nufa ba sai yau, gaskiya bamu kyauta ba.." hajiya adama tace"ay kun goge laifinku, tun da kuka zo yau gaba dayanku don ma babu jikalle na..."
Mami tace"Allah sarki, Ya tafi school, abunda yasa ma bamu tsaya jiran shi ba, sai marece suke dawowa.."

Fira ce ta barke tsakaninsu yadda kasan dangi Waya, daga bisani bayerabiyar dake a gidan ta shirya masu abinci akan dining, suka hallara gaba daya suka zauna suna ci, uncle dan iya sai santin abincin yakaye yi, ita dai anila hankalinta kamar ba akwance yake ba, ta kasa cin abincin, saboda wani irin faduwar gaba da take ji..
"Anila meke damunki ne? Naga kamar bakison cin abincin" cikin kulawa hajiya adama tay maganar, cikin sanyin jiki Anila tayi murmushi tace"babu komai mommy, abincin ne yayi min dadi shiyasa nake santin shi" dariya hajiya adama tay"karki damu idan ma baki koshi ba zansa akara maki ne nafi so ku ci ku koshi dama saboda ku akai girkin dayawa" murmushi kowan nan su yayi, zahra ba baka sai kunne Hankalin ta na akan plate din fatan doyan da take ci......

_______________________________
'?

A hankali motar dr shureim ta kunno kai cikin entrance gate din asibitin, bayan yayi parking din motar, Ya dan juya ya kalli zeenatu data langwa6e kanta kan shoulder dinshi, kwata kwata batasan inda suka zo ba, ta nutsu tana shakar kamshi turaren shi ta wani lumshe idanunta...
Cikin sanyin murya ya furta"zeenatu mun ?araso" buWe idanunta tayi tare da gyara zamanta, kwata kwata bata lura da inda suka zo ba, kusan atare suka fito daga motar, kamar ance ta kalli saman ginin karaf idanunta suka sauka akan sunan asibitin da aka rubuta da manyan haruffa masu daukar ido, wani irin bugu kirjinta yayi da sauri ta dafe saitin zuciyarta,
"Yaya shureim! Ina ne nan? Kamar asibiti nake gani? Dama nan zaka kawo ni"? Cikin rawar murya tay maganar tana ja da baya
"Zeenat ki kwantar da hankalin ki, kamar yadda kika gani asibiti ne, wurin auntynki benazir na kawo ki, kullum saita tamabayi kina ina meyasa baki zuwa dubata...." bai ?are maganarba, zeenatu ta juya a firgice ta dam?i murfin motarsu ta kutsa kai zata koma ciki da sauri Ya cafki hannunta ya fiddo da ita yana fadin meya haka zeenatu? Meke damunki ne? Benazir din ke bakison gani" wani irin kakarwa jikinta ya farayi ta Waura hannu biyu akai ta fasa wata iri gigitacciyar ?ara wadda tajanyo hankulan visitors din dake zarya a harabar asibitin, gaba daya hankalin mutane ya dawo kansu wasu har sun fara tambayar meya faru? wasu kuwa sunyi tunanin wani mugun abun akai mata...."
Cikin shesshekan kuka da murya mai ?araji take fadi "bazan shiga ba Yaya shureim ka maidani gida, wayyo Allahna na shiga uku, na bani ya shureim...." tsantsar tashin hankali ne akan fuskarshi gaba daya tabi ta rikitashi, ga jama'a da suka tasa shi gaba suna tambayar me akai mata...bai san sa'adda ya janyota kan kirjinshi ya rungumeta sosai kamar zai maida ita cikinshi, idanunshi sun kaWa jawur yai saurin kai la66anshi saitin kunnanta, A hankali ya fara zuba mata kira'ar alqur'ni wohoho zokaga idanu mutane sun nutsu suna ba idonsu abinci, wasu sai santin karatun shi sukeyi, yayin da wasu kuma suka kokwanton watakil aljanu gare ta, wani irin sanyine ya ratsa zuciyar zeenatu, gaba Waya ta narke mashi tana faman sauke ajiyar zuciya, tuni ta nemi kukan da takeyi ta rasa shi, tayi shiru sai ?ara nutsa kanta cikin kirjinshi takeyi, mutanan dake kallonsu sunyi masu ?awanya hada masu daukarsu hotuna da video hakan yasa shi kare fuskarshi ya ?ara ?an?ame zeenatun shi, ahaka yajata suka nufi cikin asibitin don bayajin zai iya juyawa da ita gida.=ؔ?

Duk ta kankame shi, mutane sai kallonsu sukeyi, nurses har tambayar shi suke yi patient ce? Yace masu a'a lafiyarta lou,
hajiya layla dake tsaye tana waya bakin kofar privet room juyowar da zatayi keda wuya ta hango su, arude take binsu da kallon har suka karaso inda take
"Shureim wacece wannan ka rungumo haka"? Ta fada tana kallonta sam bata gane wacece ba saboda ya rufe fuskarta.
"Mami zeenatu ce, tazo duba jikin benazir ne"
A ruWe tace"meke damuntane? Ke zeenatu ya akai? Ko bakison zuwane aka matsa maki? Muryarta kasa kasa ta furta"bana jin dadin jikina..."
"Haba shureim kasan bata da lafiya ka taso ta? Ko likita kukazo gani ne"?
"A'a mami, lafiyarta qalou, zanyi maki bayanin abunda ke damun ta, mu shiga daga ciki....."

___________________________________
'?

A lokacin Unaisah tana zaune kan chair din gaban gadon Benazir, hannun ta ruke da glass na ruwa, magani take bata in ta sanya abaki saita bata ruwan ta sha, ta maida kanta kamar ?aramar yarinya agaban unaisah, har yanzu bata daina binta da kallon kurullan ba...
"Mommy ki maida hankali kan ruwan da kike sha, kada ki shake" murmushi taskar mata"bana gajiya da kallon ki ne, Kin sace min zuciyata" da mamaki unaisah take kallonta, kalaman matar suna sanyata kokwanton kamar ta dawo hayyacin ta
Shigowarsu dr shureim dakinne Yaja hankulansu ga kallon kofar,
"Benazir yau Allah yayi, zeenatu tazo dubaki, sai dai kamar bata jin dadin jikin ta,..." da wani irin yanayi benazir ke kallon zeenatu wadda ta 6oye fuskarta jikin shureim...cikin sanyin murya ta furta"Zeenatu...."! shiru bata amsa mata ba, Unaisah dai ta zuba ido tana kallon matashiyar dake kankame da shurem, jikinta sai kerma yakeyi kuma ta?i dago da fuskarta...
"Zeenatu bakiga auntyn naki ba"? In a low voice ta furta"bana son ganinta" waro ido waje benazir tayi sam ta manta da pretending din da takeyi saboda ruWewar da tayi, lamarin ya daure masu kai, arude hajiya layla ta kalli shureim suka hada ido, unaisah dake kallon su abun ya bata mamaki aranta ta ayyana kowacece wannan take ta wani boye fuskarta? Yanzu haka bawani kyan kirki gareta ba, in banda wulakanci hada wani cewa bata son ganin mamanta, yanzu haka yar kishiya ce... Acikin zuciyarta take wannan sambatu
Banezir kuwa jikinta yayi sanyi lakwas zuciyarta ta karaya da jin kalmar da zeenatu ta furta abun Ya girgizata sam takasa magana sai motsa la66anta take
"Pls kada hakan Ya dame ku, bayin kanta bane, Ina tunanin iska ne suka shiga jikin ta..." calmly ya zayyana masu komai dangane da abun da ya faru ranar farko da ya koma gida har yayi mata maganar benazir ta share shi, har zuwa ga abunda ya faru yau, mami ta tafa hannu tana ambaton "inna lillahi wa'inna ilaihirraji'in zeenatu Allah ya baki lafiya, Allah ya yaye maki abunda ke damunki, baiwar Allah ashe shiyasa tadaina zuwa asibitin, sannu zeenatu ta faWa tana le?en fuskarta, banza tayi da ita, benazir dai takasa magana kallon su kawai takeyi, ita dai unaisah ta baza kunne tana sauraron su bakomai ya bata haushi ba face Yarinyar da take ta boye fuska.

"Yaya shureim ka maidani gida! Kada daddy ya dawo ya iske bana nan!..."
Cikin kwantar da murya yace"ko ya dawo ba abunda zaiyi maki, ai ni na fito dake, da anjima zan maidaki, mu karasa ciki ki zauna..." yai maganar yana kokarin janyota cikin dakin, aikuwa ta turje tana yan fizge fuzge Hankali atashe mami tace"shureim abun da ban tsorofa kamar ba zeenatu ba, pls ka maida ita gida, tunda ta nuna bata son zama nan din..
Shi dai baison Ya maida ta gida saboda bai shirya komawa ba
"Mami babu kowa gidan, ita da kanta ta nuna batason zama ita kadai shiyasa na taho da ita..." ya fada fuskarshi ayamutse...
Saukowa Benazir tayi daga kan gadon ta tsaya agabansu cikin karyayyar murya ta furta"zeenatu! dagaske bakison gani na"? da wata irin tsiwa ta furta"Bana son ganin ki, ki daina yi min magana...." kafin ta ?are maganar, Benazir takai hannu ta dam?i shoulder dinta dakyar ta rabata daga jikin dr shureim ta jijjigata da karfi har mayafin daya rufe fuskarta ya zame kan kafaWarta....

Kamar daga sama sukaji Sautin fashewar glass kusan atare suka kai dubansu ga Unaisah wadda ta mi?e a sukwane tana faman zazzare idanun ta, tsantsar tashin hankali da rudani ne akan fuskarta
"Azeezaty meya faru...." hada baki sukayi wurin tambayar ta, la66anta sai kerma sukeyi gaba Waya ta rikice ta kasa magana, gabanta na faduwa ta nufi zeenatu wadda ke ta kerma tana zare blue eyes dinta akan fuskar Unaisah

Wani irin gumi ne ya wanke fuskar Angel duk da sanyin A.c din dake a dakin, ta sanya tafukanta ta murza idanunta saboda tana kokwanton ko dai gizau takeyi mata ne? In ba haka ba tayaya mutumin daya mutu zai dawo araye? Ta kasa yarda da abunda idanunta ke nuna mata, kusan sau uku tana murza su don su dawo dai dai, Hankulan su dr shureim na akanta, sun rasa gane meke damun ta! Ko dai tasan zeenatu ne? Meyasa ta razana da ganin zeenatu harta fasa water glass din hannun ta! Dukansu kansu ya daure

Agaban zeenatu ta tsaya suka fuskanci juna, ido cikin ido, dafe kai unaisah tayi da hannayenta biyu saboda wani irin sara mata da yayi, zuciyarta ta fara dakan uku uku, Muryarta adabarbace ta furta*"UNAIZAW'S'*


*Daga Alkamin Boss Bature=?%?
'?*


*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440*ASSALAMU ALAIKUM
Mata masu abun dadi
*Zuzeam empire* takawo muku babbar gara basa
Duka akan 5500 ki daure ki mallaki naki kar dama ta wuceki Garabasa gara basa =????=????=????=??<؁?=؃? ?

Wa.me/+2348144015291 For more information say hi =?K? Ina uwar gida da Amaren bayan sallah zuzeam empire tashirya tsaff dominku=؃?=؃?=؃? muna gyaran ciki muna saida kayan gyaran jiki dilka sabulu dadai sauransu

*DAHUWAR KAZA*

Kin taba cin *DAHUWAR KAZA 5in1* wato *Ni ima, Matsi, Chikowa, MAllaka, da Karin soyayya*
Duk me buqata TAYIMUN magana ta Pvt *Akwai kyauta <؁? mai tsoka ga mutun 5 da suka fara siya*

*INA MASU JEGO DA AMARE*
Karku bari wannan dama ta wuceku
*08144015291*
Zuzeam empire

ASSALAMU ALAIKUM Mata ga wani sirri mai abun mamaki amma mata aji tsoron Allah kada ayi amfani da wannan dama kijuya mai gidanki yanda bai kamata ba amfaninshi shine a tafin kafar ki kawai zaki shafa lokacin kwanciya zakiga daukar hankali wurin mai gida amman don Allah karki juyashi yanda bai kamataba amana ce na baki 08144015291. 1000 kacal =?L?
Munada kaya kala kala wanda bazasu faduba kedai kidau number kimin magana ngd

Infection set
Sabon budurci set
Niima set
Basir set
Matsi mallaka
Amarya set
Uwar g1da set
Mai jego set

Dadai sauransu


*DAGA AL?ALAMIN BOSS BATURE
'?=؋?
'=?%?*

_________________________________




Agaban Zeenatu ta tsaya suka fuskanci juna, ido cikin ido, dafe kai Unaisah ta yi da hannayenta biyu saboda wani irin sara matan da yayi, zuciyarta ta fara dakan uku uku, Muryarta adabarbace ta furta"UNAIZAW'S'
Arude Hajiya Layla ta maimaita sunan Unaisah
Dr Shureim yace"wacece Unaizah"? Cike da fargaba Unaisah ta nuna Zeenatu da yatsan ta"ita ce, Yar uwarmu Unaizah...." gaba daya ta rikita lissafin ?wa?walwarsu, Zeenatu da ta gama ruWewa idanunta Azazzare ta furta"bani bace! Ni bansan ki ba, ban ta6a ganin ki ba. ..." Sautin muryar Zeenatu ya ?ara rikirkita ta, runtse idanunta tayi brain Winta ta fara tariyo mata muryar Unaizah idan tana magana! Tabbas wannan Unaiza ce ta dawo...."

fashewa tayi da kuka ta cakumi hannayen zeenatu"wallahi ke ce, Unaizah din mu, yar uwarmu wadda ta rasu tayaya akai kika rayu bayan kin mutu ..."? Tashin hankalin da ba'a saka mashi rana.

Al'amarin yayi matu?ar Waure masu kai, Hankali atashe Benazir ta furta"babyna wacece Unaiza? Shiru Angel ta yi hawaye na sintiri kan fuskarta...
Dr shureim yace"kodai tayi maki kama da yar uwarki ne? Ita wannan sunan ta Zeenatu ba Unaizah ba, bayan haka naji kin ambaci yar uwarku wadda ta mutu in banda abunki wanda ya mutu ay baya dawowa watakil sunyi maki kamane...." kalaman dr Shureim Sunyi tasiri a cikin zuciyarta, amma taya haka zai yiwu? Komai nasu iri Waya kamar mutun Waya! farar fatarsu, da launin idanunsu blue, hatta blonde hair dinsu iri Waya, bugu da ?ari surar jikin su, tun daga kan sirantakar su har big boobs din iri Waya.

Gaba Waya ta jefa kanta aruWani, su Benazir sun kafe ta ido suna kallonta,
Kokwanto ta fara yi kodai gizau fuskar Unaizah takeyi mata akan fuskar yarinyar? Nan take tayi believing da abun da zuciyar ta ke fada mata saboda tasan ba mai yiwuwa bane, wanda ya mutu ya dawo, abu Wayane zaisa ta yarda da abun da idanunta suka gane mata, wanda bakomai bane face ?an uwanta suga yarinyar nan! muddin suka ruWe suka ambaci sunan ta da unaizah to anan ne zata gasgata abunda idanunta suka gane mata...."

Lokaci Waya ta sauke ajiyar zuciya, sam takasa janye idanunta daga kallon fuskar Zeenatu, A hankali ta kau da idonta tare da kallon su shureim wata irin kunyarsu ce ta kama ta, muryarta na rawa ta furta"dan Allah, ku yi hakuri, na ruWe ne, wallahi tayi min kama da wata dana sani, amma ita tama mutu tun da jimawa...." nannauyar ajiyar zuciya suka sauke, har suna hada baki wurin furta"Allah yaji?anta da rahama.."

Yawu Unaisah ta haWiya mai zafi a makoshin ta, kafin ta sake kallon Zeenatu dake kallon ta"sister kiyi hakuri dan Allah, na tada maki hankalin ki, kuskuren fahimtane...." murmushi zeenatu ta sakar mata, su kansu saida sukayi mamakin murmushin da tayi ma Unaisah
Cikin sanyin murya ta ce"Kada ki damu, babu komai...." mi?a mata hannu Angel tayi don su gaisa, da sauri zeenatu ta zira hannunta acikin nata sukayi musabaha, yau ne karo na farko da suka fara sanin junansu amma ga dukkan alamu sun kamu da kaunar juna, tabbas da ace lokacin da aka kawo masu Unaiza ta fada mata twins ne su wlh da ba abunda zai hana ta dafe alkur'ani tayi rantsuwar wannan Yarinyar Twin sister din Unaizah ce!! Ta dai bar abun aranta har zuwa lokacin da Allah zaisa ta hadu da su Batool sune zasu kara tabbatar mata da abunda take zargi na kamannin ZEENATU da UNAIZAH.........=ؔ?.

Kafin wani ya ?ara furta kalma a cikin su, wayar shureim ta fara ringing, a hanzarce ya curo wayar daga aljihu yai picking call Win

"Shureim! Ka dawo da zeenatu gida, Ina jiran ka" rass yaji gaban shi ya faWi, tun daga kan yanayin muryar Alhaji musa ya fahimci ba lafiya, ko jiran amsar shi baiyi ba ya katse kiran.

"Wanene Ya kira"? Hajiya layla ta fada tana kallon fuskarshi

"Uncle ne, Yace in maida zeenatu gida"

Ta6e baki hajiya layla tayi ba tare da tace komai ba

Har lokacin Zeenatu bata cire hannun ta daga na Unaisah ba, sun ?urawa juna ido kowa da abun da yake sa?awa aranshi......

"Muje zeenatu" muryarshi ce ta katse shirun nasu, sallama yayi masu hajiya layla, ya ru?o hannun zeenatu suka tafi, Unaisah bata daina kallon su ba, har le?en?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? su tayi abakin kofar dakin itama zeenatun suna tafiya tana waiwayon ta hada Waga mata hannu tayi mata bye bye...=ؔ?

_________________________________
'?

*CHIEF OWAIS=?%?
'*

Slowly dankareriyar motar shi ta kunno kai cikin villa dinsa, yana daga zaune ya hakimce a backseat, su biyu ne a mazaunin baya big guy dake a gefen sa, kowan nansu kaki ne a jikin shi, da alama sun kwaso gajiyar aiki duba da yadda kowan nan su ya lumshe idanun shi kamar masu jin bacci.. .. bayan sun karasa parking space agent din dake driving nasu yayi parking

A hanzarce Wani agent daga cikin jami'an dake kai komo a harabar ya karaso ya buWe masu murfin motar.

"Sir, mu shiga daga ciki" ya faWa yana le?en fuskar shi yayi shiru, soft lips dinsa sun bushe sun Wan ciza kalarsu pink kamar bazai motsa ba, big guy yayi tsammanin bacci yakeyi hakan yasa shi kai hannu ya dafa shoulder din shi, da wata irin kasala ya buWe reddish eye dinsa tare da kallon big guy

"Mun ?araso gida, nayi tsammanin bacci kake yi.." yamutsa fuskar shi yayi, da zolaya big guy yace"ka bani dama in goya ka mana.." harara chief ya jefa mashi tare da zura kafar shi ya fito daga motar, da sauri jami'an dake a wurin suka buga kafa tare da sarah mashi, ko ta kansu baibi ba ya nufi cikin gidan, big guy yana abiye da bayan shi....

Har ya kusa shiga main falo, wayarsa ta fara ringing, gajiya ta hana ya dauki wayar, kaitsaye ya nufi upstairs Yana shiga daki, Ya rage kayan jikin shi ya fada toilet....
Ganin ya shiga ciki yasa big guy yin kwana ya fita daga dakin..
After some mins, ya fito daga wanka waist dinsa a Waure da towel ya nufi walk-in closet dinsa ya shirya kanshi cikin hanley shirt tare da black trouser na shan iska..


Bakomai yake son gani ba face Danish, Yau da tunanin shi ya wuni a office, Yaron ne ya tsaya mashi arai, baisan meyasa yake jin shi sosai acikin ranshi....


Yana ?o?arin zama gefen gadonsa, phone dinsa ta fara ringing sai time din ya tuna da kiran da akayi mashi dazu

?aukar wayar yayi daga kan pillow Ya duba sunan mai kiran nashi
Yayi mamakin ganin kiran ta! saboda basu cika yin waya ba...daidaita nutsuwarshi yayi kafin yai picking ya kara wayar a kunne tare da yi mata sallama ya gaishe da ita cikin girmamawa.

On the other hand muryar sheikha mujeedat ta amsa mashi sallamar shi cike da dattako ta fara yi mashi magana cikin harshen turanci tana hadawa da arabi

"My in-law, did you see the message I


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login