Showing 54001 words to 57000 words out of 298130 words

Chapter 19 - KURKUKUN KADDARA (TAKUN KARSHE) BY BOSS BATURE.doc

Yanzu tayi baki ta rame babu ?ugun nan nata da kirjinta duk sun zube kamar mai fama da wata lalura,"
Aneelerh tace"abun da yafi Waure min kai da ita ummi, kwata kwata bata da natsuwa, ko magana take yi yatsun hannayenta zaki ga suna kerma kamar wadda sanyi ya kama"
Ummi tace"Muje muji meke damunta," gaba dayansu suka nufi kitchen din gidan, Koda suka shiga basu ganta ba, Har ta kamma aikace aikacen da take Yi, tayi wanke wanke tayi mopping dinsa.
Ummi tace"baiwar Allah gata da ?o?arin yin aiki, banji dadin halin da take aciki ba"
Fitowa sukayi daga kitchen din suka nufi bedroom din Ana.
Abakin Door room din Suka dakata da yin tafiyar, Aneelerh ta kwankwasa mata kofa, kusan sau uku Tana buga kofar kafin suka jiyo motsinta ta cikin dakin, buWe kofar tayi tare da le?owa tana kallon su
Fuskarta a yamutse, idanunta sun yi jajir da su.
Murmushin ya?e ta ?a?alo akan fuskarta, cikin girmamawa ta gaishe dasu tana ?o?arin 6oye damuwarta
"Wurin ki muka zo mu shiga daga ciki" mami ce tayi maganar, da sauri Ana ta matsa masu hanya suka shiga dakin, Daga tsaye suka tsaya tace mashi su zauna saman gadonta
Ummi tace"ba zama ya kawo mu ba, zuwa mukayi don muji meke damunki Ana, meke faruwa dake ne? Duk kin canza mana kin rame kinyi ba?i! Baki da lafiyane"?
La66anta na kerma ta furta"babu komai lafiyana lau madam, wallahi babu abun dake damuna"
Cikin kwantar da Murya mami tace"Kada ki 6oye mana komai, Ki Wauke mu tamkar iyayenki, dan Allah ki fada mana damuwarki, In sha Allah zamu share maki hawayenki,
Mami na rufe baki Aneelerh tace"Ana please kada ki bani kunya, Saboda mun Wauke ki da daraja shiyasa muka damu da damuwarki, Kina gani dai mami da ummi da kansu suka zo dakin ki yau duk don saboda sun damu dake, Idan kika ce babu abunda ke damunki, kinyi mana karya saboda babu yadda za'ai ki rame batare da ciwo ko wani abu ba, dole da akwai wani abu da baki son mu sani"

Gaba Waya sun Waga mata Hankalinta, Cikin kwantar da murya suke yi mata magana amma sai ta dinga ganin kamar suna yi mata faWane, Dafe kanta tayi da hannu biyu tana ambaton sunan Allah tamkar musulma.
Muryarta na rawa take fadin"Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un, na ro?e ku ku ?yaleni, ku tafi kawai, nagode da kulawarku agare ni,nagode"
Hankulansu atashe suke ambaton sunanta haWi da tambayarta meke damunta.
Gaba Waya ta rikice masu, sai sambatu takeyi tana rokonsu akan su tafi subar dakinta, a karshe ta watsa da gudu ta shige toilet taja ?ofa ta datse. =?3?

Kallon juna suka somayi da tsantsar mamaki da rudani aka fuskokinsu,
..mami tace"to fa, Anya kuwa lafiya"?
Ummi tace"bafa lafiya, Ni dai inaga kamar hada aljanu ke damunta.
Jikin Aneelerh yayi sanyi, tun datake da ana bata ta6a Waga mata murya ba sai yau da ta rikice masu tana korarsu daga dakinta, tabbas babu lafiya!

"Yanzu ya zamu yi da ita"? Mami ce tayi maganar,
Ummi tace"yakamata mu sanar da su Abie, dangane da halin da take aciki"
Sun jima a dakin Ana suna yi mata magiya akan ta fito daga toilet, amma taki fitowa a karshe dole suka hakura suka bar mata dakinta..

*Daular Obie Estate*

Gaba Waya Manyan matan Family din sun hallara a gidan Hateem domin yi masu bangajiyar tafiyar da su ka yi, musamman saboda zuwansu akayi masu shimfiWa ta alfarma a katafaren Garden din gidan hateem, garden ne na alfarma cike ya ke da tsiro da furanni launuka daban daban masu ban sha'awa, ga wata irin ni'imtacciyar iska mai ratsa fatar jikin mutun, daga can cikin garden din akwai wani ?aramin tafki wanda ke acike da tsaftaccen ruwa launin blue sky, inda fararen agwagi suke shawagi acikin sa, an tsara komai da kyau, a tsakiyar garden din akwai wani katafaren wurin zama, kewaye da ciyawar da aka yi wa ado, Lallausar darduma ce mai wani irin laushi a jikinta irin ta sarakuna, An kewayeta da tuntuye, yayin da suke a zaune kowaccensu ta Wauki wanka na kece raini na mutunci, mata ne masu duniya, ajin farko, waWanda suka gaji arzi?i tun kaka da kakanni, wayayyune masu ji da ilmin da Allah ya basu, mace ta farko Gimbiya mujeedat ce a kishingiWe saman dardumar tayi shiga ta alfarma cikin tsadaddiyar Arab gown launin Ash colour anyi mata adon sparkling stones, masu Waukar ido, ta yafa mayafin saman kafaWarta, ba?ar sumar kanta ta sauko har saman dardumar da suke, daga gefenta First Lady ce Hajiya Malikat Sarauta ?ar sarkin Yarbawa jihar Lagos, Mace mai ji da kanta, mahaifiyar Chief Owais, A launin fata chocolate colour ce, taji hutu, bata da yawan fara'a, tana da ?aramin baki ga dogon hanci, idanunta masu kyan gaske sunyi kama da Asian eyes, kayan jikinta Na yarbawa ne, Wrap around skirt ta sanya tare da farar shirt, anyi mata naWin head akanta, tun daga kan wuyanta har hannayenta adone na zinarai, bayan Hajiya Malikat sai Hajiya Laurat uwar ji da izza, ?anwar Alhaji Musa, Idan ka gansu atare da Hajiya malikat baka ta6a gane cewa kishiyoyine saboda kowaccensu bata Waukar raini, ita malikat arziki da sarauta ta gada, ita kuma Laurat Arzi?ine gare su na fitar shari'a, sai dai daga ganin fuskarta zatayi rashin mutunci idan aka ta6a, daga ka kalli fuskarta zaka shaida ?anwar Alhaji musa ce, Kamanninsu har sun 6aci da shi, hatta launin fatarsu kala Waya ce, Hausa fulani ce, ta Wauki wankan shadda launin dark brown anyi mata ado, Wuyanta na asanye da sar?ar diamond, haka yatsun hannayenta zabban diamond ne masu kyalkyali da daukar ido.

Mace ta gaba, Hajiya Madina ce matar senate Lateef, barumaya ce, tana da hasken fata da tarin sumar kai, hatta gefe da gefen fuskarta akwai tsagensu na rumawa, Tana da kyau iya gargado sutura tanayi mata kyau, daga ganin fuskarta tana da kyakkyawar zuciya ko ba'a faWa maka ba, Hadaddiyar atampa chiganvy ce a jikinta tabi shape din jikinta, Itama ta dauki nata adon na zinarai.

Bayan Ita sai matar His excellency Deen, Hajiya Jamila, Bafullatanar usili ce, ?ar sarkin Jihar adamawa state, Fara ce jawur da ita, tsabar kyanta kamar ba'indiya.

Daga ita sai Matar Abdul Razak, Her excellency Muhibbat, Shuwa Arab ce ?ar mai duguri, fara doguwa ga gashi har gadon baya, family dinsu sunyi ?aurin suna a 6angaren Arzi?i, Mace ce mai ji da kyawu da wadatar arziki, tana sanye cikin shiga ta bubu gown ta lace, ta kashe Waurin kallabi, awarwaron dake a hannayenta na zallar zinari ne.

Mace ta karshe basai nayi maku bayaninta ba, Kun riga da kun santa, bakowa bace face Aunty Masifatu Hajiya saratu, mutuniyar, wankan material ta Wauka, gaba Waya ?amshin turarensu Ya karaWe iskar garden din hakan ba ?aramin ?ara ma yanayin ni'ima yayi ba.

Daga tsakiyarsu Katafaren Faranti ne na azurfa, mai girman gaske wanda masu hidima suka kawo masu shi, An cika shi da Soyayyun Kaji jar suya, da kayan marmari nunannu, tare da juice masu sanyi.

Fira su ke yi atsakaninsu cikin harshen turanci tamkar ba su son furta magana.

"Naji daWin ziyarar da kuka kawo min, kuma naji daWin ganinku, Sai naji dama A ?asar nan nake zaune, saboda mu run?a sada zumunci a tsakaninmu akai akai" gimbiya mujeedat ce tayi maganar tana binsu da kallo Waya bayan Waya.
"Ni kaina naji dadin haWuwar da mu ka yi, bazan Iya musalta farin cikin da nake a ciki ba, Allah Ya ?ara HaWa kawunanmu da zuri'armu" hajiya malika ce ta fada, tare da kai hannu ta Wauki Yankan Tufa tana sha.
"Canada tamkar gida take awurina ina yawan zuwa saboda business din da nake yi Acan, In sha Allah zan dinga zuwa Ina kawo maku ziyara, Har sai kun gaji da ganina" hajiya Laurat ce ta faWa tana duban gimbiya mujeedat, murmushin gefen fuska Mujeedat ta sakar mata tare da lumshe idanunta.
Hajiya Jamila tace"naji kamar kuna Bankwana, Tun Kafin jibin tayi ko kun manta da family dinner da zamu Yi a gobe?
Hajiya saratu tace"Kamar kin shiga zuciyata, nima tun Wazu maganar da nake ta so Inyi masu kenan, ai gobe muna da gagarumin shagali In Allah yakaimu da rai da lafiya, dole kowa ya halarta" ta faWa tare da kai hannu cikin faranti Ta yago cinyar kaza ta tura abaki tana tauna
Hajiya jamila na dariya tace"daWina dake saratu baki wasa da cikin ki, Zaman mu anan kin cinye fiye da rabin kaza, shiyasa gaki nan kullim ?ara ?iba kike yi,"
"Kinsama kanwar nan tawa ido" acewar Gimibiya mujeedat.
"Kibarni da ita aunty, da duk wani mai sanya min ido akan cin abincina, nasan maganinku, zanyima yayyena magana su ?ara maku kishiyoyi, ?wara ku lalla6ani ku dinga lallashina idan ba haka ba kun san sauran" dariya su ka yi gaba dayansu,
"Meya yayi zafi, nayi shiru bazan ?ara tanka maki ba, Ci ki ?oshi, Idan ma kina bu?atar ?ari zansa akawo maki" hajiya jamila ce ta faWa tana tura mata farantin agabanta, Hajiya sarah tayi dariya da zolaya tace"Bari naja bakina nayi shiru, naga wasu sun fara haWe min fuska saboda nayi maganar kishiya"
Murmushi kowannansu ya saki,
Gimbiya mujeedat tace"ko kaWan banji fargababa, because I know who my husband is. He doesn't want to remarry; I'm enough for him." She said proudly and gently.

Hajiya laurat tace"ai dama irinku ba'ayi maku kishiya, wane mutun, ballanta kuma mijinki da gaba Waya rayuwarsa acikin turawa yayita, ba lallai Yana da wannan ra'ayin ba, tun da suma mace Waya su ke aure"
Her excellency Muhibbat ta murmusa tare da cewa"ni dai koban fada maku ba kun riga da kun sani, ba'ayi mana kishiya, Mijina bai ta6a gigin kula wata ?a mace ba"
Hajiya malikat dake sauraransu tace"nima nan bada jimawaba zansa mijina yayi waje da wata" ta faWa da zolaya tana kallon Hajiya laurat, dariya suka sanya gaba Wayansu.
Hajiya Laurat tace"Ni da sharafudden mutu karaba takalmin kaza, badai mutun ba sai Allah, me raba ni da shi sai mutuwa"
Yamutsa fuska Hajiya malikat tayi"alfarma fa nayi mashi ya aure ki, saboda yana jin shakkar tunkarata da zancen auranki yasa shi ?in sanar dani sai dai naji daga saman an shafa fatihar auranku, wato yanzu kin samu wurin zama shiyasa har kike da bakin fadin mutu karaba takalmin kaza," cikin raha suke Yin firar tasu.
Hajiya Muhubbat tace"ai ni ina mamakin dauriyarku da har kuka Iya haWa kanku, babu mai jin sirrinku, Gaskiya kun burgeni, amma ni fa wallahi bana tunanin zan Iya zaman lafiya da kishiya, shiyasa tun kafin abdul razak Ya aureni saida muka ?ulla yarjejeniyar bazai yi min kishiya ba, mahaifina ma saida Yaja mashi kunne akan hakan"

Jinjina kai Hajiya madina tayi'lallai abun naki azimin ne, ni kuwa dai bana jin zan Iya hana Mijina Yin aure, tun da Allah ya Halasta masu auren mata har huWu, Idan Ya nuna yana so zan goyi bayanshi, kuma Idan Ya aurota zamu yi zaman lafiya da ita idan har ba ita bace ta bijirema hakan ba"

Wani kallo her excellency Muhibbat Ta yi mata"babu zuciya a kirjinki, Shiyasa bakya kishin mijinki"
"Bawai don bani da kishi bane, nafiso idan ma kishin zanyi inyi irin na matan manzon Allah SAW, ni fa da ace mijina Yana bin matan banza ?wara ya auro mata uku a lokaci Waya, amma idan nace zan tauye mashi hakkin shi in hana shi auran abunda yake so to fa zan jefa shi ga halaka ne, sannan ban Isa In hana zuciyarshi son wata ?a mace ba"
Jinjina kai su kayi jin bayanin Hajiya madina badan sun fahimce ta ba.
Hajiya Jamila tace"godiya yakamata muyiwa Allah daya bamu mazaje nagartattu, nagari masu ?aunarmu tsakani da Allah, Har Yau Ina alfahari da kasancewata Waya daga cikin surukan dattijon Arzi?i, Allah Ya saka mashi da gidan Aljanna, Ya haifa mana zaratan maza sadaukai, Tsakaninmu dashi sai son barka" Murmushi hajiya saratu tadinga saki jin ana yabon mahaifinsu, wani irin dadine Ya lullu6eta
Hajiya Muhibbat tace"Ai Zuri'ar Obi komai sun haWa Allah Ya basu, kyau, nasaba, ilmi, wadatar arzi?i, ?awayena har tambayata sukeyi wai babu sauran ?a'?an shi da suka rage? Don su aura suma su shigo daga ciki, nace masu sai dai Jikokinsa ?a'?an cikin su in suna so" dariya sukayi gaba Wayansu.

Bayan sun lafa, kowaccensu Ta sanya hannu a faranti ta dauki abunda take son ci, wasu nama Wasu kayan marmari wasu kuma lemu suke sha.

_______________________ '?

A hankali Motar Sir Mubarak Tashigo Gidan Hateem, A Harabar ajiye motoci yayi parking dinta, fitowa yayi daga front seat ya zagaya ta back seat Ya bude ma mom turai kofa, A hankali ta fito ta sanya atampa riga da skirt sunyi mata kyau, Ta yafa mayafi saman kafadarta, yayin dashi kuma yake asanye da Shadda.
Kallon juna sukayi, da sauri ta kau da idonta gefe, hannunta ru?e da ?ar handbag dinta
Muryarta ?asa ?asa ta furta"dan Allah kabarni in koma gida, bansan meyasa ka tursasa min akan inzo gurinsu ba, na faWa maka basu ?aunata, wallahi ci mun mutunci zasuyi"
?aure mata fuska yayi"kar na kuskura nasake jin kin furta maganar nan! bana jin dadin yadda kike ware kanki daga cikinsu! Dame suka fi ki? Tsoron su kike ji? Baki Iya mayar masu da martani in suka gaya maki magana"?
Tuni idanuwanta sun cicciko da ?walla muryarta tamkar zata fashe mashi da kuka tace"Ina da banbanci dasu, Har Yau har gobe sun?i mantawa da matsayina agidanku, Suna yi min kallon ?as?antacciya ?ar aiki, babu abunda Ya canza"


*DAGA AL?ALAMIN HAFSAT BATURE
'?*_ *~
'=؋?BOSSLADIESWRITERS=؋?
'~*_



3,F 'DB/1=؋?
'=?%?


~Takun ?arshe=?%?~



B5) -( 1HE'F3J) :J1 9'/J) (JF 'D3,F'! E9 *7H1'* E9B/)=؋?=ؘ?=??


An extraordinary romantic love story between prisoners with complex twists d'=؋?=ؘ?



Daga al?alamin Boss Bature=؋?
'



__________________________
'?



Tuni idanuwanta sun cicciko da ?walla muryarta tamkar zata fashe mashi da kuka tace"Ina da banbanci dasu, Har Yau har gobe sun?i mantawa da matsayina a gidan ku, Suna yi min kallon ?as?antacciya ?ar aiki, babu abunda Ya canza"

Ya fahimci ba?aramin jin shakkarsu ta ke yi ba, muryarshi a kausashe ya furta"kamar ba matar Sir mubarak ba, kin bani kunya, wlh daga yau zan baki last warning, idan na kuskura na sake ganin kin zubda hawayen ki ko kina jin tsoron wani acikin su, sai na sa6a maki" ?iris ya rage ta fashe mashi da kuka, jin yadda yake mata magana da faWa.
Zare mata ido yayi"ina fata kin fahimce ni"? Muryarta na rawa furta"yea..h" ru?o hannunta yayi acikin nashi, yaja ta a hankali suka nufi katafaren falon gidan, ko da su ka shiga masu yi masu hidima suka taras sai kai komo su ke yi a cikin falon, ganin sir mubarak yasa suka yi saurin gaishe su cikin girmamawa bayan ya amsa masu ya tambayi ina gimbiya mujeedat.

?aya daga cikin hadiman ce ta bashi amsa da cewa"su na a garden"

Dam?a mata hannun Turai yayi wadda tuni jikin ta yayi sanyi lakwas.

Cikin kuwala yace da hadimar "she's my wife, inaso ki rakata wurin su, ki bi min ita a hankali' murmushi hadimar tayi aranta ba karamin burgeta yayi ba, daga gani yana daraja matarshi
"In sha Allah yalla6ai" ta faWa tare da ru?o hannun mom Turai suka nufi ?ofar fita daga falon, tana tafiya tana waiwayon shi, kamar yadda shima yake kallon ta har sai da ta 6ace ma ganin shi kafin ya nufi Wakin prime minister.

Jin motsin shugowar Sir Mubarak ne Yasa shi BuWe idanunsa Yana dubanshi
Daga gefen gadon shi Ya zauna Yana fadin"?anina Ya Gajiyar tafiya," mi?ewa Hateem Yayi da wata irin kasala Ya zauna Yana fuskantar Sir mubarak
"Gajiya tabi Jiki, yayana nakaina, kaima ya gajiyar taka"
Da zolaya Sir mubarak Yace"nifa Sojane tafiyar da mukayi bata isa ta gajiyar dani ba" murmushi Hateem Ya sakar mashi
Cikin kulawa Sir mubarak Yace"Meke damunka? Naga yanayinka ya canza ko baka Jin dadine"?
Cikin sanyin Murya Yace"lafiyana lou" ya fada yana kokarin danne damuwarshi
"Nifa Yayanka ne Hateem, baka Isa ka 6oye min damuwarka ba, dan Allah ka faWamin, Idan ba haka ba hankalina bazai kwanta ba, na fahimci tun da kazo ?asar nan ka canza gaba daya"
Ru?o hannun sir mubarak Yayi acikin nashi ya dam?e shi sosai.
Muryarshi ?asa ?asa Ya furta"bansan ya zanyi ba da ?aunar yaron nan na wurin Owais, shine silar duk wani hali da nake aciki, Har mafarkin shi nake Yi" ya faWa yana mai sanyaya muryarsa.

"Allah Ya jarabce ni da son shi, bani da ala?a da shi amma sai nake jin kamar ni na haife sa, na faWa maka ne saboda kana Waya daga cikin waWanda suke fahimtana"

Tun da ya fara magana Sir mubarak yake binshi da kallo mai nuni da tausayawarsa gare shi, yasan bakomai ke damun shi ba face rashin samun Wa namiji, shiyasa ya kwallafa rai akan yaron da owais ke ru?o.

"Ban ta6a ganin shi ba, amma saboda kai In sha Allah zanje har gidan owais Win In ga Yaron zuwa Gobe In Allah Yakaimu"

"Yana kama dani, tamkar Anyi photocopy din fuskana, hasken fatane kaWai Ya banbanta mu da shi, Fatarshi farace Sol, tamkar Nazli, Dalilin dayasa kaga nashiga halin nan, bana son inbar ?asar nan batare da yaji saukin lalurar shi ba, ina matu?ar son mu gana dashi, sai dai na rasa wannan damar da nake da ita, baba ya hanani kusantar shi, Gidan Owais dinma An hanani zuwa saboda shi, dole In hakura" cikin karyayyar murya ya faWa yana faman sauke numfashi.

Lamarin ya Waurewa Sir mubarak kai, yana neman rudar dashi, Aranshi Ya ayyana wannan wata irin kaunace haka? Abu kamar aikin asiri Allah na tuba.

Lallashin shi ya somayi yana kwantar mashi da hankalin shi, Har saida Yaga yafara sakewa tukunna suka cigaba da tattaunawa a tsakanin su.

__________________
'?

Lokacin Da Hajiya Turai, Ta shigo garden din tare da Hadimar data rakota, Tunkafin Ta ?arasa inda su Gimbiya mujeedat


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login