Showing 210001 words to 213000 words out of 298130 words

Chapter 71 - KURKUKUN KADDARA (TAKUN KARSHE) BY BOSS BATURE.doc

wani baccin ne ya kuma daukarta...

_________________________________
'?

*Hajjaty*

Tun da sanyin safiya bugun kofa Ya farkar da ita, tana tsaka da jin dadin baccin ta, da wata irin kasala ta mi?e ta sauko daga kan gadon tayi mi?a haWi da yin hamma, ?ar rigar bacci ce a jikin ta, sai da ta fara daukar hula ta lullu6e kanta kafin ta nufi kofar tana tambayar wanene"?

Daga waje tajiyo muryar sofia cikin tashin hankali tace"Aunty ni ce sofia, ki buWe min kofa" da sauri hajjaty ta buWe kofar ta le?a kai tana kallon sofia wadda gaba Waya babu kwanciyar hankali atare da ita ..tunkafin taji me zata faWa mata gabanta ya fara faWuwa.

"Sofia! Meke faruwa ne? naganki kamar ba lafiya"? Yarfa hannu safiya tayi murya na rawa tace"marwa! Aunty mun shiga uku, kizo kiga abunda ke faru ! Marwa ta kuturce. .." aruWe hajjaty ta ce"bangane me kike nufi ba? Meya faru da ita? Wata irin kuturta . "? Bata jira hajjaty ta kare maganar ba, taja hannunta da sauri suka nufi dakin marwa dake anan corridor din da Wakunan house maids din gidan su ke..

Shigarsu ke da wuya hajjaty tayi arba da ?an aikin gidan gaba dayansu, sun hallara, fuskar kowan nansu sharkaf da hawaye cikin tashin hankali suke sallallami idanunsu akan marwa.

Suna ganin hajjaty suka buWe mata hanya don taga abun tashin hankalin da suke kallo,
Lokacin da ta sauke idonta kan marwa dake nannaWe kan katifarta rass taji gabanta yayi mata wani irin mahaukacin bugu na tashin hankali, ta waro idanu waje, agigice ta daura hannayenta biyu saman kanta, ta zabga salati tana ambaton inna lillahi wa'inna ilaihirraji'u!!

la66anta na kerma ta furta"Mar..marwa! Meya faru dake? Ya akai kika koma haka? ta faWa tana kallon yatsun marwa da suka dunkule irin na kutare ga wani ruwa mai yau?i dake gangarowa ta tsakaninsu,, la66anta sun shafe babu hudar baki kamar ba'a ta6a halittarta da shi ba, wani irin nishi take saki, idanunta sun kaWa jawur ga zufa data wanke jikin ta baiwar Allah ita kadai tasan azabar da take ji, sai faman zare na mujiya takeyi jikin ta nata kerma.

Fashewa hajjaty tayi da kuka, gaba daya sautin koke koken su Ya cika dakin
"Wayyo Allah! Na shkga uku! Dan Allah ku fadamun meya faru da ita? kaina ya kulle nagaza yarda da abunda idanuna suke nuna min! Jiya jiyan nan mukayi aikin dinner tare da ita lafiya lou muka rabu da ita...taya akai ta samu wannan lalurar ta kuturta? Ina bakinta yake"? Cikin shesshekar kuka tayi maganar
Abla tace"Aunty bamusan meya faru da ita ba, yau da safe mun tashi zamu fara aikin breakfast, mun ga bata fito daga daki ba, shine nace ma sofia taje tayi mata magana kada mu makara, bayan tafiyar sofia har mun fara aiki muka jiyo sautin ?ararta daga dakin marwa shine muka taho da gudu mu duka dan muga mike faruwa a nan muka tarar da marwa cikin wannan halin.. ." ta ?are maganar tana kuka
Sofia tace"wlh bansan meya faru da ita ba, Nima haka na sameta, ina shigowa dakin na isketa a nannaWe kan kafita, har ina zolayarta nace mata bana son iya shege kina ji inata ?wala maki kira kinyi shiru baki ce min komai, wlh aunty dana zo gaban katifar naga hawaye idonta gashi babu hudar baki, yatsun hannunta sun kuturce bansan sa'adda na fasa ihu ba, ni ban ta6a ganin tashin hankali irin wannan ba, Allah daga gani Aljanune suka shafe ta . ..." gaba daya duk sunbi sun ruWe, hankalin su Ya tashi, jikin hajjaty na 6ari tace"ba kallonta yakamata mu tsaya munayi ba, bari inje in sanar da mutanan gidan..." da sauri ta fuce daga dakin... .

Kafin wani lokaci gaba Waya mutanan gidan suka hallara a dakin marwa, da sauri maids din suka basu hanya don su shuga ciki, baba obie ne kan gaba jikin shi sai 6ari yakeyi, Pravin da twins suna abiye da shi, har sunyi shirin zuwa office wannan abun tashin hankalin Ya ris?e su, hada Hajiya saratu ta shigo ta zumbula buba ajikinta, sai faman raba idanu takeyi tun kafin ma taga meya faru da marwan!!

lokacin da sukayi arba da marwa gaba Waya hankulansu suka tashi, sunyi matu?ar razana da ganin yadda halittar marwa ta canza, kowa sai tambayar ba'asi yakeyi, Tafa hannu hajiya saratu tayi"La'haula walakuwata illa billahil azim! Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un! Allahumma ajirni filmusibati.. Gaba Waya tabi ta rikice, "Ya akai Haka ta faru? Wata irin lalura ce wannan"? Ta faWa tana zare na majuya
Masu aikin suka hada bakin wurin fadin wlh bamu sani ba, haka muka same ta,
Idan hankalin su twins yayi dubu toh ya tashi, wani irin ?yan?yami da ?yamar marwa ne Ya kama su, babu wanda Ya lura suka sa6e daga dakin suka yi tafiyar su don bazasu juri ganin tashin hankalin nan ba.
Tsabar tashin hankali da kiWima Ya hana baba Obie furta kalma, dama da ?ar cazbahar shi a hannu sai faman jan ta yakeyi yana ambaton sunan Allah
Pravin dake a ru?e da kofa fuskar shi a hautsine Yana ta faman zazzare idanu kamar na kwarton muzuru har wani gumi Ya haWa muryarsa na rawa yace"yarinyar nan ba ta rasa iskokai akanta, daga gani aikin aljanune, taya za'ace farat Waya mutun ya tashi ba baki? yatsu kuma sun kuturce"?

Jin wannan maganar Ta pravin Yasa hankalin hajiya saratu yayi mugun tashi, nan fa ido ya raina fata, dama a tsorace take da lamarin, baban tashin hankalinta kada itama abun ya shafeta, tunda kwana nan suna mutunci da marwa saboda aikin le?en asirin da take yi mata, batare da kowa Ya lura ba, ta lalla6a ta fuce daga dakin marwa, jiki na kerma ta koma bedroom dinta, ta yi shirin zuwa office don ta bar gidan, saboda rashin tausayi maimakon ta tsaya su nema mata mafita tunda dai ita takeyiwa aiki
Baiwar Allah marwa ba halin Yin magana, kukan zuci take mai Wacin gaske, ga abu tana so ta fada amma takasa sai kallon hajjaty da pravin takeyi hankalin ta yafi kakarta akansu

Dakyar baba obie Ya haWiye tashin hankalin shi, Ya dubi maids din dake kuka cikin sanyin murya yace"kuyi hakuri ku kwantar da hankalin ku, ba kuka yakamata kuyi mata ba, addu'arku take bu?ata..." ya fada tare da kallon Hajjaty"ku taimaka ku dauko ta, muje asibiti aduba lafiyarta. " da sauri hajjaty da Abla suka haWa karfi wurin cuccu6ar marwa suka fito daga dakin sauran masu aikin suka bi bayansu, tunkafin su fito baba obie yayi waya da Waya daga cikin jami'an gidan, Aka fiddo da mota mai kama da bus, aciki suka shigar da ita, kowan nan su Ya samu wurin zama, motarsu baba obie da pravin tana abiye da tasu a jere motocin suka fuce kaitsaye suka nufi asibiti=ؔ? tunkafin sukai asibitin marwa take ta kallon hajjaty kamar zata hadiyeta ita kanta hajjatyn dake aruke da ita tayi matu?ar tsorata da kallon da marwa keyi mata ga wani nishi da gurnani da takeyi=?"?

(Tashin hankalin da ba'a saka mashi ranaS'W')

__________________________________
'?

A zaune take kan dinning chair, ta sanya abaya dogo ajikinta, table din gabanta cike Yake da kayan breakfast ita kadai ta rage a dining, tana cikin shan tea a cup, ?amshin turaren dr shureim Ya daki hancin ta, da sauri ta Wago tare da kallon inda take jiyo sautin tafiyarshi, a tsanake Yake tafiya cikin kamala, Ya sanya shadda a jikin shi ta zauna mashi yayi wani fresh da shi hannun shi ru?e da car key,
Tunda ta kafe shi da ido sam ta kasa daina kallon shi, saboda yayi mata kyau
Karasowa yayi gaban dining din, fuskarshi dauke da murmushi Ya furta"sanyin idaniya, ina fata kin tashi lafiya"? Farfari tayi mashi da ido hadi da sakar mashi murmushi kafin tace"hubbyna na tashi lafiya, ina fata kaima haka"
Yace Alhamdulillah,
"Yaya shurem, Ka zauna mu yi breakfast, ko ka riga da kaci ne? Yau ni kaWai na rage a dining, ban iske kowa ba .."
"Bana jin yunwa, Inason zan fita ne" yanayin fuskarta ne Ya canza, kamar zata fashe mashi da kuka tace"dan Allah ya shureim kada ka tafi kabarni agida ni kadai, kaga mommy ta tafi office, daddy da uncle sun je party meeting, kullum sai ni kadai kuke bari agida bana aikin kome" ta faWa da shagwaba...
Shiru yayi yana tunanin meya kamata yayi? Shi ma baison suna tafiya su barta agida ita kadai baisan ya zaiyi da ita bane tunda bata son zuwa asibiti wurin Benazir, gashi har benazir ta fara tambayar shi ina zeenatu, itama hajiya layla abun ya fara damunta duk in yaje sai tace wai meya hana zeenatu zuwa.
Wata dabarace ta fado mashi aranshi, da sauri ya dubeta ta kura mashi blue eyes dinta masu walwali
"Zaki rakani mu tafi atare inda zanje"?
"Ina zamuje"?
"Wani wuri ne..." shiru tayi jim kafin tace"ni dai saika fadamin ina ne"
"Yawon buWe Ido" waro ido tayi kafin tace"dagaske"? Jinjina mata kai yayi alamar eh, da sauri ta mike tana fadin"yaya shureim bari naje na canza kaya"
"Okey, ki same ni a mota, but karfa ki dade" amsa mashi tayi da toh, jikinta na rawa tsabar zumudi ta nufi part dinta
Murmushin gefen fuska shureim ya saki aranshi ya furta"yau zanga meke akanki my zeenati"! Ya faWa tare da juyawa ya fuce daga falon

After some mins, Yana zaune a driver's seat, Ya dan jingina kanshi jikin headseat, har ya lumshe idanun shi Yaji motsin buWe car door, A hankali Ya kalli zeenatu dake kokarin shigowa ciki, wani irin sanyayyan kamshin turarentane Ya ratsa hancin sa, kamar wadda zataje gasar miss world, wata hadaddiyar emirati abaya ce ta sanya launin yellow, abunka ga jinsin turai ta fito fara fess rigar tayi mata kyau, ga wani veil da tayo rolling, hannunta ru?e da wayarta, kafarta kuwa wasu highhills ne masu tsini, harta zauna dr shurem bai daina kallon ta ba...
Farfari tayi mashi da ido voice dinta da shagwa6a tace"yaya shureim wannan kallon fa" kayataccen murmushi ya sakar mata, tare da kai hannu ya shafa sajen shi, key yai wa motar, ya Wanyi reverse kafin Ya fara driving slowly Ya nufi katafaren gate din gidan, tunkafin Ya karaso waWannan Samudawan security office din suka yunkuro kamar zasu rufe motarshi da bugu ba don komai ba sai don saboda Ya dauko zeenatu...
Ba arziki yayi parking motar, ya sauke glass din Yana kallon su
da kakkausar murya daya daga cikin su Yace"da iznin wa zaka fita da ita.. " saboda karfin hali na dr shureim Ya wani hade fuska Yace"daddyn ta ne Ya bani izni" arude zeenatu ta kalle shi wato taji ya shureim yayi karya agabanta
"Amma mu bai fada mana ba"!
"Ku kira shi awaya sai kuji" ya fada yana ?ara tamke fuskar shi
Kiran alhaji musa sukayi wayar tayi ta yin ringing ba'ayi picking ba, dr shureim Allah Allah Yake kada Alhaji musa ya Waga, kai hada addu'a yayi a zuciyar shi, cikin sa'a bai Waga ba..
Muryar zeenatu na kerma tace"ku kira mommy ku tambayeta, ay itama tasan da zancen fitarmu, daddyne ma yace ya tafi dani..." ba suyi ?asa a gwiwa ba suka kira hajiya saratu bugu uku kafin suka samu ta Waga...
"Ranki ya dade, da izninki dr shueim zai fita da zeenatu"? Kallon juna zeenatu da dr shureim sukayi duk suka sha jinin jikin su, fargabansu kada hajiya sarah ta kwafsa masu

"To amma shi yalla6ai yasan da fitar su?
Hajiya sarah tace"eh ya sani, kawai ku barsu su tafi"..kusan atare dr shueim da zeenatu suka sauke ajiyar zuciya.. munafukan gate officers din ba don sunso ba suka basu hanya, dr shurem Ya ?ara wa motar gudu Ya fuce daga gidan....

Lumshe idanu zeenatu tayi tana dariya tace"ya shureim kasan Allah da ace daddy ya Waga kiran nan da sukayi mashi wallahi bazai bari ka fita dani ba, ni narasa gane dalilin dayasa yake kullena kamar wata matar aure..."
"Mommynki ta rufa mana asiri wlh, naji dadi my zeenatu, kinga yanzu zamu sakata mu wala..." yai maganar hankalinsa na akan driving din da yakeyi, A hankali ta daura hannunta saman dayan hannunshi gefe tare da lumshe idanunta, har satar kallon ta sai da yayi kamar wata jinjira komai nata burge shi yakeyi...

________________________________
'?

Gaba Wayansu sun shirya tsaf, zasu ziyarci gidan uncle abdallah, tun daga kan mami, ummi, zahra, abi, da uncle Wan iya, kowannansu ya Wauki wanka na mutunci namu na hausawa, mutun biyu ke babu a cikin su, mahboob wanda tun safe ya tafi kai baby junaid school, har yanzu bai dawo ba..
A tare suka fito daga falon gidan, suka nufi harabar ajiye motocin su,
Mami tace"yau dai Allah Ya nufa zamu cika mata alkawari, baiwar Allah mun saka mata rai, kullum ayta za'aje za'aja amma shiru.." ummi tace"nasan zatayi farin ciki idan taganmu kwanmu da kwarkwatarmu don ma babu junaid, ay da sai tafi jin dadi munzo mata da Wan jikallan ta..." .murmushi kowannansu Yasaki,
A bakin motocin suka dakata da yin tafiya, suna jiran Aneelerh da zahra su fito,
Abie Yace"wai zaman me sukeyi agidan? Kwalliyar ce har yanzu ba'a gama ba?
Uncle Wan iya yace"da rabon mu tafi mu barsu agidan sun taho daga baya, dama tafiya indai da mata za'ayi ta to fa sai an 6ata lokaci, su komai nasu da nawa babu karsashi..." ya faWa yana haWe fuska....

Acan cikin gidan kuwa, fitowa zahra tayi ta dauki wankan atampa, an yafa veil a kafada, hannu ruke da jaka, ta ca6a uban ado, dakin aneelerh ta nufa, kafin takaiga kofar dakin sai ga Aneelerh fito cikin sauri, wata hadaddiyar lafaya ta laga a jikin ta,launin orange mai adon stones, ta fito Wass abunta, itama ta ruko handbag din ta, zahra na ganinta taci burki tana fadin"Aunty aneeleeh! kinga yadda kikai kyau? Meyasa baki fadamin lafaya zaki sanya ba nima ay saina sanya nawa" ta fada tana hade fuska, murmushi Anila tayi"kai zahra ay kin ma fini kyau, kinga su abie suna jiranmu, mu tafi kada mu 6ata masu lokaci" ta fada tare da ruko hannun zahra suka fara tafiya, har sun kusa fita daga falon muryar Ana ta katse masu hanzarin su

"Aunty Anila, Allah ya kiyaye hanya agaishe min da hajiya adama..." dakatawa sukayi da yin tafiyar, a wani irin yanayi Anila ta dubi fuskar Ana wadda ke acan tsaye kofar kitchen jikinta sanye da riga da mini skirt, ta Waure kanta da hula sai faman sakar mata murmushi takeyi .
Batasan ya akai ta tsinci kanta da jin faduwar gababa,
"Zahra kunyi kyau sosai, kun burgeni, sai naji dama hada ni zaku tafi" murmushi zahra ta sakar mata"mungode kada ki damu next time idan zamu ?ara zuwa hada ke zamuje, yanzu dai ki koma kitchen, pls kafin mu dawo ki gyara mana bedrooms dinmu sunyi datti..." amsawa tayi da toh, kafin ta sake kallon Anila wadda keta kallon ta ko kyaftawa bata yi murmushi Ana ta sake yi mata
"Aunty anila, adawo lafiya.."
Dakyar ta jinjina mata kai, cikin sanyin murya ta furta"Ana ba lallai mu dawo da wuri ba! Ki kula da gidan, sai anjima" awani slow ta kau da idonta daga na Ana, taja hannun Zahra suka fuce daga gidan...

Ana tana a kitchen tana goge gogen floor da wiper ta jiyo tashin motocin su,

*AGIDAN UNCLE ABDALLA"

Hajiya Adama Yau ba zama, tunda Anila ta sanar da ita zancen zuwan su, ta fara yan gyare gyaren gida, ganin tana ta wahala ita kadai ga girkin da zata yi masu ko farawa batayi ba, hakan yasa Uncle abdalla Ya dauko mata hayar house help wata bayerabiya kakkarfa, atare da ita suka fara girkin cikin kankanin lokaci suka kammala shi, hajiya adama har mamakin matar takeyi kamar inji bata gajiya da aiki, tana da kwazo da ?warewa ta bangaren aikace aikacen gida, kafin wani lokaci sun kammala tsaftace gidan..

da sauri hajiya adama ta shiga toilet, tayo wanka, ta fara shirya kanta,wani tsadadden leshi ta sanya a jikinta, ta kashe daurin dankwali, ta zauna kan mirror chair tana ?arasa yin make up Win ta...
Sallamar uncle abdalla ce ta katse ta,
"Har yanzu ba su iso ba"? ta cikin mirror ta kalle shi suit ne a jikin shi..
"Nima naji shiru, amma ina ji araina sun kusa karasowa,
"Kodai basu gane gidan bane"?
"Bana tunanin hakan, ay na tura mata address din gidan tun jiya, bari na kira Anila naji.." ta fada tare da mi?ewa ta nufi wayarta dake ajiye kan mattress, kafin ta Wauko kiran waya ya shigo da sauri ta duba sunan mai kiran nata, murmushi tayi tare da kallon uncle abdalla"Anila ce ke kira" picking call din tayi ta kara wayar a kunne
"Anila kun taho ne"?
On the other hand anila tace"Eh, dama na kirane in fada maki mun kusa shugowa unguwan naku" wani irin farin cikine ya lullu6eta"Allah ya kawo ku lafiya" bayan ta katse kiran ta kalli uncle abdallah"tace min sun kusa isowa, yakamata muje mu taro su"
Murmushi uncle abdalla yayi"naga kina ta zumudin zuwan su, idan ma don saboda junaid ne kwara ki fidda rai, yau ranar school ne, ba lallai su zo da shi ba" daure mashi fuska tayi"ko baka fada ba, na sani, farin cikin dakaga inayi badan komai ba sai don saboda za'a kawo min ziyara gidana, kasan ba wani ke gareni a garin nan ba..." tay maganar tare da daukar mayafi ta yafa akanta,
Tayi gaba yabi bayanta. daidai lokacin da suka fito daga entry hall, suka hango mai gadin gidan Ya buWe gate, a jere motocin suka kunno kai cikin gidan,
Bayan sunyi parking, hajiya adama ta nufi motocin da sauri kafin ta karaso anila ta rigata fitowa da sauri ta nufe ta suka rungume juna fuskar kowannansu dauke da annurin farin ciki.

Abie da Uncle dan iya suka nufi uncle abdalla dake tunkaro su, suka fara yin gaisuwarsu ta manya Sassannun ku, da zuwa, ku ?araso ciki , Mamie da hajiya adama suka rungume juna fuskar kowan nan su Wauke da murmushi, bayan sun raba jikinsu, Ummi ta mi?a mata hannu suka gaisa a mutunce,kafin ta janyo zahra tayi hugginta dinta, daga bisani suka haWu gaba daya suka shiga falon gidan, yau ne karo na farko da su anila suka fara zuwa, zahra sai yan kalle kalle takeyi gidan ya burgeta ginine babba, ita kanta anila tayi mamakin haduwar gidan surukan nata, an wadata gidan da duk wani abu na biyan bukata.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login