Showing 48001 words to 51000 words out of 298130 words

Chapter 17 - KURKUKUN KADDARA (TAKUN KARSHE) BY BOSS BATURE.doc

shi.
Murmushi benazir tayi"Allah sarki, kada ki damu ai yanzu tunda ina nan zamu dinga zuwa yawo sosai, Harma estate din nasu zamu Iya zuwa duk da bansan su ba amma indai na tuntu6i zaki mukayi magana da shi nasan zai gayyace ni zuwa gidansu, ya jima yana da burin inje gidansu saboda ya nuna ma Iyayen shi ni, Amma na?i amince mashi saboda bana son zuwa nigeria a lokacin"

"Idan ma zaki gidansu ?awarki Aneeleeh dan Allah ki tafi dani, nima inason zuwa, Naji kuna magana da su mom layla akan zaku je gidan"

"In sha Allah, atare zamu tafi," taji dadin maganar Benazir fatan ta Allah yasa ta samu ?awaye agidan kawar Benazir, tana da burin ganin ta tara friends sai dai daddynta Ya hanata Yin kawaye, baison kowa ya rabeta.


*d'EX-PRISONERS


Shigowa Wakin Naufal Yayi, fuskar shi babu walwala, shima babu suturar a jikinshi sai gajeran wando, sumar kanshi duk ta yamutse har saman wuyan shi, Kunsan atare Unaisah Da Sajeed suka juyo suna kallon shi
Harara ya watsa ma sajeed tare da cewa"?an rainin wayau, ashe nan ka shigo, kasa inata nemanka, Hankalina Ya?i kwanciya ganin Halin da ka farka daga bacci"
Murmushi Sajeed Ya sakar mashi, tare da saukowa daga saman gadon unaisah bayan ya mi?a mata wayarta ya nufi Naufal Ya rungumo shi Yana fadin"Sorry My baby Boy, Na tayar maka da hankali, ashe ka damu dani har haka? Halan ma kuka kayi saboda rashin ganina da baka yi ba" ya fada da zolaya yana shafa mashi fuskarshi.

Tsoki Naufal Yaja ba tare daya tanka mashi ba Ya dubi Unaisah
"Sister barka sannunki"
Murmushi tayi dimple dinta biyu suka lotsa
"Yawwa rabin raina, halan Sajeed ne Ya 6ata maka rai"?
Yamutsa fuska yayi kafin yace"eh mana, kawai Ina kwance Ina bacci na jiyo shesshe?ar kukan shi ya cika min kunne na, ba arzi?i na farka Hankali atashe na tada shi daga bacci ina tambayarshi lafiya yake kuka, Bai tanka min ba kamar wani shashasha haka yabarni ya fito daga dakin, Ina ta neman shi ashe nan ya shigo" Ya faWa yana jifar Sajeed da harara"don yaga na damu da shi ne, Allah nan gaba idan Ya ?ara yi min haka, Bulala zan sanya mashi"

Dariya su ka yi gaba Wayansu, Sajeed yace"na fi ?arfinka Naufal, mai buguna sai ruwan sama da rana," ya fada yana nuna mashi faffadan kirjinshi da damtsen hannunshi.
NannaWe hannun riga Naufal yayi yana fadin"ba kai kaWai Allah Yaba kirar karfin ba, Nima ina da ita, babu abunda zaka nuna min in banda girman jiki"
Unaisah dake kallonsu kamar ta samu tv, Wayarta dake a hannunta ta danna ta shiga Camera, Ta saita su tana Waukarsu Video batare da sanin su ba, saboda sunyi mata kyau, sai taji inama ace hada Danish dinta da kuwa shi zai kar6i kambun faWan nasu, domin kuwa Danish Yafi su tsayi da kuma kyawun Sura duk da suma Win ba daga baya ba musamman Gabriel Namiji ne.

A yayin da take Waukarsu video, bakomai take tunawa ba face garkuwarsu, lokacin da ta ris?e shi a Wakin Gidan kurkukun ?addara Kwance Yana bacci da red shirt a jikin shi, yayi mata kyau fiye da tunanin mai tunani, duk da a lokacin a matsayin giant yake saima ya ?ara yi mata kyau, tana matu?ar ?aunar komai nashi ta ?osa ya dawo normal mutun kodan suci gaba da bama junansu kulawa.

Tayi zurfi acikin tunaninta, Shesshe?ar kukan Azeeza Ya fargar da ita, da sauri ta janye wayar daga saitin fuskarta, su Sajeed dake atsaye suna kokoyi shida Naufal jin kukun Azeeza ne Yasa suka dakata kusan atare suka kalli ?ofar shigowa dakin.

Kamar Mahaukaciya Haka ta shigo sanye da ?ar gown wadda bata rufe gwiwar ?afarta ba, fuskarta sharkaf da hawaye tayi jawur da ita, rigar jikinta ta ji?e da ruwa
daga bayanta Jamimah ce atsaye ta ru?e rugu tana faman sakin murmushin mugunta.

da sauri Unaisah ta sauko daga saman gason, ta nufi Azeeza ta ru?o hannunta tare da rungumeta tana tambayar ta lafiya take kuka
Muryarta da shesshe?ar kuka tace"jamimah ce ina bacci ta watsa min ruwa ajikina, shine wai take cewa nayi fitsarin kwance bayan itane ta kwarara mun ruwa a kasan rigata.... " tunkafin Azeeza ta ?arasa maganar, Jemimah tayi saurin cewa"wallahi ?arya take yi min, Fitsarin kwance ne tayi mana a Wakin mu, Ni bani na zuba mata ruwa ba" Ta faWa tana faman gumtse dariya.

Cikin muryar RaWa Naufal Yace da Sajeed"babynka tayi fitsarin kwance, Yakamata kaje ka wanke mata" harara Sajeed Ya watsa mashi tare da ingije shi, Ya nufi Jemimah, ganin Yana tunkarota Yasa ta juya da niyar ta gudu sai dai kafin ta fuce daga Wakin, Yayi hanzarin cafkota da hannu biyu ya Waga ta sama yana fadin"Mugunta ko? Ai ba ke kaWai kika iyaba kowa ma Ya iya ta, rasa kunya 6eran tanka, da wasu kunnuwanki kamar na zomanya, Jibi kumatunki duk kin shanye ma mutane madara da bonbita, Yau zanyi maganinki" Ya fada tare da Juyawa ya nufi Toilet da ita, Kuka tadinga yi mashi tana kokarin kwacewa, da gudu naufal yabi bayan shi yana fadin"please bro, Ka kyaleta yarinya ce bata da wayau" ko sauraron shi baiyi ba yaja kofa Ya datse.

Azeeza dake kwance Jikin Unaisah sai faman sauke ajiyar zuciya take Yi, Taji daWi Sajeed zai rama mata abunda Jemimah tayi mata, ba tun yau ba kusan kullum sai jamimah tayi mata mugunta don taga suna kwana a Waki Waya.

"Ki yi ha?uri da sister dinki, nasan halinta bata jin magana, Kunnan ?ashi ne da ita, amma please ki daina bari tana ganin kukanki, shiyasa take ?ara rainaki saboda tasaba sanyaki kuka... "
Cikin sanyin murya Azeeza tace"Toh, amma kiyi mata magana tadaina jana fada, har fadi takeyi wai ni ban isa da ita Ba, maganarki kaWai take Ji"
Murmushi unaisah tayi"zan yi mata magana idan ma bata daina ba zamu fara koya mata hankali ne"
Fitowa Sajeed Yayi daga cikin toilet Yana faman sauke ajiyar zuciya, fuskarshi Wauke da murmushin mugunta.
Naufal dake kallonshi yace"Mugu Ina ka baro mana jamimah"?
Harararshi yayi" ka shiga ka Waukota, wata'?il ?afafuwanta baza su iya daukarta ba shiyasa ta kasa fitowa"

Ya faWa tare da wucewa Ya nufi Azeeza, Ru?o hannunta yayi Acikin nashi ya rabata daga jikin Unaisah
Ya zauna daga gefen gadon Yana fadin"Har nagaji da yi maki magana akan ki daina bari Waccan ?aramar halittar tana sanyaki kuka, serious idan baki daina ba zamu 6ata" ya faWa yana daure mata fuska.
Muryarta ?asa ?asa tace"zan daina"
Harara ya watsa mata"haka kullim kike fadamin, last warning zan baki daga yau idan na ?ara ganin hawaye akan fuskarki da sunan jamimah ne tasa ki kuka Jikin kine zai gaya maki" yai maganar tare da kama kunnanta yace"Idan kunne Yaji"? da sauri tace mashi Jiki Ya tsira"

Dariya ce ta kubce ma unaisah da naufal, shima sajeed din dariyarce tazo mashi sai dai Ya?i barin ta kubce mashi don baison raini ya fara shiga tsakanin shi da Azeezarsa, Yafi son tana jin shakkarshi.

"Jemimah!" Jamimah ta"! Naufal Ne ya kira sunanta, Shiru taki ta amsa mashi, Sajeed Yace"zuciyar ce ta motsa, tana jin ka ?ar rainin wayau"
Mi?ewa unaisah tayi da sauri ta nufi toilet din, tana shiga ta taras da jemimah zaune cikin kwamin wanka da sajeed Ya cika da ruwan mai uban yawa, Rigar jikinta duk ta manne ma fatarta, ta Waure fuska sai shesshe?ar kuka take Yi kamar zata haWiyi zuciya tsabar 6acin rai.

Ganin Unaisah yasa ta fashe da kuka rai a6ace ta dinga bugun ruwan da hannayenta tana fadin"wayyo Allahna Anci mutuncina, Zuciyata tafarfasa take Yi min, Genie kinga abunda Sajeed Yayi min ko? Kina gani baki hana shi ba, Saboda rashin mutunci ya jefa ni acikin ruwa"

Hatta su Sajeed dake adakin saida suka jiyo maganganun da Jemimah takeyi a toilet, gaba Wayansu suka sanya dariya hada Azeeza.

"Am sorry My Little sister, Sajeed bai kyau ta miki ba, Amma kiyi hakuri dan Allah" unaisah ce ta fada Cikin lallashi da lallami Ta nufi jemimah, ta sanya hannu ta Waukota daga cikin ruwan,
"Kinyi wanka"? Idanunta na fitar da hawaye tace"a'a ni ban yi ba"
"Okey, Bari nayi maki wanka, Sai in Wauko maki wasu kayan ki canza"
Ta fada tare da cire mata rigar, shaf shaf tayi mata wanka ta daure mata jikinta da towel, Asaman bayanta ta goyo jemimah, suka fito daga toilet din, sai faman zumbura baki take Yi, Hada jifarsu Sajeed da harara.
"Azeeza mu tafi dakinku, Inaso Ku shirya in yi mana hotuna da wayata" amsa mata tayi da toh,
Sajeed yace"Mu ma bari muje mu shirya ayi mana hotunan, Ko mun samu na ajiyewa saboda tarihi"
Yayi maganar tare da mi?ewa Ya dafa kafaWar Naufal, suka fuce daga dakin.


*d'BATOOL

Kusan mintuna da tafiyar Unaisah, Chief Ya shigo dakin sanye cikin shiga ta white thobe launin Sky blue, tabi shape din jikin shi, Hannun shi Waya ruke da wayar shi, Ya karata a kunnanshi ga dukkan alamu waya yake yi.

"Yanzu na shigo gidan, In sha Allah Uncle Idan na shiga bedroom dinsa zan kira ka video call kaga fuskarshi, nasan hakan zai kwantar maka da hankalin ka"

On the other hand, Prime minister yace"nagode my Son, bansan meyasa nakasa cire shi arai na ba, Na ?wallafa rai akan shi"

"Kada ka damu uncle, Nafi so ka kwantar da hankalin ka, baifi awanni daka dawo daga tafiya ba, nasan kana bukatar hutu, Idan rabon ka ne shi watarana zaku gana"

"Ina fatan hakan, nagode da kulawarka, sai naji ka".

"Okey" ya ambaci hakan tare da zame wayar daga kan ear dinsa.

Yayin da yake tafiya A hankali yake bin ko'ina na room din shi da kallo, Kafin Ya sauke idon shi akan Glass table din dake dauke da breakfast dinsa.

?arasa shiga ciki Yayi, batare da 6ata lokaci ba, Ya zame jallabiyar jikin shi, Daga shi sai short Ya nufi toilet Ya shiga domin yin wanka.
After 15 mins Ya fito Waist dinsa daure da white towel, a gaban dressing mirror ya tsaya da niyar ya gyara jikin shi, kwatsam A lokacin da baiyi tsammani ba kunnuwansa suka jiyo mashi sautin motsin mutun a bedroom dinsa.

A hanzarce ya Waura idanunsa kan madubin, ta ciki ya hangota ta fito daga hanyar zuwa Gym Room dinsa kamar Aljanna, Hannunta Waya ru?e da mayafinta, Ga wannan Uban gashin kan nata data ta saki saman bayanta yayi mata tamkar hijabi, Lamarin ya Waure mashi kai ganin matashiyar mace a Wakin kwanansa, Wacece ita? Tayaya akai ta shigo mashi bedroom din sa? Da iznin wa"? Acikin zuciyarsa ya furta hakan ba tare daya kau da ido daga kallon ta ba, ?arfin halin ta yayi matu?ar bashi mamaki, tsawon lokacin daya shigo dakin har ya shiga bathroom yayi wanka duk tana a ciki ko me take yi!?

Gaba Waya Hankalinta ba akanshi yake ba, batasan ma da zaman shi a dakin ba, har ta ?araso tsakiyar dakin bata lura da chief Owais ba, idanunta ba su hango mata shi ba, Sai faman sauke ajiyar zuciya take Yi kamar wadda tasha gudu.

Ganin bata da alamun motsawa tabar mashi room dinsa ne yasa shi juyowa A hankali Ya nufe ta, sam bata ji motsin takun shi ba, saboda Ta juya mashi baya sai ?an waige waige take Yi, duk kallon da tayima dakin nashi bai isheta ba.

A lokacin da batayi tsammani ba, Taji saukar hannun mutun saman sumar kanta, Kafin tayi wani yun?uri Ya dam?i gashinta, wata irin firgita Batool tayi, A gigice Ta fasa ?ara Sautin Ya cika kunnuwanshi dasauri ya sakar mata gashi, hakan ya bata damar juyowa don ganin wanene.
Wani irin bugu zuciyarta tayi lokacin da idanunta suka sauka akan faffaWan ?irjinshi, da waWannan Strong arms din nashi, ta zazzaro mashi ido waje la66anta na kerma take ambaton"INNAHU MIN SULAIMAN WAINNAHU BISMILLAH" adabarbarce ta furta hakan, kamar wadda taga wani mugun abu, Kallo Waya da tayi ma fuskarshi har suka haWa ido ba ?aramin gigitar da ita yayi ba, duk tabi ta ruWe, Mayafin hannunta tuni ya jima da zamewa saman floor, juyawa tayi da gudu tana neman hanyar fita daga dakin sai dai takasa gane ta ina ?ofar da suka shigo take, sai faman bin bango take yi, Jikinta ya hau yin kerma kamar wadda Sanyi ya kama.

Chief dake atsaye yana dubanta, Kallon mahaukaciya Yake Yi mata saboda kalmar data furta mashi da kuma firgitar da tayi kamar taga wani mugun abu, Ya rasa gane me ya ruWar da itane, ta6e la66ansa yayi kafin Ya juya ya nufi cikin Wakin,
Batool dake ta neman kofar fita, tuni zufa ta ji?eta yadda kasan babu A.c a dakin, Mugun tsoron shine Ya kamata hada ?arin babu sutura a jikin shi shiyasa ta rikice da ganin al'amurransa, towel din daya Waure waist da shi ko gwiwarshi bai rufe ba.

Jin takun tafiyar Shi abayantane Yasa ta ?ara ruWewa, A gigice Ta juyo tana duban shi, sumar kanta ta rufe mata gefe da gefen fuskarta, har Ya sanya Short a jikin shi tare da singlet fara ?al.

Fashe mashi tayi da kuka tana fadin"nashiga uku, dan Allah ka buWe mun ?ofa in tafi Wakin mu, wallahi ni ba 6arawo bane, bada niyar wani abu na shigo maka Wakinka ba.

Fuskarta sharkaf da hawaye tayi maganar tana faman jan majina.

Bai tanka mata ba, yama rasa bakin magana, mamakin ta ya gama kama shi, sai yanzu ya gane fuskarta a cikin Yaran da suke kula da su.

Gently Ya juya Ya nufi gaban side drawer din shi, ya buWe Ya dauko jotter da pen asaman drawer din Ya Waura jotter, rubutu yayi mata bayan ya kammala ya cire paper din ya tunkari Batool Ya mi?a mata takardar, gabanta na faduwa ta sanya hannunta dake kerma ta kar6a tana kallon abun da ya rubuta mata.

Muryarta da shesshe?ar kuka Ta furta"ai..ai.. Ni Ban Iya karatu ba, sai dai in kaima Unaisah ta karanta min"

Wannan maganar da ta furta mashi ta ta6a zuciyar shi, har sai da ya Waura reddish eyes dinsa akan soft brownish lips Winta da suka jike da ruwan hawayen ta, ga wani uban gumi da ta haWa a jikin ta, shi abun da ya Waure mashi kai ruWewar da tayi kamar taga wani mugun abu, ita kanta Batool din tunfarko taso idan suka haWu ta natsu ta yi mashi bayanin abunda ya kawota dakinsa, sai dai dalilin sha?ar da yayi ma sumar kanta ne, Yasa ta firgice mashi ta kuma fahimci bai san da maganar zuwan ta Wakin shi yi mashi aiki ba!.

Ta?i Yarda ta Wago su haWa ido saboda ?warjinin da yayi mata, gani take yi kamar zai rufeta da bugune yadda yayi mata rumfa da kirjinsa.

"Dan Allah ka buWe min ?ofa in tafi daki, zan kai mata ta karanta min"

ba tare daya furta mata komai ba, Ya dafe Glass door din dakin nan take ?ofar ta soma zugewa a hankali, Jikinta har rawa yake Yi wurin yin saurin fucewa daga dakin kamar za tayi tuntu6e.

Ta tafi tabar mashi Mayafinta akan floor, komawa yayi gefen gadonshi Ya zauna da sanyin jiki, wata irin yunwa ce ke addabar shi, bazai juri jiran wani yayi serving na shi ba,
Da kanshi Yayi serving abunda zaici, Kakkauran tea ya zuba a cup Ya soma kur6an shi atsanake, Yayin da brain dinshi ke tariyo mashi kalaman Batool
Ai ni ban Iya karatu ba, zan kaima unaisah ta karanta min, Abun Ya tsaya mashi aranshi, Duk da bai kalleta dakyau ba, zai Iya bata shekaru goma sha bakwai zuwa sha takwas, a wannan shekarun bata Iya karatu ba? Bai yi tsammanin abun yakai haka ba.

Bayan fitar batool daga dakin chief, nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke, tana tafiya idanunta akan paper Win daya bata, Har ta sauko down ta nufi dakin su.

Lokacin da ta shiga bata taras da kowa ba, yanke shawarar shiga toilet tayi don ta wanko fuskarta, asaman gadon su ta Waura paper din, da sauri ta shiga toilet ta wanke fuskarta, fitowa tayi tareda nufar gado nasu, isarta keda wuya ?afarta dake sanye cikin wandon pakistan ta harba hotunan da suke yashe kan floor ba tare data lura da su ba, nan take hotunan suka gangara ?ar?ashin gadon suka shiga ta yadda babu mai iya ganin su.

Mi?a hannu Batool tayi ta Wauki Paper din Ta juya da sauri ta fito daga dakin tana neman su Unaisah.

Sautin Muryoyin su Tajiyo A falo suna surutu cikin takun sauri ta nufe su, tun kafin ta ?arasa ta hango su tsaitsaye sun yima Unaisah rumfa hannunta ru?e da waya tana yi masu hotuna, tun daga kan Haris, Naufal, Javed, Sajeed, da su Azeeza jamimah, parveen and Hannah kowannansu ya sanya sutura mai kyau ajikin shi, Unaisah ce tasa suka Wauki wanka, don tayi masu hoto.

Babu wanda Ya lura da Batool acikin su, Camera taja hankulansu, har saida Ta furta Sunan Unaisah tukunna suka Wago da idanunsu akanta.
Kallo Waya da Unaisah tayi mata saida taji gabanta ya fadi ganin yadda kumatunta suka yi ja alamar tayi kuka
Gaba Waya sun lura da yanayin Batool babu walwala,
Ru?o hannunta Haris yai acikin nashi"Sister baki da lafiya ne"?
Shiru tayi batace mashi komai ba, Hankalinta na akan Unaisah
"Me akayi maki? Kuka ki ka yi"? parveen ce tayi mata tambayar, girgiza mata kai tayi alamar a'a.
hannah ta ru?o hannunta tana fadin"Sis Batul ki zo ay mana hoto atare dake"
Fahimtar halin da take aciki ne Yasa Unaisah mi?a ma Sajeed wayar hannunta, bayan ya kar6a tace"ka cigaba da yi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login