Showing 36001 words to 39000 words out of 298130 words

Chapter 13 - KURKUKUN KADDARA (TAKUN KARSHE) BY BOSS BATURE.doc

Allah ne"

"Amma kasan wani abu"? Girgiza mashi kai owais yai.

"Dawowar nan da kayi, Ka canza min Owais, Ka ?ara Girma kuma Ka ?ara Kyau"

"Shiyasa ka ?ura min ido Kana kallona ko"? fuskar Obie da murmushi Yace"ai ba laifi bane don na kalli Jikana, kai Win mallakina ne, Halak malak, Mahaifinka ma ya sallama min kai tun kana ?araminka, Ni ke kula da kai, gaskiya Owais Ka more ni sosai, komai nawa akanka Yake ?arewa, duk inda zan taka tare dakai nake zuwa.... " tun daya fara maganar, Chief ke sauraron shi, A lokacin Ya kammala Yi mashi tausar, Har ya mayar da man kan mirror.
Hayewa yai saman gadon, Ya kasance Suna fuskantar Junansu.

"Ban taba tunanin zan kai wannan lokacin araye ba, bani da burin daya wuce inga girmanka, graduation Win ka, harma da auran ka da ?a'?an ka, Sai gashi cikin Ikon Allah da raina da lafiyana, Ka girma ka kammala karatu harma kana aiki, sai dai auran ne har yanzu baka da niyar yin shi balle har in sanya rai da zan ga jikokin da zaka sama min" ru?o hannun shi chief yai acikin nashi ya ru?e shi gam, kafin ya soma yin magana a tsanake.

"Kada hakan Ya dame ka, in sha Allah nan bada jimawa ba, Mafarkin ka zai zama gaskiya, ko dan saboda farin cikin ka zan yi ?o?arin yin hakan"
lumshe do baba obie yai wani irin farin ciki ne ke ratsa zuciyar shi.

"Allah Ya nuna mana lokacin, zanyi farin ciki mara misaltuwa, kuma za'ayi shagalin bikin da ba'a ta6a yin makamancin shi ba,"

duba agogo Chief Yai"baba dare yayi sosai, Yakamata mu kwanta mu huta, Gobe da Safe In sha Allah zan ?ara yi maka tausar, don kaji daWin jikin ka" amsa mashi yayi da toh, kafin ya soma ?o?arin gyara kwanciyar shi, saukowa owais yai daga kan gadon Yaje ya kashe switch din dakin, Ya dawo ya kunna masu fitilun gefen gadon, daga bisani ya haye ya kwanta gefen baba obie, daga kwance suka cigaba da yin fira sama sama, har bacci yafara daukar owais, Jin shiru yadaina magana yasa baba obie juyowa yana duban shi, shafa gefen fuskarshi yayi tare da sumbatar shi kafin yayi mashi addu'a ya tofe shi, ya janyo masu lallausan duvet Ya lullu6e rabin chest din su.........d'


*(After Some Days)*


Bayan wasu ?an kwanaki, tun ranar da Baba obie ya yanke alakar Prime minister da Danish bai sake gigin zuwa inda yake ba, Yabar komai a hannun sheikh Imam da chief Owais, saboda a halin yanzu baida lokaci, ba azaune yake ba, ranar lahadi suka fara halartar National mosque tare da manya manyan malaman addini suka gudanar da taro, aranar litinin kuma Ya ziyar ci majalissai dokoki ta Nigeria, sunyi zaman tattaunawa da ?an malissa a ?ar?arshin jagorancin senate president lateef, tare da kakin majalissai wakilai, sun karrama Hateem a matsayin babban ba?onsu, sunji dadin tattaunawar da sukayi dashi kasancewar shi mutun daya iya mu'amala da mutane duk inda aka zauna dashi sai an ?aru da baiwar da Allah yayi mashi na iya tsara kalami, ga farin jinin dake gare shi, gidajen jaridu basu da abin yaWawa daya wuce ziyartar national assembly da prime minister yayi, komai daya tattauna da shawarwarin daya bama shuwagabannin Nigeria, saida ?an jarida suka yaWa shi a social media, duk aranar ya ziyarci gidajen marayu da gidan Yari, yayi masu kyaututtuka naban mamaki wanda ya gigita mutane zunzurun kuWi ya bayar da za'a tallafi rayuwarsu da shi, aranar talata yabar garin abuja shi da Iyalan shi da ?an uwan shi tun daga kan senate lateef his excellency deen and his excellency abdul razak tare da Sharafudden da hajiya saratu, Sir mubarak da kuma mu?arrabansa na ?asar canada, Chief of staff, national security advisor, 6angaren masu ba su tsaro Royal canadian mounted polices and Nigerian Soldiers.

kasancewar A privet jet din mai girma sharafuddeen suka yi tafiyar basu jin wahalar zuwa ko'ina, arana Waya sai suje har sama da gari uku, ?an mintuna jirgin yake sauke su suje inda zasu je, kafin marece su lula zuwa wani state din.

Wuri na farko da suka fara ziyarta bayan barin su abuja, masauratar yarbawan jihar lagos suka fara sauka an mutuntasu an kuma karramasu sanin matsayinsu a ?asar, kafin suka Wuce Garin Kano, anyi masu kyakkyawar tarba, kwana Waya su ka yi awashe garin ranar da zasu baro garin saida suka biya kasuwannin kano da gidajen tarihi da gidan gwamnati, daga bisani suka ziyarci jihar bauci, a katafaren wurin sha?atawar nan me suna Yankari anan suka yaWa zango tare da gwamnan jihar, ha?i?a Prime minister ya mori lokacin shi a Nigeria, yaji dadin yawon buWe idon da suka je tare da ?an uwanshi, sai dai abu Wayane bai goge ba a tunanin shi wato Danish, da shi yake kwana da shi yake tashi, ko abinci zaici saiya tuna da shi, aranshi ya ayyana inama ace hada shi suka taho yawon nan da Allah ne kaWai yasan irin farin cikin da zai yi.



A ranar Alhamis suka dawo Birnin Abuja amatu?ar gajiye, friday za'a shirya mashi family dinner, Ranar sataurday Hateem zai bar Nigeria agurguje zasu koma Canada.

____________________________
'?


Idan muka koma 6angaren su Unaisah cikin ?an kwanakin nan wata irin sha?uwace ta shiga tsakaninsu da ummin america, musamman Batool sun kulle da ita, Har karatun kur'ani ta fara ?o?arin koya masu ranar da suka ji ta yi masu ?ira'a tsantsan mamaki ne ya kama Unaisah, don ita bata ta6a tsammanin ummi ta iya karatun kur'ani ba sai gashi tana yi mata ?arin karatu cikin suratul ba?ra, har tambayarta tayi aunty ummi dama kin iya karatu, sai tayi dariya tace mata hadda gareta ai, tun tana ?ar shekara goma sha bakwai ta haddace alkur'ani mai girma, Unaisah ta jinjina mata aranta ta ayyana amma ya akai take aikata sa6on Allah bayan ita din mahaddaciyar al?ur'ani ce, wata kil kuma wata jarabtar ce ta ubangiji Allah wa'alamu.

Damuwarsu Waya ayanzu ?an uwansu Danish ya?i dawowa dai dai, Har yau babu wani cigaba kamar kullum yana akwance idanuwanshi arufe wanka da cin abinci su boss ne ke taimaka mashi, da kuma salsabeel dake zuwa dubashi kusan kullum sai yazo, tare da shi ake Wawainiyar kula da garkuwa, haka zalika sheikh imam kusan agidan yake wuni, wurin yi mashi addu'o'in da zasu bashi kariya, Hatta ?an uwan shi su Sajeed sai da Imam malik Ya koya masu addu'o'in da zasu dinga yi mashi hakan ba ?aramin daWi yayi masu ba, sau uku suke zuwa duba shi a Wakin shi don suyi mashi addu'a safe rana da dare, Ita unaisah har tsakar dare tana zuwa Wakin shi ba tare da sanin kowa ba, duk ta ?agara ya yadawo hayyacin shi, akwai abubuwa da dama da take son yi mashi albishir, na farko tana so ta faWa mashi dangane da prime minister Hateem dake kama da shi na biyu abun arzi?in daya fara fito mata a ?irji, ta riga ta yanke shawarar fada mashi idan ya dawo normal, ta hana kowa yagansu a 6oye take Waure su da mayafi ta matse su don karsu bayyana agani, abunda bata sani ba, batool tuni ta ganota duk in zata shiga toilet tsakar dare don tayi masu kallon ?urulla sai batool tayi mata la6e, ta dinga ti?ar dariya kamar cikinta zai ?ulle.

Tun ranar da ummi tayi tozali da sheikh imam bata ?ara bari sun haWu ba, da zarar yazo gidan take komawa Waki ta zauna ko bakin ?ofa bata fita har sai ta shaida tafiyar shi tukunna take saukowa down stairs.

A 6angaren su Benazir, since last week taso zuwa gidansu Aneelerh Allah bai nufa ba, saboda rashin samun layin Abie din Aneelerh, Alhaji ubaid yayi trying layin shi baya shiga, kuma shi kaWaine dama yake da numbar shi, Adole Benazir ta ha?ura da zuwa gidan su tun da bata da hanyar da zata samu address din su, bata ji dadi ba gashi har Mamie tafara yi mata zancen komawarsu Jos, don ma alhaji ubaid yace ba yanzu ba sai sun cike wata Waya ai da tuni sun jima da komawa, mamie bataso hakan ba, saboda ita bata son suna zama gidan Alhaji musa, badan bata jin daWin gidan nashi ba sai don saboda ranta dake raya mata cewar ba don Allah yasanya suka zo gidan shi ba, don kawai yaji daWin juyasu son ranshi shiyasa yake son su zauna masa agida, taci alwashin indai Alhaji ubaid bai basu damar komawa joss ba cikin watan nan to zata kama hanya ta tafi ne koda ita kadaine! Sau?inta Waya Hajiya sarah tana janta ajiki matar tana da mutunci duk in tadawo daga office sai ta ware masu lokaci sun shiga garden ita da mamie donsu tattauna kan abunda ya shafi rayuwarsu da ta ?a'?an su, ba ?aramin Webe mata kewa take yi ba.

Haka Itama zeenatu bata da matsalar komai ayanzu, Benazir ta zama tamkar ?awarta, har gyara mata gashi takeyi tayi mata kwaliya, dr shureim ne yake daukarsu a motarshi su fita yawon sha?atawa, kullum sai sun fita yawo ko gajiya basayi. To meya fi ransu? Nima da zan samu mai fitar dani yawon binshi zanyi.

A 6angaren Pravin kuwa, Takaicin duniya Ya ishe shi, tun da yaji cewar baba obie ya amince yaran su cigaba da zama a estate dinshi duk irin wahalar dayasha wurin ganin ya tunzurasu donsu ?i amincewa da shi amma abanza, ba?in ciki da hassada ne ke damun shi, Ranshi ya 6aci matu?a ya kuma ci alwashin sai ya raba ala?ar yaran da chief owais, burin shi kawai su bar estate din. Ko ita hajiya saratu a yanzu tadaina damuwa da zancen yaran tun da taji hukuncin da baba obie ya yanke sai ta sanyama zuciyarta salama, idan pravin yai yun?urin tunzurata don taje ta tada maganar a wurin baba obie, sai tace mashi itafa yanzu bata su take ba, tun da ba'a kanta suke zaune ba, Owais shi zai kula da komai.
Idan ta faWi hakan sai yaji tamkar ya rufe ta da bugu.
Kullum tunaninshi ta wace hanya zai 6ullowa lamarin???

Alhamdulillah Jikin dr. Jazz yayi sau?i, da taimakon ?an uwanshi da suke bashi kulawa, har gida yake shiga don ya gaishe da Baba Obie, sannan yaci gaba da zuwa gidan su khadeeja kamar yadda ya saba zuwa domin duba lafiyarta.

Idan muka koma wurinsu Aneelerh, shiru har yau zahra tana zaman jiran sakon Hajiya saratu harta fara tunanin kodai dama wasa take yi mata ne? Ko kuma tayi mistake ne wurin tura mata hotunansu twins don ta za6i Waya? Tarasa ina zata tsoma ranta taji daWi ta riga data ?wallafa rai akan su twins shiyasa duk ta damu kanta, kullum ne saita duba chat dinsu da hajiya saratu har tsakar dare duk don taga kota tura mata amsar maganarta amma shiru kake ji har yau, ganin yadda ta Waga hankalintane yasa Aneelerh kwantar mata da hankali tace taci gaba da addu'a idan rabonta ne zata samu, sannan tayi mata uziri watakil tamantane ko kuma ta shiga busy a aiki shiyasa bata samu damar bata amsa ba,
Aneelerh Ba ta jima da fada mata hakan ba, Sai ga mahboob yazo masu da labarin tafiyar da sukayi zuwa wasu states din nigeria, Jin hakan yasa taji sau?i acikin zuciyarta.

Hajiya adama tun bayan da suka kawo baby junaid, kusan kullum saita kira donsu gaisa dashi har video call suke yi, ta jima tana mamakin yadda junaid yake yi mata surutu idan ta kira shi awaya, amma lokacin da aka kai masu shi kamar wani salihin bawa baya surutu sai in yana son cin wani abu tukunna yake buWe baki yace abashi, nan take ta fahimci yafi son zama wurin mommynsa, yanzu tasama ranta dangana bazata ?ara raba shi da maman shi ba, idan tana son ganin shi ita za ta je gidan ko kuma ta gayyaci aneelerh tazo mata da shi, yanzu haka Aneelerh ta fidda masu lokacin da zasu je gidan ita dasu mami da ummi hada su uncle Wan Iya gaba dayansu zasu je kai masu ziyara, tun da ta sanarma hajiya adama farin ciki kamar ta zuba ruwa ?asa tasha, taji dadin zancen zuwansu................

Atakaice kenan abubuwan da ke faruwa atsakanin family din kowani 6angare.


*=؋?BABE UNAISAH ANGELd'*


fitowa tayi daga toilet, Jikinta asanye da bathrobe fara ?al ta Waure igiyoyin rigar saitin waist din ta, fatar jikin ta da alamun lemar ruwan wankan da tayo, A hankali take tafiya tana tunkarar Dressing Mirror, ta wutsiyar ido take kallon Batool dake akwance saman gadon su, tana fuskantar ceilling tamkar maiyin bacci, alhalin nan kuwa idonta biyu....

On mirror Chair Unaisah ta zauna, fuskarta babu annuri babu walwala, kamar bata da ?oshin lafiya ko wani abunne ke damunta wanda yayi silar canzawarta.

Body lotions din su ta Wauko ta buWe murfin, ta soma bin ko'ina na jikinta tana shafe shi da mai.

Bayan ta gama shafa man, ta feshe sako da lungu na jikinta da turare, ?amshin shi ya buWe room din, hatta Batool sai da ?amshin Ya ziyarci Hancinta.

Sumar kanta ta soma gyarawa, ta busar da ita tabi da smoothing serum ta cuccuWata, tunkafin ta kammala kunnuwanta suka Jiyo mata sautin knocking ?ofar room dinsu da ake Yi daga waje.

"Batool, nasan idonki biyu, je ki le?a ki ga wanene ke yi mana knocking, may be ko aunty ummi ce,"

Fuskar Batool Ayamutse ta buWe idanuwanta, ta sauko daga saman gadon tana mi?a haWi da yin hamma ta nufi ?ofar, ?ar rigar dake a jikinta bata wuce gwiwarta ba.

BuWe ?ofar Wakin tayi, tare da le?awa ganin big guy ne yasa tayi saurin zuwa ta dauko Mayafi ta lullu6e kanta kafin ta dawo bakin ?ofa ta kuma le?awa tana fadin"Barka da safiya Ina kwana"

Kamar kullum da face mask a fuskarshi ya amsa mata da lafiyalou, yakike fatan na same ki lafiya' bayan sun gama gaisawa yace"ina Jari "?

"Tana a ciki, Yanzu ta fito daga wanka, ko in kira maka ita"? ?aga mata gira yai alamar eh, juyawa tayi da sauri ta shiga dakin, A lokacin Unaisah ta koma gaban Closet dinsu, tana laluban Suturar da zata sanya, Jin motsin shigowar ta yasa ta juyo tana kallon Batool
"Wanene"?
"Big guy ne Yake son ganin ki"
"Ni kuma"? ta faWa da alamun mamaki"ni nama yi tsammanin boss man ne, Ko me zai faWa min bari dai naje naji dame yazo"

Ta faWa tare da Waukar Hijab ta zura ajikinta, Ta nufi ?ofar dakin cikin girmamawa ta gaishe da shi ya amsa mata da fara'arsa
"Batool ta fada min kana nemana, gani toh" yadda tayi maganar taso ta bashi dariya.
"Kina wani abune"? Girgiza mashi kai tayi"a'a, ba abunda nake yi"
"Yawwa My baby Girl, Kin tuna maganar da muka ta6a yi dake last week"? Shiru tayi tana faman ?yafta ido a ?o?arinta nata tunano maganar da sukayi
"Namanta, ka tuna min mana"
Numfasa yai kafin yace"ba kince kinaso kiyi ma chief namu godiya ba game da alkhairin da yake yi ma ki" murmushi tasaki tare da cewa na tuna.

"Good, Yanzu abun da nake so dake, Kinga ni ke Wawainiyar kai mashi abinci har ma da gyara mashi room din shi, saboda bai yarda da kowa ba Yana da wuyar sha'ani, Nima don ya aminta dani shiyasa ya yarda ina masa aiki a part dinsa, abun da Yakamata Yanzu ke nakeso Ki cigaba da zuwa part dinsa kina yi masa hidimar kai mashi abinci, breakfast lunch and dinner, sannan yana yawan shan coffee, a rana sau shida nake kai mashi, gyaran daki kuma sau biyu ne safe da dare before ya kwanta bacci, sai kuma gyaran falo dinsa da toilet dinsa da dressing room din shi hada gym room dinsa......" tunda yafara kora mata jawabi, ta zaro mashi idanu waje tana kallon shi, ganin kamar ta ruWene Yasa shi sassauta muryarshi yace"Ko ba ki Iya aikin mata bane"? Murmushin ya?e ta sakar mashi tare da cewa"Na Iya, amma naji kace Yana da wuyar sha'ani kuma bai yarda da mutane, Tayaya zai yarda Ina zuwa part dinsa yi mashi aiki"? Ta jefa mashi tambayar tana duban shi.

"Kada ki damu, zai yarda da ke, abun da yasa kika ga Na baki wannan aikin saboda ta hanyar kyautata mashi ne kaWai zaki Iya biyanshi da Wawainiyar da yake yi maku, tun da shi ba'ayi mashi godiya baiso,"

Jinjina kai tayi kamar tana fahimtarshi,
"Shikenan, Yaushe zan fara zuwa yi mashi aikin"?
Murmushi yasaki jin ta amince fatan shi Allah yasa Chief Ya yarda da ita.
"Yanzun nan zaki fara aikin, Gyara mashi Room dinsa, baya aciki daga sallar asuba ya nufi gidan kakansu Obie, kafin Ya dawo please ki tabbatar kin gyara mashi ko'ina na part dinsa, before ki gama ni kuma zan kawo maki breakfast din shi, duk idan nakai mashi abinci sai na tsaya nayi serving nashi kema haka za ki yi, nasan kina da natsuwa chief baison mutun mai ?azanta yana son mai tsafta, kullum ki tsaftace jikinki da suturar ki kafin ki shiga part dinsa.... " wani kallon take bin da shi a fakaice.

"Baka da matsala dani, In sha Allah zanyi komai yadda ya dace,"
Har cikin ranshi yaji daWin maganar data furta mashi,
"Mu je in nuna maki Wakin" da sauri tace"Ai ban gama shiryawa ba, ka bani mintuna yanzu zan dawo" amsa mata yayi da toh, da sauri ta koma Wakin a lokacin batool ta shige bathroom tana wanka.
Shaf shaf ta nufi glass wardrobe dinsu, ta shirya kanta cikin Turkish gown launin Yellow, rigar tayi mata kyau ta kuma bi shape din jikinta, tana da belt a tsakiyar ta, tayi rolling mayafi akanta, kafin ta Wauko Cashmere slippers mai gashi gashi launin yellow ta zura a ?afarta.

Bayan ta kammala kimtsawa, Ta fito daga Wakin, Shi kanshi Big guy daya kalle ta sai da gabanshi Ya faWi ganin kyan da tayi, satar kallonta ya dinga yi batare data ankara ba.

Tafiya suka soma Yi, tana


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login