Showing 216001 words to 219000 words out of 298130 words

Chapter 73 - KURKUKUN KADDARA (TAKUN KARSHE) BY BOSS BATURE.doc

sent you on WhatsApp"!

"I just got back from work, ban kaiga dubawa ba..."

"Okay, ka duba yanzu, ina so zamuyi magana dakai" amsa mata yai da toh ta katse kiran..

Zama yayi gefen gadon kafin ya shiga whatsapp dinsa, kaitsaye idanunsa suka sauka akan sakon gimbiya mujeedat, calmly ya fara karanta abun da ta turo ma shi

_*DNA Paternity Test Report* _

A tsanake yake bin bayanan da result din ya kunsa har yakai karshen sakamakon

_"DNA Profile Match: 99.99%. Paternity Index: 100,000,000:1 (extremely high probability). Conclusion: The DNA analysis conclusively confirms that Danish is the biological son of Sheikha Mujeedat bin khalid AlMaktoum._

Lokaci Waya chief ya zabura ya mi?e jikinshi na tsuma, tsantsar ruWani da al'ajabine akan fuskarshi, A kalla ya maimaita karanta sakon yafi sau ashirin kamar irin bai fahimci me aka rubuta ba saboda tsabar kiWima da mamaki! Tayaya haka zai yiwu? wai ma Wani Danish din ne? Na wurin shi da yake ru?o ko wani ne daban"?

Gaba Waya ya ruWe tayaya ma akai gimbiya mujeedat tayi DNA test din? A yaushe? kuma daga ganin result din original ne daga babban asibitin toronto"

Wahallan Yawu ya hadiya da sauri yai scrolling ya shiga contact ya buga mata call yana faman fitar da numfashi mai Wumi.

Kiran na shiga Gimbiya Mujeedat ta Waga..." la66ansa na kerma ya furta"mommy, ki yi min bayani, ki fahimtar dani! Na gaza yarda da abun da nagani I can't believe! I was confused, is this DNA test true? ya fada hankali atashe.

Sanyayyar muryar gimbiya Mujeedat ce ta ratsa kunnanshi

"Owais, kamar yarda hankalinka Ya tashi ka shiga rudani, nima haka na shiga, zanma iya cewa fiye da yadda ka shiga! Owais tun arana ta farko danayi tozali da yaron nan naji a jikina Wana ne! Jini na ne shi, duk da bani da tabbaci But what strengthened my suspicions is the unconditional love Hateem has for him"

Shiru ta Wanyi kafin taci gaba da cewa" na san zakayi mamakin tayaya akai nayi gwajin!" bayani ta fara kora mashi dangane da yadda ta yanki gashin danish batare da sanin shi ba.

jikin chief yayi mugin yin sanyi kamar wanda aka zarewa laka, gaba Waya yasha jinin jikin shi, ya girgiza bilhakki..."

"My trusted doctor conducted the test. When the results came out, I was shocked, wlh har zazzabi nayi owais..." muryarta na rawa ta ?are maganar cikin rauni na murya

"Owais ka fadamin me kake tunani akan yaron? Kaima kana zargin jininmu ne"?

Numfasawa chief owais yayi wata juwace ta nemi daukar shi da sauri ya koma ya zauna, yana faman jan numfashi sam ya kasa bata amsar tambayar ta, abunne ya rikirkita shi.

"Owais naji kayi shiru bakace komai ba! Ni raina yana bani Omair dinmune, jinjirin dana haifa ba araye ba, amma in shine tayaya zamu iya gano gaskiyar lamarin? ni dama tun time din dana haifi yaron hankalina baikwanta da yadda aka hana mu ganin koda gawarsa ba, na dade da radadin abun a zuciya ta..."dakyar chief ya samu kwarin gwiwar furta"kin fadama uncle sakamakon DNA test din"?

"Ban fada masa ba, saboda bana so in daga mashi hankalin.." jinjina kanshi yai kafin ya furta"bazan boye maki ba, tunaninmu yazo Waya, nima ina zargin babyn da kika haifa ne! Amma har yanzu bamu da ?wa??waran hujjar da zamu tabbatar da hasashenmu in gaskiyane! Dole saimun fara yin bincike mun gano tayaya akai jinjirin daya mutu ya rayu! Sannan su wanene suka sace shi daga asibitin da abun ya faruS'

"yanzu muna da shaida Waya a hannu, ki ajiye result din dakyau, kibar komai a hannuna nayi maki alkawarin zan binciko komai, in har yaron nan Wankune zai dawo gare ku in sha Allah, sannan pls mommy kada ki bari uncle yaga result din nan..." ta amsa mashi da toh, kwantar mata da hankali yaci gaba da yi, daga bisani su ka yi sallama.

Shiru yayi jim yana tunani! idan har ya tabbata dan uncle dinsa ne to wanene ya sadaukar da shi? Yana jin fargaban ace hateem dinne ko wani daga cikin uncles dinsa tun da sadaukarwar na jininka ne kadai zai iya bada kai. W'

Yana jin fargaban ranar da zai gano koma wanene! A sukwane ya fito ya nufi bedroom din Danish saboda ya yi maraicin ganin shi ya ?ara jin ?aunar yaron a zuciyar shi fiye da kullum

Baijima da fita ba, sai ga big guy ya hauro up hannun shi ruke da wooden tray na kayan abinci, knocking kofar yayi jin shiru ba'a bude ba yasa shi tunanin koya yi bacci ne ko yana toilet
Yanke shawarar shiga ciki yayi, ya danna code din kofar ta bude kafin ya shiga da kayan abincin.

A bakin door room din Danish ya tsaya tare dakai hannu yayi knocking almost 3 times ba'a buWe mashi ba, baya jin zai iya juyawa batare daya sanya shi a cikin idanun shi ba.

Tura kofar yayi tare da sakai ya shiga da sallama, yana zura ?afar shi ya fara cin karo da papers din da ya kacaccala ya kekketasu akan floor, murmushi chief yayi aranshi ya furta hmm dakin Wan koyo.

Ya yi ma bedroom din nashi kaca kaca, kamar ance ya Wago da idon shi karaf Ya hango zanen da yayi akan white board din da yake koya mashi rubutu da shi, wata halitta ya zana kamar jagwalgwalo daya ?ura ido saiya gane maca ce, yar diyar roba da marker yayi zanan, kafafuwanta kamar na cokula, ga gashin kanta a haukace ko wacece wannan?

Murmushin gefen fuska chief ya saki kafin ya wurga eye balls dinsa kan bed dinsa a kwance ya hango shi, sai sharar bacci yakeyi kamar matacce, yar singlet ce a jikin shi fara kyal, tare da short ja, yayi wani fresh dashi.

Gaba Waya ya barbaza papers din da yayi amfani da su, ga notebooks dinsa daya watsar, hannun shi yana aruke da pensil da alama yana cikin yin practicing na rubutu bacci yayi awon gaba da shi.

Cikin takun sanWa chief ya ?asa daga gaban gadon ya zauna tare da sunkuyar da kanshi saitin fuskar danish ya ?ura mashi ido yana kallon shi, wani irin bugu zuciyarshi ta fara doka mashi, kamannin shi sun 6aci da yaron hatta dogon hancin su, da launun hair dinsu, da shape din bakinsu iri Waya sak, uwa uba reddish eyes dinsu masu kyan gaske da jan hankali, yadda yake yin baccin cikin kwanciyar hankali ba karamin kayatar da chief yayi ba, har baisan sa'dda ya manna masa peck a forehead dinsa, ya daura zira ziran yatsunsa saman tattausar farar fatar fuskar Danish mai kama data jinjiri saboda hasken ta da laushinta ya shafa ta a hankali..

In a low voice ya furta"I hope you will be my cousin, I will be proud of you. I will give you all my care. If it is confirmed that you are my blood cousin, I myself cannot describe the joy I will feel. I will hug you tightly, I will shed my tears on you, kuma nayi maka alkawarin zan ?watar maka duk wani hakkinka na rayuwa da aka tauye maka! WaWanda sukayi silar sadaukar dakai zansa suyi danasani mara amfani....." cak ya tsaya da magana ganin ya fara motsi, da sauri chief ya dago da kanshi batare daya dauke ido daga kallon shi ba, gyara kwanciyar shi yayi.

Ajiyar zuciya ya dan sauke ganin bai farka ba, hakanan yai sha'awar karanta rubutun da yayi a jikin papers din daya watsar kan mattress, paper din farko jagwalgwalone yayi bai iya gane komai ba, paper na biyune yaga ya rubuta I miss you, my Angel. Come back home..."

yayi mamakin handwritting dinshi cos yayi kokari ba kadan ba, har kokwanto yayi anya shi ya rubuta? Wayar paper din ya dauko ya duba rubutun dake akai.

"I'm waiting for you, chief. Come back home..." murmushi chief yayi har dimple dinsa ya lotsa...
Next paper daya duba sunan Daddy hateem ne ya rubuta duk da akwai kuskure amma yayi kokari..." bayan ya kammala reading dinsu, ya ajiye mashi abun shi gefe daya, har zai mike yaji ya dam?i hannun shi, ya Wan furgita saboda bai tsammaci zai farka ba..a hankali ya buWe idanunsa sunyi ja dakyar yake ware su akan fuskar chief, da wata irin kasala ya furta"You're back." jinjina mashi kai yai alamar eh..

Mi?ewa zaune yayi tare da yin mi?a chief ya bi shi da kallo, ya jinjinama girman jikin shi, ba karamin kato bane ko'ina na jikin shi a murWe yake irin na majiya karfi masu jini ajika.

"Fadamin kayi missing dina"? Daga mashi gira yai"nayi missing dinka sosai, tun dazu nake jiranka don muyi karatu baka dawo ba..." cheif yace"ai naga ka fara" ya fada yana nuna zanen dake akan white board din.

sunkuyar dakai danish yayi hadi da yin murmushi.

Da zolaya yace"abunda na koya maka kenen"! Girgiza kai yay "a'a!
"Wacece ka zana? Na kasa gane fuskar, Jemaima ce ko Azeeza"? Dagangan ya kira sunan su don ya bugi cikin shi...
Kasa ?asa da murya ya furta"Angel" dariya ce ta kubce ma chief, danish ya kura mashi ido yana kallon shi.

"Haba my bro, Unaisah ce wannan Aljanar? Abu kamar agidan mahaukata, Ai ni dana ganta ?arama nayi zaton jamaimah ne ." sunnar dakai kasa yayi batare dayace uffan ba...
nan take chief ya fahimci halin damuwar da yake aciki harya Wan rame ta wurin kwarin idanun shi sunyi ja.

"Fadamin meke damunka.."?
Shiru yayi jim kamar mai tunanin wani abu
"Ina so Unaisah ta dawo gida, I miss her, I want to see her. She forgets me, Bata nema na..." kasa ?arasa maganar yayi da sauri ya cusa kanshi cikin pillow.

wani irin tausayin shine ya kama owais cikin sanyin murya ya furta"am sorry danish, unaisah zata dawo gobe in sha Allah, kuma ka daina tunanin ta manta dakai, kana aranta...." muryarshi da rauni ya furta"har yanzu fushi take dani, bata sona"

har yau chief baisan soyayya ce atsakaninsu ba, yafi tunanin shakuwace mai karfi shiyasa ko kusa abun bai damun shi.

"Ina wayarka"?

"Tana akan mirror," ya faWa batare daya dago da kan shi ba
Mi?ewa chief yai ya nufi mirror din ya dauko wayar, ya danna power ta kawo haske
Wayarsa ya curo yayi copying contact din Unaisah ya saka awayar Danish...

Kiran sunan shi yayi, dakyar ya amsa mashi na'am
Na sanya maka contact din angel a phone inka, zaka iya kiranta ku gaisa, ko ka tura mata text message kamar yadda na koya maka..." dago da kanshi yayi wani irin dadine ya lullu6e shi, mika mashi wayar chief yayi yatsun hannun shi na kerma tsabar zumudi ya karba saida ya shiga wurin rubuta sakon ya kasa tabuka komai.

Mi?a ma chief wayar yayi"ka rubuta min..." girgiza kai chief yayi"kai ya kamata ka rubuta...yamutsa fuska yayi kafin ya fara kokarin rubuta mata sakon saida ya kammala chief ya duba abunda ya rubuta dakyar ya gane meya ke nufi a sakon ya hade kalmomin babu space babu ?a'idojin rubutu irin dai na yan koyo,
"Kayi kokari" ya faWa tare da mika mashi phone"ka danna send" ya amsa mashi da toh...
"Zan shiga gym ko zaka bini? Daga mashi kai yai akamar eh, da sauri ya mike chief ya ruko hannun shi kamar wa da kani suka fita a tare.=؞?

_________________________________
'?

Meya faru bayan komar dr shureim gida?

Tsaye yake gaban sofa ya goya hannayen shi kan kirjinshi, fuskar shi babu annuri idanunshi sun kaWa jawur tsabar 6acin rai da fusata, abun da ya faru bayan fitar shureim da zeenatu kwatsam Motar su Alhaji musa ta kunno kai cikin gidan tunkafin bodyguard din dake driving dinsu yayi parking saiga kira daga likitan shi dr Mark, bayan yayi picking ko sallama baiyi ba muryar mark ta katse shi"yalla6ai! Da sanin ka dr shureim Ya fita da zeenatu...." lokaci Waya yanayin fuskar shi ya canza zuwa tsantsar bacin rai

Saida ya mula yasha iska kafin ya furta"bada sani na ba"!

Dr mark yace"yalla6ai, dole fa sai kayi takatsantsan idan ba haka ba zamu iya samun gagarumar matsala, saboda mutane sun Wauki hotunan dr shureim tare da zeenatu rungume da juna, a bainar jama'a sai yaWa shi sukeyi a social media..." a kiWime Alhaji musa ya furta"what! Are you sure"?

"?warai kuwa yalla6ai, ka duba whatsapp dinka, zan tura maka hotunan ka gani da idon ka..." katse kiran yayi, wani irin gumine Ya wanke fuskarshi saboda bacin rai! Har shi zai sanya doka agidan shi a karya"?

Alhaji ubaid dake zaune gefen shi Ya lura da yanayin shi
"Musa lafiya? Meya faru ne"? Ko kallo Alhaji ubaid bai ishe shi ba, Ya buWe murfin motar Ya fito tamkar mayunwacin zaki Ya nufi gate security officers, suna ganinshi suka mi?e suna jiran tsammani
Wata irin tsawa ya daka masu da ta gigita dodon kunnuwansu, yana huci ya furta"da iznin ubanwa kuka bari dr shureim Ya fita da zeenatu huh!? Kafin in fita basaida na gargadeku akan kada ku kuskura ku bari ko kofar falo ta le?o ko ba....." ya Wage sai masifa yake zazzaga masu ta inda yake shiga batanan yake fita ba.

Alhaji ubaid Har ya fara kokarin lallashin shi aikuwa Ya daka mashi tsawa kamar Wan cikin shi Ya nuna shi da yatsa yace"karka kuskura kasa baki, magana nake akan ?ata, ka wuce ka shiga ciki" jikin Alhaji ubaid na 6ari kamar mazari Ya juya ya nufi cikin gidan abisa umarnin Alhaji musa wato ?anin shi >?#?


Hankulan gate officers din ba karamin tashi yayi ba, tsantsar tashin hankali da firgici ne akan fuskokinsu.

Dakyar wani daga cikin su ya samu kwarin gwiwar fadin"yalla6ai har tambayar shi mukayi da iznin wa zai fita da ita yace mana da izninka, munyi kokarin tuntu6ar layinka amma baka Waga ba...." bai ?are maganar ba sakamakon zazzafan marin da Alhaji musa ya wanka mashi wlh daga tsaye duk girman jikin mutumin saida Ya dur?ushe kan gwiwowinsa.

Kallon sauran gate officers din yayi waWanda tuni sun sha jinin jikin su, babban tashin hankalinsu taya zasu fahimtar da shi cewa su ba laifin su bane? Alhaji musa bala'e ne, wani irin bauWaWWan mutunne, bahago mai wuyar sha'ani.

Wani mai rabon shan duka daga cikin su ne Yayi shahada wurin furta"yalla6ai, har kiran hajiya sarah mukayi awaya muka tambayeta da izininta zasu fita tace mana eh, ta kuma ce kaima da sanin ka...." bai kare maganar ba, Alhaji musa ya daddage Ya kwashe shi da mari da tafukan hannayenshi biyu nan take bakin officer din ya fashe jini ya fara bulbulowa.
kallon sauran yayi yana jiran jin bayani daga gare su, sai tsuma suke yi suna ja da baya da alama sun razana....
"Ban ta6a sanin ku dakikai bane sai yau! Wallahi ku kuka da kanku! ....." zubewa sukayi akan gwiwowinsu suka dinga rokonshi sunayi mashi magiya don ya yafe masu, ko ta kansu bai bi ba, Ya nufi cikin gidan cikin takun nan nashi na izza,

bawan Allah Alhaji ubaid Ashe yana la6e ta window yana leken abunda Alhaji musa yakeyi ma masu gadin gidan, Yaji haushi ranshi Ya 6aci sai.......=ؔ?

Adaidai lokacin da motar dr shureim Ta kunno kai sai ga motar hajiya sarah yau ta dawo da wuri, atare suka nufi parking space bayan sunyi parking, kusan atare shureim da zeenatu suka fito, kafin hajiya sarah ta fito da sauri zeenatu taje ta rungume ta

"Sannu da dawowa mommy, ya aiki"?
Shafa kanta hajiya sarah tayi"lafiyalou my baby,..." ta fada tare da kallon shureim murmushi suka sakar ma junansu,
"Sannu da dawo Aunty, ya aiki?
"Lafiyalou shureim ya mai jikin"?
"Mai jiki Alhamdulillah, taji sau?i sosai, gobe muke sa ran za'a sallame ta...
da fara'a tace"Alhamdulillah, amma naji dadi, gobe in sha Allah tare dani zaku tafi..." atare suka jera suka nufi falon gidan, basu san bomb yana nan zaune yana jiran su ba.

Lokacin da suka shiga falon kusan atare suka ci burki suna kallon shi, akace labarin zuciya atambayi fuska, tundaga kan yanayin shi suka sha jinin jikinsu, Yana zaune kan sofa ya haWe fuska kai kace bai ta6a dariya ba, ya murtuke fuska ga wani gumi da ya jike gaban rigar shaddar jikin shi, tsabar fusata zufa ta ko'ina take tsastsafo shi."

Kallon kallon suka fara jefa wa junansu, tsakanin dr shureim da hajiya sarah, kamar an dasa masu aya sun gaza ?arasa shiga ciki....

"Daddy, yaushe ka dawo..."? Zeenatu ce ta ambaci sunan shi, da sauri ta nufe shi har takusa isa, Hajiya sarah tayi saurin cafko hannunta, shigowa ciki dr shureim yayi kamar jira yake su shigo ciki Ya mi?e agadarance ya nufi shureim Yana huci Ya furta"shureim da iznin ubanwa ka fita da zeenatu"?
Har saida gaban shureim ya fadi saboda kalmar ubanwa da alhaji Musa ya furta.


dakyar ya iya buWe baki Yace"bada iznin kowa ba, ni na fita da ita saboda ta fada min tagaji da zama ita kadai agidan...." bai kare maganar ba Alhaji Musa ya dam?i gaban rigar shi ya jijjiga shi idanun shi jawur Ya kalli cikin idanun shureim.

Hankalin su hajiya Sarah ba karamin tashi yayi ba, Allah kadai yasan mai yayi niyar yi mashi amma sai ya fasa ya saki kwalar rigar ya cije la66ansa a zafafe ya ce"shureim ni kayiwa karya? Ka ce da iznina ka fita da ita? Dama malamai suna karya? Kai ko kunya baka ji ba? Ina tsoron Allahn da addinin naka huh? Runtse ido dr shureim yayi har cikin ranshi baiji dadin furucin Alhaji Musa ba, kuma bai ta6a tsammanin zai iya kallon tsabar idon shi ya gaya mashi hakan ba.


"Ka bani mamaki shureim? A bainar jama'a ka rungume zeenatu a kirjinka, ?ato dakai baligi salon kaja min zagi a idon jama'a, so kake ka zubda min mutuncina da kimata..."? Fasa ?ara zeenatu tayi ta fashe da kuka tana fadin"Daddy ka daina yi mashi faWa! banaso, Ka kyale shi! ba laifin Shi bane nice na rungume shi.."

bata ?are maganar ba, Ya dankara mata ashariya kamar bamaguje

watsawa tayi da gudu ta nufi upstairs tana kuka tamkar ranta zai fita, tsautsayine Yaja Hajiya sarah ta buWe baki furta"Yakamata kasan irin kalaman da zaka gaya mashi, wannan ba dacewa bane, shureim baiyi abun kunya ba kaine kayi abun kunya! Akan wani dalili zaka rufe shi da fada saboda kawai ya dauki yar uwarshi ya fita da ita! Shi ne laifi?...." kafin ta kare maganar Alhaji musa ya yai kukan kura ya Waga hannu zai Webe ta da mari da sauri Dr shureim ya shiga tsakaninsu, kai tsaye marin sauka akan fuskar shi,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login